MAI KWAƊAYI

40

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```


``` NAFISAT ALIYU SASAAL```



 ```Page 40```


________kai tsaye Asibitin Dr.Aryaan suka wuce da ita,baƙaramin azaba Halima tasha ba,saboda targaɗen data samu aƙafa da goshinta da'akayiwa dressing,saboda yankan bai shiga sosai ba.


Aminu na cikin tashin hankalin ihun da Halima takeyi kiran Faisal ya shigo mai. Jiki na rawa yaɗaga daƙyar ya iya yariƙe tarin maganganun bakinshi yafara gaishe shi,sannan ya ɗora da bayanin duk abinda ya faru, sai dai bai san Salim ba balle yagaya mishi ƙanin Mubeena ne.


Baƙaramin ruɗewa Faisal yayi ba kan abubuwa uku, yaushe Maysarah ya dawo?ta yaya wani a waje zaisamu key ɗin sashen da Halima take? Sannan Maysarah zai ƙara tabbatar da kuɗin daya cinye tunda ga ƴar Halime atare da shi.

Banda yasan dawowar shi batareda kammala abinda yakaishi zai haifar mai da gagarumin matsalaba da babu abinda zai hanashi dawowa.



 Katse kiran Faisal yayi,yana juya mobile ɗin a hannunshi yarasa wazai fara kira,Mubeena,ko Dr.Aryaan ko Maysarah.

Shawaran yafara kiran Mubeena zuciyarshi tabashi, yafara jin tayaya wani yasamu key ɗin sashen da Halima take.



Barcinta tasha har da minshari dayake ranar Sunday ne basu farka ba sai lokacin da sukaga dama,sai bayan sunyi Breakfast ta ɗauko wayanta don kiran Salim taji yaya suka ƙare da Halima.

A nan taga rurutun Miss called ɗin Mijinta,gabanta ne yafaɗi "to ko dai ansamu matsalane" ta faɗa tana ƙoƙarin kiranshi.

"Babu abinda bayanin Faisal yasata sai ƙullewar ciki"wallahi Dear Salim ne fa,ya ganta awajena shine fa yace idan ban bashi key ɗin wajenta ba zai tona mana asiri,don Allah kabawa Maysarah haƙuri". Ta ƙarasa faɗa tana fashewa da kuka.

"Mubeena! Ni zaki ciwa amana,anya kinama da hankali kuwa,kina goyon bayan bunsurun ƙaninki ya haikewa ƙaramar yarinya kamar Halima, bayan kinsan wannan ne dalilin dayasa na rabota da Kakarta, ohh sakamakon da zakiyiwa Salmanu da Halime kenan right? Wallahi ko Maysarah zai kashe Salim bazance komai ba,mahaukaciya kawai!" kafin tasamu zarrar yin magana ya kashe kiran.

Kuka tasa mai ƙarfi tana nufar hanyar toilet saboda gudawan daya taho mata.


★kai tsaye gidan Mahaifinshi aka wuce dashi. Goggo kamar ta goyashi,ɗan rungumarta yayi da sumba a goshi,kafin ya wuce sashen da aka ware mai.


Wanka yayi ya shirya cikin ƙananun kayan Louis Vuitton navy blue,fuskarshi na nan kamar kullum ba sauyi,amma duk da haka sai dai Goggo ta lura da ɓacin ran dayake ciki,bata ɓata yawun bakinta wajen jin damuwarshi ba,don tasan ba faɗa zaiyiba.


A ɓangarenta yayi Breakfast tare da su Mom Fahima da Sumayya da gulma ya shigo da su.

A ɗan takaice yataya Sumayya murna aurenta,tare dayiwa Mom Fahima Allah yasanya alkhairi.

Ƙwalla kwance a idanuwan Sumayya take amsa mai saboda kyawun dataga yaƙara mata,gashi kai tsaye yanuna bai damu da auren da zatayi ba.


A Parlourn ya bar su cikin takunshi mai tafiya da nutsuwar dubban matan da suka san kan su.

Gidan Faisal aka fara biyawa da shi ya ɗauki abinda zai ɗauka kafin su wuce gidanshi. Duk da tsarin da sukayiwa gidan bai yimai ba tun da ba haka yanuna yanaso ba,da wannan ɓacin ran yawuce Asibiti.



Barcin wahala ne ya ɗauke Halima,Aminu ne yake ta zarya akanta,sai Faisal da baya cikakken hour bai kira ba.

A haka Maysarah da sojojin dake tsaron lafiyar shi suka shigo Asibitin.


Ajiyar zuciya Aminu ya sauke lokacin daya hango su,yanajin inama Maysarah yayi aure ya ɗauke Halima ta koma gidanshi,"ko kuma ya aure ba tunda kai Mahaukaci ne"ya bawa kanshi amsa yana gumtse murmushin dake ƙoƙarin kufcemai.


Aminu ne yayi mishi jagora har ɗakin da take ciki,ganin yanda kanta yake a buɗe ga dogon wandon jikinta duk yayi sama har anaganin cinyoyinta, sai ranshi yaƙara ɓaci yana kuma jin hukuncin dayayiwa Salim kamar yayi kaɗan,kallo fuskar Aminu kawai yayi yabar ɗakin dasauri.


Zama yayi yana ƙare mata kallo da idanuwanshi masu kaifin gaske yana tantance shekarunta. A hankali ta fara buɗe idanuwanta,kafin ta buɗe su fes acikin nashi idanuwan da ɗai-ɗaikun mutane ne ke iya jurewa kallon su, ihu ta kurma tana banbance tsananin girman shi zaune agaban godonta da ɗaurarren fuskarshi da babu ɗigon fara'a....✍🏻