MAI KWAƊAYI

45

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

``` NAFISAT ALIYU SASAAL```



 ```Page 45```


________Tsakaninta da shi akwai ɗan tazara kuma hankalinshi gaba ɗaya baya kanta,ƙare mai kallo ta tsaya yi, sanye yake ciki LV Tracksuit dark brown sai RL Double Sole Black daya fito da tsananin hasken ƙafarshi dayafi na fuska,murmushi ne ya ƙwace mata haɗe da ɗan girgiza kanta"ai har ka tafi bazaka ganni ba dan tsoro kake bani" ta faɗa tana ƙoƙarin saɓa jakarta da ɗan sauri gudun kar ya kamata.


Cikin sa'a har ta ɓacewa ganinshi anata tunanin hankalinshi nakan abinda yake yi,abinda bata sani ba duk yana kallonta saboda tun shigowar motar su yasan itace,mamakin ƙinshi da gudun shi datakeyi ne ya kama shi,bai taɓa ganin mai shekarun Halima da wawtarta ba,banda haka tayaya kana rayuwa cikin gidan mutum kuma ko gaisheshi takasa yi? share shirmenta yayi yaciga da abinda yake yi.



★washe gari gudun kar su haɗu a mota taƙarayin Breakfast. Da farko Shukura share ta tayi sai da tayita bata haƙuri kafin su shirya.

"Kiyi haƙuri na ƙara tambayarki so ɗaya" Halima ta faɗa da nuna rabin yatsarta. Haɗe rai Shukura tayi tana jiran kalan tambayar da Haliman zata kuma yi mata.

"I have a lot to say amma bari na faɗi kaɗan please menene aure" ta faɗa abinda Yusha'u da Salim sukayi ƙoƙarin yimata na dawowa ranta.


Cikin yauƙi da wawta Shukura tafara bawa Halima labarin irin soyayyar da sukeyi da Mijinta amma yace ba za suyi abinda zasu samu baby ba sai taƙara girma. Baki hanci ido Halima ta saki tana kallon shukura dake labari har da ƙanƙame jikinta da fari da ido.

"Amma Shukura bakyaso kika aure shi ko? yayi miki girma da tsufa, Sannan dan Allah soyayyar da daɗi?" Halima ta faɗa da tausayin Shukuran da take ganin ita kamar daɗi takeji.


" Eh mana amma ai yanzu ina son shi"


" Why?"

"Saboda soyayyar shi🙄 ke soyayya akwai daɗi"

" To ni maiyasa babu wanda yace yana sona" Halima ta faɗa so sluggish.


"Nima fa haɗamu akayi" Shukura ta faɗa da iya gaskiyarta saboda ganin yanda jikin Halima yayi sanyi. Har aka tashe su Halima taƙi ta saki ranta tunaninta da burinta itama ta samu wanda zai ce yana sonta taji abinda Shukura take ji.



Da sanyi jiki ta shigo parlourn ita dai bataga kowa kuma dama batayi tunanin samun kowa ba tunda tun safe Aunty Rahina tace zataje unguwa sai dare zata dawo,duk da Parlourn akwai sauyin ƙamshi mai sanyi da daɗi bata kawo komai ba aranta.


Harta miƙe ta hango hilimin chocolate kala-kala a ƙaton farin leda zaro idanuwanta tayi tana sakin dariya nishaɗi batare da tunanin wanene ya ajjiyeba ta jefar da school Bag ɗin tana ƙoƙarin zuwa ɗauka.


Tun shigowar ta yake kallonta dama kuma wajenta yazo, baitaɓa ganin silly girl irin wannan yarinya ba.


"Hey" ya faɗa da Muryar da yasan bata so.

A take wanda ta ɗiba suka zube ƙasa,idanuwanta ta waro ta zuba mai.sanye yake cikin gutayen kayan shan iska masu aji da tsada.

"zo" ya faɗa yana ɗauke kanshi daga kallonta.


Kamar ɓarauniya haka ta ƙaraso wajen shi tana ƙoƙarin zama a ƙasa yanuna mata gefenshi, a ɗosane ta zauna kunyar kanta na kamata.


"Kin ganni jiya baki ce sannu da zuwaba" ya faɗa da ƙaramin murya mai ɗaɗin gasken daya sirka da gurɓataccen hausan shi da baya fita da kyau.


" Sannu da zuwa ina wuni?" Dariya ta bashi amma sai ya riƙe abinshi.


"Maiyasameki a school?" Saboda ya lura chocolate ne ya dawo da annuri fuskarta


"Babu komai"


"Really? Ko na kira abokina ya tambayi ƙawarki" ya faɗa badon yasan shukura ba,abokinshi kuma dayake nufi ƙanin director makarantar su ne,amma dayake tasan Maysarah da Mijin Shukara aikin su ɗaya sai tayi tunanin sun san juna,kuma fes Shukura zata tona mata asiri.

Girgiza kai tayi alamar a'a

" To menene matsalan"


"Ƙawata na da Miji nikuma babu wanda ya taɓa cewa yana sona" ta faɗa da iya gaskiyarta cikin kamewar rashin sabon dake tsakanin su.


Kasa riƙe dariyarshi yayi amma kaɗanne ya samu damar suɓucewa kyawawan lips ɗinshi, bayason ta gane shirme take faɗa, don sosai yakejin daɗin maganarta.


"Okay kince dama kina sona ko? to nima ina sonki shikenan🤨?" ya faɗa yana kallonta da kyau.


Kunya da dariya yasata rufe fuskarta,kafin a hankali ta zame hannunta tana kallon shi, ƙasa yayi da nashi idon don yabata daman tantace abinda takeson gani.tun ganin farko da tayi mishi tasan shi din mai kyau ne,amma yau tasamu damar ƙara gazgatawa,a bazata ya ɗago nashi idon duk don yaga shirmen da zata ƙarayi, da iya gudunta ta tabar wajen tana dariya. Har ta wucewa ganinshi bai motsa idanuwanshi daga bin bayanta da kallo ba.


Bayan wasu mintuna a hankali ta leƙo fuskarts parlourn ko zata ƙara ganinshi amma sai taga bayanan dariyar nishaɗi tasaki tana dafe saitin zuciyarta.



Kasa barci tayi har sai da Aunty Rahina ta dawo,cikin sanyinta daya haɗe da nishaɗi take bawa Aunty Rahina labarin Uncle Maysarah.

Duk wawtar Halima da Mijinta yake faɗa bata taɓa tabbatarwa ba sai ranar banda hauka irin na Halima maiya haɗa Namijin kamar Maysarah da irinta,balle ga kalar zuri'ar daya fito masu tinƙaho da burin auren kuɗi.

Bata dai tanka mata ba, a shirme tabar zancen Halima.

Gaba ɗaya washe gari da taje School labarin Maysarah daya sirka da yabo da zagi take ta bawa Shukura. Itama dayake gwanar surutu ce sai sukayi ta kus-kus har suka rabu.


Kamar yanda ba bu wanda yasan sanda Maysarah yazo, hakama babu wanda yasan sanda ya tafi sai neman shi sukayi suka rasa.


Kamar wawta da shirme haka Halima tafara dasawa ranta damuwa da Maysarah musamman lokacin dayace ai shima yana sonta,yarinta ya hanata gane illar da take yiwa kanta da kuma tantance girman tazarar dake tsakanin su.


Dawowar Faisal waje ɗaya ne yamayar da wajen Halima wajen zuwanshi duk dare,lokuta da dama har sai barci ya fara ɗaukarta sannan zai tafi.


Itama Mubeena sauyin Faisal da yawan daren daya tsira kai wa awaje duk bai dameta ba acewarta idan ya gaji zai dawo hayyacinshi.



Aboki kuma ubangida ga Mijin Sumayya daya karɓi Numbern Maryam ne ya nace da kira,ƙarshe dayaga tana mishi hanya-hanya kai tsaye sai ya tura magabatan shi Abuja wajen Mahaifinta.


Kuɗi kam akwai shi irin wanda Uncle Suraj ɗin yake buri har sama ma da haka,amma kyawun fuska kam sam babushi sai dai muyi fatan Allah yasa yanada zuciya mai kyau.


A take Uncle Suraj da Uncle Ghali da baƙin ciki kamar ya kashe shi suka bawa ɗansu izinin zuwa hira wajen Maryam.


Maryam kamar ta haɗiyi zuciyarta tsabar takaici don ita ba iya kuɗi takeso ba harda kyawun fuska tayaya zata nunawa haɗaɗɗun ƙawayenta shi amatsayin Mijinta. Duk koke-kokenta ita kaɗai tayi abinta a ɗaki don tasan tunda Mahaifinta ya amince to aure fa ba fashi sai dai idan Ubangiji bai ƙaddaraba. Yanzu shikenan Yusrah tayi nasara akanta kenan kuka ta ƙara fashewa dashi.


Itama dai Goggo zumuɗi da Maitar ɗan nata dayafito fili ne yasa dole ta amince da kuma fatan Allah yaganar da su,su dinga tantance mai kyau da mara kyau bawai komai dan kuɗi ba.


Cikin wasu kwanaki Maryam duk ta rame magana kaɗan kuka,kaifaffen gargaɗin da Mahaifinta yayi mata ne ya hanata gayawa Goggo bata son Mijin da ake ƙoƙarin liƙa mata.



Hankali da nutsuwar Yusrah da iyayenta gaba ɗaya sai ya koma kan yanda zasu shawo kan Maysarah ya aureta.


Da asirce-asirce da makircin da dukka iyayenta suke dashi suka samu kan Goggo,shi dama Abdulnaseer zance Mahaifiyarshi shine dai-dai bashida ta cewa.


A daren ranar Abdulnaseer da Goggo suka nemi layin Maysarah,daga yanayin muryarshi ya nuna baya gida,maimakon su saurara ya samu natsuwa kai tsaye Goggo ta sako mishi zancen abinda suka yanke,bai gane maganarta da kyau ba don alokacin yana wajen aiki kai tsaye ya amsa mata da......✍🏻✍🏻


🍜🍜 Bismillah