MAI KWAĆŠAYI

36

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

```SASAAL```



 ```Page 36```


________Kiran Asubahin farko ta farka,amma batada cikakken lafiyar miƙewa saboda zazzaɓi mai zafin daya rufeta,a haka sanyin asuba yayi ta shigarta har gari yayi haske sosai,zuwa lokacin ko idanuwanta bata iya buɗewa dakyau,dole ta maidasu ta lumshe tana jiran ikon Ubangiji a kanta.


Tun daga nesa take jin takun mutum, Addu'a ta farayi a cikin zuciyarta Allah yasa ba Mubeena bace ko Faisal,tun da suna sane da a waje ta kwana.


Lokacin da yayi tozali da Halima kasa riƙe ƙwallar shi yayi,da hanzari ya buɗe ƙofar ya ɗauketa kamar ƴar baby zuwa parlourn.


Kuka ta fashe dashi bayan ya ajjiyeta tana ƙoƙarin miƙewa tabar parlourn,kuma taƙi kallo fuskarshi duk Maganar dayake mata da ƙaramin murya da saika rantse ba Faisal Suraj Bari bane mai tsanani ji da kanshi da tutiya da arziƙinsu.


"Wajen Inna nakeso" ta faɗa tana ƙoƙarin ƙwace riƙon dayayi mata.


Ko motsi baiyi ba sai idanuwanshi daya zuba mata, ko Mubeena dayayiwa so mai ƙarfi a baya kuma har lokacin ba wai ya daina sonta bane,amma abinda yake ji akan Halima na neman shafe wannan son zuwa tsananin tunaninta da bai san ta ina zaifara ba.


Bai kulata ba,ya miƙe da kanshi yaje ya haɗa mata ruwa wanka sannan yaja hannunta har Bathroom ɗin, ya turata bayan ya cire Hijjab ɗinta kwantaccen sumar kanta nakarasa nakasa nutsuwar shi.


Abokinshi Dr Aryaan da Maysarah kaɗai yake dubawa a familyn su ya kira saboda yana buƙatar sirri akan lamarin Halima,kuma Dr Aryaan mutum ne mai tsananin sirri domin bai taɓa tattauna matsalar dayasa kullum Maysarah idan yazo Abuja sai ya duba shi ba, da shi duk da Abotar dake tsakanin su.



Bayan sun gama waya atake yayimata order abinci.


Sosai wankan ya taimaka mata har ta ɗanji ƙarfi ajikinta,zuciyarta cike da zullumin abinda take hangowa kullum idan ta kalli idanuwan Uncle Faisal.


Tausayi ya bata yanda ya nuna damuwarshi akanta, kuma yarantse mata mantawa yayi da keys É—in,ko ba komai Faisal ya haifi wanda ya girme mata sosai,amma yanayin kuÉ—i da kwanciyar hankalin dayake ciki da tsananin gayu sai yafi yanayi da Ć´an 30yrs .


Kafin zuwa Dr Aryaan abinci dayayi order ne yafara isowa.


Potato chips kawai ta iya ci da shima batafi wasu mintuna ba ta amoyo shi. Bai barta ta huta ba yaƙara haɗo mata tea mai kauri tasha. Damuwar da Faisal ya shiga ne ya wanke duk wani ɓacin ran Halima ta kuma ƙara tabbatar da dagasken mantawa yayi.


A sirrince Dr Aryaan yazo gidan kamar yanda Faisal ya buƙata.


Bayan ya gama duba Halima ya bata magani ya fara tattara kayanshi yana ƙoƙarin tafiya.

Faisal da damuwa yayiwa yawa kuma yarasa abokin faÉ—awa jan Aryaan yayi zuwa sashen shi.


Babu abinda ya ɓoyemai sai sauyin dayakeji a ranshi dangane da Halima amma duk da haka Aryaan ya gano shi kuma bai ɓoyemai ba.


Shawarar dai ɗayace,karka kuskura yabari son Halima yayi wannan tasirin saboda haɗi ne da bazai taɓa haɗuwaba har abada da yaya Mahaifinshi ma ya amince da auren Mubeena balle Halima.


Shawarar nisantar ta Aryaan ya ba shi. A gidan yayi Breakfast sannan ya wuce,har ranshi kuma baiyi mamakin mutum kamar Faisal da son Halima ba,ita dama mace ko awani zuri'a ta fito abar so ce ga wanda Allah ya Ć™addarawa,balle yarinya mai kyau irin wannan. Dariya Aryaan ya bawa kanshi.



Bayan ya gama ya kimtsa cikin kayan dake bayyana kuÉ—in su ajikinshi ya fice yabar gidan. Itama Mubeena tana gamawa ta fice ita da Ć´aĆ´anta zuwa gidan su Faisal.


Siyayyan kayan ciye-ciye ya jibgo mata kamar bai san ciwon kuÉ—in ba cereals ne kala-kala da manyan biscuits masu tsada da kayan fruits fresh masu kyau a ido.


Barci ya sameta tanayi don haka batare da jin komai na girman kai ba ya jera mata komai a mazauninshi sannan yabar sashen.


A daren ya shiryawa Halima komai harda drivern da zai dinga kaita school shima duk a sirrince.


Victoria mai dafawa masu hidimar gidan abinci yajawa kunnen kullum ta dinga kaiwa Halima abinci,kuma duk ranar dabata kai ba abakin aikinta.


Jirgin safe zai bi,domin bayaso ya wuce kwana uku saboda bikin Sumayya da bai wuce kwana goma ba.


A daren ya ɓoye key ɗaya ya riƙe ɗaya domin bawa Halima ƙoƙarin miƙewa yafarayi domin zuwa wajen Halima suyi sallama, dasauri Mubeena ta bar wajen maɓoyarta, murmushi Faisal yayi ya koma ya canzawa mukullin wajen zama,bai san yaushe Mubee tazama haka ba,amma zaiyi magani ta.



A Parlourn ya sameta tana karatu tana kuka.

Yana tunkararta jikinshi na ƙara mutuwa,a hankali ya zauna a gefenta amma baiyi yunƙurin kai hannunshi jikinta ba.


"Uncle waye Maysarah? Ina zanganshi don Allah? " Ta faÉ—a tana kamo hannayenshi.


Tsoro da fargaba ne suka dirarwa Faisal a lokaci ɗaya, a ina Halima tasan sunan Maysarah?sai dai iya sunanshi awani wajen amma ba sanin waye Maysarah ba,domin da tasan waye asalin Maysarah da ko sunanshi bazaso ta ƙara ji ba.



"Diya Maysarah ƙani nane amma ganinshi ko saninshi ba abu bane maiyiwuwa ba, maiyasa kike son ganinshi?"


"Mamana tace shi ya biya mata kuɗin karatu,ya siya mata ƙafan roba,da ta nuna bata so ya ƙara bada kuɗi aka siyomata sanda mai kyau, tace shine yafara cika mata burinta na zuwa Makarantar boko,amma ta rasu bata ganshi ba, Uncle Dan Allah kace mishi ina sonshi kuma ina son ganinshi. Ta faɗa da kuka iya ƙarfinta.


Daƙyar ya lallasheta kafin suyi sallamar da dukkan su ran su ba daɗi. Domin kalmar tanason Maysarah ba ƙaramin sukarshi yayi ba


Mubeena dake manne da ƙofar tanajin komai da iya gudunta takoma sashenta kuma tayi sa'ar Faisal bai ganta ba.


Sai yanzu ya gane dalilin janyewar komai na Maysarah daga gareshi,to wanene Maysarah yake turawa wajen Marigayiya Halime?.....✍🏻


Barkan mu da dare