MAI KWAƊAYI

42

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```


``` NAFISAT ALIYU SASAAL```



 ```Page 42```


________Ɗakyar Inna ta tsagaita kukanta, amma duk da haka ranta sam ba daɗi.


"nayi miki alƙawari har bayan raina ƴaƴana za su kula miki da Halima"Goggo ta faɗa da sigar lallashi. Batasan Halima amma sai taji tana sonta saboda duk yaron daya fito daga tsatson irin su Inna na rashin kwaɗayin abun wani abun sone ga kowa. Saboda mafi akasirin ƙiyayaya nafarawane daga sanya ido da kwaɗayi akan abinda ba naka ba.



Sai da sukayi sallar azahar sannan dukkan su suka bar gidan zuwa duba Halima kafin Inna ta tafi. Kamar Inna tayi tsuntsuwa ta ganta agaban Halima haka takeji,tunda ko waya Faisal baya bari suyi, acewarshi kar hankalin Halima ya tashi taƙi mayar da hankali kan karatunta.



Ranta ba daɗi tayi Breakfast, sai dai har ƙarfe sha biyu na rana yawuce bataga kowa ba,sai Nurse ɗin dake leƙota jefi-jefi ko tana buƙatar wani abun,bayan tayi sallar azahar barci ya ɗauke ranta ba daɗi.



Har su Inna suka shigo barcinta takeyi dogon cushion ɗin dake ɗakin Goggo da Maysarah suka zauna bayan sun leƙa cute face ɗinta da barci yaƙarawa kyau.



Inna abakin gadon ta zauna cikin jin nauyi,saboda kunyar su Goggo da takeji.


A hankali ta buɗe idanuwanta sai cikin na Inna, ƙoƙarin zama tafarayi"Inna dagaske kece ko mafarki nakeyi,ya ya akayi kikaji kiran dana miki jiya"

Ta faɗa tana kamo hannun Inna da tsananin farin ciki.


"Gaisuwar kenan Halima"

Inna ta faɗa da dariya a fuskarta.


" Ohh na manta, Inna ina wuni ya hanya" ta faɗa tana rufe fuskarta.


"Lafiya lau Halima,ga Haji..."bata bari Inna ta ƙarasaba tafara bata labarin daya maƙalemata a wuya tun jiya,cikin sanyinta daya haɗe da zumuɗi tace."Inna kinga wani dogon mutum jiya jikinshi a murɗe kamar jikin masuyin dakon nan na kasuwa, idanuwanshi kamar zai cinye mutane muryarshi abun tsoro,kin san wai me yace?"

Inna da kunyar surutun Halima ya gama kamata ta girgiza kai alamar a'a duk da bata gano wa Haliman take nufi ba.


"Ohh ni fa ba dodo bane nine Maysarah da kike nema,yanzu gani mai yasa kike nemana" ta faɗa da kwaikwayar muryarshi,haɗe da kyalkyala dariyarta na ƙuruciya da nishaɗin ganin Innar akusa da ita.


Kunya kamar ya nutsar da Inna amma labarin Halima baƙaramin dariya ya bata ba amma ba halin darawa.

Dariyar Goggo dake sauraron Halima ne yadawo da hankalin Halima kan su,tana juyawa kuwa idanuwanta ya sauka cikin na shi. Ihu tasa iya ƙarfinta tana ƙanƙanme Inna haɗe da kulle idanuwanta.


Wannan karon itama Innar dariya tasa.

Tashi yayi ya nufi hanyar barin ɗakin"dawo mana Alhaji Maysarah yau Allah yanuna mun dai-dai da kai,ashe da ƴan dako kaya kake kama bansaniba.." bai ƙarasajin tsiyar Goggo ba yabar ɗakin.

Ƙaramin murmushi yasaki don Goggo batayi ƙarya ba,yarinya kamar aljana,ya faɗa aranshi.


Baƙaramin nishaɗi Goggo ta samu da wawtar Halima ba saboda dama can Halima abun so ce ga duk wanda ya zauna da ita.


Sai bayan sunyi sallar la'asar suka fito,Inna tayiwa Halima dabarar anjima zata dawo,da haka sukayi sallama.


Inna bata tambayi asalin abinda ya samu Halima ba kamar yanda suma basu gayamata takamaiman abinda yasameta ba,sun dai cemata faɗuwa tayi.


Lafiyayyan mota ba wanda suka zo dashi ba Maysarah yasa akai Inna aciki da sabon driver mai ƙaramin shekaru ba kamar Bala da shekaru shi sun fara ja ba, kuɗi mai yawa ya ajjiyewa Inna agefenta bayan motar yaɗan fara tafiya. Kuka Inna ta fashe da shi tana kallon kuɗin haɗe da tunowa da Halime da Halima alokaci ɗaya,a can sukabar Bala sai washe gari zai taho. Itama taso kwana amma bada niyyar haka tazo ba don gidan biki tacewa Baba Shehu zataje gudun zargi,saboda kamar raƙumi da akala yanzu ya koma da ƴan uwanshi,darajar Babangida ne kawai yake zaunar da ita,shima kuma ya kusayin aure ta tattara abunta ta koma ƙauye 



🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂


Kai tsaye Asibiti suka kai Salim,nan ma wajen dubashi baƙaramin azaba yasha ba,yanaji aranshi shi da Mace har abada ko da ta aure ce.


Bayan kowa ya fita ya rage dagashi sai Mubeena da taƙi tafiya,ta ƙara matsowa kusa dashi cikin ɗan ɗaga murya da fushi ke bayyane aciki tace" wallahi zan gayawa Daddy Maysarah ne yayi maka haka,saboda kawai kaje zance" ta faɗa cikin tsananin son zuciyarta,tunda idan da gaske zance yaje,menene ya jefashi a halin dayake ciki?


Dasauri ya rufe mata baki hannunshi na rawa"a'a Sis Mubee,kinsan waye Maysarah kuwa? to menene abinda Daddy zai iya yi,ko kinmanta da arziƙinshi muke taƙama,ga Yusra ta ƙwallafa mishi rai,ke kanki Faisal zai iya rabuwa dake,kiyi tunani" ya faɗa yana sakin wahallen kukan azabar dayasha da wanda yake kan sha.


Ranta aɓace ta fara gyara ɗan mayafin dayake saƙale akafaɗarta don tafiya gida, knocking sukaji anayi dasauri Salim yakwanta ya rufe idanuwanshi jikinshi na rawa da Addu'ar Allah Ya sa ba Maysarah bane.


Fuskar Faisal a ɗan kame ya shigo,yayiwa Mubeena yamai jiki sannan yaɗan zauna batare da wani maganar ya shiga tsakaninsu ba. Jin kai da son karta bishi gida yasa tayi fuska yatafi shikaɗai, hakan kuwa datayi yayi matuƙar yiwa Faisal ciwo. Shima nashi gidan iyayen ya wuce,da wassafa irin hukuncin dazai mata


★washe gari da Bala zai tafi Goggo ta haɗamai alkhairi maiyawa ya kaiwa Inna shima ta bashi nashi kyautan.da Maysarah ya tashi bashi nashi tukuicin kuka Bala yasa tsabar farin ciki,yanajin lokaci yayi dazai bar aikin bauta aƙarƙashin su Faisal ya kama sana'a.


Matar Aminu driver kanta kamar zai fashe lokacin data tabbatar da zamanta a sashen da Maysarah ya ware musu. A ranar aka sallamo Halima. Tayi tunanin gidan Faisal zata ƙara komawa amma sai taga akaita gidan da lafiyayyan part ɗin yafi waccan komai, taji daɗin sauyin da kuma samun nutsuwa aranta,duk da rashin jindaɗin gano wayon da Inna tayi mata don da ƙunci ta kwana,amma duk da haka rashin ganin Maysarah yafi komai yimata daɗi.


Aminu da Matarshi da ƴar su ɗaya data fara tasawa sannu suke ta yi mata kamar zasu goyata tsabar kulawa. A daddafe tayi wanda sannan ta kwanta tana sakin ajjiyar zuciya,a take kuma tunani Maysarah yafaɗo mata,rufe fuskarta tayi tana dariya dafatan Allah yasa karta ƙara ganinshi.




Lefen Sumayya ne ya girgiza zuciyar alhalin su Faisal tare da ƙara ɗammarar aurar mai kuɗin dayafi na nasu iyayen,kowa sai ya koma bindiddigi suwaye iyayen Mijin sumayya aikin maiyake yi,Mom Fahima kanta kamar zai fashe tabbas surukanta sun fitar da ita kunya, a take kuma taji tana tsananin son auren, nan da nan kowa ya fara jan Sumayya ajiki,waɗanda basu wani shiryawa bikin ba sai suka fara harama ko suma zasu samu nasu rabon acikin Abokanan ango,pre wedding ɗin su ma baƙaramin burge dangi yayiba ga Angonta kyakkyawa amma ba irin dai Maysarah da suke buri ba.


Lefen Sumayya da bayyanar hotunan su da haɗaɗɗen Angonta bai ƙara komai aran Yusrah da Maryam ba sai ƙara shiryawa mallakar Maysarah da kota halin yaya, yanda lefen su da komai nasu sai ya kafa tarihi akaf ahalinsu.


Wannan shine burin kowaccen su.


Gadan-gadan biki ya ɗau zafi Maysarah Da Mahaifinshi da Mom Fahima manya kuɗaɗe suka zuba don yiwa Sumayya kara, haka kowanni ɓangare na ƙoƙarin ganin shine abin kyau da kallo a gagarumin bikin Sumayya da kowa a baya yakeyiwa Mom Fahima shaguɓen bamai kuɗi bane....✍🏻