Chapter Three
"Ina yini Baba Azumi" Kulu ta faɗa lokacin da ta haɗu da Baba Azumi dake shirin karya kwana dan shiga gidanta.
"Lafiya qalau Hauwa kulu, ina Meron, aikuwa kinga kin hutar dani, ɗazun Jabiru ya bani saƙo yace na kai muku, kinga biyo ni ki karɓa kice ma Meron ina nan zuwa kuma Insha Allahu".
Kaman yanda Baba Azumi tace haka ta bawa Kulu ƙatuwar leda cike da kaya da wani buhu na tsarabar birni da Jabiru yazo musu dashi musamman.
Tana shiga gidan Zulai na fitowa daga lokon bayi, ƙurrr tabi hannun Kulu da idanu ganin yanda take riƙe leda da buhun hannunta da ƙyar. Haka tana kallo Kulu tashige ɗaki tayi saurin binta ta laɓe a jikin ɗakin.
Ba ƙaramin kaya Baba Azumin ta aiko musu ba, kayan birni ne kala-kala dan abubuwan ma banda taliya babu abinda suka san sunansa, sai biscuits shima Kulu ce ta tuna cewa ta taɓa ganinsa a wajen wata 'yar yayan ƙawarta Sani dashima dama acan birnin yake aiki yataɓa kawo 'yarsa Rabi. Saida Mero ta aika Kulu taje tayiwa Baba Azumi godiya, tace kuma itama da zarar mijinta ya dawo zata tambaya taje tayi godiyar da kanta.
Da wata iriyar masifa da karaɗi ya ɗaga labulen ɗakin ya kutsa kai, hankali tashe duk suka miƙe ko waccensu a firgice. Kan Kulu yai da azama kamar kura taga nama ya damƙo ta ya hau rafka mata mari, ganin yaƙi tsayawa da marin yasa Mero shiga tsakaninsu dan kare 'yarta. Ido rufe Kallamu ya ɗaga hannu ya rafkawa Meron mari ya kuma ɗagawa da shirin tafka mata wani Kulu ta riƙe hannunsa.
Meron ta rintse idanu tana shirin karɓar wani marin ta tsinkayo muryar Kulu na ɗaga sauti.
"Baka isa ba wallahi Baffa akan idona bazai yiwu ka kuma marin mahaifiyata ba mai jin ƙaina, ni banda ka ci sa'ar ma uba uba ne dan an zageka har na wani tsaya faɗa da mutane, nifa na fara tantama Baba anya ma kuwa kaine ka haifenin da gaske, tom ko ma dai mene ne ni ina faɗa maka kar ka sake dakar min mahaifiya dan wallahi zan baka mamaki" ta ƙarashe tana huci idanunnan a zazzare babu alamar tsoro ko danasani a cikinsu.
"lallai yarinyar nan na yarda abinda ake faɗa akanki gaskiya ne, dan dama tabbas da zarar yarinya ta fara bin maza take raina manya da ƙanana, ke kuma ma abin naki ya wuce kowa har yazo kaina saura kuma mahaifiyarki. Ko da yake ma dai tunda so kike a faɗa bara na faɗa miki kisani ni ba mahaifinki bane ba dake na auri uwarki kuma ki shirya ganin hukuncin da zan ɗauke dan aurar dake zanyi bazan zauna da karuwa a gida ba.
Da sauri Mero ta mike tana magana cike da ɓacin rai, "ya isheka haka Malam kar ka sake iskanta min 'ya, na gaji da baka baki kuma akan 'yata nagaji da yin shiru dan haka kar ka sake iskanta min 'ya.
"Dama aike kike koya mata komi wallahi tallahi kinji rantsuwa ta ku shirya ke da 'yarki dan tabbas aure zan mata kuma zan samo ɗan iska irinta ne na aura mata. Tsabar idonki yayi tsauri har kin isa ki kawo min tukuicin fitsararki gidana mara kunya". Yanayi yana kallon buhu da ledar da yagani a ɗakin saidai bashi da halin ɗauka dan yanda Kulu ta riƙe masa hannu tana masa kashedi ya basa mamaki.
Ita kuwa Kulu tunani ta shiga ƙirjinta na tsananta da bugawa furicin Kallamu na cewa wai da 'yarta ya aureta na ta daɗa dawo mata.
"Inna wallahi in har dagaske Baffa ba shine mahaifina ba se na fi jin daɗi, dan wallahi Inna najima ina wannan tunanin najima ina yawan cewa ina ma bashine mahaifina ba, dan duk wani zagi da tsana da akemin shine yake janyo mini. Inna kinyi shuru kinƙi ki bani amsa nifa gara ma a ce min shegiya da akirani 'yar wannan azzalumin mutumin mara ima..."
Kwaf! taji Innan tata ta kwaɓe mata baki, "akul kar na ƙara jin bakin ki ya furta zagi ga manya bare wanda yake matsayin uba a wajenki, ke bama iya manya ba ko yaro kin san bana goyon bayan zagi a bakinki."
Tabbas mahaifinki ya mutu tun kina ciki, ina haifarki kuma na auri wan mahaifinki, kinga kuwa ko ƙinƙi ko kinso dole ki kirashi mahaifinki, kuma daga yau se yau kar nasake ganin kin masa tsawa bare har ki nuna masa yatsa, in kuwa kika sake naimiki alƙawari se na karya yatsan, ja'ira kawai tashi ki ɓacemin a gani". Inna ta ƙarashe faɗan cikin ranta kuma tana maijin ɗaci da zafi da takaicin auren Kallamu.
Jin tabbacin cewa Kallamu ba babanta bane yasata jin wani irin farin ciki, abinka da yarinta ba hankali Kulu ko damuwa da cewa mahaifinta ya rasu batayiba ita dai tunda ba Kallamu ne babanta ba ai shikkenan, yanzu itama ta dena jin haushi idan 'yan gari sun kira ta 'yar masifaffe.
Nucy kuwa ƙawayenta na social media tashige bincika a haka har tasamo wata wadda ta yarda ai mata ciki ta haife ta bada ɗan ta karɓi kuɗinta. Ba ƙaramin jin daɗin saurin samun nasarar hakan nucy taiba haka itama Nafisa. Saidai kuma daga baya ita yarinyar tace ita ba kowa zata iya sakarwa jikinta ba saidai in matar ta yarda mijinta ne zai yi cikin, jin hakan yasa nucy ganin ai ta kwana gidan sauƙi sun rage girman zunubi tunda ɗansa ne zasu sa ya riƙe, kuma tunda dai se yanda suka juya Aliyu ai samin goyon bayan sa bazai musu wuya ba.
Saidai nucy na sanar da Nafisa Nafisan tace fafur bazata yarda wata karuwa ta kwanta mata da miji ba, duk ƙoƙarin nucy na nuna mata ai hakan yafi musu kwanciyar hankali amma tace ita sam bazata yarda ba, daƙyar nucy ta shawo kanta kan cewa za'a samo yarinya 'yar ƙauye wadda bata taɓa sanin namiji ba a juyar mata da tunani a kawo musu ita kawai, shima dai hakan daƙyar Nafisan ta yarda dan dai tana cikin tsanani bata da wata mafita sai a wajen nucy ɗin. Ƙarshen Shawara dai aka yanke cewa Rabi zata samo yarinya a ƙauyensu nucy kuma zatazo ta ɗauki yarinyar su cale Marocco inda Aliyu da Nafisa suke rayuwa.
TUNA BAYA
Aliyu ɗan wani gawurtaccen Alhaji ne mai suna Alhaji Ahmad Ali da ya tara dukiya kaman wanda ya tattara dukiyar duniyar baki ɗaya. Mutum ne mai yawan kirki da yawan alkhairi ga son mutane. Ya buɗe kampaninnika da tarin yawa a kasar sa Nigeria dan samun cigaban ƙasar tasa da samarwa matasa aiyukanyi. Sosai kuma Nigeria ke samin cigaban tattalin arziƙi sabida yanda ake fita da kayan kampaninnika na Alhaji Ahmad Ali kuma 'yanƙasa ma suke samun wadatuwar kayan anfani batare da an dogara da na wasu ƙasashen ba.
Tun daga sanda Aliyu ya taso mahaifinsa da ke kiransa da Aliyu ɗan yafi jin daɗin hakan ke ta ƙoƙari wajen ganin ya ɗorashi a kan harkar kula da kampaninnikan sa dan ƙasar ta samu ƙarin cigaba. Amma dan shi Aliyu tunanin sa baya nan burinsa kawai yazama pilot kaman yanda yake faɗa tun yana yaro. Hakan kuma shine yasa Alhaji Ahmad ya barshi yabi zaɓin ransa dan bayason yara bin ra'ayin sa a dole matukar abinda suka kawo bai haramta ba. Gashi Allah bai bashi wani ɗa namiji ba bayan Aliyu sai mata guda biyu Ramlat da Ƙanwarta Fatima, su biyu ne suke ta ƙoƙari wajen cika muradin mahaifin nasu da yayansu Aliyu ya kasa.
Aliyu ya taso miskilin mutum saidai mutum ne mai matukar son kusanci da family ɗin sa. Duk miskilancin sa baya iya yi a gaban ahalinsa dan yanda farin cikinsa ke yalwatuwa duk sanda ya sami zama dasu. Kwatsam Nafisa ta ƙyalla ta ganshi ta mayata ga son mallakar sa tun tana fuskantar cin mutumci a wajensa har ya zamana ta shawo kansa ya dage fafur itace abar son sa burin rayuwarsa. Dafarko da Aliyu yazowa da mahaifansa zancen auren Nafisa a birkice Mahaifiyarsa Hajiya Binta ta tsorata sabida sanin halin ɗan ta datai na miskilanci, daga baya kuma da tagano cewa yarinyar 'yace ga prof. Balkisu sai tasami nutsuwa dan a iya sanin da taiwa prof ɗin bata taɓa kawo cewa za'a sami baragurbi a gidanta ba. Tunda Nafisa tai nasarar aure Aliyu saida aka shafe shekaru biyar basu haihu ba ciki harda mutuwar Mahaifinsa. Hakan yasa Hajiya Binta da suke kira Mommy ta ɗaga hankalinta ta shiga tunanin ko suna cikin yaran zamani marasa son haihuwa, duk da dai a iya saninta da Aliyun ta a baya shiɗin mai son tara 'ya'yane kaman yanda yasha faɗa mata sai ya cika mata gida da jikoki.
Ganin irin matsin da Mommy ke musu ne yasa Nafisa dagewa saida ta raba Aliyu da son sakewa cikin 'yan uwansa ta hanyar nuna masa basu yarda da qaddarar Allah ba shi kuma ya yarda da hakan.
Hakan ne yasa daga ƙarshe Nafisa ta tunzura Aliyu suka bar ƙasar ma baki ɗaya, yazama na Mommy har tayi fishi da Aliyun, daga baya kuma taga fishin ba mafita bace tunda babu abinda ya canza ta yanke shawarar nuna masu karfin girmanta.
Dama zai iya barin Uwa ya bi mata? i doubt followers kuɗan ce wani abin.