Chapter Four
Kulu dai 'yace ga Malami bawan Allah, Malam Ali mai gona. Malam Ali mutum ne namiji mai ji da karfi da zuciyar neman halal. Gashi Allah ya hore mishi ilmin Qur'ani duk ƙauyen da yake babu kamarsa. Sosai kuma 'yan ƙauyen suke samin albarkar iliminsa ta yanda yake koyar da yara da ƙanana tun bayan mutuwar malamin sa Malam Isa, Ali yayi karatu sosai a wajen Malam Isa ɗan asalin ƙasar Nijer kwantagora, wanda kafin mutuwar sa ya aurawa Almajirinsa Ali 'yarsa guda da ya mallaka kuma mahaifiyarta ta mutu tabar masa ranar da ta haifeta, hakanan kuma mutanen ƙauyen ke anfana da dukiyar Malam Ali sabida yawan kyautar sa. Malam Ali ya kasance baiyi rayuwa a asalin ƙauyensu ba, yayi tafiya mai nisa neman kuɗi daganan ya haɗu da mahaifin matarsa yasami ilmin addini. Hakan sai yasa 'yan uwansa duk sanda suka zauna dashi basa fahimtar juna sabida jahilcinsu suna masa kallan mai tsattsauran ra'ayi.
Matar Ali wato Mairo Isa mutuniyar kirki ce mai tsananin haƙuri, a tarihin ta sam ba'a taɓa saminta da abokin faɗa ba, Mairo tasha wahalar matan uba sabida yanda kowacce tazo kishi takeyi da ita, har saida son sama mata uwa yasa mahaifinta auren mata huɗu kuma shi a tsarin da baya saki, bayan mutuwar malam Isa ne kuma matansa suka tattare ɗan abinda yayi saura na dukiyarsa sukai babakere suka hana tilon 'yarsa Mairo komi, hakan ya janyo Habiba bata da komi bata da kowa sai mijinta Ali.
Bayan shekara guda da rasuwar Malam Isa Allah ya azurta Mairo da samin haihuwar mace, Malam Ali yasa mata suna Hauwa'u sunan mahaifiyar Mairo dan kawai yasata farin ciki.
Wata tafiya da Malam Ali yayi ganin gida ananne ajalinsa ya sauka, sai kaninsa ne Kallamu yaje ma iyalinsa da labarin mutuwarsa tare da roƙon ta yarda bayan ta haihu suyi aure dan ya raini abinda zata haifa 'ya ko ɗa ga ɗan uwansa da kansa.
Tunda Mairo ta auri kallamu da ita da 'yarta basu taɓa samin farin ciki ba kullum cikin masifar sa da ta matar sa Zulai suke. Haƙuri kuma irin nata bai sa ta taɓa ko tunanin bijire masa ba sabida yanda take tsoron garin kwatar haƙƙinta wajen miji ta jawa kanta shiga wuta. Kaf matan garin tausayin ta sukeyi saboda ko bakomi ai suma suna anfana da ilmin ta, takan koyar dasu sallah da abinda yashafi addini duk sanda ta sami goyon baya, kamar idan maigari ya bawa Kallamu umarnin ana buƙatar matarsa ta faɗakar da matan garin.
Yara kuwa ban da hantara da zagi ba abinda suke yiwa Hauwa'u da mahaifiyarta ke ka'rantawa sunan mahaifiyarta da Kulu. Bakuma komi yasa suke mata tsangwama haka ba saidai yanda Kallamu ke zaginsu suma suka yanke shawarar su rama akan 'yarsa.
Haka suka cigaba da rayuwa har zuwa yau kwatsam da yazo ma Mero da mummunan labarin da ya tayar mata da hankali tayi kuka kaman ranta zaifita ta kuma rasa inda zata sa ranta taji daɗi...
Prof. Balki 'yace ga Prof. Mahdi, ta taso dason ilimi tun yarinta bayan girmanta kuma sai burinta ya karkata wajen son ganin ta gaji mahaifinta itama ta zama professor, Allah da ikon sa kuma sai ya cika mata burinta kaman yanda taso, ta zama professor abar kwatance a fannin Qur'an and Sunnah, gashi duk cikin 'ya'yan mahaifin nata babu wanda yakai matsayin da takai a rayuwa. Saidai bawa baya iya kaucewa ƙaddararsa duk matsayinsa kuwa, domin ita jarrabawa ma wanda Allah ke so da rahma shi yafi jarraba. Kamin Prof. Balki ta sami cika burinta tasha fama da ƙalubale na rayuwa musamman a gidan aure. Tana rayuwar aure a gidan mijinta zama na lafiya qaddara tasa ya auro mata Raliya, wadda ta hana ta zaman farin ciki a gidanta ta kuma hana mata sakewa da mijinta. A lokacin da Ibrahim mijin Balkisu ya auro Raliya suna da 'ya'ya mazaje guda biyar, kuma su kaɗai ne 'ya'yan da Allah ya azurta Balkisu dasu, duk da yanda take da kwaɗayi da burin ganin ta sami mace amma Allah bai bataba, itama kuma bata ja da hukuncin mahaliccin taba. Tunda Ibrahim ya auri Raliya Balkisu ba ta sake gane kansa ba, ya dena bata haƙƙinta na kwana bare ta sa ran zaiyi hira da ita, ba iya ita ba ma har 'ya'yan ta indai a wannan fannin ne sun koma tamkar basu da uba. Balkisu takan yawaita kuka tana mamakin butulci irin na mijinta Ibrahim ganin duk wani abu na rufin asiri da ya samu a rayuwa ya samu ne daga mahaifinta ta dalilinta, dan sabida irin son da Abdulkarim kewa 'yarsa Balkisu. Saidai abinda Balkisu bata gane ba duk abinda mijinnata yakeyi ba son ransa bane sharrin Raliyane wadda ta shiga rigar musulunci a munafunce sabida son abin duniya, tana maƙale da dangin mahaifiyarta na Jos da na Abiya states.
Allah cikin ikonsa abinka da masu kyakkyawar zuciya duk tsaface-tsafacen Raliya da dangin ta sai ta kasa cin nasara akan Balkisu da 'ya'yanta, sai mijinta Ibrahim da yakoma kaman remote control device se yanda akayi dashi, kuma da yake ita Balkisu tana da kyawun zuciya bata taɓa kawo cewa Raliya na wani tsafi ba bare har ta cutar da ita ko mijinta, iya tunanin ta Ibrahim ya nuna mata halin butulci ne irin na ɗan Adam ɗin da kayiwa rana.
Ko bature yasani ya kuma tabbatar da wannan kalmar ta "no condition is permanent". Allah cikin ikonsa duk da irin makirci da Raliya ta gama shiryawa da buri da ta ɗauka na wulaƙanta Balkisu da zarar ta haihu sai Allah ya hana mata dama, cikin ikon mafi tausayin bayinsa sai jini ya ɓallewa Raliya ta dalilin haihuwa, duk kuma yanda akaso a tsaida jinin aka kasa tana ji tana gani tana kiran sunan yesu cikin hukuncin Allah aka zare ranta.
A lokacin mutuwar Raliya ne Ibrahim ya dawo hayyacinsa ta dalilin mamaki na kiran Yesu Almasihu da ta riƙa yi maimakon sunan Allah, ya shiga kogon tunani da taraddadin dama Raliya bata musulunta ba dagaske, yayi danasani sosai ya kuma ƙyamaci auren tubbabbiya, sosai kuma ya shiga damuwa da tunanin makomar 'yarsu da tunanin yanda zai sama mata tarbiyya ta tabbata cikin addinin musulunci.
Bayan mutuwar Raliya ba ƙaramin tashin hankali aka shaba da 'yan uwanta kan cewa sai an basu jininsu, ta ƙarfi Ibrahim ya hanasu ya sanya mata suna Nafisa tare da damƙa amanar ta a hannun matarsa Dr. Balkisu a lokacin tana matsayin Dr.
Tunda Balkisu ta dawo hannun Balkisu take bata kulawa da qauna ta musamman kasancewarta dama mai burin haihuwar 'ya mace, 'yan uwan Raliya kuma da suka ga anfi qarfinsu sai suka nemi maslaha da roqon alfarma har Ibrahim ya amince sukan zo suga 'yar Raliya Nafisa duk lokacin da suka buƙaci hakan, amma duk abinda zasuyi iya kaci a gidan bai basu izinin a fitar masa da 'ya ba kuma haka rayuwar ta cigaba har zuwa girmanta sanda ta fara bijirewa Balkisu, haka a cikin irin wannan rayuwa Allah ya karɓi rayuwar Ibrahim yana mai baƙin cikin irin halin da yaga Nafisa 'yarsa na nunawa.
Tun bayan mutuwar Ibrahim Nafisa ta qara bijirewa Balkisu duk da yanda su Khaleel, Umar, Usman, Aliyu, da Saddiqu ke ja mata birki, daƙyar Balkisu ta sami damar shawo kan Nafisa ta hanyar aminta da tayi da karatun ta a qasashen waje, ita bata damu da kowace kasa bace itadai burinta tabar Nigeria.
Tun daga wannan lokacin Prof. Balkisu bata iya gane komi game da Nafisa dan ƙarshe ma guduwa tayi dangin mahaifiyarta na Abiya, ko ta tafi jos shima dangin uwar tata ne, se da taji wahla sannan ta dawo mata, tabbas ya kamata mutum ya godewa Allah ga duk irin rayuwar da ya tsara masa, gata dai da tana ta burin samun 'ya mace, yanzu kuma ta samu tana neman zame mata masifa, dan ita tana ɗaukan nafisa matsayin 'yar da ta haifa ne....