MAI KWAƊAYI

48

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

``` NAFISAT ALIYU SASAAL```



 ```Page 48```


________Kan inda yatsun Mubeena suka fito fes a fuskarta. Rintse idanuwanta tayi zuciyarta na bugawa da dasauri-dasauri.


Bai kula da halin da ta shiga ba yaƙara motsowa kusa da ita ƙamshin shi na shiga hancinta da kyau.


Fuskar ya kamo da dukka hannayenshi don har lokacin kallon yarinya ƙarama sosai yake mata,yana bin gefe da gefen kumatunta da kallo saboda dukka shatin yatsun Mubeena ne.


"Fuskana zafi" ta faɗa cikin sanyin daya haɗe da yanayin da take ciki ba kuma don tanajin zafin ba,wani iri takeji kamar ana mata tafiyar tutsa.

 

A hankali ya janye kyawawan hannayenshi,kafin ya tashi gaba ɗayanshi.


"Bari na kira su dubaki kar marin ya sa miki ciwo,anjima zan dawo"

Ya faɗa yana kallonta dakyau.

Kanta ta girgiza alamar bataso.


" Kiran su,ko tafiya na?"


"Banaso ka tafi" ta faɗa da iya gaskiyarta tana narke idanuwanta masu tsananin haske da sangarta yasa suka ƙara komawa abun birgewa mussamman ga mai kallon cikin su.


"Goggo zanje gani,bani few hours kinji" ya faɗa da Muryar dake ƙara zautar da Halima yana kallon tsadadden agogon diamond ɗin hannunshi.


Kanta da tagamai alamun taji amma duk da haka ƙwalla na kwance acikin idanuwanta.


Motsowa yaƙarayi duk don ta kwantar da hankalin domin shi har yanzu a yaranta yake barin labarin da Inna ta ba shi da kuma alherin da yayiwa Halime Mahaifyarta,banda haka tayaya Halima tasan ta so abu mai kyau? Wannan shine tunanin Maysarah amma har cikin ranshi yanajin Halima daban da ragowar mutane.


Hannayenta marasa kauri ya kamo cikin nashi lafiyayyun hannayen.


"Dagaske yanzu zandawo" ya ƙara faɗa yana ɗage mata cikakkun girar shi.


Maimakon ta bashi amsa sai ta samishi kuka.


Hannunta yaɗan matsa yana kallon kwantaccen suman gaban goshinta.


Bai ce komai ba ya saki hannunta ɗaya, tsadadden wayanshi ya ciro kai tsaye ya kira layin Inna .


Inna dake zaman jiran tsammani dasauri ta ɗauka,miƙawa Halima wayan yayi,bayan ya tabbatar da hankalinta nakan waya da Inna Sannan ya bar ɗakin.


Sai da yabiya wajen babban likitan dake kula da Halima, yayimishi bayani sannan yabar Asibitin.



🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂


Kamar yanda Mubeena taje asibitin bada sanin Faisal ba haka yabarta a tsaye, yayi tafiyarshi kuma yahana driver daya kawota komawa da ita.

Ita dama Rahina ta jima da tafiya gida don tasan ba barinta ganin Halima za'ayiba.


Idanuwan Mubeena kamar zusuyi aman wuta tsabar jan da sukayi,danasanin son Salmanu na kama zuciyarta don duk shine mafarin wannan musibar da take ciki.


Tarasa wa zata kira saboda jikinta ba ko sisi ga shi bata fito da Card ɗinta ba, dole haka ta kira Salim. Shima sai ta ɓoyemai dalilin rashin samun abu hawa don tasan da zarar ta ambaci sunan Maysarah to kozata mutu bazai zo ba.


Bata ɓoyewa Salim komaiba tunda dama tuntuni yasan tushe zancen.

"Amma Mubee kinyi shirme,ke kinsan waye Uncle Suraj ko Faisal zai mutu akan soyayyar yarinyar da bata fito daga gidan arziƙi ba,bazai bari ya aureta ba,to menene damuwarki a ciki,kuma kinsan yanda lamura suka ƙara kwaɓewa wallahi a yau Yaya Faisal ya sakeki Iyayenshi sai sunfi kowa farin ciki,don a dole suke miki dariya,balle yanzu da gabar Yusrah da Maryam ya ƙara ƙarfi,kuma kinsan duk iyayen mu ne a ƙarƙashin wannan gabar."



"Amma Salim haka zanyi ta rayuwa wallahi sai na kori Halima acikin zuri'ar mu sannan hankalina zai kwanta"

Ta faɗa da tsananin kuka.


Kallo anya kanki ɗaya kuwa Salim yake mata lokacin da suka tsaya kafin security ya buɗe mu su gate.


" Ko da wasa karki bari ki ƙara shiga hanyar Maysarah,don zaimiki abinda har su Daddy sai sun tsaneki,ki bar kanki da sanin iya fuskarshi da kirkinshi amma karki kuskura kisan asalin ɗayan halayyar Maysarah".


Ya faɗa dai-dai lokacin dayake gyara parking a parking lot ɗin gidan.



Kamar munafuka haka tafito daga motar Salim zuciyar fal fargaban abinda Faisal ya shirya mata da juya maganganun Salim aranta.

Gaba ɗaya kishin daya rufe mata ido yasa tama manta da ƴaƴanta.


Jiki a sanyaye ta shiga parlourn da Sallama kamar ba ita ba.


🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂


"Halima yaya jikin naki" Inna ta ƙara tambayar Halima.

" Naji sauƙi Inna Aunty Mubeena ce tazo ta ƙara marina,wai na bata wayana,nikuma bansan inda yakeba" ta faɗa tana fashewa da Kuka.


" Subhanalli Mubeena kuma? Garin yaya? Yanzu ai ba gida ɗaya kuke ba ko?"

Inna ta faɗa fargaba na ƙara shigarta.


" Eh mana wai ina ƙwacen Mazajen mutane"


Wannan karon ƙaramin dariya ne yaƙwacewa Inna tarasa yaushe Mata dayawa zasuyi hankali,banda haka menene ya haɗa Faisal da Halima.


"Inna maiyasa kike dariya duk ta kubramun fuska fa"


" To Halima ko zaki haƙura ki dawo kano da zama" Inna ta faɗa da tausayawa.


"Idan na dawo Uncle Maysarah zai zo ya aureni?"


"A'a Halima munfa gama wannan maganar dake kince kema kinfasa son shi har fa alƙawari kikayimin" 


Shiru Halima tayi " kinyi shiru Halima ko kin manta"


Dasauri tace"eh Inna"

Dariyar nishaɗi tasa "Allah ɗaya garin babban sam halayyarki da na Halime ta akwai banbanci mai nisa,ita bata karya alƙawari."


Kuka tasawa Inna saboda tace Ita mai karya alƙawari ce kuma ta kira Mahaifiyarta da Halimen ta. Daƙyar Inna ta tsagaita dariyarta sannan ta lallasheta kafin suyi sallama.


Maimakon Halima ta ajjiye wayan sai ta tafi kallon hotuna wanda kusan duk na Marry ne Abokiyar aikinshi kuma mosiyarshi.


Ƙurawa Marry idanuwanta tayi kafin kuka mai sanyi ya kwace mata,hawaye wasu kan wasu.


🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂


A parlourn ya samu Goggo tana kallon labarai.

"Wa nake gani haka kamar Maysarah" ta faɗa da tsananin farin ciki a fuskarta.

"Anya ba ɓatar hanya kayi ba"


"Baki bari nagaisheki ba".Ya faɗa dayanin rashin fara'arshi.


"Ai ganinka yafimin gaisuwarka Angon Yusrah" ta faɗa cikin son sauƙaƙawa kanta sanar dashi baikon shi da Yusrah.


Kamar yanda tayi hasashe hakan ne yafaru don bai nuna yagane ma maitake nufi ba.


"Lafiya dawowar bazata haka" ta faɗa badon tanasa ran samun amsa ba.


"Halima ba lafiya"


"Subhanalli menene yake damunta"


A taƙaice yabata labarin zuwanta Kano da abinda Inna ta sanar da shi,zuwan Mubeena ne kawai bai sako ba acikin taƙaitaccen bayanin nashi.


Jinjina kai Inna tayi,kafin tace "to kai yanzu kana son nata" ta faɗa tana gumtse dariyarta don tasan amsar da zai bata.


Kallonta yafarayi da mamaki kafin ya ɗan girgiza kanshi kamar mai ciwon wuya,alamar a'a.


"Amma maiyasa ka baro aikin ka don kawai tana ciwo Maysarah"


Lion eyes ɗin shi ya zubawa Goggo kamar wanda yake nazartarta.


Dariya tayi irin nasu na manya kafin tace 


"Maysarah anya ba son yarinya nan kake yi ba? Banda haka tayaya zan yarda ka baro aikin ka ne kawai don batada lafiya, kaje kayi tunanin idan har kaji a ranka kanason Halima to nayi maka alƙawarin shigewa gaba wajen nema maka aurenta"


"Goggo maiyasa zan so Halima yarinya ƙarama"


Ya faɗa yanayin Fuskarshi na sauyawa.


"Kaje dai kayi tunani,duk abinda ka yanke zuwa safiya ka sanar dani idan kai bakaso saina tuntuɓi Salim,don zasuyi matuƙar dacewa" ta faɗa tana kallon shi da gefen ido.


Bai ƙara cemata komai ba ya nufi sashen shi.



Bai bawa zancen Goggo muhimmancin dazai yi wani tunani akai ba,don haka kaitsaye bayan yayi wanka ya ɗan ci abinci da Goggo tasa aka kawo mai kwanciya yayi,amma sam saiyaji bai samu nutsuwar dayake so ba hankalinshi gaba ɗaya na kanta. Tunawa da ɗaya wayanshi a hannunta yasa kai tsaye ya lalube wayanshi domin kiranta.


Da kukanta da sam ba hayaniya aciki tasamai bayan ta tabbatar muryarshine.

Har cikin kanshi yakejin kukan nata. Da murya mai tsananin taushi gaske yace.....


Barkanmu da dare ƙawaye na Bismillah mu🍜