Chapter 16
๐๐_*RAMIN K'ARYA*_ ๐๐
NA
IKILIMA ADAM
*( Kyauta daga Allah)*
Marubuciyar da ta nishandantar daku a littafanta kamar haka:
Kai ka jawa kanka
Kanwata
Rai daya ( Jan zaki)
Rudani
Makauniyar shari'a
And now
Ramin karya yan karin magana suka ce kurarre ne , mu je zuwa.
Da sunan Allah mai Rahma mai jin kai .
SHAFI NA SHA SHIDA
Baki na rawa ya ce " kiyi shiru" ya fada yana mai cigaba da tafiya da ita. kokawa ta fara yi dashi tana neman sauka , da yake karfi ba daya ba , har dakinsa ya isa da ita , yana ajiyeta ya koma ya sakawa dakin key , hannunta cikin nasa yana kokarinsa zare key a jikin kofar. " Don Allah karka rufe kofar nan" ta fada a hartsige . Idanunta na kawo ruwa. Kallonta yake cikin idanu , ganin yanda gumi ke sassarfo mata ya sanya shi , kallon ac dakinsa yayi ganin yana kunne ya sanya shi fadin" zafi kike ji kenan"?.
" A'a" ta bashi amsa a tsorace.
Ajiyar zuciya ya sauke kana ya ce " na sauke wani abu da nake ji akan ki , tun hirar da mu ka dan taba dazun na ji na amince dake a matsayin abokiyar zama , ba abunda zan miki za ringa kwana dakina Kuma a kan gado. Rashin yarda ne ze sanya ki ga abunda baki yi zato ba " ya fada cikin tabbatarwa. Sheshekar kuka ta fara , murya na rawa ta ce ," don Allah ka barni na kwana a kasa , wall...." . Dakatar da ita yayi ta hanyar fadi.
" Rike kalaman ki , zabi ya rage naki" ya fada yana mai kokarin cire hannunasa kan handle din kofar , ganin ya koma daga ciki ne , ya sanyata kai dubanta akansa idanunta sharkaf da hawaye. Tana kallonsa har ya shiga wanka ya fito , ganin yana shirin canza kaya a gabanta ne ya sanyata juya masa baya . Shi kuwa duk motsinta akan idanunsa , sai da ya gama shirin kwanciyar ya kalleta yana mai zama bakin gado.
" Taho mu kwanta dare yayi" .
Babu amsa , kyale shi tayi tana sheshekar kuka. Latsa wayarsa ya shiga yi , kusan mintuna talatin yana fira ta whsap yana rufe wayarsa. Ya dawo da kallonsa akanta ganin tana nan tsaye kamar an datsa . Jin takun tafiyarsa ya sanyata firgit ta dawo daga duniyar gyangyadi data fada. Soma ja da baya ta soma , shi kuwa yana karasowa har ya zo gab da ita suna jin numfashin juna , fuskarsa yake karewa kallo yanda take da siritattacen kyau , kana ya sauke idanunsa kan rigar barcin da Sumayya ta basu daga Hajiya babba , ganin rigar ya kama ta , Wanda ya san boobs dinta ya dan bayyana kadan ya sama. Ita ma inda idanunsa yake kallo , ta kalla tare da saka hannayenta ta kare su . Kwafa yayi da baki .
" Zaki taho ko na dauke ki ?. ".
A hanzarce tayi gaba ganin kamar ya shirya wancen kudinsa sa. Gefen gado ta kwanta kamar me jin sanyi , shi wutar dakin ya ragewa haske kana ya hau gadonsa yana mai kallon yanda ta bashi ba. Har ya so ya taba ta sai ya fasa tare da kudundune kansa a bargo.
Kashe gari
Jidda tun da Asuba ta tashi ta tada sallah nafila, kana tana zaune kan sallaya domin jiran time din sallah yayi .
Fitowarsa Adamsy ne ya sanyata kai duba akan sa. Kana ta sauke kanta kasa. Yana fitowa kallo daya ya mata ya dauke kai tare da fita , inda ya zarce dakin Lailat domin tashin ta daga barci. Koda ya shiga iske Lailat yayi tana sharara barci daga ita sai brezia da pant , rintse idanunsa yayi ganin cikin nata da ya dan turo.bubbuga kafafunta yayi hakan ya zaburar da ita ,ta farka .
" Ki tashi ki yi sallah , kiyi istigifari" ya fada yana mai fita daga dakin.
Mika ta soma tare da zama bakin gadon , tana kallon fitarsa . Ganin ya fice ta koma ta kwanciyarta don barci ne a idanunta.
Kusan karfe goma na safe , Jidda da Ummi suka shirya cikin atamfar da alhaji ashiru ya dinka musu na aurensu , brown mai zanen flower , riga da zani , ba karamin kyau ya musu ba , sabuwar hijab da takalmi suka sanya , sai da suka shiga dakin yara. Tere da shirya su , suma kaya suka sanya musu masu kyau. Ummi ce ta kalli Jidda .
" Ina zamu je naga kin saka an shirya su ".
Numfasa Jidda tayi kana ta ce " Ai dasu zamu tafi dubo yaya Iro".
" Kina ganin Ubansu ze yarda kuwa ?".
Dan jimm tayi kana ta ce ", ai na gayawa Mamy ta ce , mu tafi dasu ai babu komi".
" Kin sanar masa zaki fita ma kuwa " Ummi ta fada cikin jiran amsa.
Kallon ta Jidda take .
" Kamarya na sanar masa , na ce miki Hajiya babba ta sani, shi me zan fada masa ".
" Dole ki gaya masa Jidda ki hanzarta kafun ya bar Gidan nan , dan zaman sa kike har yanzu , yaya Abdullahi sai da na gayamasa da fitar mu.".
Shiru tayi tana nazartan, kalamanta. Kana ta dago kai , tana kallon kofar ganin ana shigowa .
Kamshi turarensa ne , ya gauraye dakin , yana karasowa falon , idanunsa ya sauka akan Jidda da Ummi da suka matsa Dan baya. Kallon yaran yake ganin duk kamar fita zasu yi. Kamar ba ze magana ba kusan mintuna goma , kana ya ce , Hussain ina zaku je ne ?". Ya magana yana mai kama hannunsu.
Ganin Hussaini na kallon nasa yana kallon Jidda ne , ya sanya shi kai dubansa akan Jidda. Ganin kamar tana kallon Hussaini din ne ya sanya shi , yin kwafa tare da zura hannayensa a aljihunsa. Kallonsa akan su . " Ina zaku je ne ?". ya fada yana kallon Jidda dake kokarin kama hannun Hussain.
Baki na rawa cike da tsoro da fargaba ta furta .
" Zamu je dubo yaya Iro ne ". cewar Jidda.
Shiru yayi kamar me nazarin wani abu , kana ya fesar da numfashi yana mai cire hannunasa daga aljihunsa.
" Wa kika sanarwa zaku fita"?. Yayi magana babu wasa .
" Mamy " ta bashi amsa tana mai sakin hannun Hussain.
" Okay " ya furta yana mai karkada kai , kana ya dan saci kallon Ummi dake yiwa Jidda magana cikin kunne . Murya Jidda ya jiyo tana fadin.
" Don Allah kayi hakuri , ka bar mu , mu tafi tunda hajiya Babba ta sani" ta fada kamar me shirin kuka.
Murya na rawa ya furta. " be careful with me". Kana ya maida kallonsa akan yaransa , yana mai zaunar dasu kan kujera. Manna musu kiss a goshi yayi dukansu , kana ya juyo tare da yunkurin barin dakin. Har ya kai bakin kofa , kana ya waigo yana kallon yanda suka zuba masa idanu.
Dawowa cikin dakin yayi yana face din Jidda tare da furta " your foot doesn't move from the house, that's understood" yana fadin hakan , ya sakai ya fice daga dakin .
Idanun Jidda nan da nan suka ciko da kwallah , jikinta ya dau rawa matuka , Ummi ce ta fara buga bayanta alamun rarrashi.
" Ummi kina jin abunda ya fada , taya ze hana in je ganin yaya Iro , shine kadai ya rage muna , taya ze ce na zauna Gida " ta fada tana shirin kuka. Hussaini dake zaune shima idanunsa ya cika da hawaye , dan duk abunda Prince yake yi ya kula kamar fada ne yake ma Jidda.
A guje Jidda tayi wajensa ta rungume sa tana kuka.
" Mu hakura da fitan tunda ya hana ki , fitan ba ze mun dadi ba ni kadai , zuwa dare tunda yau ma sashin nasa zaki kwana. ki koyi yanda zaki masa magana in sha Allah ze bari" cewar Ummi cikin tsigar rarrashi.
" Zan je na tari , yar aiki dake kula da sashin mu , ta fadawa Mamy mun fasa fita kawai , karma ki gayamata shi ya hana " cewar Ummi cikin nutsuwa.
________________
Misalin karfe shida na yamma , wani bawan Allah ne zaune fuskarsa dauke da fask mask , a gefensa wani dattijo ne , computer ce a gabansu da dukan alamun abu suke yi mai muhammanci a ciki.
Kallonsu yana kan computer , inda sunaye suka bayyana kamar haka.
Surayya da Rayyah , kadija , Sumayya.
" Sunan ya'yan Sarki mata kenan" cewar wanda ke sanye da fask mask.
" Eh sune , amma daya daga cikin tayi aure , uku ne yanzu a Gidan" cewar Dattijon. Nan suka saisaita muryansu suna magana cikin sirri.
__________________
Alhaji Faruk , dakin Mahaifinsa ya nufa. Ganin yanzu ya samu lafiya.
" Abba na zo ne akan maganar Jidda " ya fada yana mai kokarin zama saman kujera .
Kallonsa yake yana shan lipton.
" Haba Umar, ka ce tana da aure , kuma auren ma dan Sarkin Lafiya , ka san girman arzikin su kuwa , taya zamu ja dasu duk da muna da namu rufin asirin" ya fada cikin sarewa.
Duk inda damuwa take t gama bayyana a fuskar Faruk. " Tunda ka fadi sai naga ka canza akan lamarin nan , a da kuwa ai kace zaka san abun yi , in ka kyaleni zan aikata barna wallahi" ya fada cikin barazana.
Kallonsa Abby yake yana nazartan kalamansa , kana ya taso tare da dafa bayansa .
" Haba dana, karka yi fushi , kayi hakuri ka bani wata biyu , zan yi dogon binkice kafin na sama mana mafita " ya fada cikin sanyi.
" Har wata biyu?".ya tambaya.
"Eh " ya bashi amsa.
Fesar da numfashi yayi .suna mai cigaba da hirarsu.
___________________
Sumayya zaune a dakin Yara tana kan Whasap.
Taga wata bakuwar lamba ta mata message .
Kusan mintuna goma ta dauka , sannan ta bude sakon. Ganin an ruta " Aslm alaikum Gimbiya Sumayya " . kama sunan da akayi ya janyo hankalinta akan chat din , duba dp dinsa tayi taga hoton wani hadadden saurayi sanye cikin farar Jallabiya , yana zaune a massalacin madina , al'kurani mai girma ne a gabansa. Ajiyar zuciya ta sauke .Bata bashi amsa ba , sai ta ci gaba amsa sakonni wayarta , sakon sa ta kara cin karo dashi.
" Be dace dake ba , ma'abociya, kyau da kwaliyya ,nagarta , ki ga sako baki amsa koda sallama ".
Tana bude sakon, taga ya turo mata da stickers din hoton zuciya.
" Wslm , dawa nake magana?". ta rubuta .
" Mai kaunarki , ne Aliyu Mustapha ".
Ganin haka ya sanya ta sauka online din gabadaya
______________
Irin sakon da akayiwa Surayya shine aka yiwa Surayyah .
Ita kuwa Surayyah sossai ta rude ganin ta samu santalelen saurayi. Ita kuwa cema yayi sunansa Faisal Musa .
Fira ya barke tsakaninsu , yanda kasan sun taba sanin juna , ita babu abunda ja hankalinta akansa irin zallar kyawunsa , dan ya tura mata zafafan hotunansa .
Cikin jin dadi ta sanarwa Mahaifiyarta , labarin komi . Sosai Humaira ta ji dadin jin haka.
" Ai daman na san wallahi , wanda ze aureki sai dan kece sa'a ki dube sa. yanzu haka Ubansa Sarkin saudiya ne , kedai duk inda arziki yake ai na mun gama samu , karki bari Zainab ta sani ,baka san bakin wani ba " cewar Humaira cikin jin dadi. Nan da suka hau murna sun samu babban Yaro.
______________&__
Prince Adamsy Gidan su Zahradeen bayan sun dawo daga sallah magrib.
Sosai suke cin abincin da hajiya ta dafa musu.
Zahradeen ke kallon Adamsy.
" Ya labarin Amaryarka , ta gayamaka abunda docto ya fada kuwa ranna da baka lafiya". Cewar Zahradeen yana kallon Prince.
Prince na kai loma tuwo bakin, ya hadiye kana ya furta me ya fadi? dan kasan ba zata iya fada min ba".
" Matsalar ce ta shaawa shine , yake son cutar dakai , kuma Docto ya mata magana , be boye mata komi ba , ya sanar da ita ta baka hakkinka sabo..." Jin prince na kwarewa ya sanya shi yin shiru.
Zazzare idanu Prince yayi , " docto ne ya yiwa wannan yarinyar bayanin nan ?". Ya tambaya a zafafe.
" Eh mana " cewar Zahradeen.
Zumbur ya mike tsaye , Yana.....
Taku har kullum kyauta daga Allah