Page 17-18
by @ummuaffan
GINSHIƘIN DUTSE...
_True life story._
*BOOK 1 Page 17-18*
_Gawurtattu uku._
©UMMU AFFAN
*MAMAN ZEE ƘAMSHI AND KAYAN MATA!*
Shahararu goma kenan aduniyan kayan mata munsan kanmu munsan kayanmu bah ako inazakisamu kayan shahararu goma aduniyan kayan mata sai awajen m zee kamshi kayan mata available online
Gakayanmu kamarhaka
Tafi budurwa duniyane
Tsumin lahaula
Gombar bujenki jagab
Shu Umar zumarmu
Mumuna da,aeki
Makalemata
Hadin me jego d amarya d uwar gidan d bazauwara
Dahuwar kaza cicibin kala kala
Shu,mar humra baka d Fara namatan aure ne kawai akwai Nayan mata
Turare wuta kala kala saiwanda kikazaba kayanmu batarkace kayane na matan kwairai kumakunsani shahararu goma aduniyan kayan mata m zee ce dakanta *** ko *** Kar abaki labari.
Sannan maganin sanyi ba Sai kinada infection zakiyi amfani dashi ba Dole ne ga KOWACE mace maganin sanyi ya zama daya daga cikin abinda ba a rasata dashi a gidanta sannan kuma
AMARYA
MAI JEGO
WACCE ZATAYI KOME
Dolene kiyi amfani da maganin sanyi kafin ku hadu da miji wannan Dole ne indai kinason kiji dadin muamala da miji.
Duk amaryar da aka kaita dakinta batayi amfani da maganin sanyi ba toh tabbas tayi babban kuskure hakama duk Mai jego data haihu har ta Bari tayi arbain suka Hadu da mijinta batasha magani sanyi ba itama ta tapka babban kuskure.
Wllhy kaya na aiki kinga ikon Allah Wai😂🔥🔥🔥🔥🔥ance wanda y iya y huta toh wanda y siya ma wllhy yafi kowa hutawa Allah dai y biya. Ku tuntuɓe ni a wannan number domin ƙarin bayani, muna aika kayanmu ƙasa-ƙasa gari-gari. Sayen nagari mai da kuɗi gida. *** sai kunzo.
*GIDAN GYARA SUPPLIMENT*
Royal jelly big
Royal jelly 30 pieces
Royal jelly small one 60 pieces inside the pack
Vitamin C-100,
Vitamin E big
Pesona
Dara
Cantik ayu
GLUTA white
Khusus ibu
Sugar wanita
Majakani 3 in 1
Eve Care
Juliet eve
Phyton buster
Phyton collegen
Glute sparkling
days ginger oil for hair
Papaya oil for breast
Garlic oil for hips
Vitamin C serum
Vitamin E serum
Busty blend
Gluta prime
Collegen+C
*Ƴan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat ****
*MASU SO A ƊAURA MUSU TALLAH SUYI MAGANA A NUMBERTA AKAN FARASHI MAI SAUƘI.*
*Page 17-18*
Kubrah wacce ta miƙe a hanzarce ta ce, "Wallahi Surayyah ki kuka da duniya, wanda bai zo cikinta ba ma jiransa take."
Tayi saurin ɗaga Innana da tayi ƙasa da kai tana hawaye. Cikin masifa Mardiyyah ke furta,
"Ai ga irinta nan, abinda Appa yake faɗa miki kenan kullum akan Surayyah amma baki gani, tun bai mutu ba yanzu ta fara saka ki hawaye yanzu idan ya gani sai ya ce daman ya faɗa ai."
Surayyah wacce ko a jikinta da halin da ta saka Innana ɗin ta riƙe ƙugu tana jijjiga jiki, "Hmmm! Ai daman ke kin fi kowa tsanata kuma na zamo kabewar kan kabari baƙincikin mai taushe, ba yadda aka iya da ni ƙadangaren bakin tulu ce wallahi ana kora ni na faɗa ruwan."
"In dai haka ne ko tur da ke, tur da haihuwar 'ya irinki. A yau ina jin ina ma ace ɓarinki nayi ba haihuwarki ba."
Innana ke maganar cike da tashin hankali. Kubrah da ke riƙe da ita ta ce,
"Idan rai ya ɓaci kada hankali ya gushe Innana, kar kije ki mata baki a haka ba ya aka ƙare balle ta kasance mai bakin uwa?"
"Bar ni na faɗi duk abinda ke raina Kubrah, a yau nayi danasanin kawo ta duniya, ji nake ina ma ba a cikin 'ya'yana tazo ba. Allah wadaran hali irin naki Surayyah, Allah ya baki kema masu miki yadda ki ka mana wallahi..."
Da sauri Kubrah ta rufewa Innana baki tana girgiza kai.
"Don Allah ki bari, ki daina yi mata baki, yana ɗaya daga cikin abinda ke ƙara tagayyara rayuwar 'ya'ya bakin iyaye musamman uwa."
Kamata tayi suka fita daga ɗakin Innana hawayenta sun gaza tsayuwa, har bakin ƙaramin gadonta na bono ta zaunar da ita kafin ta ɗaura da cewa.
"Kiyi haƙuri Innana, don Allah kar zuciya ta saka kiyiwa Surayyah baki, don Allah kiyi haƙuri aikin gama ya riga ya gama, ita kuma a haka tazo mana."
Innana kam ta kasa magana ba baka sai kunne, hawaye kawai ke zuba a kuncinta, wai 'yar da ta kawo gidan duniya ce ke mata haka? Allah ya gani ba tayi wa iyayenta abinda Surayyah ke mata ba, wannan jarabawa ce kawai ta Ubangiji. Zuwa ƙauye ya ganta domin tana so taje ko rubutu ne ta amsowa Surayyah don tana ganin kamar harda iskokai ne ke ɗawainiya da gangar jikin nata.
A can ɗakinsu kuwa Mardiyyah da Surayyah chachar baki ba kama hannun yaro, tun suna yi a tsaye har suka zauna ba su fasa ba, lokacin da Kubrah ta dawo daga ɗakin Innana ta dubi Autah ta ce,
"Je ki kawo mana tuwo da munyi sallar isha'i muci don gata can ana kira." Fita tayi tana hararar Surayyah don magana ne ba tayi ba tana tsoran bugun da Surayyah zata nakaɗa mata, amma sosai take jin zafin abinda tayiwa Innana yau. Ji take da ita ce babba yau sai sunyi dambe a gidan.
Kubrah ta kalli Mardiyyah ta ce,
"Da sallah ki ka tashi kika yi da ta fiye miki wannan faɗan, domin idan ta ita ne sai ku kwana kuna yi."
"Ai Allah na gode maka da zan bar gidan nan naje bodin, idan ba hutu na zo ba ai na daina ganin abin haushi abin tur. Ku kan sai dai ince kuci gaba da kauda kan don idan ɗan marayan zaki ya kuma girma da alama ba ƙaramar ɓarna zai ba."
"A hayye! Chass! Ai maganar ciki ba magana ba ce a fito fili a faɗa mana, da baki ya yi tsami ."
Cewar Surayyah tana kaɗa ido, tsaki Mardiyyah taja da cewa.
"Ai daman kowa ya yi zagi a kasuwa ya san da wanda yake."
Surayyah ta miƙe tsaye, "To ayi a gaban mutum mana idan ba tsoro ba?"
Kubrah ta ce,
"Mardiyyah tashi kiyi sallah, idan kuma alwalar ta karye kije kiyo wata."
Fita tayi daga ɗakin kamar zata tashi sama.
"Mtsuwww!! Aikin na ayya gayyar tsiya."
Cewar Surayyah tare da kwanciyarta saman katifar da take kai.
Bayan sun idar da sallah suka fara cin tuwon, suna jin shugowar su Appa da mazan gidan, har ɗakin Appa ya leƙo yana tambayar duk suna ci? Suka amsa masa da suna nan tare da masa sannu da zuwa.
"Ina Surayyah?"
Ya tambaya don bai hangota tsakar ɗakin ba, don duk suna zaune suna cin tuwo. Tasowa tayi daga kan katifar tana mutsitstsika idanuwa.
"Appa gani nan."
"Oh na ɗauka ai baki gidan ne?"
"Ina nan."
Ta faɗa tana tura baki gaba, wucewa ya yi ita ma ta fito ta zuba miya a nata tuwon domin daman kowa da robarsa kowa ya san nasa ta koma ciki.
Ko da Appa ya shiga ɗaki mursisi Innana tayi bata nuna masa duk abinda ya faru ba, don ta san kota faɗa dariya zai mata ko ya ce kaɗan ma ta gani. Tuwansa ta kawo masa ya fara ci, tayi shuru ita don ko abincin ta kasa ci, ya dubeta bai dai ce komi ba. Zuwa can ta ce,
"Malam idan da dama ranar Alhamis ina so zanje Ɗandume."
Ɗandume can ne tushen Innana a can aka haifeta haka danginta duk suna can na cikin Katsinan ba su da yawa don ita ma anan ta girma hannun Gwoggonta.
A natse ya ɗago ya ce, "Ɗandume kuma Kuluwa? Me ya faru da zaki je gida haka cikin gaggawa, ince jibi ne Alhamis ɗin? Ko wani aka rasa a can ɗin?"
''Ko ɗaya malam, kawai dai ina son naje na sada zuminci ba daɗewa zanyi ba kwana ɗaya ko biyu zan dawo, zuminci ne ya motsa kuma kasan dai abu ne mai kyau."
Kallonta ya yi amma sam bai yarda da furucinta ba, ita kuwa bata so ta ce masa matsalar Surayyah ce zata kaita domin tasan halinsa ya tsani camfe-camfen nan na ƙaƙabawa mutum aljani ko ace za a amso taimako, sai ya ce ba wani nan a dai yi addu'a shi ne daidai. Haka ta lallaɓa shi da daɗin baki har ya amince zata je kwana biyu ta dawo, sai lokacin hankalinta ya kwanta ta samu ta ɗanci tuwon kaɗan don kar ta kwana da yunwa amma ba wai don bakinta da daɗi ba. Ita kaɗai tasan ɗacin da zuciyarta ke mata, idan ta tuna abin kuwa sai taji hawaye na bin kuncinta. (Hattara yara, zubar hawayen iyaye akanku babban bala'i ne a gare ku, kar ka yarda ka saka iyayenka kuka domin kukan da zaka yi silar hakan bala'i ne a gareka, Allah ya shirya mana zuria baki ɗaya)
A daren ranar kam Surayyah bata fita ba, sakamakon har bacci ya kwasheta ba a kawo wutar nepa ba, daman da ta ganta ne fa hankalinta ke tashi sai ta fita gidan kallo, yau kam 'yan nepa sunyi maganinta har bacci ɓarawo ya yi awan gaba da ita wajen goma na dare ba su kawo ba. Sai cikin tsakar dare suka kawo nepar lokacin kuwa bata san a duniyar da take ba. Domin idan ta kwanta bacci kamar kasa bata farkawa saboda jikinta duk a tsamace yake na shegen yawo da gantalinta dole jiki yayi tsami idan aka kwanta kamar matacciya.
Da safe sai wajen takwas ta farka, ba wacce daman tayi gigin tashinta cikinsu, don ko Innana na mujiya ta saka mata. Bayan tayo alwala ta zo ta kuma kwanciya, sukam suna waje suna aikace-aikacensu tunda ranar anyi sanarwa ana hutun dimokraɗiyya day na ranar kawai hakan yasa Kubrah da Mufidah Autah ba su je ko ina ba.
Wajen tara da rabi ta kuma fitowa, tana duba kokonta taga duk ya huce, ɗan tsaki taja tare da ajiyewa, ta saka dumamen tuwo kanka ɗaya tazo ƙofar ɗaki ta zauna.
Tana jin Kubrah da Mardiyyah suna hirarsu har da Autah ma, sai dai ta kallesu ta taɓe baki da haka ta kammala cin tuwon taje ta wanke hannu ta koma ɗaki.
Juyi kawai take akan katifar domin duk jinta take a takure. Abinda ya faru jiya ne yasa ta ɗan ɗaga fitarta yawo yau amma duk da haka tasa a ranta lokacin da sukayi zasu haɗu da masoyinta nayi dole ta fita, sai dai duk abinda zai faru ya faru, yanzu ma daurewa kawai tayi. Tana cikin wannan halin ne ta jiyo sallama kamar muryar Hindu ƙawarta, bata san lokacin da ta miƙe tsaye ba, leƙawa tayi ta dagar ɗakinta ai kuwa ilai Hindu ce, zaraf ta fito daga ɗakin tana washe baki.
Hindu kuwa gaishe da Innana dake tsakar gidan tayi, sannan tayiwa Kubrah da Mardiyyah sannu ta nufi gurin Surayyah dake tsaye bakin ɗakin tana washe baki kamar gonar auduga.
Tana ƙarasowa kuwa ta finciki hannunta suka shige ciki.
"Kai ƙawata nayi murna da zuwanki."
"Ke dai bari ai ina faɗa miki yau Lawan ne ya ba Innata dubu biyar ya ce yau ɗaya dai na huta da tallar nan."
"Shegen sama kura ta hangi biri, amma fa Lawan ɗin nan yana burge ni, da alama ɗan gari ne."
"Ke dai bari kawai, ai wallahi ƙaunarsa ƙara ruruwa take a zuciyata. Ina matuƙar sonsa, jiya da dare kaza fa guda ya kawo mini haka ya danƙawa Inna dubu biyar."
Tafawa suka yi, Surayyah har da haɗiye miyau ta ce,
"Shi ne ko a tuna da ni?"
"A gaban Inna fa ya ba ni, kin san har cikin ɗakinmu ya shiga ya gaishe ta, shine ya ba ni a gabanta tasha rabo kin san gidan yawa kuma ko don ace saurayina ya kawo kaza kin san Inna sai ta ba kowa."
"Hahhhahhhh!"
Suka kwashe da dariya, Surayyah har da riƙe ciki ta ce, "Ai Innarku burge ni take ba irin Innana ba da komi cikin kaffa-kaffa."
Nan take ba Hindu labarin abinda ya faru jiya, amma duk nunawa tayi laifinsu Innana da Mardiyyah ne. Hindu ta ce,
"Wallahi ni har na mance da wani abu wai duka, ashe har yanzu ana duka."
"Ai kuwa anayi musamman idan aka tsaneka, ai ni 'yan gidammu sun tsane ki, ke kam kinji daɗinki Innarku na ƙaunarki."
Dariya kawai Hindu tayi tayi ta ce, "Ai dole ta ƙauna ce ni tunda idon nera ce."
Ita dai Surayyah bata fahimci me Hindu ke nufi da idon nera ba suka ci gaba da hirarsu...
*IDAN KUN YI ABIN DA YA KAMATA DA YUWUR DA YAMMA NA MUKU PAGE ƊIN GABA 19-20*
*UMMU AFFAN GHT SUPPLIMENT.*
Duk abinda ka ke buƙata a wannan company mai albarka zaka same shi a hannunmu ina Kaduna ne, amma duk jihar da ka ke anan zaka amshi kayanka babu wani batun kuɗin mota a aika maka saboda muna da blench a ko wacce jiha dake faɗin Nigeria. *** Sayen na gari mai da kuɗi gida.
*Royal jelly* Mai da tsohuwa yarinya, ƙarin Niima jiki yayi kyau yyi sulbi kamar tawarda
*Garlic oil* _maganin infection sadidan ga tightening da yke ka sa skin kyau sa namiji sunbatu
*Ganoderma reishi* xai ciccciko Miki da gaba ya motso d shaawa ya matse mace gam Yana gigita maxa
*Constifree tea* masu kashi d tauri Yana sake ciki ya wanko duk wani dattin mara ya gyra skin yyi fresh
*Longzit* matan da suka Kai shekaru 40 Niima y fara karanci a jikin su ku Sha longzit ku bn labari
*Panicept* duk wani ciwon Kashi da gabobi in Sha Allah matsala t kau
*Sto care* ina masu ulcer duk karfin ulcer in Sha Allah xai magance masu shekara da shekaru Basu Yi axumi b sun gwada sun fara axumi ynxu
*Female care* masu matsalar alada , infection,rikecewar jini matsi duk wata harka t gaban mace in Sha Allah.
*Kaɗan daga cikin kayan da muke da su, kai tsaye ka/kiyi magana ta wannan number domin sayen kayanmu masu ƙyau da inganci ****