43
💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔
( shi ya san gidan mai rowa)
```By```
``` NAFISAT ALIYU SASAAL```
```Page 43```
________Duk wannan bidirin da'akeyi Salim na gadon Asibiti,ko da ba Asibitin yakeba babu abinda zaiyi gigin fitar dashi wajen bikin,saboda tsoron Maysarah dayakeji yafi na kunyar Iyayenshi,duk da har lokacin babu wanda acikin su ya tambayi asalin musabbabin faruwa lamarin,sai Goggo da duk zuwa sai ta tambayeshi,amma baya bata amsa sai kuka,dole haka tagaji ta ƙyaleshi.
A ɓangaren Halima ma batasan anayiba,hankalinta a kwance yake, ga farin cikin samun damar waya da Innarta.ga kulawar Aunty Rahina(matar Aminu) da take samu don macece data iya morar arziƙi babu ruwanta da girman kai.
★Washe gari da Faisal yazo baƙaramin farin cikin yaji ba ganin abinda Maysarah yayiwa Halima na sauyin kyakkyawan wajen da baiyi tunani ba. Yana ganinta yaji haushin komai ya bar ranshi. Yarasa dalili baya iyajin haushin Halima.
Sai dare yabar gidan ranshi fari fes da labaran dayasha awajenta.
Ɗaurin auren Sumayya aka farayi kafin shagulgulan dasuka shirya wanda yasamu halattar dubban al-umma, Abokanan arziƙi,da dangi baki ɗaya,har da masu zuwa ganin ƙwaƙwafin mai zaije ya dawo.
Anjon Sumayya yayi kyau ba kaɗan ba,ya kuma yi rabon kuɗin daya ƙara haukata ƙwaɗayayyun irin su Uncle Ghali.
Idan na Maimata irin kyawun da Maysarah yayi cikin shadda mai taushi da tsadar gaske ƙyauyancine.yayi kyau irin kyan dake tarwatsa zuciyar maƙiyi.
Bayan an gama É—aurin aure akafara hotuna cikin birgewa da wayewar daya ratsa kowannen su.
"Wata bata auren mijin wata" shine furucin daya suɓucewa laɓɓan Sumayya lokacin data hangi Maysarah Yusrah na nane agefenshi. Tsarin shaiɗan ta fara nema da kuma tuba ga Ubangijinta a cikin zuciyarta. Tare da ƙara godewa ni'imar Allah dayayi mata.
kwalliyar Maryam yafi na Yusrah kyau da tsari, don haka cikin tsokana cousin ɗin su dake ɗaukar su yace Maryam ta matso don tafi Yusrah dacewa da salon hoton dayake son ɗauka,duk Maysarah dake ƙoƙarin barin wajen baisan sunayi ba,don ko Yusrah dake nane agefenshi tuntuni bai lura da ita ba,duk hotunan yawanci yana gaisawa da dangine suke ɗaukarshi.
Cikin tafiyar daya dace da shafaffen cikinta tamatso gefen Maysarah da kyau dai-dai kuma lokacin daya juyo domin barin wajen aka ɗauke su. Yusrah da anata hotunan babu wanda Maysarah ya juyo dakyau sai taji kamar zata fashe,ko kallon arziƙi bata samu daga Maryam da takejin kamar ta kasheta ba.
Agajiye ya nufi gidan da mutuniyarshi take domin hutawa.
Zaman ciki ne ya isheta don haka ta fito ɗan zagayawa tunda ƙafarta yayi sauƙi sosai.
Tsakanin inda take da parking lot akwai tazara sosai,don haka bata lura da shigowar motarshi ba tana can tunanin shirmenta da baya ƙarewa.
Daga ɗan nesa ta hango shi kuma tsaf ta gane shi ,dasauri tafara ƙoƙarin komawa ciki,saboda batason ganin fuskarshi.
Tafiyarta ba sauri sosai amma haka take ƙoƙarin ganin ta tsere mai.
Tana daf da shiga parlourn,taji husky voice ɗin shi dayaƙara buɗewa duk don yaƙara tsoratar da ita yace."Hey Haleema tsaya anan"ya faɗa da salon Hausar shi mai birgewa, da ƙarfin saurin da batasan zata iya ba ta faɗa parlour tana sakin ajiyar zuciya.
Murmushine ya ƙwace mai bai taɓa ganin yarinya mara wayo ba irinta ba, don ya ga yaya zata ƙarayi sai ya fasa wucewa ɓangarenshi ya biyo bayanta. Aminu daya tuƙo Maysarah ƙin ƙarasowa yayi yakoma wajen motar yana dariyar wawtar Halima.
Wai"Hey Haleema tsaya anan, ji wani Hausa da wani jikinshi kamar mai cin duwatsu daga ganin wannan mugu ne nasan da Mammyna tasan haka yake da ko taimakon shi bazata nema ba balle taso ganin shi." Ta faɗa tana taɓe ɗan mitsilin bakinta. ɗago kan dazatayi idanuwanta suka sauka akanshi,ɓaƙaramin kyau yayi mata ba amma wannan kallo nashi ne bata so.
Dasauri tamiƙe akan ƙafafun da bata iya takawa dakyau tana ihun neman ceto dasauri Aunty Rahina dake haɗa lunch a kitchen ta fito,sai dai babu kowa awajen sai Halima dake ihu. Sauyin ƙamshin wajen yasa Aunty Rahina yarda da wani ne yabiyota.
Bata ƙara gigin fitowa parlourn gidan ba,balle tsautsayi yasa ta ganshi, Abinci sai dai akai mata ɗaki,duk da Aunty Rahina tace mata ba zuwa zai yi ba ita kanta ko saninshi batayiba amma sam Halima ƙin yarda tayi. Har wayewar gari bata ƙara fitowa ba
★ Da safe Maysarah yabar ƙasar batare da sanin kowa ba,sai Goggo daya sanar ta waya,itama tana ƙoƙarin tambayarshi Halima mutuniyarshi ya katse kiran.
Maryam dake gefenta hawaye ne ya cika idanuwanta,haushi da takaicin uban kuÉ—aÉ—en da ta zuba wajen siyan surutar dazata sa ranar na kamata.
A ɓangaren Yusra zumuɗin dare yayi ne aranta tana wassafa shigar da zatayi da turarukan mallakar data siya dole Maysarah ya yaba yakuma tantanceta a matsayin matar aurenshi ...