ALLON ƘADDARA

Chapter 9

by @oumfatima33

✨ *ALLON* *ƘADDARA* ✨




    *OUM FATIMA*




 *DASHEN ALLAH* *WRITERS* *ASSOCIATION* 




 *page 9*




 *Washe gari*


Bayan mun yi sallar asuba ina ƙoƙarin jan bargo in shige Aunty ta shigo ɗauke da kayan amfanin ta. Haɗin dilka ne da ta kwaɓa tun jiya tasa a firgi shine ta ciroshi ta barshi ya huce sannan ta nufo ɗakin "Allah Aunty bacci nake ji, ki bari sai anjima" na faɗa ina ƙara shigewa bargo "ke tashi kin ji ko bana son shiririta, bakya ganin bamu da isasshen lokaci, duka fa sati biyu ne garemu maza taso muyi abin da ya kamata" tashin nayi ina lumshe ido ta bani tawul tace "ɗaura maza". Kayan jikina na shiga cirewa na ɗaura tawul ɗin na zauna saman kujerar da ta aje min saman wata tabarma da ta shimfiɗa da alama ta aikin ce.


Garwashin da ta shigo dashi ta aje a gabana ta zuba wani turaren icce mai ƙamshi sannan ta rufa min wani ƙaton bargo wanda fuskata ce kaɗai a waje tace "zaronmin tawul ɗin" ba musu na cire na miƙa mata ɗumin hayaƙin yana ta ratsa jikina ta ko ina, nan da nan zufa ta shiga ƙaryo min. Madara mai sanyi ta miƙo min a kofi na riƙa sha ina haɗa zufa.


Minti sha biyar nayi kafin ta bani tawul ɗin na ɗaura sannan ta cire min rufar. Zuwa lokacin na gama jiƙewa tako ina fatata tayi laushi. Wannan haɗin dilkar ta shiga shafa min ko ina a jikina da fuskata, sai da ta tabbatar ta murji ko ina kafin ta barni na tsawon mintinan da ake buƙata.


Wata galan ta bani da wata madara mai dumi a ciki tace muje bayin. Wankan madarar shanu ne sabon tatsa tayi min kafin ta haɗa min ruwa mai kyau ta zuba wasu mayun turaruka tace in yi wanka ta fice a ɗakin. Ina fitowa na samu tana haɗa wani garwashin, turaren icce ta fara yi min kafin ta bani wasu haɗin khumra tace in rinƙa amfani dasu.


Zuwa lokacin gaba ɗaya na canza fatata har wani sulɓi take tana sheƙi, ga wani azababben ƙamshi dake tashi a jikina. Fita tayi ta nufi kiching bayan ta faɗa min in saka kaya masu nauyi in rufe ko ina a jikina "to" nace mata sannan na shirya cikin wata baƙar Abaya mai ɗan nauyi na saka safa. A matuƙar gajiye nake, don na jigatu a hannun Aunty ga wani irin bacci ina ji amma haka dole na haƙura na fice sabo da zuwa wurin aiki. 


A saman dining na same su suna karyawa, zama nayi nimaina gaishe da Uncle Bashir mijin Aunty ya amsa min da kulawa yana ce min "amarya ashe an sa lokaci, to Allah ya nuna mana yasa alkairi" murmushi kawai nayi ina sadda kai sai Aunty ce ta amsa da Ameen.


Gaishe ni su Afiya suka yi su duka suna murna za'ayi biki a gidansu. Ina kammalawa na miƙe nayi wa Aunty sallama zan wuce wurin aiki tace "ki nemi hutu a wurin aikin nan don ba ƙara zuwa zaki yi ba sai bayan biki".


"Aunty ai da saura, inna kai musu katin gayyata sai in nemi hutun"


"Ah to ki kai da wuri don ba mayar min da aiki baya zaki riƙa yi ba da fita rana".


"To Aunty" kawai na faɗa mata na fice.



**** Haka naci gaba da karɓar gyara wurin Aunty inda cikin sati ɗaya nayi bala'in sauya wa na ƙara kyau na murje fatata sai silɓi da sheƙi take, gefe ɗaya kuma ina shan maganin sanyi da na rana. A cikin satin Alhaji Babba ya bugo IV inda na kai wurin aikin mu na nemi hutu, aka bani ana ta min fatan alkairi.


Gefe ɗaya kuma Momy ta ɗaga hankalinta ta ɗagawa Abba da Nabeel wanda duk yabi ya rame ya fita hayyacinsa sabo da masifar Momy wanda yanzu baya ma bari su haɗu ya kuma kashe wayoyin sa. Shi kuma Abba biris yayi da ita ya ba iska ajiyar ta yaci gaba da shirin bikin sa. Sosai hankalin ta ya tashi ganin ba fashi ana ta shirin biki har yau saura kwana biyar a ɗaura auren, ga zigar Ƙanwarta dake ƙara tunzura ta sabo da ƴarta dake son Nabeel ɗin. Don haka daga ita har Nabeel ɗin basu da kwanciyar hankali.


Ɓangaren Ammy kuwa ita ma a sanyaye take shirin bikin ita da ƴar uwarta sai abokan arziƙi wanda Aunty Ade itace kan komai na shirin don taga Ammy ba iyawa zata yi ba.


Ɓangarena Baba Malam ya hana waɗannan bidi'o'in don haka kamu kawai zamu yi ran Laraba, walima Alhamis sai ɗaurin aure juma'a. Ƴan Adamawa dama wasu basu tafiba tun bikin Hamma, ƴan Katsina kuwa saura kwana huɗu ɗaurin aure suka zo aka ci gaba da shiri.


Alhaji Babba ya haɗa lefe akwatuna masu kyau da tsada set biyu Red da purple. Masha Allah kaya sun yi matuƙar kyau sai sam barka da fatan zaman lafiya.



 *Laraba*


A cikin gidanmu muka shirya kamun muka yi abinmu inda ƴan uwa da ƙawayena suka halarta. Sosai abin ya ƙayatar su Anisa manyan ƙawayen amarya sai hidima ake yi da baƙi ita da su Asiya, Nabeela, Kadija da sauran. Aminatu kuwa sai da Abba yayi mata jan ido sannan ta shiga cikinmu, su Aunty Zainaba ma duk sun halarta haka taro ya watse cikin farin ciki, don Abba ya jawa Momy kunne sosai akan ta kuskura ta tada hayaniya a wurinnan sai ranta yayi mummunan ɓaci. Ƙwaffa tayi tace "ai in kasan wata baka san wata ba" lokacin da ya fice daga ɗakin ta faɗi haka tana tunawa da shawarar da ƙanwarta ta bata. Hakan yasa ta saki jikinta ake hidimar lafiya wanda mamakin hakan ya kasa ɓoyuwa daga fuskar mutanen gidan.


Nabeel kuwa da ya san halin mahaifiyarsa yasan da abinda take shirya wa, ba haka kawai ta ƙyale ba bayan alwashin da tasha. Shi dai addu'a kawai yake yi akan koma miye Allah ya sauwaƙa.


Ammy har yanzu a cikin fargaba da zullumi take sabo da tasan shirun da Habiba tayi bazai zama alkairi ba, amma koma minene ita dai tana yiwa ƴarta addu'ar neman kariya wurin Allah.


Haka biki yaci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali, ranar Alhamis muka yi walima inda abokan aikina duk sun halarta. Ranar juma'a ƙarfe 11:00am aka ɗaura aurena da Ya Nabeel lokacin muna part ɗin Dady nida ƙawayena da yake a can muke matarsa Aunty Mamy ta bamu ɗaki muke yinin mu a ciki. Dady ne ya shigo yake faɗa mata cewar an ɗaura "Alhamdulillah Allah yasa alkairi ya basu zaman lafiya".


"Ameen" ya faɗa yana ficewa, shigowa tayi ɗakin da muke ta shaida mana cewar an ɗaura, tare su Anisa suka ɗauki shewa suna rungumeni. Ni kuma zubewa nayi ƙasa nayi sujjada ina miƙa godiyata ga Allah da ya cika min burina. "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!, Ko yanzu na Allah ya karɓi raina zan tafi da farin cikin kasancewa ta matar Ya Nabeel" na furta hawaye na sauko min. Gaba ɗaya jikin mutanen dake ɗakin yayi sanyi sosai suna mamakin soyayyar dake tsakanina da Ya Nabeel, ciki harda Aminatu da jikinta yafi na kowa sanyi sabo da sanin da tayi Momy baza ta taɓa barin mu tare ba. Tuni ita ta zubar da makamanta sai ma tausayi da muke bata nida Yayanta, dama can Momy ce take ɗorata a turbar tsanar Ammy da ƴarta. Yanzu da Abba yasa ta shiga cikin ƴanuwanta sai taji ta sake sosai tana farin ciki.




*** A ɓangaren Ya Nabeel ma farin cikin da yake ciki baya musaltuwa, duk da can ƙasan zuciyarsa a tsorace yake da abin da Mahaifiyarsa zata iya. Bayan sun dawo daga walimar da suka yi ɗakinsa ya shige ya kirata suka daɗe suna hira da musayar magan-ganu masu ratsa zuciya.


Haka kawai yake ji kamar wanda suke bankwana da juna, sai yake jin kamar wannan itace magana ta ƙarshe da zata shiga tsakanin su. Don haka sun daɗe sosai a kan waya kafin suyi sallama shima don abokansa sun dame shi akan ya fito.


Nima jikina yayi sanyi haka kawai har sai da Anisa ta tambaye ni "Hanan lafiyar ki kuwa?, Tunanin mai kike ina ta magana baki jiba?" Ɗagowa nayi muka haɗa ido da Aminatu tayi min murmushi nima na mayar mata kafin na kalli Anisa nace "nima ban sani ba Anisa, haka kawai gaba na ke faɗuwa, sai naji kamar ina jin tsoro!" Na faɗa a matuƙar sanyaye kamar zan yi kuka.


"Ke ba komai fa, ki kwantar da hankalinki ko wace amarya haka take ji ranar aurenta, fargabar rabuwa da gida ne da kuma tunanin sabuwar rayuwar data tunkaro ki, duk da cewar wanda zaki yi rayuwar da shi ba baƙo bane a wurinki masoyinki ne kuma ɗan uwanki dake tsakanin ƙaunar ki, kinga kenan zai kula dake sosai bazai bari abu marar kyau ya tunkaroki ba, ki kwantar da hankalinki kinji ko" sosai kalaman da tayi amfani dasu suka bani ƙwarin gwiwa naci gaba da harkokina.


Biki yaci gaba da gudana cikin aminci, sosai mutane suka yi min kara don wasu ma ban yi zaton ganin su ba amma suka zo. Bayan sallar magrib aka shirya ni don miƙa ni gidan mijina, a ɓangaren Hajjo aka haɗa mu nida Ya Nabeel aka yi mana nasiha mai ratsa jiki da kashe gaɓɓai, wurin Ammy na aka kaini muka yi sallama tayi min addu'a sosai inda muka rabu ina ta kukan da ban zaci zan yi shi ba. "Ashe haka auren yake?, Ashe haka ake ji yayin rabuwa da gida?" Sune tambayoyin da na riƙa yiwa Aunty Ade dake riƙe dani. "Ko wace mace da kika gani a gidanta har ta tara iyalinta to da haka ta fara, kuma bata kai matakin da ta kai ba sai da tayi haƙuri ta jure sannan ta kaishi, sabo da haka ina ƙara jaddada maki kalmar haƙuri a zaman aure don shike jagorantar komai" Aunty Ade ta bani amsa yayinda ni kuma nake kuka sosai.


Haka aka sani a mota Aunty Ade da Aunty Surayya suka sani a tsakiya sai Samha a gaba sai Ya Shaheed da zai kai mu. Sauran motacin su Ya Fu'ad ne da wasu daga cikin abokan Ya Nabeel suka kwashi sauran mutane.


An kai ni gidana da yayi matuƙar tsaruwa, Baba Malam ya zuba min kaya masu kyau da tsada. An zuba komai da ya dace. "Masha Allah gida yayi sosai sai fatan Allah ya bada zaman lafiya" itace kalmar da kowa ke faɗa lokacin da suke zazzaga wa.


Nasiha su Aunty Ade suka ƙara min kafin suyi mana sallama suka wuce gida aka bar ni da su Anisa su taya ni zama kafin Yaya ya shigo. Samha su Aunty tabi zasu sauke ta gida tace min gobe zata dawo insha Allah.


Muna zaune har ƙarfe 10:00pm sannan muka ji ƙafan buɗe gate. Ya Nabeel ne ya shigo sai Ya Shaheed ya biyo bayansa yana ƙwala kiran sunansa, bai tsaya ba sai da yazo tsakiyar falon kafin ya tsaya yana watsi da wata ƙwalbar flower mai kyau da aka aje saman Centre table. Ƙaran tarwatsewar abu da naji ne yasa na ɗago da sauri daga lulluɓin da aka yi min. "Innalillahi wa inna ilaihirraju'un Nabeel kana cikin hankalin ka kuwa?, Wai mike faruwa ne?, Tun a gida nake tambar ka kaƙi cewa komai" kuka ya fashe dashi yana cewa "shike nan rayuwata bata da amfani, mutuwa zan yi Shaheed, Momy ta gama lalata min rayuwa bani da sauran wani amfani a duniyar nan!" Ya ƙara sa faɗa yana matsanancin kukan da ya ƙara tada mana hankali. Tashi nayi na nufe shi ina tambayar shi "minene wai Muheeb?, Ka faɗa min mana!" Na faɗa a hargitse. Kasa kallon fuskata yayi sai kukan da ya ƙara saki wanda yasa ni fashewa da kukan nima. 


Wata farar takarda ya zaro ya miƙa wa Ya Shaheed yana zubewa kasa tare da sakin azababben kukan da yake fitowa daga ƙasan zuciyarsa yana ƙona illahirin jikin sa. Hannu na rawa Ya Shahed ya shiga ware takardar ya duba, da sauri ya jefar ya da ita yana furta kalmar "innalillahi wa inna ilaihirraju'un, ka sake ta Nabeel?, Kuma saki uku?, Hasbunallahi wa ni'imal wakil!".


Kamar saukar aradu haka naji saukar maganar a cikin kaina kafin naji wani dumm sai kawai naga duhu ya mamaye ganina na zube ƙasa sumammiya. Da gudu suka nufo ni kafin su ƙara so shima Ya Nabeel ya zube a sume...



Comment and shere 




 *OUM* *FATIMA*