HAUWA KULU (The Village Girl)

HAUWA KULU (The Village Girl)

by @muslimerhabba

Bismillahir Rahmanir Rahim. Alhamdulillah Rabbil Alamina, wassalatu wassalamu ala sayyidil mursalina. Ina godiya ga Allah mahaliccin kowa da ya bani ikon fara rubuta wannan littafi, kaman yanda muka fara lafiya Allah ya bamu ikon kammala shi lafiya. Allah yasa abinda hannayena zasu rubuta ya zama mai anfanar damu baki ɗaya duniya da ƙiyama.


Littafinnan dai na kuɗi ne, amma nayi alƙawari insha Allah zanyi free pages guda biyar, daganan sai wanda ya saya ne zai cigaba da karatu, dan Allah kar a riƙa fitar min da littafi idan har nagama free pages, Allah ya bamu ikon rike amana.



Free page 1


Sauri yakeyi sosai kamar ƙafafunsa sa ɓalle ko kace ya tashi sama, tabbas in ya damƙi yarinyar nan yau se ta gane shayi ruwane, dan ya gaji da jaye-jayen maganar tsiya da kullum take jayo masa. Yana tafiya yana kwaɗa uban tsaki idanuwannan jayur kamar an shafa musu jawa, 'yan unguwa kuwa kowa yaganshi albarkacin bakinsa yake tofawa.

Tun Mero na tsakar gida tana faman jiran dawowar Kulu ta kawo musu ɗan niƙan garin masarar har tagaji da jira gyangyaɗi ya fara ɗibarta. Firgigigit ta farka sakamakon ƙarar sautin kukan Kulu da ya ratsa ilahirin kunnuwan ta da kwanyarta, idan da sabo yaci ace ta saba da halin yarinyar nan tata 'ya guda ɗaya tilo da Allah ya bata. Ita dai kam baza ta dena roƙon Allah ya shirya mata Kulu ba ko ta huta da bakin mutane.

Kaman yanda tayi tsammani dai hakan ce ta kasance, tasan babu wanda ke iya sa 'yartata kuka idan ba Kallamu ba, Kulu ga rashin ji shikuma mijinnata Kallamu ga rashin haƙuri.

Yana riƙe da kunnuwanta duka biyun fuskarta da gashin kanta duk gari buzu-buzu, ga hannunta riƙe da ƙwaryar garin gagam a hannunta ta tsage duk azabar kamun kunnen da take ji taki sakin ta.

"Innalillahi, me zan gani Kulu yauma garin kika zubar mana? Ya Allah ka nuna min lokacin shiriyar wannan yarinya". Mero ta faɗa hankali tashe idaniyanta kamar sa zubda hawaye.

Caraf Kallamu ya karɓe da faɗin "shikkenan abinda kika iya uwar son 'ya'ya, tom Wallahi yau duk inda zakuyi ke da 'yarki kuyi ku nemo min gari na dan nagaji da asara, idan ba haka ba kuwa a abincinku na sati guda dan ba a banza nake nemo hatsin ba" ya ƙarashe yana mai dunguwar da Kulu ya fice tabishi da hararar tsana kaman tace ya mutu su huta. Juyawa tai ta kalli mahaifiyarta yanayin fuskar ta yasa itama tai rau-rau da idanu tana shirin bata haƙuri. Shigewa ɗaki Mero tayi tare da saurin banko ƙofar ɗakin nata tasa sakata.

Durƙushewa Kulu tayi a ƙofar ɗakin mahaifiyar tata tana kuka tana roƙon Mero ta buɗe ƙofar, Zulai ce ta fito daga ɗakinta tana ta zuga uban tsaki.

Se da Mero taga ana gab da sallar magriba gashi bata da wata mafita ta yanke shawarar bara dai tafito, tabbas dole yau ta yankawa Kulu layi dan dole ta ajjiye wannan halin masifar ko sa sami nutsuwa da salama su zauna lafiya. Dama jira Kulu keyi mahaifiyartata ta fito, dan haka tana fitowa tai azamar kama ƙafafuwan ta tana janta tana roƙon ta da tayafe mata bara ta sake irin hakan ba. A rayuwar Kulu babu abinda ke ɗaga mata hankali irin tashin hankalin mahaifiyarta bare yanzun da taganta har da zubar da hawaye.

Cikin sigar lallashi itama Mero ta shiga yiwa 'yartata nasiha da ta yi koyi da haƙuri ta dena wannan faɗace-faɗacen musamman ita da take mace. 

"Inna bani bace nake tsokana kuma Inna ana taɓa min zuciya ne ta yanda bana iya jurewa. Inna babu dama na haɗu dasu sai sun zagi babana kokuma su kirani 'yar borar gida, ni kuma ina iya haƙuri akan komi amma bana iya jurewa in aka zagar min mahaifana". Ta ƙarashe tana kifa kanta cinyar Innan tata. 

Sosai tausayin 'yartata ya ratsa ilahirin jikinta, saidai kuma a haƙiƙanin gaskiya iya gatan da zata yiwa Kulu shine koya mata haƙuri dan in mune yau wataran ba mu bane.

Nasiha mai ratsa zuciya tai mata tankar wadda ke yiwa wata babba kuma saida Mero ta tursasa 'yartata tai mata alƙawarin zata dena faɗace-faɗace. 

Ranar dai haka Mero da 'yarta suka haƙura suka kwanta ba abinci sai ruwa rabonsu da abinci dama tun kokon safe, banda ruwan hawaye babu abinda bayin Allah nan ke zubarwa har Allah ma ji ƙan bawa ya nufe su bacci ya ɗauke su.


Turkey


Me yasa zata uzzurawa rayuwar mu dacewa se mun haihu Haidar, naga dai 'ya'yannan in min haifa namu ne kuma mu zamu ji daɗin morar su. Tom kuma tunda mu mu ce mun haƙura da haihuwar ba se ta barmu mu sarara ba, why would she be immersing her local life into ours dan Allah, gaskiya ya kamata ka ja mata warning she has stated pushing me to the wall gaskiya, mtssssssssssss" Nasma ta ja dogon tsaki tana mai shigewa ɗaki fuuuuuuuuuuu.

Gaba ɗaya in hankalin Haidar yayi dubu yau ya gama ɓaci, ta yaya ma Mommy zata riƙa masa irin haka, ace a rayuwa babu yanda za'ayi su haɗu ko a gaisa sai ta sako matarsa da zagi, gaskiya indai haka zata riƙayi shi zai dena kiranta ma a waya. Rai a ɓace cike da damuwar fishin farin cikinsa tilo ya kama hanyar ɗakinta dan lallashinta saidai ɗakin nata tariga tasa key ta rufe.

Ita kuwa hamshaƙiyar dan haushi taji haushin yanda Mommy ke sa mata ido, sai dai a cewar ta hakan bazai hanata sukuni ba, dan haka kau tsaye ta cire kayanta tashige bathroom ta sallo wankanta. Tana fitowa tai shigar ta mai tafi da tunaninsa ta ɗafe gado ta shiga lallatsa wayar hannunta.

Banda tarin damuwa babu abinda ke tattare da Mommy, mutum ta ƙarfin tsiya ya kafe sam bai damu da haihuwa ba, ita kuwa zata nuna masa cewa tafarkin yahudu wannasara tafarkin asara ne, kuma ashirye take da yin maganinsu dagashi har matar tasa.....