50
💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔
( shi ya san gidan mai rowa)
```By```
``` NAFISAT ALIYU SASAAL```
```Page 50```
________Da ƙaramin kukan daya ƙwace mata ta shige jikinshi sluggishly.
Bai cemata komai ba,har kusan few minutes sannan ya rage tsahon shi zuwa dai-dai saitin kunnunta na dama.
"Ki daina kuka ko na koma bakyason ganina?" ya faɗa da ƙaramin sauti mai daɗin dayasata saurin girgiza kanta.
Sakinta yayi yana ƙoƙarin kallon fuskarta,dasauri ta juya har da haɗawa da ɗan gudunta tanufi sashen su.
Ajiyar zuciya mai sanyi ya sauke. Sannan ya nufi jerin motocin dake jiranshi driver motar Maysarah da shine a waje yaketa leƙe da gulmar ganin ƙwaƙwaf. Dasauri ya buɗemishi yashiga. Mamaki da al'ajabin son sanin wacece Halima a awajen maigidan nashi na kama shi.
Bata biya wajen Aunty Rahina ba kamar yanda ta saba kai tsaye ɓangarenta ta shige kuma tayi sa'ar babu kowa a Central parlourn.
Takasa yarda ma Maysarah ta gani,sai takejin kamar mafarki take yi, silalewa tayi ta kwanta ƙasan lallausan carpet ɗin da'aka ƙawata ɗakin dashi.
MUBEENA tayi kuka kuma babu irin magiyar da batayiwa Faisal kan yayi haƙuri ta tuba ta daina ba,amma yaƙi sauraronta ƙarshe sai da ciwo mai zafin gaske ya kwantar da ita. Wannan dalilin ne yasasanta tsakanin su bayan ta warke ya ƙara tunatar da ita abinda kullum yake gayamata,karta kashe nata auren da janyo rikicin da zatayi datasani nan gaba,banda shirmenta ta kwana da sanin ko zai mutu Uncle Suraj bazai taɓa karya alfahari da jin kanshi yabari ya auri Halima data fito daga dangin talakawa gaba da baya ba,amma sam Mubeena taƙi fahimtar hakan. Kuma har lokacin dayake ƙara maimaita mata bawai ta yarda bane ita dai burinta ace Halima tabar cikin zuri'arsu gabaki ɗaya kuma har abada.
Domin yanda tayi Imanin duk kyautawawar da Maysarah zaiyiwa Halima bazaisa ya taɓa son ta ba,batayi Imanin Faisal zai iya gujewa son Halima ba. Abinda Mubeena takasa ganewa da fahimta shine,rubutaccen ƙaddara ne yasa Motocin Maysarah suka buge Halime harta rasa ƙafafuwata sannan daga baya taɓacewa ganin dukkan su shida Faisal, amma ƙaddarar sai sun sake haɗuwa har ƴarta tayi rayuwa acikin su yasa Mubeena faɗawa soyayyar Salmanu duk tasan baza'abari ta aure shi ba. To dukka ina zata kai wannan girman ƙaddarar da ƙarfin Ikon Allah? zurfafa sai taga bayan Halima a cikin zuri'arsu zai iya janyo mata abinda zata yi datasanin shi har abada.
MAYSARAH bai samu dawowa ba sai dare sosai, wannan dalilin yasa bai nemi Halima ba, don gaba ɗaya agajiye yake hutu kawai yake buƙata, don ko su Goggo basu samu damar ganinshi ba.
Halima bata damu da rashin ƙara nemanta da Maysarah baiyi ba don a kan kunnen taji sanda Motocin shi suka shigo gidan.
Amma duk da haka sai ta kasa barci, ramar da ta ga yayi baƙaramin tsaya mata arai yayi ba.
Kasa jurewa tayi tafara neman inda take tunanin ta zuba layukanta,amma bata gani ba,wasa-wasa sai da tayi wajen hour tana nema kafin ta gansu acikin wani tsohon jaka da Uncle Faisal yayimata kyautarshi last year.
Kai tsaye kan waya ta mayar da layukan,Zuciyarta na bugawa dasauri-dasauri ta lalubo numbern shi,sai dai idan taje zata danna kira sai ta fasa,to idan ta kirashi ma mai zatacemai shine tambayar da tayiwa kanta,cikin suɓutar hannu ta danna kiran kai tsaye ya tafi, garin ƙoƙarin ta katse sai ta fita daga wajen kiran gaba ɗaya hannunta na rawa ta katse kiran da batayi tunanin yashigaba don bataji ringing ba.
Dai-dai lokacin daya kimtsa cikin Pyjamas masu tsananin taushi idanuwanshi na lumshewa da kansu saboda barcin dake cikin su, wayoyinshi ya janyo domin kashe su, idanuwanshi sukayi katari da kiran Halima awayan da Mutane kaɗanne keda Number.
"Halimah"ya faɗa da ƙaramin sauti ya shafa saman fatar lumsassun idanuwanshi,girman abinda yakeji akanta bazai barshi yayi barci batare da yaji damuwarta ba,tunda yasan layukanta sunjima a ƙasa,kai tsaye ya kira Numbern sai dai bata ɗaga ba yaƙara kira nan ba bata ɗaga ba.
Kai tsaye saukowa yayi daga gadon ya zura slippers.
Layin Aminu ya fara nema, lokacin 11:30pm
Lokacin Aminu nanan a maƙale a Parlourn yana chating ɗin satar da maza sukeyi, don Rahina nacan barcinta yayi nisa.
Da farko tsabar shaukin hirar da suke da sabuwar budurwar shi bai lura da kiran Maysarah ba,saboda a silent yasaka wayan kuma dama bai taɓa kiranshi da layin ba.
Sai da kiran yaƙara shigowa sannan ya amsa.
Da Husky voice ɗin dake tsoratar da Halima yayiwa Aminu magana ya buɗemishi ƙofa.dasauri Aminu ya zabura gabanshi na faɗuwa Dafatan Allah Yasa bawani laifin yayi ba.
Sai da yaɗan dakata kar yayi zargin zaman jiran maiyake yi a Parlourn sannan ya buɗe mai.
Sama-sama ya amsa gaisuwar Aminu ya nufi ƙofar ɓangaren Halima.
Cikin sanɗa ta taso ta buɗe ƙofan sashen nata saboda tanajin sanda yake amsa gaisuwar Aminu,dama kuma a tsorace take,shiyasa takasa zama.
A hankali ta kwanta a tree sitter ta lulluɓe har kanta da blanket ɗin da ta ɗauko bayan ta kashe hasken komai sai dim light.
Knocking yafarayi yaji shiru kawai yana murɗa handle ɗin yaji ƙofan ya buɗe.
Ganin Aminu na tsaye har lokacin yayi ƙasa da kanshi yasa ya ɗan juyo da cewa.
"Bamatsala idan zan fita zata rufe da kanta"
"Okay Sir".
Aminu yafaɗa yana juyawa dasauri yakoma na su Parlourn ya cigaba da chating ɗin shi,haɗe da waiwayen hanyar Bedroom ka da Rahina ta kama shi.
Murmushin da bai shiryawa bane yaƙwace lips ɗinshi, bai taɓa ganin yarinya mara wayo irin Halima ba,ta buɗemai kofa amma takashe wuta parlourn, maitake nufi? Tayi dabara🤣
Yana kunna switch ɗin Parlourn ya hango Mutum nannaɗe da blanket.
"Halimah are you Okay" ya faɗa da sautin da bataso saboda yanayin yanda ta kwanta kamar mara lafiya.
Tsit tayi jikinta na rawa da duk addu'ar dayazo bakinta.
Ƙarasowa yayi ya yaye blanket ɗin, kyakkyawar fuskarta ya bayyana,fatar idonta na rawa alamun idanuwanta biyu.
"Halimah" ya faɗa yana tsugunna dai-dai Fuskarta yana kai hannunshi gefen fuskarta da wuyarta don jin ko fever ne ke damunta.
A zabure ta miƙe saboda batayi tunani zai kai hannunshi kan fuskarta ba.
Kasa motsi yayi yana kallon kyakkyawar fuskarta dake sunkuye.
"Baki da lafiya ne"
Kai ta girgiza
"Banason body language"
"Lafiyana ƙalau" ta faɗa da sanyinta.
"To maiyasa kike Kirana kuma na kira baki ɗaga ba,kinason ɗagamin hankali ko Halimah"
Idan yakira sunanta ƙara kashe ta yake yi da ranta don komai nashi mai aji ne da daɗi sauraro ko gani.
"A'a" ta faɗa a hankali.
"Menene matsalan to"
Shima yafaɗa yana zama agefenta haɗe da kallonta da lumsassun idanuwanshi.
"Maiyasa to karame fuskarka yayi ƙarami ba babba ba kamar da"
Ta faɗa tana rufe Fuskarta.
Da iya ganinshi yake kallon ta, abubuwan dayake ƙorarin dannewa suna tasowa da kansu,sanyi da raunin da bai san yanadashi bane yaji yana shigarshi.
"Tunani Halimah" ya faɗa kamar ba waccan Maysarahn ba.
Dasauri ta ɗago Fuskarta gaba ɗaya tana ware fararen idanuwanta akanshi,shima har lokacin kallon ta yake yi,da wani irin kallonda, da Halima tanada da wayo kaitsaye zata canki menene a cikin zuciyar shi.
"Maiyasa kake tunani?" ta faɗa kamar zata yi kuka.
"Zaki sani Halimah amma sai kin ƙara wayo" ya faɗa still yana kallon cikin idanuwanta.
Shagwaɓe Fuskarta tayi kamar zata yi kuka.
"Ohhh nooo Halimahhh".....✍🏻
Soyayya daɗi idan har da kai zanayi in ba kai wazana kalla abayan rai......🎻🎻🎻🎻🥁🥁🥁🎹🎹
Barkanmu da dare ƙawayena🤝