BAZLA❤️

Page 3

by @farnanahhh

Page 3


Su Ammi na zaune a parlor bayan kammala cin abinci, suna hira sai ga kamal ya shigo, ya qaraso yana gaida Ammi, Ammi da fara’arta ta amsa tana ce mishi “Kamal Ashe ka dawo” yace “Eyh Ammi na dawo” tace “to MashaAllah, an kammala karatu ko” yace “Ammi an gama” tace mishi “Allah ya taimaka yasa aci amfaninshi” ya Amsa mata AMEEN

Ammi ta kalli Bazla tace ki kawo mishi abinci mana, yace “ni Ammi a qoshe nake ma” tace ayi haka kazo bakaci komai ba” yace Alhamdulillah Naci abinci” tace to shikenan 

Wayar Ammi ce ta fara ruri ta daga bakinta dauke da sallama, a daya bangaren aka amsa sallamarta, da fara’a tace Alhaji ina wuni ya aikin, ya amsa mata da “Alhamdulillah ya qara da tambayar ina shalelenshi” Ammi tace gata nan a zaune ga Kamal ma da Hafsa ma sunzo” yace “yau manyan baqine a gidan kenan” tace mishi “aikuwa dai” ya tambayeta sunyi fitar ne dazu, tace mishi “munje arziki ma mukayi wallahi wani muka dan buge a mashin” cikin tashin hankali yace “SUBHANALLAH kuma shine baki kira ba hajiya” tace “abun fa baiyi tsanani ba a hannu ne yaji ciwo, kuma muna kusa da wani pharmacy sai mukaje can aka duba” yace “hajiya shiyasa nace miki ki bari a daukar miki driver amma ke sai kice bakyaso” tace “tunda dai abun da sauqi ai Alhaji Alhamdulillah sai dai muce Allah ya tsare gaba kuma ni maganar driver nan gaskiya banaso” yace to Ameen ki gaida su Kamal din ni zanyi wani aiki yanzu” tace “zasuji” sukayi sallama ta aje wayar

Kamal ya kalleta yace Ammi wani abu ya faru haka, tace “wallahi kuwa kamal” yace “Allah ya tsare gaba” ta amsa da Ameen 

Kamal yace “bari na dauko tsarabarku naga Bazla sai hararata ake” ya fada yana tashi yana dariya, Bazla tace “laaa bro yaushe akayi haka” itama tana dariya

Sai gashi ya dawo hannunshi dauke da wata gift box mai kyan gaske tareda wata leda yazo ya miqawa Bazla box din ya bawa Ammi ledar da ke dauke d turarruka

Bazla ta buda box din ta tashi tana tsalle saboda murna, Ammi tace “ke wai bakida hankali ne, meye na wannan ihun”, Bazla ta taso tace “Ammi Kiga fa meye a ciki” Ammi ta duba taga Agogone a ciki mai kyan gaske da wata siririyar sarqa da akayi mata ado da wani abu mai zanen heart, sai kuma wani hadadden turare set biyu sai kuma wata qaramar box a ciki, ta dakko box din ta buda taga zobe a ciki mai kyau

Ta dinga murna tace “thank you so much bro, naji dadin wannan tsarabar, Allah ya saka da Alkhairi” yace “Ameen little sis” Ammi tace “lallai Kamal waton tsarabar kanwarka tafi tawa” yayi dariya yace “ A’a Ammi” ya miqe yace Hafsa ta tashi su wuce gida

Sukayi sallama da Ammi suka fita, Bazla ta rakasu har mota tana qara yi mishi godiya.


——————————————


Da sallama dauke a bakinsa ya shiga cikin dakin mahaifiyar tasa, kansa a kasa yana cigaba da takawa cikeda nutsuwarsa ya qarasa kusada matar da take zaune akan kujera irinta alfarma cikin tsadadden atamfar ta mai matuqar daukar ido tana aiki da tsadaddar wayarta.


Dago kanta tayi tana kallon yaron nata cikeda so da qauna da kuma kulawa. Kallo daya zaka mata ka tabbatar da cewa itace mahaifiyarsa, ta shafa kansa tana mai cewa “Kamal har kun dawo kenan, ya kuka baro Ammin taku?” gyara zamansa yayi yana me cewa “lafiya qalau muka barota mommy, tace a gaeshe ki”ya qarasa yana me sunkuyar da kansa, “Masha Allahu, ba tare kuka dawo da Hafsat bane? Kou a can ka barota?”Mommy ta karasa tana tambayarsa.”ta wuce dakinta tace tanada dan uzurine”.ya bata amsa.


Kallonsa tayi taga tamkar da alamun magana a bakinshi, ta gyara zamanta da kyau tana fuskantar yaron nata tace dashi “naga kamar bakinka da magana Kamal” qara sunkuyar da kanshi qasa yayi yana tunani ta yadda zai fara gaya mata.


Can dae ya sauke ajiyar zuciya yana qara yin qasa da kanshi yace”Mommy dama..dama…” “dama me Kamal?, kayi magana mana ka tsaya kana kame kame, ko akwae wata matsala ne?” girgiza kansa yayi alamar a’a ya bude baki yana mai sosa kansa yace”Mommy dama nace idan ba damuwa Dan Allah ko zakiyiwa Daddy magana, amm, aje a nemamin auren Bazla?”ya qarasa da kame kame yana me kara sunkuyar da kansa qasa.


Murmushi tayi saboda batayi zaton wannan ne abunda ya kasa gaya mata ba. Kallonsa ta qarayi tana murmushi tace”dama akan wannan ne kake ta wani kame kame, wannan ae abun farinciki ne” ta qarasa fada tana me daukar wayarta, dagowa tayi ta sake ce mishi”amma dama ka gaya mata ko kuwa?”girgiza kansa yayi, “to ae ba damuwa, bari in sha Allahu yanzu zan kira Ammi muyi maganar kafin Daddyn naka ya dawo se na gaya masa”ta fada tana me kara wayar a kunnenta tana me yin sallama. Tashi yayi ya fita domin ya bata wuri.


_____________________________


Fitowa Ammi tayi tana me murmushi tana cewa”in sha Allahu hakan za’ayi, Allah dai ya tabbatar mana da alkhairi” sukayi sallama kowa yana me farinciki da wannan abun.


Kallonta Bazla tayi tana cewa”Ammi ke dawa kike wannan wayar kinata murmushi haka?” Kallonta tayi sannan tace “nida Mommyn ku ce”ta karasa tana me zama akan kujera.

______________________________