46
💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔
( shi ya san gidan mai rowa)
```By```
``` NAFISAT ALIYU SASAAL```
```Page 46```
________ta bari yaje gida zasuyi magana, ya faɗa yana katse kiran.
Kafin dare yayi Uncle Ghali ya kira Goggo yafi sau biyar,duk da sunan ya kirata ne ya gaisheta.
Har cikin ranta bata ƙaunar auren Maysarah da Yusrah, saboda tasan maza irin su Maysarah baza su so auren macen mai rawar kai irin Yusrah ba.amma kullum tana gayawa Allah Ya tabbatar da abinda yafi alkhairi.
Kamar wasa daga ranar basu ƙara samun layukan Maysarah ba,Haushi da takaicin hakan yasa kai tsaye Abdulnaseer ya nemawa Maysarah auren Yusrah.
Tsabar farin ciki ranar har ƙwarya-ƙwaryar walima su Uncle Ghali suka shirya. Shi dai Salim dayaji tushen labarin ba da sanin Maysarah duk suke wannan bidirin ba tausayi Yusrah da iyayen nashi suka bashi,don ko Mahaifin Maysarah bai san halin Maysarah yanda shi ya sani ba,kuma ko Yusrah zata mutu yasan bazai aureta ba,jan bakinshi yayi ya tsuke don yasan ko yafaɗa bayarda zasuyi ba.
Mubeena da ramar damuwa ya fara bayyana ajikinta saboda damuwar rashin zaman Faisal a gida ga wani ƙiba da fari dayake ƙarawa,tun tana ɗaukar fitar shi shirme har ta dawo hayyacinta,haka tazo taya ƴar uwarta murna. Gaba ɗaya hankalin su da burin su na kan ƴar lelen su mai shirin kawo musu arziƙi shiyasa ko lura basuyi da ramar Mubeena ba balle su tuntuɓeta matsalarta.
A ɓangaren su Uncle Suraj daƙyar Maryam ta taushi zuciyarta ta bisu gidan Uncle Ghali. Shima Uncle Suraj danne na shi zuciyar yayi duk da mahaukatan kuɗin da wanda zai auri Maryam ɗin yake sakar musu hakan bai sa yadaina jin baƙin cikin suɓucewar da Maysarah yayiwa Maryam ba.
Yawan ambaton sunan Maysarah da bawa sababbun ƙawayen da sukayi ita da Shukura labari yasa suke kiranta da Mrs Maysarah.
Duk lokacin da suka kirata da haka sai taji kanta yaƙara girma.
Duk ranar Friday Faisal daga masallaci wajenta yake wucewa bazai tafi gida ba sai dare. Kwalliya tayi sosai cikin light Brown Abaya daya ƙara fidda hasken fatarta har da sa jan jambaki,ba don komai ba sai don alƙawarin dayayi mata na kiran Maysarah su gaisa kafin washe gari ta wuce Kano wajen Inna.
Tun tana jiran Faisal har barci ya ɗauke ta bai zoba,bata jima da tashi ba aka kira sallar magriba,ranta ba daɗi tayi sallah. Sashen Aunty Rahina ta wuce, bata iya ɓoye damuwar son Maysarah da takeyi ba don har cikin zuciyarta dagaske take tunanin sonta yake yi.
Cikin damuwa take bawa Aunty Rahina labari.
Kasa magana Aunty Rahina tayi,ganin yanda Halima ta zuba mata ido tana jiran mai zatace yasa tayi murmushin dayafi kama dana tausayin wahalar da Haliman takeson ɗorawa rayuwarta tace"ki kwantar da hankalin ki ai lokacin zuwan Oga Faisal ɗin bai ƙure ba kinji" Rahina ta faɗa da shigar lallashi.
Sai bayan ta bar sashen tana ƙoƙarin kwanciya Faisal ya kirata a waya,sai da yayi Miss called kusan huɗu sannan ta ɗaga,kafin yayi magana ta samishi kuka haɗe da ƙorafin ƙin zuwanshi. "Wallahi taron baikon Maysarah da Yusrah ne yariƙe ni amma gobe kafin ki wuce Kano zanzo kinji,"
Daƙyar da haɗiye kuka mai ƙarfin daya taho mata" to Uncle" ta faɗa tana yanke kiran.
Wayar Faisal yabi da kallo yana murmushi haɗe da girgiza kanshi. Mubeena dake laɓe Allah Allah take yi yashiga wanka ta ɗauki number koma wacece yake waya da ita.
Yana shiga Bathroom ta fito daga maɓoyarta,da sauri ta ɗauki Numbern.
Kasa motsi Halima tayi sai wani irin kuka mai raɗaɗi da zafi da take yi.
Dagaske dama wasa yake mata kamar yanda Uncle Faisal yasha faɗa mata kenan ita yayiwa ƙarya, to wallahi idan taje Kano bazata dawo ba.
★bata wani san tasha ba amma ai tanada wayo kuma tana da ilimi,batare da jiran driver ba da sassafe ta haɗa kayan masu muhimmanci don bazata iya ɗaukar mai yawa ba.
Daƙyar da suɗin goshi Halima tagane kan komai har motar su yacika suka kama hanyar Kano.
Batasan yanda zata kai kanta gidan Inna ba don haka ta kirata a waya.
Hankalin Inna a tashe ta zo ɗaukar Halima da tsabar kuka idanuwanta sun kumbura fuskarta yayi jajir.
Ko zaman arziƙi basuyi ba Inna ta rumgumota jikinta tana tambayarta abinda ya faru.
Tsaf Inna tagama sauraron tatsuniyar Halima,don sunan data bawa labarin Halima kenan.
"Halima yaushe zakiyi hankalin da zakisan wacece ke,meye amfanin labarin Mahaifiyarki da kika karanta,ke kinsamu Muhalli mai kyau kina tare da Mutanen da suke lallaminki da gayamiki magana mai daɗi,suturar sawa,kayan kwalliya dukka mai tsada kike amfani dasu ga Ilimin Boko dana Arabia, to Mahaifiyarki duk bata samu wannan ba ita dai burinta ta samu ilimin bokon ko da na gwamnati ne,ta dalilin haka ta rasa idanuwanta,ƙafafuwanta,ƙarshe ta mutu bata cika wannan burikan nata ba saboda rashin gata. Gudun kar hankalinki ya tashi yasa na hanaki ko da ganin hoton Mahaifiyarki ne Halima,amma wata ƙila idan kika ganta zaki dawo hayyacinki ki gane banbancin ki da Maysarah da kike burin soyayya da shi har kike kuka da gudowa dan zai yi aure."
Hoton Halime ta ɗauko mata jikinta sanye da kayan Makaranta lokacin farkon fara zuwanta.
Tayi kuka mai tsanani gaske tausayi da tsanani ƙaunar matashiyar da take ganin sanye da Kayan Makarantar gwamnti da sandar dogarawarta guda biyu a gefe da gefe hammatar ta wanda ta amsa sunan Mahaifiyarta na ratsa ta,sai take ganin kamar itace a tsaye banbancin su kaɗan ne.
Kamar wasa Aunty Rahina taje kiran Halima basu ganta ba,duk gidan sunduba babu ita,duk wanda zasu tambaya Halima sai yace bai ganta ba, Baba Maigadi da shi kaɗai yasan fitar ta da inda taje sai yaƙi faɗa gudun kar yarasa aikinshi,driver dayake kaita Airport shima yace bai ganta ba,
★har washe gari babu Halima babu labarin ta, Faisal yayi nemanta har Makarantar su amma babu ita,maimakon suyi hikimar kiran Inna sai kaitsaye Aminu ya tafi neman layin Maysarah.
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Duk wani ƙulli da baikonshi shi da Yusrah duk yanada labari,amma bai tanka musu ba,kuma ko da ya kira Goggo da Mahaifinshi bai nuna musu yasan komai ba,suma nauyin jin kamar basu kyautamaiba tunda ga yanayin aikishi sai suka kasa gayamai,danasanin gaggawar amincewa Ghali na kama zuciyar Abdulnaseer,dama kuma tun faruwar lamarin Goggo ta janye hira da su ba kamar da ba.
Yana wajen aiki Aminu yakira shi. Sosai ya danne duk wani abu dayake ji bayan gama sauraron bayanin Aminun cikin kame-kame,batare da yacewa Aminu komaiba yakatse kiran.
Kai tsaye Number Bala dayake kasuwa yakira kuma dama shi yake zuwa ɗauko Halima a Airport duk ƙarshen wata idan tazo. Bai gama sauraron gaisuwar Bala ba yace yaƙara tura mishi number Inna zaiyi magana da ita.
Jiki na rawa Bala ya turamai Numbern,shima kuma sai ya kasa zaman kasuwar ya nufi gidan Inna.
Dai-dai lokacin da Inna ke ƙoƙarin shiga gida bayan ta kai Halima tasha ta sata a motar wani maƙocin su tare da bashi amanar yakaita har ƙofar gida idan ya sauke fasinjojin daya ɗauko,kuɗi mai tsoka Inna ta bashi yanata godiya, kiran Maysarah ya shigo Wayarta,ƙin ɗagawa tayi don numbobin basu yimata kama dana mutane ba,sai da yaƙara kira a karo na Uku sannan ta ɗaga tanajin muryarshi taganeshi.
Bata ɓoyemai zuwan Halima ba amma sai ta ɓoyemai dalilin zuwanta,kuma ta shaidamishi tana hanyar komawa. Da haka sukayi Sallama.
Kafin Motar su Halima ya shiga Abuja zazzaɓi mai zafi ya rufeta saboda kuka da damuwa. Duk da tunasar da ita matsayinta da asalinsa da Inna tayi,bataji ɗigon son Maysarah ya ragu a zuciyarta ba duk da yarda da yayi mata nisa.
Maƙocin su Inna baisha wahalar gane kwataccen da Inna da Halima suka yimai ba, sai dai ya kasa gane layin, juyowa bayanshi yayi domin tambayar Halima,don da agaba take amma da fasinjoji suka sauka saita koma baya. Wuyanta a karye da idanuwa juye ya ganta, toshe bakinshi yayi fitsari na neman ƙwacemai. Jikinshi na rawa yakira Inna,itama Inna cikin tashin hankali ta kira Number da Maysarah yakirata dashi,amma bai ɗaga ba tana ƙoƙarin neman layin Bala kiran Maysarah ya shigo,cikin kuka tayimishi bayanin da driver yayi mata.
Kafin minti goma su Aminu dake kusa sun isa ga Halima anwuce da ita Asibiti.
Ƙara kiran Inna Maysarah yayi,ya tambaye ta ko Halima na da wani ciwo ne da basu sani ba? Cikin ruɗewar halin da Halimar take ciki takwashe dalilin gudowar Halima wajenta ta sanar dashi......✍🏻
🥱Barkan mu da dare