MAI KWAƊAYI

41

by @nafisatusasaal01


💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

``` NAFISAT ALIYU SASAAL```



 ```Page 41```


________"Mallam Aminu! Uncle Faisal! Inna!Ku zo ga wani ƙaton mutum a ɗakina, please ku zo dan Allah na roƙe ku" ta faɗa tana rufe fuskarta da tafukan hannayenta.


Mamaki da wautar yarinyar yake gani muraran,kuma har lokacin bai motsaba kuma bai daina kallonta ba.


"Hey" ya faɗa yana ƙoƙarin ɓoye murmushi wautarta dake neman suɓucewa laɓɓanshi.

Tanajin girman muryarshi daya banbanta dana sauran maza manya data sani sai taƙara sakin wani ihun.


"Ohh ni fa ba dodo bane nine Maysarah da kike nema ne,yanzu gani maiyasa kike nemana?" ya faɗa yana rage girman idanuwanshi a kanta dama muryarshi shi daya bata tsoro.

"Maysarah? Shine wannan ƙaton mutumin amma Uncle Faisal yace ƙaninshi ne,how comes?" Ta faɗa azuciyarta. A hankali ta ware dogayen yatsunta guda biyu data rufe fuskarta da shi kaɗan, tananan take ƙare mai kallo.yana iya hango ƙwayar idonta ɗayan da take satar kallon shi da shi,duk da ɗan kaɗanne ya bayyana.


"If you have something to say, why don't you just say it,ki daina kallona da small eye ɗin ki." Dasauri ta mayar da yatsunta ta haɗe,tsoro da kunyar kanta na kamata.


Da shi ma'abocin dariya ne babu abinda zai hanashi darawa,"yarinya ƙarama kina leƙe fuska mutane" ya faɗa yana miƙewa saboda murmushi dake neman ƙwacewa fuskarshi.


Yana juya baya ta ƙara ware yatsunta wannan karon dukka ta ware tana bin buɗaɗɗen bayanshi da kallo,har ya kai baƙin ƙofa yaƙara juyowa kawai don yaga yaya zatayi saboda yasan bayanshi take kallo,dasauri taƙara rufe fuskarta,tana sakin ƙaramin dariyar kunyar ƙara kamatan dayayi.


Yana barin ɗakin fuskarshi ya koma yanda yake,kai tsaye baza'ace Maysarah baya magana ba sai dai bashida surutu musamman kan abinda bai shafe shi ba, rashin fara'a kuma halittar shi ce,jin kai da izza kuma ya sameshi ne ta zuri'ar daya taso da kuma yanayin aikinshi da basason raini.




Gaba ɗaya hidimar Biki da ruɗewar bayyanar Maysarah cikin familyn ya mantar da su Uncle Ghali Salim,dama kuma ba ma'abocin zaman gida bane.


Bayan sun gama Dinner gaba ɗayan su a sashen Goggo. Goggo take tambayar ina Faisal da Salim bata gansu ba.

Mubeena ta ƙasan idonta da yayi zuru-zuru tsabar fargaban da take ciki, ta ke kallon gefen da Maysarah yake idanuwanshi a kulle kamar mai barci,amma yanajin komai,kuma baimotsaba.

Ga amsar inda Salim yake Mubeena tasani amma ko motar giya takesha kullum bata isa ta faɗa ba, don tasan kwanan zance.


"Faisal in sha Allah da daddaren nan zai sauka" Uncle Suraj yafaɗa yana kallon Mubeena.


"Shifa Muhammadu( Salim)? Ɗan juma(Uncle Ghali) naji kayi shiru ko ya tafi yawon daya saba"


"A'a Goggo ɗinkunan su ya tafi karɓowa na hidimar Biki" Uncle Ghali yafaɗa kamar dagaske.


Gama hirar su baifi da Minti biyar ba Faisal ya shigo,sai dai kamar abayan juna suke,Salim shima ya shigo da wando a hannu fuskarshi a kumbure kamar wanda yayi mummunan accident.


"Meye wannan Salim accident kasamu maiyasamu gabanka kake tafiya haka" Mommyn su Mubeena ta faɗa cikin kuka.


Dukka hankalin su sai ya koma kan Salim gabanshi nannaɗe da bandeji,a sace Mubeena dake kuka ta ƙara kallon Inda Maysarah yake ko motsawa baiyi ba,kamar ma bai san maiyake faruwa ba,shima Faisal a sacen yake kallon fuskar Maysarah da babu wanda zai ce yanada hannu ko sani kan halin da Salim ɗin yake ciki.


Ganin Goggo ta matsa da tambayoyin dake neman fito da ainihin Laifin Salim ɗin muraran sai suka wayance suka bar gidan dukkan su har Mubeena,tunda dama Salim ɗin baiyi magana sai kuka.


"Anya Goggo ba garin kwashe-kwashen Salim bane yasamu wannan matsalar" Abdulnaseer ya faɗa da alhini a fuskarshi.

"Dole mana amma dayake Ɗan juma gwanin son ƴaƴane ai gashi yana ƙoƙarin ɓoye laifin shi,har da guduwa da shi can su suka sani babu wanda zai samun bawan jini" Goggo tafaɗa cikin ƙarfin hali,saboda ganin Salim acikin yanayin dayazo mu su abin tausayi ne.


Shi dai Uncle Suraj daga Allah ya kiyaye bai ƙaracewa komai ba shida Iyalanshi da dama can haushin su Uncle Ghalin sukeji.


Mom Fahima da Sumayya basa nan suma balle su tofa,


"Ohh Alhaji Maysarah dunkum,ko jaje aika yimusu tunda kana jin su ko?"


Goggo ta faɗa tana dariyar halinshi.

"Ai naga barci ma yake yi Goggo"Uncle Suraj yafaɗa yanajin daɗin barcin da Maysarah yakeyi,a tunanin shi da idonshi biyu da bayan su Uncle zaibi saboda Yusra da suke zargin yafiso akan Maryam.


"Bakasan Maysarah ba kenan Sirajo wallahi idanuwanshi biyu baƙin hali ne kawai" 

 

Duk yana jin su,kuma still bai motsa ba har kowa yabar parlourn sai Faisal daya ƙara matsowa daf da shi,saboda shima yasan idon shi biyu.


Kamar daga Sama yaji Maysarah na gaishe shi,saboda dama su suke zubar da kansu saboda kwaɗayi abun duniya, amma Maysarah babu wanda baya girmamawa acikin su.


Kasa amsawa yayi,saboda kunyar kan shi dayake ji.

" Haƙuri ya fara ba shi,kafin ya ɗora da godiyar abunda yayiwa Halima"

"Wacece asalin Mamanta maiyasa kuma take son ganina" ya faɗa yana zama da kyau haɗe da kafe Faisal da ido.


Wa su lokutan mutane basa fasa halin su musamman mutanen da suka ɗauki ƙarya amatsayin mafitar su,bai ɓoye mishi asalin labarin Halime ba amma sai ya ƙara jaddadamishi ya kashewa Halime waccen maƙudan kuɗin,saboda alamu dayake ganin kamar wani can daban ne yake taimakawa Halime ba Maysarah ba, Bala ne kawai yayi mata ƙarya da sunan Maysarah.


Tsaf yake kallonshi,tare da ajjiyeshi amatsayin daya zaɓawa kanshi acikin zuciyar shi.


"Aminu Driver na da Iyali"


Cikin ƙoƙarin ɓoye fargabarshi yace "eh"


"Ina suke?"


"I think suna bayan garin nan"


"Ka sanar dashi ina son su zuwa gobe, bani number Kakarta" kai tsaye tsadadden wayarshi ya miƙa mai.


Kamar Faisal zai saki kuka haka yasa mishi number Inna.


Daga haka ya miƙe yayimishi sallama har ya ɓacewa ganin Faisal bai janye idanuwanshi daga kan bayanshi ba,duk da yanajin ya wanke kanshi amma duk da haka yakasa jin shi dai-dai,miƙewa yayi yana neman layin Aminu don zuwa Asibiti ganin Halima.




Har bayan tafiyar Maysarah bataga Aminu ba, sai Nurse da take kula da ita,zuwa yamma liƙis a fitar da ita da taimakon Nurse ɗin da take kula da ita. wani Asibitin aka ƙara kaita wanda yafi waccen kyau da alama kuma zaifishi tsada,sai lokacin taga Aminu har faɗawa yayi saboda zirga-zirga.


Daganan bata ƙara ganin kowa ba har barci ya ɗauketa bayan Nurse tayi dabarar yimata wanka, tare da kawo mata lafiyayyen Dinner.



Faisal kamar zai fashe lokacin da ma'aikan Asibitin suka hanashi ganin Halima, acewar su yanayin da take ciki bata buƙatar ganin kowa,yasan aikin Maysarah ne kuma bashi da zarrar kiranshi yayi ƙorafi, jiki a saɓule Aminu ya kaishi gidan su Mubeena,kar suyi zargin wani abun daban.sai bayan tafiyar Aminu Faisal ya tuna da saƙon Maysarah,dole wayan Aminun yakira ya sanar dashi. A ɓangaren Aminu kuwa bakinshi kamar zai yage saboda murna,yasan dole tukuici Oga Maysarah zai yi mai.



Lokacin da Inna ta gama sauraron roƙon Goggo fargaba kar dai Halima mutuwa tayi suke ɓoyemata, shiyasa kai tsaye ta amince zata biyo Bala su taho idan Allah ya kaimu.

Sallama sukayi da Inna,Goggo ta miƙamai wayan tana jiran ƙarin bayanin wayar daya sata tayi batare da tasan tushen zancen ba.

" Gobe zakiji komai"

Ya faɗa yana ƙoƙarin fita.

"To Allah yakaimu" don tasan ko ta nemi ƙarin bayani ba yi mata zai yi ba.


★Misalin ƙarfe goma Inna da Bala suka shigo Abuja,kai tsaye danƙareren gidan Maysarah Bala ya wuce da su,basu sha wahalar ganewa ba saboda wayan dayakeyi da Aminu.


Idon Inna kamar zai faɗo ƙasa tanajiran taga ta ina Halimarta zata ɓullo,daƙyar ta iya taɓa abin karin da'aka kawomusu ranta fal tsoron daular da aka kawota.


Sai da suka huta sosai Maysarah yazo gaisheta,kasa kallonshi Inna tayi ta ɗurkushe aƙasa,zuciyarta kamar zai faɗo. Ganin kamar ganinshi na takurata yasa ya miƙe don jiran Goggo taƙaraso ko zata saki ranta,a sace Inna tabi bayan shi da kallo tana sakin ajiyar zuciyan tashin dayayi.



Bayan wasu mintuna suka ƙara shigowa da Goggo,daƙyar Goggo tasa Inna ta koma kan haɗaɗɗu kujerun parlourn. Bayan sun ƙara gaisawa Goggo ta buƙaci jin komai daga bakin Inna,saboda ɗan guntun bayanin da Maysarah yayi mata kafin ƙarasowarta


Tambayarta tarihin Halime abune mai tsananin ciwo acikin ranta amma bata yanda zata yi.


Da kuka ta ƙarasa Goggo na tayata, idanuwan Maysarah kaɗawa sukayi sosai.


"Halime ta,ta tafi da burin ganin Maysarah tayi mishi godiya amma Allah bai nufa ba,sai dai Bala yayi mata alƙawarin kai ɗiyarta Halima ko shi da kanshi idan ya samu damar ganinshi zai sanar da shi".ta faɗa cikin ɗacin zuciya fuskar Halime da burinkanta dake dawowa Inna a rai.


"Ga Maysarah nan agabanki,amma sam bamusan tsananin halin da ƴarki ta shiga har yakai haka ba,Bala kuma Allah Yasaka mai da alkhairi ya cika ɗan halak. Da wannan muke neman yafiyarki tare da Inganta rayuwar abinda Halime ta bari."


Goggo ta faɗa zuciyarta da tsananin tausayin Inna.



Kuɗi masu yawa Maysarah daya kasa magana yaje ya shigo da su,ya ajjiye agaban Goggo,ita kuma ta miƙa su gaban Inna dake gefenta,sannan cikin taushin murya Goggo tayi mata bayanin shawarar da sukayi da Maysarah na ta dawo Abuja da zama cikin gidan da yanzu take ciki ga Aminu driver da iyalanshi da zasu zauna tare.


Girgiza kai tayi hawayenta na ƙara gudu.

" Wallahi bazan iya karɓar ko sisin ku ba, kuma bazan iya kashe aure na nadawo nan ba,don nasan dangin mijinta baza su lamunce ba, ko da shi ya amince min,dalilin haka kuma Babangida zaiji ba daɗi.amma don Allah ga Halima nan inason burin Halime nayin ilimi da samun rayuwa mai inganci ya cika a kanta,don Allah na roƙe ku tunda kunada hali ku cika mata wannan burin" ta faɗa tana durƙushewa.


Kuka Goggo ta ƙara fashewa da shi Maysarah shima runtse idanuwanshi yayi yana datse kiran dayayiwa Mahaifinshi don yaji komai.....✍🏻


Nayi page mai tsaho yau so naga comments idan kunji daɗi