MAI KWAƊAYI

44

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

``` NAFISAT ALIYU SASAAL```



 ```Page 44```


________Dinner Sumayya ya ƙayatar kuma Dollars sunyi kuka,amma duk wannan bidirin banda Yusrah da sai a lokacin tasan da tafiyar Maysarah.


Ƙunci da gumi duk ya ɓata kyan da tayi,kuma dagasken tayi kyau sai dai Maysarah da tayiwa yayi mata nisa.


Shagulgulan bikin Sumayya da tafkeken gidan da aka kaita kafin su bar ƙasar abun birgewane da kuma ƙarawa mai burin mallakar Miji ɗan gayu mai Naira a hannu ƙara ɗaukar harama da zage damtse.


A cikin Abokanan Ango aka samu wanda ya liƙewa Maryam,ba don taso ba tabashi numbernta da sunan zata rage zafi dashi don baiyi mata kala da irin Mazan da take burin aure ba, tasan kuma Mahaifinta bazai taɓa son wanda ba hamshaƙi ba ya aureta.



Bayan biki jama'a suka watse kowa ya koma muhallinshi, ciki harda Mubeena da Faisal.

Dawowarta gida yasa ta fuskanci girman laifin da tayiwa Faisal,don gaba ɗaya ya koma mata wani Faisal ɗin daban. kamar ba Faisal ɗinta mai tsananin sonta ba.



Tsadadden Makaranta da abun hawa mai tsadan gaske Maysarah ya canzawa Halima,idan tace hakan bai birgeta tayi ƙarya.



A wasu lokutan acikin daƙiƙu yana yawan tuna Halima amma hakan bashi da wani tasiri ko Ma'ana a rayuwarshi domin kallon yarinya ƙarama kuma sha-sha yakeyi mata.


Rayuwa ya miƙa kowa na rayuwarshi dai-dai da wadatar shi.


Cikin shekara ɗaya Halima ta ƙara tsaho da kyau kamar shekarunta sun haura hakan,duk ƙarshen watan duniya sai Aminu ya kaita ta gaishe da Inna,haka duk ƙarshen sati sai yakaita ta yinawar Goggo cikin ikon Allah bata taɓa katari da wani agidan ba harta dawo sai Mom Fahima,itama kuma ganin farko da tayiwa Haliman taji ta birgeta,amma dayake ba gwanar son Mutane su raɓe su bace sai take kamewa daga sakar mata fuska


Tsadaddun kayan da Haliman take sawa ne yasa hankalinta fara karkata kan su waye iyayen Halima?,duk yanda ta kaiga dakar cikin Goggo bata samu amsar komai ba. Kuma daga ranar Goggon ta dakatar da zuwan Halima gidan don bayanzu takeson su san wacece Halima ba har sai takai matakin da takeson bayyanar mu su da ita a matsayin dazai basu mamaki da kuma girgiza zuƙatan su.



Dakatar da zuwanta gidan Goggo sam baiyi mata daɗi ba,saboda nashaɗin da take samu idan taje gidan.


Akai-akai ake canzawa Halima kayan kwalliya da surutu na manyan Brand masu tsada haka atamfofinta duk na manya kuɗine,gyaran kai da sauran buƙatun ta akwai wacce Maysarah ya tanada take kai Halima lokaci zuwa lokaci. sai tazama ƴar hutun gaske,idanuwanta suka ƙara haske dakyau.


Shima Faisal duk tafiya sai yayi mata tsaraba.


Kamar yanda Maysarah yake tuna Halima lokaci zuwa lokaci haka itama take tunawa dashi,wasu lokutan kuma sai tayi ta mamakin duk wannan hidimar wanene yake yi mata tasan dai ba Faisal bane. Kai tsaye zuciyarta ta bata tabbacin Goggo ce,saboda sosai take sonta.



Sabuwar ɗaliba kuma ƙawar Halima ce ta fara sauya tunanin Halima daga na yara zuwa na manya. Itama sa'ar Halima ce,daga yanayin komai da take amfani dashi duk da a Makarantar mai tsada ne zakasan daga gidan da Naira ya zauna ta fito, sai da ƙawacen su ya miƙa sannan Shukara ta sanar da Halima ita Matar aure ce.

Da mamaki Halima take kallon Shukura lokacin da take sanar da ita ita fa Matar aure ce,"tayaya wani zai aure ki kina yarinya ƙarama haka Shukura" Halima ta faɗa da tsananin mamaki a fuskarta.


"Nice ƙarama ina da 14yrs ki kirani ƙarama" Shukara ta faɗa da jin haushin kiranta ƙarama da Halima tayi.


" To ai Mutum mai hankali babba bazaiyi aure da irinki ba, please are you serious?"


" Of course 🙄Ki bari gobe zansa shi ya kawo ni school da kanshi" ta faɗa cikin nishaɗin son Mijinta.


Hoto Halima tamayar da Shukura har suka tashi.

Ko da taje gida ta kasa yarda kamar Shukura tanada Miji.



★tsabar zumuɗin son ta tabbatar da zancen Shukura yasa a Mota tayi Breakfast.


Batafi 30minutes da zuwa ba su Shukura suka ƙaraso.


Tsoro mamaki da dariya ne yasa Halima dake hango buɗaɗɗen Mijin Shukara sanye da kakinshi rufe bakinta saboda dariyarta dake ƙoƙarin bayyana, ba kuma komai ta tuna ba sai Maysarah.


Shima Mijin Shukara kyakkyawan matashin Soldier ne da hutu ya huda.


Bai kai ga ƙaraso kusa da Halima ba ya koma idanuwanshi narke akan Shukura dake ƴar mitsila a gabanshi.


Da ɗan gudu Halima ta isa ga Shukura dake tahowa inda take cikin yauƙi da iyayi kamar ba

 ƴar 14yrs ba. Da zumuɗi da tarin tambayoyin maiyasa ta aurin irin Maysarah ta isa gareta.


"Allah!😳 Wannan babban mutumin ne Mijinki mai kama da Maysarah? God forbid wallahi bazan auri Miji tsoho ba.to wai ma maiya gani ajikinki yake sonki, har ya aureki?" Halima ta faɗa tana ƙarewa jikin Shukura da ƙirjinta dayaɗan fara fitowa kallo.


"Wasu irin silly questions ne haka" Shukura ta faɗa fuskarta ba fara'a. Tana jin haushin wannan gorin da mutane dayawa sukeyi mata.


Har suka wuce gida taƙi ƙallon Halima saboda haushin data bata na cewa batada abinda Mijinta zai sota dan shi.


Ranta ba daɗi da fushin da Shukura takeyi da ita ta dawo gida.


Sababbun Motoci da ƙarin sojojin da ta gani a gidan ne yasa tsoro ya ɗan kamata,jiki a mace driver da nutsuwa yaƙara shigar shi ya buɗe mata kofa.


Cikin sangarta daya hudata ta sauko,ɗan miƙa tayi da hamman da atake ya maƙale....


Manage please 🙏🏻