JANNAH

26

by @mommuhseen

Saboda gigicewar da nayi da dimaucewar da nayi ko takalmi babu a k'afata haka na fito a firgice na doshi titin cikin unguwar tafiya kurin nakeyi idona ya bushe babu ko d'igon hawaye ajikin fuskata,alokacin da mota zata zo tabi ta kaina zanfi kowa farin ciki saboda wani irin zafi zuciyata keyi mun, kaina yana juya mun juwa na daukata zubewa nai k'asa gefen hanya dafe da kaina da nakejin kamar zai tarwatse gida biyu, mota naji ta tsaya gabana kafin naji fitowar mutum, bana fatan sake kallon fuskar daya daga cikin yan gidan can so nake duk wani moment dake cikin kaina ya fita, Babaah uwani da mannir drivern yah Asaad ne suka fito daga motar, muryar babaah ce naji ta durkusa gabana cikin kuka tana cewa,


"Ba zaki iya tafiya a k'afa ba, bakida lafiya kar b'acin rai yasanya kije ki fad'i a hanya,taso muje kishiga mota mu kaiki gida,yallab'ai ya bamu umurnin karmu sake mu barki kitafi ke kad'ai,duk kayanki na kwaso miki kiyi hkr"


Numfashina sama da k'asa kurin yakeyi idan nace zanyi magana zan iya rasa wanda zan shak'a, kuma ko zan mutu anan bazan bisu ba ina haki nace,


"Babaah uwa.........uwani.......ku....ku a aje mun kayana nan, bazan biku ba, karki matsa mun wallahi tallahi bazan biku ba, don Allah........don Allah kitai maka mun kitafi ku aje mun kayana"


Na cigaba da shashshekar numfashi na, duk lallashin da take mun ban sake tanka Mata ba alamun cewar bazan bitan ba, tana zubar da hawaye haka ta sauke mun akwai da babbar jikkata tana ta kuka tace, "Allah ya kawo sauyi acikin rayuwarki Murja, Allahu ya wanke miki zuciyarki daga wannan bakin cikin, amman don girman Allah kice mun gida zaki daga nan"


Sai lokacin wasu tafasassun hawaye suka hau zubar mun kirjina yana d'agawa nace, "banda wan......wani......sauran......sauran gata daya wuc....wuce gidanmu babaah ta, insha Allah gida.......gidanmu zanje"


Rungumeta nai muna kukan tare kamar ba zamu daina ba, daker muka rabu bansan iyakar lokacin dana dauka anan ba har Allah ya kawo mun mai napep na shiga,ganin halin da nake ciki yasa ya fito ya saka mun kayana yana mun sannu, saida muka fito daga unguwar yake tambayata ina zani, ko za'a kasheni bazan iya kai kaina gidan mu ba tun zowana gidansu Yallab'ai zuwana d'aya gidanmu, kuma daddare ne bazan iya gane hanya ba.


Nace masa, "don Allah kad'an jirani in tambaya bansan hanya ba"


Kayana nahau bin cikawa ko Allah zaisaka inga yar wayata daya bani, don bansan ina zan dosa ba dole na nemesa saida na haukace kayan tas sannan cikin wata yar leda danaga babaah uwani ta sanyo mun kudina dake cikin dakina anan naga wayar, kunnata nayi ganin ta mutu idanuna zafi suke ga kaina dake wani irin azabebben ciwo, kiransa na somayi ban san na saka kuka ba bansan yaushe kukan zai tsaya ba, kila sai najini jikin innamu tukunna........"hello......hello Jannah.....Jannah......."

Kuka nakeyi wanda baya fita nace, "banzan iya gane hanyar gida ba kayi masa kwatance"


Banjira cewarsa ba na mik'a ma mai adaidaita din wayar, inajinsa yana amsawa da to yana sake tambayarsa har suka gama, ya bani wayar yana cewa "baiwar Allah kiyi hkar zaman aure ya gaji haka, yadda naji ya rud"e da alama yagane kuskurensa ki yafe mashi"


Idanuna na lumshe ina jin inama ace matsalar gidan mijice na samu, inama ace yaji nayi ko sakina mijina yayi zan tafi gidanmu, inama ace unguwa naje zan koma gida amman nasan yaudarar kaina nake, duka wadannan hasashen ba gaskiya bane kuma bazasu tab'a zama gaskiyar ba inata tunane tunanena har muka iso kofar gidanmu, wata irin muguwar fad'uwar gabace ta sameni, tsoro ya dirar mun fargaba ya shigeni jikina yana kerma na fito shikuma ya sauke mun kayana cikin zaure, na sallamesa amman sai yace, "Aa baiwar Allah na barmiki, Allah ya daidaita lamarin ya kawo mafita"


Kwalla suka zubo sharrrr na share na amsa masa da Amin, haka ya tafi yabarni nafi karfin minty talatin ban shigaba don da alama baba na nan baifita ba, inajin muryar innamu tana cema zainab,


"Wai don gidanku bakiga lokaci ba? Allah yasa atareki a zane gobe bazaki makara ba"


Zubewa nai cikin zauren na saka kuka mai tsananin tsuma zuciya, kerma kurin jikina keyi mezance ma innamu?mezance wa baba? Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, ya Allah ga baiwarka ka rufa mun asiri ka taimaka mun............inata kukan naji motsin zainab ta fito zata tafi tana cewa innamu tatafi, zabura tayi kamar zata ruga Saida taga nice sannan cikin mamaki tace, "Yaya murja kece? Meke faruwa kika tsaya zaure, kishigo mana"


Kuka nake wanda ba sauti sosai saboda banda karfi jikina ya saki kwarai,nace "kitaimaka mun mushiga ciki banda lafiya Zainab"


Cikin sauri ta saki jikkarta ta kamani muka k'arasa cikin gidan,

Shigarmu kenan innamu ta saki bokiti tana salati, "Murja menake gani haka? Lafiyarki kuwa"


Bakin d'aki na zauna daidai baba ya fito daga d'aki shima yana cewa, "wace murjar? Ince duka yau kwana biyar da zuwanta."


Kukan da nake rusawa cikin bakin ciki shiyasa sukai tsaitsaye suna kallona, innamu a firgice ta iso inda nake tana cewa , "ba kuka zakiyi ba sanar damu abunda ya faru zakiyi, bakida lafiya ne? Meya faru dake har baki iya tafiya murja? Innalillahi yauni nashiga uku ke kiyi mana magana mana"


Baban ma isowa yai inda muke yana mun magana, zainab duk ta rikice tace "Baba harda kayanta fa tazo, gasu can azaure kila korarta sukai.............a zabure baban yace "kora? Da kikai masu me murja? Ke don kwal ubanki kimana shiru ki mana magana, nace mekika aikata aka koreki murja? Karki ce mun sata kikai?..............innamu ta fashe da wani irin kuka tana cewa, "malam ba sata tayi ba, daga yadda take wannan kukan kad'ai zasa ka gane, sannan zainab kamota tayi bata iya tafiya dubeta dakyau malam, me kuwa zatayi?.........murja ta gama lalata rayuwarta, malam ga dukkan alamu murja ta gama ba namiji mutuncinta, wayyoni Allahna hazbunallahu wani imal wakil,........"


Ta silale kasa tana saka kuka mai tada hankali, Baba kamar yai hucking haka yake kallona, zuwa lokacin kukana ya dauke difff saboda tsananin tashin hankali, nufoni yayi yana magana idonsa da kwallah yace "dagaske ne murja kin salwantar da mutuncinki? Dagaske ne abunda innaku tagani? Ki musamun kice ba gaskiya bane kafin zuciyata ta buga, ki musa mun naceeeee!!!"


Ya fad'a da wata gigitacciyar kara har sandarsa na fad'uwa, nishin wahala nake ina kerma jikina rawa kawai yake nace, "walla......wallahi talla......tallahi baba bada son.......son raina ba, wallahi ba....baba fyad'e akaimun, na rantse da Allah daya busa mun rai baba fyad'e akai mu......mun,ban bayar dakai na ba baba......innamu ki gafarta mun wallahi bani na bada kai......kaina ba, har qur'ani zan iya dafawa cewar ban bada kaina ga......ga.....gakowa ba na tsare kaina yadda ya kamata wallahi ta karfi akai......akai man"


Saukar duka naji ta ko ina innamu ta rufeni dashi tana kuka mai tsuma rai, tana cewa "karya kike murja, karya kike tayaya za'ai miki ta karfi inbaki nada kofa ba,murja na baki tarbiyya daidai gwargwado murja meyasa zakiyi mana haka,innalillahi wa inna ilaihir rajuun ya Allah kanagani"


Ta zube cikin karyewar zuciya,baba kuka innamu kuka zainab kuka nice kawai zuciyar tawa ta bushe murus,babu ko d'igon hawaye a fuskata baba ya dauki sandar sa cikin zafin nama ya rad'a mun ga goshina cikin bakin ciki yace, "zaki gaya mun ubanda yai miki wannan abun ko kuwa? Wallahi zan iya lahanta ki kowa ma yahuta inbaki bud'i baki kin gaya mun ba.........dafe kaina nayi ina sakin kara saboda tabbas ya fasa mun goshi, ina cewa "baba ka gafarceni wallahi ban sani ba,ban san ko waye ba baba cikin dare akai mun, bana cikin hayyacina baba har suma nayi kwana na biyu asibiti bansan inda kaina yake ba, ka rufa mun asiri bana ka yafe mun, wallahi bazan tab'a aikata wannan abun da son raina b............."karya kike murja, ba abunda ke saurin canzawa kamar dan adama tabbas dukiya da jin dadin duniya ya sanya kin canza, ki gaya mun waye yai wannan abun ko kibar mun gidana murja, kiyi mun bayani........."



Zainab ta tareni tana bashi hakuri yadda ya dago zai buga mata sandar karfen sa dole ta kauce,tana ta kuka tome zance masa? Allah ma yasani bansan ko waye ba idan nace yallab'ai ne na cucesa saboda har cikin zuciyata nasan bashi bane, duk da kuwa gashi nan fuskarsa ce jikin mutumin amman zuciyata ta kasa yarda.........zoki fitar mun gida murja! Zoki fice mun ,kije ki nemo wanda kukai iskancin dashi sannan ki dawo mun,inhar baki gaya mun ko waye ba wallahi ba zaki zauna mun gida ba, shiyasa suka koroki saboda mugun halin da kika aikata, kash kash murja ina amfanin rayuwarki?.......da sandarda ya biyoni inajin innamu na kirana tana kiran baban amman inaaa zuciyarsa tayi nisa wajen aikata abunda takeso, dani da kayana haka baba ya jefoni waje idonsa hawayene yake cewa, "bazan yarda dake ba murja saikin kawo mun wanda kukai wannan abun, ba zaci sakayyar da zakiyi mun ba kenan, kije ba zan miki baki ba amman Allah shine zaimana sakayya"



Sai lokacin hawayena suka dawo sabbi nace, "baba kaifa ubana ne! Kasan ko wacece ni ka zab'i ka koreni daga gidanka saboda kaddara ta fad'a mun,? Baba kune fa kuka tilasta mun yin wannan aikin, innamu ta assasa zuwana wannan aikin, yau kaddara ta fad'a mun akan silar aikin shine zaku koreni? Shikenan baba zan tafi nabar maka gidanka, amman ka sani bazan tab'a dawowa ba, ranar da kuka samu gaskiya aranar ne nasan zaku neman.............bugo k'ofar gidan yayi ya saka kuba, inajiyo innamu tana masa magiya akan yabarni na dawo hannunka baya rub'ewa ka yanke ka yar, yadda nakejin kukan innamu haka nakejin na zainab amman bai saka baba ya bud'e gidan ba, ni kuma zuciyata ta gama bushewa ji nake koda zai dawo ya bud'e yace na shiga bazan tab'a shigaba,yayanmu bainan akai abun don haka naja kayana na zauna daga nesa kadan na had'e kaina da guiwata,kukan ma ya dauke jini keta d'iga daga goshina ban damu ba,fata nake kawai mutuwa tazo ta daukeni na huta saidai mutuwar bata zo ba amman YALLAB'AI YAZO..................