MAI KWAĆŠAYI

49

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

``` NAFISAT ALIYU SASAAL```



 ```Page 49```


________"Menene matsalan",maimakon amsa sai ta kashe wayan gaba ɗaya. Lumshe lafiyayyun idanuwanshi yayi,mamaki da ƙarfin halin yarinya na kamashi.

Baiyi niyyar fita ba,don haka yaƙara gyara kwanciyar shi.


A ɓangaren Halima tayi kuka harta gaji tasawa ranta sallama,barcin ƙunci ne ya ɗauketa,tanayi tana sakin ajiyar zuciya alamun tasha kuka.


Sai wajen magrib ya farka,wanka yaƙarayi ya shirya cikin Ferragamo Blue da slide masu taushi a ƙafafuwanshi ya nufi sashen Goggo.


Bai sameta ba,don haka ya wuce sashen Mom Fahima. Tare da Mahaifinshi ya sameta suna hira, da ƙwarewarta wajen iya dukan cikin mutum tafara yiwa Maysarah kirarin Ango kasha ƙamshi da fara'arta amma cikin zuciyarta babu kyawun gani.


Maimakon taga abinda takeson gani fuskarshi sai yayi kamar bai san yaren da take magana ma da shi ba,don a baturen shi ya fara gaishe su bayan ya zauna saɓanin ita da take mai kirarin da yarenshi na Hausa. Daƙyar ta iya amsa gaisuwarshi kafin tashi tabar parlourn gudun kar su gano hassadar dake neman halaka zuciyarta.


Bayan sun ƙara gaisawa kai tsaye Abdulnaseer ya tambayi dalilin wannan zuwan nashi na bazata.

Kamar yanda ya gayawa Goggo haka ya maimaita mai.


Murmushi kawai Abdulnaseer yayi kafin yaÉ—an numfasa saboda nauyin Maganar dayake son yimai.

"Inm nace ba Goggo ta sanar dakai baikon ka da Yusrah ko?"

Girgiza kanshi yayi.

Kafin ya fara magana da muryar dayasan duk munafurcin Mom Fahima dake laɓe bazata iya jiyo su ba.

"Bani da ra'ayin auren Yusrah Daddy,amma komai zai yi dai-dai da kanta zatayi bayani."


"Bayani kuma Maysarah,banason abinda zai lalata zumuncin mu,"


"I know Dad,shiyasa nace zatayi bayani da kanta" 


Kai kawai Abdulnaseer ya jinjina amma bawai don ya gamsu da abinda Maysarah yafaÉ—a ba.



Barcin hour ɗaya tayi tafarka, jikinta duk ba daɗi wannan dalilin yasa taƙarayin wanka bayan wanda tayi bayan tafiyar Maysarah. Bayan ta fito ta shirya cikin LV waist pleated skirt milk color da Black shirt free size sai LV scafe shima baƙi ta ƙulleshi a wuyarta rabin kwataccen sumar kanta na waje. Fuskarta sam babu fara'a.


A haka Maysarah ya murɗa ƙofan a hankali bayan ya nemi izinin da bata amsa mai ba,tunda daga Black Slide ɗin daya haska fararen ƙafafuwanshi take ƙaremai kallo har zuwa Lion face ɗin shi.


Bayan yaƙaraso ya zauna tayi ƙasa da murya wajen gaishe shi badon ta so ba.

" Ina wuni"

"Ina wuni? Menene Ina wuni?"

Ya faÉ—a yana kallon yanayinta da rasa gane ainihin menene matsalarta.

 

Shiru tayi batace komai ba.


"Menene matsalan Halima,nima ai nace ina sonki ko?" Ya faɗa yana motsowa kusa da ita,still batace komai ba sai ƙoƙarin riƙe kukanta da take yi.


"Gobe fa zan tafi Halima,banaso na tafi kina fushi umh"


Tanajin gobe zai tafi tasamishi kuka harda shesheƙa.


Kanshi ne yafara ɗaukar zafi tayaya ma zai iya auren yarinya ƙarama ta haukata mishi kai,shi da yake son soyayya mai tsayawa a rai,dole Macen da tasan kanta ne ta dace dashi ba irin Halima ba.


"Wajen Baturiya budurwa zakaje?" Ba sosai yagane abinda take nufi ba,ya amsa mata da "eh"


Kuka taƙara sawa harda rufe fuskarta," Halima kinada lafiya kuwa,gayamin exactly abinda yake damun ki" ya faɗa yana kallonta da mamakin ita kuma haka Allah ya hilicceta da kuka kamar Jaririya.


Dasauri ta ɗauko wayanshi dake gefenta, kunna wayan tayi ta nemo hotunan Marry ta miƙamai.


"Kinsanta ne"kai ta girgiza

"To menene matsalan".


"Kace wajenta zakaje"

" Ni Halimat" dasauri ta É—aga kanta.

Ya lura idan ya biyemata ƙaramin mahaukaci zata mayar dashi,don haka ya janyo dukka hannuwanta ta sauko ƙasa,kan cushion ɗin dakin ya zaunar da ita shima ya zauna kafin ya fuskanceta da kyau.

"Halima ina sonki kamar Mahaifin ki amma bana aure ba,nayi miki girma amatsayin miji,amma kibari idan kika gama karatu ko wanene ki kawo zanyi muku aure da shi,kina so?" Kallon shi takeyi da iya ganinta kalamanshi suna yimata zafi kamar wuta,kai tsaye abayanin Maysarah yana nufin bayasonta tunda bazai aureta ba,kamar Shukura da Mijinta.

"Halima kingane abinda nake nufi" kanta ta É—aga mai alamun ta fahimta.


A daren aka sallami Halima. Sai dai duk yanda yaso tayi magana taki tanka mai.


Shopping ɗin chocolate da Ice cream kala-kala da duk wani cereals dayasan tanaso yasa akayimata. Amma har Maysarah yabar ƙasar yakasa samun maganar Halima kamar lokutan baya.


Sanin zuwa Maysarah da tafiyarshi lokaci ɗaya yazowa Yusrah da Iyayenta,kuma basu bata damar nuna fushin ko ƙorafi kan abinda yayi ba,ko kiranta da baya ɗagawa Uncle Ghali yace karta damu wuyarta suyi aure.



Duk yanda Mubeena take tunanin ta hanyar da Faisal zai hukuntata abinda ya wuce haka,ya daina yin daren da yake yi da amma zaman gidanshi shi da babu duk ɗaya ne,sannan ko tafiya idan zai yi sai dai taji abakin ƴaƴanta ko abakin surukanta,tunani da zullumin sauyin Faisal ɗin yaƙara tsananta agareta ne yasa duk tabi ta rame.

Iyayenta kuma babu wanda yake ta ita,kullum zancen su Yusrah. Salim ne kaÉ—ai mai tausarta da babban yayan su da baisan asalin tushen damuwarta ba.



Acikin wata bakwai komai na bikin Maryam ya kammala kuma har lokacin Maysarah bai ƙara dawowa ba tun su Goggo na faɗa har sun haƙura saboda ƙorafinshi kullum akan aikin sa ne.


Ta yarda da Matsayinta ta kuma gane kuskurenta,nayin shishigi da ganganci a rayuwar waÉ—anda sukafi Ć™arfin, Bayan tafiyar Maysarah da wata É—aya labarin mutuwar Shukura ya riske su a Makaranta,wanda ake kyautata zaton Mijin tane tamishi laifi yayi mata dukan da har sai da kanta ya kumbura,kwananta biyu a Asibiti ta rasu,kuma dama ta É“angaren Uba suka haÉ—a dangi da Mijin da iyayenta suka aura mata saboda Ć™wadayi da son zuciya tunda su É—in talakawa ne sosai. Sunaji suna gani mutuwar Shukura yabi ruwa tunda shiÉ—in mai kuÉ—i ne Halima tayi kuka mara iyaka sai takejin inama ita mai kuÉ—i ce ta biwa Shukara haƙƙinta.

Ta ɗauki darasi da samun nutsuwa mai girma a gangar jikinta dama zuciyarta,sai takoma shiru-shiru ta dawo batada wata ƙawa a Makarantar su,luyakan Wayarta da Faisal yake kira da shi kanshi Maysarah duk ta zubar da su.burinta ta kammala secondry school ɗinta ta koma gaban Inna su cigaba da gwagwarmayar Rayuwa talaucin su.


Gyara kwanciyarshi yayi,tunani abunda ya raina na neman birkita duk wani nutsuwan daya rage mai,ya rasa mai yake mishi daÉ—i,idan yasota ya cuceta,tayaya zai yi rayuwar aure da mitsitsiyar yarinya irinta aganinshi cutar zai yi yawa.


Kiran Goggo ne yaƙara shigo mai, a kasalance ya ɗaga kuma ko da bata kira ba,yazame mishi dole yaje yaga yaya ta koma,a wani hali take ciki,maiya canza ta takoma batason jin ko muryarshi ne.



Tun safiyar ranar jikin Halima yake a sanyaye,don duk ranar da kafin ta fita ta tuna bazata ga Shukura ba idan taje Makaranta sai taji burin tayi ilimi mai zurfi duk yabar kanta.



Ko da taje Makaranta takasayin komai,ga wanda yasanta a baya yana ganinta zaiga uban ramar da tayi, Uncle Faisal da Mallam Aminu da Aunty Rahina sun tambayeta har sun gaji.tunda babu wanda yasan Shukura balle ta basu labarinta Inna ce kawai tasani itama kuma Haliman ta ɗauke ƙafa da zuwa duk ƙarshen wata don saitayi wata uku sannan take zuwa shima kwana biyu takeyi ta dawo haka Inna zatayi ta yi mata faɗa dags ƙarshe ta koma lallashinta.


Sai Six pm Driver yayi parking a harabar gidan, a kasallace ta sauko,da idanuwanta da suka É—an tasa saboda kukan data sha a Makaranta.


Paul Smith Black ne ajikinshi wanda ya ƙara fito da hasken shi da tsananin ramar dayayi na tilasta haramtawa kanshi abinda Allah Ya halatta mai.


Da dukka idanuwanshi da damuwar rashin ganinta yasa sukayi weak yake kallonta da tsananin ramar da itama tayi.


Batayi tsammanin ganin shi ba.wannan dalilin yasa taji komai data yaĆ™a a baya na neman dawo mata sabo fil, da sanyinta daya haÉ—e da damuwa ta nufeshi. hannayenshi ya buÉ—e mata dukka yana lumshe idanuwanshi....✍🏻


Allah yayi mana tsari da Mazaje masu dukan matan su.


Barkanmu da dare🍜