ALLON ƘADDARAFree

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

ALLON ƘADDARA

  • 1views
  • 54chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · Chapter 1

✨ *ALLON* *ƘADDARA* ✨      *OUM* *FATIMA*  *DASHEN* *ALLAH* *WRITERS* *ASSOCIATION*  *Page* *1* *BISMILLAHIRRAHMANURRAHEEM* ƘADDARA!.Kalmar ƙaddara nada girman da baki ba zai taɓa iya fayyace taba, sai dai ya faɗi iya abin da ya sani a game da ita. Kamar yanda yake a tabbataccen zance tun daga farkon halittar da Allah ya fara halitta a duniya wato Annabi Adam (A.S).Kowanne mutum yana rayuwa ne a bisa doron ƙaddarar da Allah ya halicce sa a kanta tun daga haihuwar sa har zuwa mutuwar sa, duk abin ya sami bawa a rayuwa to yana rubuce ne a cikin *Allon* *ƙaddararsa* . Kamar haka nima tawa rayuwar ta zo min a bisa doron ƙaddara ta.Sai dai a nawa ɓangaren tawa ƙaddarar mai zafice da a kullum take buɗe min sababbin shafuka masu wuyar karantawa da sarƙaƙiyar da take wajiga rayuwata.Baza ku taɓa fahimtar mai nake nufi ba har sai kun san labarina.Suna na shine SAFIYYAH MUHAMMAD BELLO (HANAN). Gidan mu ya kasance babban gidane da yake ɗauke da Iyalai da yawa da suke zaune a wuri ɗaya suna rayuwa. A taƙaice dai zan iya kiransa da Family house.Mahaifina da ake kira da Muhammad Bello su biyar Iyayensu suka haifa, su huɗu duk Maza ne sai autar su da ta kasance Mace. ALHAJI USMAN shine babba a cikin su da ake kira da Alhaji babba, babban ɗan Kasuwa ne da yake da manyan Shaguna a kasuwa da ake kawo duk wani nau'in Sutura na Maza da mata. Ba anan ya tsaya ba yana harkar gwala-gwalai, suna kawo kayan daga Ƙasashe da ban da ban.Sai mai bi masa ALHAJI MUKHTAR. Shi kuma ma'aikacin gwamnati ne da yake aiki da ma'aikatar ilimi wato Ministry of Education.Sai MUHAMMAD BELLO da ya kasance Alƙali ne da yake shari'a a Kotun Musulunci sannan kuma Malamin Addinin Muslunci ne da yake karantarwa da kuma yaɗa da'awa, a taƙaice dai shi ɗin babban Malami ne mai koyi da Sunnar Annabi Muhammad (S.A.W).Sai na huɗu ALHAJI SA'EED. Shima dai yana harkar Kasuwanci ne a Kasuwa tare da Yayan sa Alhaji Usman. Sai Autar su SURAYYA da take aure a nan cikin Kanon. Dukkanin su suna zaune a cikin garin Kano a cikin Unguwar Nasarawa.Kakannin mu sun kasance ƴan asalin jihar Adamawa ne. Fulanin Yola ne Kasuwanci ne ya kawo su garin Kano har suka kafu a nan suka hayayyafa.Kamar yanda na faɗa a baya Gidan mu babban gidane da yake ɗauke da ɓangarori guda shidda. ɓangaren Kakar mu, wato mahaifiyar Iyayemmu shi zaka fara tarar wa da ka shigo babban gate ɗin gidan in ka tsaallake Boys quarter. Sai ɓangarorin Iyayemmu Maza guda huɗu. Ɓangaren Alhaji Babba (Alhaji Usman) shine na biyu da zaka samu. Sai na Alhaji Mukhtar da muke kira da Dady, da yake daga can gaba kaɗan sai na Mahaifin mu da na Alhaji Sa'eed da muke kira da Abba da suke daga ɗayan side ɗin, ma'ana suna fuskantar na su Alhaji Babba. Ko wane ɓangare gini ne wadatac ce mai ...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters54
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play