37
💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔
( shi ya san gidan mai rowa)
```By```
```SASAAL```
```Page 37```
_______"Bala" ya faɗa yana gyara zamanshi,tunaninshi yaƙara faɗaɗawa ta yanda Maysarah zai iya sauraron Bala da matsalar Halime kai tsaye,dole akwai wanda yake tsakani,to waye wannan? Duk yanda ya kaiga hasaso wanda zai zarga ya kasa kuma yasan ba lallai Bala ya gayamai gaskiyar komai ba.
Kunyar kanshi ne yakamashi dayasanin cin manyan kuɗin daya karɓa da ƙarairayin da yayi tayiwa Maysarah na kamashi. Da wannan tunane-tunanen ya nufi sashen Mubeena.
Dariyar ƙeta Mubeena ta bushe dashi, bayan ta samu tasha daƙyar, wassafo yanda zata bautar da Halima cikin ruwan sanyi,batare da tasan tsare-tsaren Mijinta akan Halima ba takeyi.
Wanka tayi ta shirya cikin kayan barci masu kyau duk don taja ra'ayin Faisal taji komai a bakinshi.
Ta taka babban Sa'a kuma batayi asarar manyan kuɗin data zuba wajen siyan magungunan matan ta masu inganci ba.
Nishaɗin da Faisal yake ciki ne yasa bai ɓoye mata ainihin inda mukullin yake ba,bayan ya ɗanyimata nasihar laɓen da take yi bashida kyau, nadama ta nuna sosai kuma ya yarda ita,cikin salon yaudarar data shiryamai suka ƙara narkewa juna, tsakanin mata da miji sai Allah.
★7:00am Mubeena ta tayashi kimtsawa cikin ƙananun kayan Levi's, baƙaramin kyau yayi ba, har bakin mota ta rakoshi ita da su Sanam. Bai kalli ko sashen da Halima take ba gudun abinda zai biyo baya,hakan da yayi baƙaramin daɗi yayiwa Mubeena ba, murmushinta sai yaƙi ɗaukewa saboda walwalar da take ciki.
A gurguje ta shirya cikin kayan gida tana goya school bag ɗinta,haɗaɗɗen wayan da Faisal ya bata take bi da kallo tana jiran kiran driver. Gaba ɗayama ta manta da tafiyar Faisal balle tasa rai da shigowar shi,saboda zumuɗin fara zuwa Makaranta.
Tana ƙoƙarin miƙewa ta ɗan sawa cikin wani abun driver ya kira. Dasauri ta tashi cikin zumuɗi ta kullo door ɗin. Da ɗan saurinta tafaɗa luxury car ɗin da Faisal ya ware don kaita makaranta. A securities ɗin gidan babu wanda hankalin shi yaje kan sanda tashiga motar balle suyi gulma,kuma tuntuni dama ɗaya daga cikin motocin Faisal ne da amintaccen drivern shi yake fita da shi idan yana gari.
Sai da yafara biyawa da ita taci abinci sannan ya wuce da ita Makaranta.
Bayan yaran Mubeena sun wuce makaranta ba da daɗewa Zee tazo gidan. Balaifi kyakkyawace amma ba sosai ba. Bayan ta cika tumbinta da kayan daɗi ta dubi Mubeena Fuskarta da alamar tambaya.
"Na ce ba,ina wannan yarinyar take"
" At school amma nasan bazata wuce 2:00pm ba,aiki na nan yana jiran shegiyar" ta faɗa ranta naƙara ɓaci.
"Shiyasa nake sonki Mubee" tafawa sukayi,suna cigaba da tattauna shirin su. A haka Yusra ta same su Fuskarta a kumbure,dayake me zafin kai ce,ko Zee bata gaisar ba ta wuce ainihin parlourn Mubeena.
Maimakon Mubeena ta bawa Zee haƙuri sai ta basar,suka cigaba da hirar da sam yadaina yiwa Zee daɗi,amma a wajen Mubeena abinda Yusra tayi balaifi bane.
Zee bata ƙara minti biyar ba,ta fara ƙoƙarin miƙewa,"me nake gani? Badai tafiya ba?"
Ba ta tsayama ta saurareta ba balle ta bata amsa ta fice abinta.
Dasauri Mubeena tabi bayanta tana bata haƙurin da batasan laifin data yimata ba.
Sosai Makarantar da ɗaliban ciki suka birge Halima, mussamman sabuwa ƙawar datayi mai irin halinta kuma sunan su ɗaya amma ita da Sadiya take amfani.
Bayan sun tashi ƙarfe biyu, sukayi lunch sannan suka ɗan kwanta suka huta na awanni biyu, kafin ta shiga ajin Islamiyyar dake haɗe da Makarantar. Sai wajen 6:00pm suka isa gida.
Zancen wulaƙanci ƙin ɗaga wayar Yusra da Maysarah yayi ne ya mantar da Mubeena dawowar Halima da aikin datayi burin sata, Yusra bata bar gidan ba sai dare sosai.
Itama Halima bayan ta gama komai nata zuwa ƙarfe takwas na dare barci mai nauyi ya ɗauke bayan sunyi waya da Uncle Faisal.
Duk nacin Mubeena da zaryar sashen Halima da takeyi bata samunta,babu abinda bata leƙa ta gani ba wanda Faisal ya siyawa Halima, da tanada abinyi da shi, wallahi da duk sai ta kwashe su,ranta ne yaƙara ɓaci da uban suturu masu tsadar da Faisal ya siyamata,cikin fushi tashiga kwashe su harda asalin wanda Halima tazo da shi.
A bayan gidan ta samu su fetur da ƙonesu.
Duk da haka washe garin daya kama weekend tayiwa sashen da Halima take tsinke da sassafe.
Baƙaramin kuka tasha ba lokacin da taga kaf suturunta babu su sai kala uku,kuma ko da Faisal ya kirata ba nacin da baiyi ba ta faɗamishi mai akayimata saboda ba haka ya saba jin muryarta ba amma taƙi faɗamai,ƙarshe daya matsa mata kuka ta sa mai, katse kiran yayi, ya kira Mubeena,bata ma nuna ta shiga sashen ba,kuma tace mishi ta manta rabonta da ganin Halima, don ko shigowa gaisheta Halima batayi, shagwaɓar yaushe zai dawo tafara yi mai," haba Dear daga Three days zakayi amma shine ka tafi har wajen sati".
Shiru taji ba amsa tana duba wayan taga yama jima da katse kayanshi,ranta ne yaƙara ɓaci da haushin Halima ta kwana,shiyasa da sassafe ta nufi sashen.
Mari mai zafi ne yafarkar da Halima kamar kayan wanki haka ta fara janta zuwa nata sashen,tun akan hanya ɗankwalin kanta ya zame,ga doguwar rigar barcin jikinta bai fi iya gwiwarta ba, kitchen ta jefa ta tana ƙara zuba mata wani marin.
Tun ƙarfe bakwai Halima ta fara hidimar Mubeena har ƙarfe goma sha ɗaya da suka fito karyawa ita da ƴaƴanta. Babu wanda bai shaidata ba acikin yaran,amma jan kunnen da Mahaifiyar su tayi musu yasa kowannen su yayi fuska.
Tana tsaye agefen su kamar yanda Mubeena ta Umarceta suka gama karyawa,sannan tace tabi bayan Sanam ta gyara mata ɗakinta sannan ta wuce ɗakin Mujaheed da Bibi duk da ta gyara.
Kamar raƙumi da akala haka take bin Sanam dake murguɗe-murguɗen jiki tana hura hancinta.
Ita dai Halima ko lura da sauyin tafiyar Sanam ɗin batayiba tsabar gajiya da yunwar dake neman nakasata.
Tayi balance tana sakin murmushin nishaɗin ganin Halima da bata rage mata jindaɗin komai ba na wahala, tunawa Faisal zai iya dawowa ko dayaushe saboda bikin Sumayya dayarage saura kwana uku su fara,yasa ta fara lissafin kalar gyaran jikin da zatayi.
Mujaheed ne ya buɗe ƙofar da'ake knocking,a ɗan zabura ta gyara zamanta fuskarta na bayyana farin cikin dayake na yaƙe.
"Salim saukar yaushe haka ba sanarwa" ta faɗa tana kallon hanyar da Halima zata fito.saboda warning ɗin Faisal na bayason familyn su susan da Halima a gidan.
Wanda ta kira Salim ƙanin tane uwa ɗaya Uba ɗaya,dagashi sai Yusra, gogaggen ɗan duniyane saboda tsabar son matanshi yasa yaƙi dawowa tare da Iyayenshi, ya koma ƙasa ɗaya da Maysarah,amma tun ranar da Maysarah ya kama shi da mace agaidan shi, yayi mishi rohon daya kusa rabashi da ranshi ya tattara ya koma Canada.
Yana ƙoƙarin zama Halima tana fitowa, fasa zaman yayi, yana kallonta daga sama har kan ƙafafuwanta, atake kuma ya wassafo yanda zata kasance mai, jajayen leɓenshi ya laso still bai zauna ba.
"Aunty na gama" Halima ta faɗa da sanyi muryarta.
" Okay maza kije sashenki" Mubeena ta faɗa dasauri a ɗan dabarbarce tana kallon fuskar Salim da har lokacin hankalinshi na kan Halima.
Bayan Halima yabi da kallo yana shafa ƙirjinshi.
"Who is she?"
"errand girl" Mubeena ta faɗa muryarta na nuna alamun rashin gaskiya.
"Errand girl? Unbelievable, ta yaya ƴar aike take da sashe a gidanki,common Mubee pls who is she?"
Dan Allah Salim karka tonamun asiri, cikin rashin wayo ta kwashe komai ta gayamai.
Dariya ya bushe da shi yana ɗaga hannayenshi"50 50 zamuyi zan rufa miki asiri zakiban mukullin sashen saboda da daddare zanje taɗi" ya faɗa yana kallonta.
Ajiyar zuciya tasauke duk da tasan mai Salim yake nufi da taɗi, kuma bazata taɓa ƙaunar ƴarta ta tsinci kanta a irin wannan taɗin ba, amma ta bushe zuciyarta ta amince mai, batare da tausayin maraicin Halima ba,a take ta ba shi mukullin duk da bai shaida mata ranar zuwanshi taɗin ba.
A Dai-dai lokacin da suke wannan ƙullin Maysarah yake ƙoƙarin shiga jirgin da babu wanda yasan da zuwanshi....✍🏻