Chapter 15
๐๐_*RAMIN K'ARYA*_ ๐๐
NA
IKILIMA ADAM
*( Kyauta daga Allah)*
Marubuciyar da ta nishandantar daku a littafanta kamar haka:
Kai ka jawa kanka
Kanwata
Rai daya ( Jan zaki)
Rudani
Makauniyar shari'a
And now
Ramin karya yan karin magana suka ce kurarre ne , mu je zuwa.
Da sunan Allah mai Rahma mai jin kai .
SHAFI NA SHA BIYAR
Shiru docto yayi sakamakon ganin yanda ta rude lokaci daya.
Zahradeen kallonta yake , yana tuna inda ya san fuskarta , samun kansa yayi da fadin " kece muka taba gani a kasuwa ko"?. yayi tambaya yana kallonta.
Kasa bashi amsa tayi , tana mai cike da mamakin kalaman docto.
" Yawwa amarya , ki yi hakuri , na shiga hurumin da ba nawa ba , amma a aikin mu shine ka gayawa pection dinka gaskiya." Isa gaban prince yayi yana taba goshinsa , kana ya dan gwada shi , ganin yana zufa ne , ya sanya shi dawo da kallonsa akanta .
" Ga magungunarsa nan , a tabbatar an kiyaye su, sannan a tabbatar an kaucewa fadawa halaka, yanda za'a sha maganin yana rubuce akan magungunan " ya fada yana mai dawo da kallonsa kan Zahradeen.
" Zan tafi , Allah ya bashi lafiya, anjima zan kirasa na gaya masa , wannan matsalar ce dai , kai ma kayi masa bayani ". Cewar docto yana tattara kayansa.
" Muna godiya doctor in sha Allah, zan masa bayani " cewar Zahradeen yana kallon Jidda dake kokarin fita daga dakin . Bawa docto hanya tayi ya fita , ita ma tasa kai zata fice.
" Ina zaki je "?. Cewar Zahradeen.
" Wajen Ummi" ta bashi amsa a tsorace.
" Tafiya zanyi , ki zauna nan ki kula da lafiyarsa " ya fada yana kokarin fita.
Kallon Prince Adamsy take , tana mai kallon ledan magani dake kan center table , tare da dawo da kallonta aka Deen.
" Sai na dawo" ya fada tare da barin dakin.
Cen cikin Masarautar labari ya karade ko ina prince Adamsy beda Lafiya.
Nura zaune kusa da Gimbiya Humaira yana mai sauraron sakon da prince Adamsy ya bata ta gayamai.
" Amma Adamu ya mugun rainaki Umma" cewar Nura yana fesar da numfashi.
" Rabu dashi , wallahi sai mun yi sanadiyar ya bar Masarautar nan , kuma bari na har abada , yayan nan da yake gani kamar kwai sai yaga mutuwarsu da idanunsa , yanda yaga mutuwar Maryam abun soyuwarsa.".
" Ai in sha Allah , buri ze cika , don Kawu Ashiru ya ce , duk yanda zanyi na tabbatar an kashe adamu da ransa , kuma hakan ne , ze faru a kusa ko a nesa "ya furta yana mai tabbatarwa. Sai kuma ya kara da fadin " Wallahi tunda har ya iya fadin hakan, sai na razanar da amaryarsa , na rantse da sarkin dake busan numfashi yarinyar nan , sai an nemeta an rasa , ai ni dashi wallahi dan halak sai yanka , ai sakon nasa magana ce a dunkule be ya tona min asiri ba , sai de nashi ya tonu" ya mai fesar da numfashi.
" Wallahi ka cika jinina , kuma duk abunda ka fada ina bayanka , zan sanar da Gimbiya Zainab yanda ake ciki , don dazun na bata labarin abunda ke faruwa , ta jinjina rashin kunyarsa , kuma ta ce har sashin nata ya shiga " .ta fada tana cizar yatsa.
" Ance be da lafiya, bara na je dubo shi " Nura ya fada yana mai tashi.
" Ok mu sai bayan Isha'i zamu leka ni da Zainab " t fada tana mai kallonsa yana barin dakin.
" Sai anjima " ya fada yayinda ya kai bakin kofa.
*******************
Lailat cikin hanzari take tafiya har tana tuntube , kai tsaye shashin Prince Adamsy ta nufa domin dubo lafiyarsa.
Kasantuwa ana kiran magrib hakan ya sanya saisaita nutsuwarta ta san daidai lokacin nan ,kila yana nafila ko yana shirin fita massalaci. Tana shiga kayataccen falon nasa , taga Jidda tana mai dauke flasks manya manya alamun abincin ne ya ci. Cikin razani take kallon bayanta.
" Ke!!!!" ta furta cikin tsawa.
Kadan ya rage , Jidda bata yi tuntube ba , don daga sama ta ji tsawar.
" Me kike yi a dakin Mijina " cewar Lailat a zafafe.
Rau rau da idanu Jidda ke kallonta , tsunkuyar da kai tayi kamar me nazari , kana ta dago kai sama.
" Mijin mu dai" ta bata amsa babu tsoro.
Soma taba hannu Lailat ta soma , tana yatsine fuska, " Ah Adamu kamata yayi ya ce bana yar bariki ya auro, idanunki tsaye yake kamar haihuwar rana " t fada , murya na tashi.
" Ko haihuwar talge ce , wannan kuma matsalar ki ce" ta fada kamar ba ita , tayi magana ba.
Lailat tuno da marin da ta mata ya sanya bata fincikota ba. Jidda na kokarin yin hanyar kitchen dinsa , yayi daidai da fitowarsa , tuno da ka'idar aurensu dashi , ya sanya ta juyowa tana murmushi mai kayatarwa .
" Masoyi har ka fito" ta fada tana mai ajiye flask din hannunta a kasa. Duk da baya jin dadi , murmushin ya kakalo .
" Eh my chocolaty" na fito kin ga har na ji sauki, na gode da kulawarki my angel, zan je massalaci coconut " ya fada yana mai kallon Lailat da hawaye ke bin kuncinta , a zafafe ta juya domin barin dakin, dan dakyar kafafunta ke daukarta.
" Lailat yanzu kika shigo " ya fada yana mai kokarin fita daga dakin.
Banza ta mishi ta fita a fusace , shi kuwa yana ganin ta fita , ya dawo da kallonsa akan Jidda fuskarsa babu yabo babu fallasa .
" Yau nan falon zaki kwana biyu " ya fada yayinda yayin yake fita daga falon.
Jidda duk inda tashin hankali yake ya gama bayyana a fuskarta.
" Me yake nufi , yabi umarnin sarki kenan" tana maganar zuci .
" A'a ka san auren nan bana soyayya bane , ba yanda hakan zata faru , zan dau mataki gudun kaddara , don ni Jidda sam bana son wani da namiji ya san sirrina , " ta fada tana sakin kukan da ya zo mata . Cikin hanzari ta fice daga dakin .
Direct dakin Ummi ta nufa a ujajan.
Tana shiga dakin ta iske Ummi zaune , Abdullahi na gefenta kamar dan hira suke tabawa kai kace sun taba sanin juna.
Shigowarsa Jidda ne ya sanya , prince Abdullahi ,zuba mata idanu har ta karaso.
" Matar yayana , ke ce " ya fada yana mai kallon Jidda .
" Ina wuni" ta fada tana mai kokarin zama . Shima ganinta kamar cikin damuwa ya sanya shi , shiga daga cikin dakinsa ya basu wuri. Be shige daki ba , sai dai ya labe daga gefe domin jin wani fira zasu tattauna.
Jidda cikin damuwa take baiwa Ummi labarin abunda mai martaba ya fada musu jiya ita da Prince , Ummi sosai ta shiga shock jin hakan.
Kana ta kara da bata labarin maganganun docto dazun .
Ummi tashi tsaye tayi cikin damuwa , kana ta dago da Jidda suna face din juna , share mata hawaye tayi.
" Jidda kin san mu marayu ne , amma Kuma duk maraicina kin fini zama marainiya , na taso naga mahaifana , ke kuma Umma ka dai kika gani baki san kalar mahaifinki ba. Mun rasa iyayen mu da kannenmu , ki sani yaya Iro kadai ya rage mana. Ina son mu samu time mu je mu kara dubo sa , don ya taba cemin akwai ajiya da Umma ta taba bashi wanda ya dangance , bamu san menene ba , amma akwai abin al'ajab " ta fada tana share kwallan Jidda.
" Kuma Adamsy ya ce , auren yarjejeniya ne , a lokacin da muke neman aiki, bayan faruwar abun nan kamar ya janye da wannan kudirin tunda ya hada aurena da kaninsa , nima babu soyayya tsakanina dashi , ganin da kika muna shine fira farko da ya shiga tsakanina dashi . Maganar kusanta kada ki yarda ya kusanceki , nima ba bari zanyi ba , kada su maida mu kananan zawarawa da kuruciyar kar mu gama sakankancewa dasu, su samu muradin su , su rabu damu " cewar Ummi cikin damuwa.
" Wallahi Ummi ban san yanda zan kwana daki daya da shi ba ". cewar Jidda cikin tsarkewan murya.
" Kawai falo zaki ringa kwana kamar yanda na ce miki ina yi , hakan shine zaman lafiyarki.".
Nan suka ci gaba da tattaunawa , shi kuwa Abdullahi rike da baki yake auna zantukansu daga bisani ya shige daka.
____________
Karfe goma sha dayan dare , Ummi tana shararan barci cike da nutsuwa har ta manta inda kanta yake .
Cikin barcin ta ji kamar ana daukarta , a hakan ya sanya a zabure ta bude idanunta. Cikin razani take kallon Abdullahi na shirin daukarta , ko kan ta magantu har ya ciccibe , baki na rawa ya .....
***
Taku har kullum kyauta daga Allah