Page 1
by @farnanahhh
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Yanda na fara wannan littafin, Ina rokon Allah yasa na gama shi lafiya..
Ina fatan zakuji dadin shi
BAZLA❤️
BY: Farnanah
Page 1
Bazla! Bazla!! Bazla!!! Kiranta take cikin bacin rai tana duba tsadadden agogon dake manne a lausashshen fatar hannunta.
Matashiyace wacce bazata wuce shekaru 18 ba, tanada tsayi, chubby ce kuma farace mai manyan idanu, da sauri sauri take qarasowa wurin matar dake kiranta tana cewa “Ammi kiyi hakuri shiryawa nake” tana me langwabe kanta a cikin shagwaba.
Dagowa matar da a qalla zatayi shekaru 40 tayi wadda zaka zaci ‘yar shekara 35 ce Saboda yanayin fatar jikinta da yadda alamu suka nuna tana cikin hutu da kwanciyar hankali, tana sanye da tsadadden lace dinta wanda farashinsa zaiyi kimanin naira dubu dari da hamsin hannunta dauke da jakar ta dayan hannunta riqe da mukullin mota tareda tsadaddar wayarta. Qarewa Bazla kallo tayi kallon sama har qasa “amma dai bada wannan shigar zaki bini ba ko Bazla?”
Bazla kallon kanta tayi da mamaki tace “Ammi don’t I look great in this?” Ta fada tana qara kallon kanta, tana sanye ne da wando baqi dogone har qasa bai wani matseta sosai ba sai rigarta wacce take fara a jiki an rubuta PRETTY GIRL sai tayi rolling da small veil dinta wanda yake launin baqi sai jakarta fara da sneakers dinta suma farare, shigar ta matuqar dace da ita kamar don jikinta a kayi kayan. Ta dago kai tana kallon Ammi tana jiran taji mai zatace
Ammi ta kalleta irin kallon kin makance tace “zakije ki daura Abaya akai kou ki sauya wasu kayan mu tafi ko kuwa, Karki batamin lokaci inada abubuwan yi, Saboda shopping din nan ba dole bane sai a fasa, kije ki canja ki sameni a mota” ta juya zata fita, har ta daura hannunta a handle na kofa ta juyo tace “minti biyar na baki” ta juya ta fita
Bazla da ranta yayi matuqar baci ta juya a fusace ta koma dakinta tana qunquni, ta bude dakin nata wanda yake dauke da lafiyayyen gadonta da lausassar katifa wanda yasha hadadden bedsheet, tareda kujeru biyu a gefe, ta buda wardrobe dinta wanda shaqe yake da kaya ta zaro wata hadaddiyar black after dress ta saka akan kayan ta fito da dan sauri sauri gudun kada ta qara laifi a wurin Ammi.
________________
Yana qarqashin mota yana dubata cike da kwarewa irin ta bakanike, ji yayi ana kiran sunansa “sufyanu kazo ana nemanka”
Ya fito yana karkade jikinsa da ya baci saboda aikin da yakeyi
Dogon matashine wanda bazaka kirashi baqi ba kuma bazaka kirashi fari ba yanada qasumba wacce ta zagaye fuskarsa, idanunsa da suke farare ya dago ya kalli mai kiransa yace “Isma’il ya akayi ne wa yake nema na haka da tsakiyar rana” harararsa Isma’il yayi yace “to dama da dare ake neman mutum to sai ka biyoni ka gani da idonka” ya juya ya tafiyarsa, Sufyanu yayi murmushi yabi bayansa saboda yasan halin Isma’il da baqar magana.
Yana zuwa ya tadda Ameer qaninsa a tsaye a bakin gareji yace “Ameer lafiya?” Ameer yace “ yaya dama Umma ce tace na kiraka Abba bayada lafiya” cikin kidimewa yace “me ya sameshi?” Ameer yace “umma tace kayi sauri kazo” Jan hannun qanin nasa yayi suka nufi hanyar gida.
Sallama sukayi suka shiga ya tadda Abba a kwance hannunsa nade da bandage, Sufyanu ya qarasa da sauri yana tambayar Umma meya sami Abban, Umma a cikin nutsuwarta tace “Nima ina zaune naji ana sallama aka shigo da shi ya fadi a mashin wai wata mota ce suka samu qaramin hadari” Sufyanu ya kasa cewa komi sai yaji murayar Abba yana cewa “kar ka damu ai kaga sun ma kaini chemist an dubani ba wata matsala bace babba ka kwantar da hankalinka” Sufyanu ya kalli Abbansa cikin tsananin qauna da kulawa yace “Abba ko dai muje a sake dubaka” Abba yayi murmushi yace “ Aa dan Albarka ai har magani an bani don babban wuri ma suka kaini” Sufyanu yace “ Abba Allah ya baka lafiya ya tsare gaba” Abba ya amsa da AMEEN ya miqe yace bari yaje ya dawo, yana kaiwa kofar gida ya hadu da Hajara qanwarsa ta dawo daga makaranta tana sanye da uniform wanda yake nuni daga makarantar boko ta taso, tace “yaya ina wuni” ya amsa mata yace “ zan siyo kayan marmari yanzu tunda kin dawo sai ki gyara” sai ta amsa da to shi kuma ya wuce
______________