MAI KWAƊAYI

38

by @nafisatusasaal01



💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)



  ```By```

```SASAAL```



 ```Page 38```



________Salim bai jima ba yabar gidan saboda Mubeena taƙi sakin jiki suyi hira.


Yana fitowa harabar gidan yaga ana knocking sashe da Halima take da sababbun furniture's.

Tunawa da may be Yaya Faisal na wannan gwanintar ne duk don Maysarah yasa yaja tsaki.


Tunowa da garaɓasar da zai kwasa kafin saukar waccen azzalumin (Maysarah) gidan yasashi murmusawa dai-dai lokacin dayake murza sitiyarin motar shi yana ƙoƙarin barin gidan.

"Ko yaya Faisal zai yi da ƴar mutane? Ko shima dai garaɓasar yake kwasa yabar sis Mubeena da sokoncinta" shi kaɗai yake surutan shi kafin yafara dariyarshi ta mugunta.



Bayan fitar Salim Zee takira a waya, saida ta kira yafi sau biyar sannan ta ɗaga muryarta a cunkushe.

Cikin rawar murya Mubeena tafara koro mata bayanin da babu komai a ciki sai son kanta da ƴan uwanta.


"Ni dai babu ni a wannan matsalar taki Mubee,saboda ko da wasa natsani kalmar fyaɗe." Kafin Mubeena taƙara magana Zee ta kashe wayarta gaba ɗaya.


Kafaɗunta ta ɗage haɗe da taɓe bakinta,don gaskiya bazata yarda asirin da Faisal yace tarufe ya tonuba,domin daga ranar tasan aurenta dashi yaƙare.


Ƙimtsa kanta tayi ita da yaran sukabar gidan.



Zazzaɓi mai zafi ne ya rufeta don daƙyar ta iyacin Breakfast ɗin da Victoria ta kawo mata, paracetamol tasha ta kwanta bayan tayi wanka. Sai dai barcin bai yi nisaba kiran Aminu driver ya shigo wayarta,daƙyar ta iya tashi ta buɗe musu ƙofa batare da bin diddigin kayan da suke ƙoƙarin shigowa dashi ba,ta shige Bedroom tayi kwanciyar. Sosai tasha barcinta kafin su gama komai.


Aminu ne yaƙara kiranta tafito ta kulle sashen sun gama, baki ta saki tana kallon yadda parlourn yaƙara komawa kamar ba wanda ta sani ba.


"Mai gida yace kishirya gobe zan kaiki gidan Abokinshi" ba tace komaiba sai nodding kai data yimishi ta kulle sashen.



Fuskarshi so furious yake sauraren mai magana a waya,kafin a hankali ya fara bashi amsa da ɓacin ran dake kwance cikin husky voice ɗinshi dayayi ƙasa sosai saboda gajiya,ba shi da ra'ayin sauka a gidan Faisal yafiso ya sauka a gidanshi da babu wanda yasan dashi sai Dad ɗin shi,amma suna ƙorafin komai bai kammala yanda yace ba.


Lokacin ƙarfe 9:00pm don haka kai tsaye ya kira Aminu,bugu ɗaya ya ɗauka da sallamar da atake yamaƙale mai jin muryar wanda baiyi tunani ba, maimakon yakira Faisal sai ya ruɗe kai tsaye ya tafi ɗaukoshi.


Da mugun speed yake tuƙa motan gudun yin laifi don yasan bayason jira.



Tun daga nesa Aminu yasamu damar ƙaremai kallo tare ƙara tasbihi ga Ubangijin dayayi halittun bayi. Sanye yake cikin Thom Browne da Levi's jacket saboda sanyin daya baro acan haka Nigeria ma da ɗan sanyi bare da daddare kamar wannan lokacin.


Ko da wasa baiyi ƙoƙarin kallon idanuwan Maysarah da gajiya da ɓacin rai yasa suka ƙara zama wani iri ba.


Sai lokacin da suka shigo compound ɗin gidan Maysarah na ƙoƙarin fita Aminu ya tuna Halima na part ɗin.


Kiran Faisal yafarayi ba ƙaƙƙautawa amma bai ɗagaba,hikimar kiran Halima ne yazo kanshi,sai dai itama bata ɗagaba kuma dama yasan da wahala batayi barci ba.kasa motsi yayi yana jiran kiran Maysarah da faɗan da zai biyo baya.



Kai tsaye ɗakin daya saba sauka ya wuce.


Tuna kayan Maysarah dake bayan motan yasa Aminu sakkowa, luggage ɗin shi ya wuce mai dashi cikin sa'a ya samu ƙofar a buɗe.



Ƙarfe goma ya tsara zuwa gidan,zuwa ƙarfe goma shabiyu ya dawo.


Kananun kaya yasa free size ya ɗauki car key ɗinshi sai gidan Sis Mubee,kiran da Abokinshi yayi mu shi ne yasashi fara biyawa kafin ya wuce.



Wanka yayi ya kimtsa cikin Pyjama mai taushi,kai tsaye parlourn ya fito,ya kunna System ɗinshi ya ijjiye daga ɗan nesa dashi yana kallo wani video da zasuyi aiki akai.


Idanuwanshi a lumshe suke saboda barcin dake neman ɗaukeshi, lokaci ɗaya bazakasan da mutum a Parlourn ba,saboda duhu.


Kamar anmintsineta tafarka, maƙoshinta abushe ga yunwar dake damunta saboda sai yanzu zazzaɓin datakeji yasaketa, kai tsaye parlourn ta fito,kayan barci riga da wando dogaye ajikinta sai ɗankwalinta daya ɗan zame baya kaɗan kwataccen sumar goshinta da kanta a waje.


Tsaf fitinannun idanuwan Maysarah da ganinta yasa suka buɗe da kyau suke kallonta.mamaki ne ya hanashi motsi.


Ganin System da batasan dashi bane yasa gabanta faɗuwa tana ƙoƙarin ƙunna bulb ɗin parlourn,dai-dai lokacin akafara kici-kicin buɗe sashen,fasa kunnawa tayi saboda tsoron daya haɗe mata. Tana ƙoƙarin yin sanɗar komawa ɗaki ta kulle kanta Wayarta ya fara ringing. Zaro idanuwanta masu haske tayi tana toshe bakinta, wanda hakan baƙaramin burge Maysarah yayi ba.


"Aunty Mubeena! Wayyo Allah nashiga uku" ta faɗa tana matsawa kusa da system ɗin cikin sanɗa,kiran Mubeena daya ƙara shigowane yasata ɗagawa kafin tayi magana Mubeena ta fara masifa.

"Ga Maysarah nan abakin ƙofa,ki buɗemai ƙofan" saboda tasan da wannan ƙaryar kawai zatayi nasara akanta, Salim ne yakirata yace ba'acire key taciki ba,kuma bayason yayi magana taji muryarshi.

"Aunty dagaske Maysarah ne?" Tuna wacece Mubeena yasa tayi saurin katse wayan tana nufa ƙofar,da tsananin farin ciki a Fuskarta.

"Ohh yau Mammyna burinki zai cika,dama nasan Uncle Faisal ba gaskiya ya faɗa ba."


Ta faɗa da dariya da kuma ƙuruciyar daya hanata fuskartar Mubeena bazata taɓa turo Maysarah wajenta ba,a dai-dai Lokacin da agogo ya buga ƙarfe goma sha daya na dare.....✍🏻