MAI KWAƊAYI

51

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

``` NAFISAT ALIYU SASAAL```



 ```Page 51```


________"not again Halimah" ya faɗa yana miƙewa gaba ɗayanshi,saboda cigaba da zamanshi zai iya ruguza duk wani ƙarfin hali daya rage mishi


Kasa magana tayi,sai ƙwallan daya cika kyawawan idanuwanta.


"Ki bari next time zangayamiki kinji"


Still bata amsa mai ba sai kallonshi da takeyi kamar bazata ƙara ganin shi ba.


Hanyar fita yayi tana binshi a baya har living room.


Yana kallonta tana kallonshi kowannen su idanuwanshi kamar zai haɗiye ɗan uwanshi ta rufe ƙofa. Bayan ta rufe ƙofar jingina bayanta tayi hawaye masu ɗubi na bin ƙuncinta.


Halima na tsananin son Maysarah,irin son da yake wahalar da mutum mussamman ga yarinya ƙarama irinta,amma dagaske Maysarah najin abinda Halima takeji kuwa?.


Stress da rashin bawa duk abinda zai dameshi muhimmaci da sanin muhimmancin barci a rayuwar dan adam yasa Maysarah yin ishashshen barci,saɓanin Halima da raba dare tayi tana kuka,da asuba takira Inna.

Wannan karon faɗan da batasan Inna ta iyaba tayi mata,kamar zata fito daga wayan ta zaneta.


Haƙuri da danga tasawa zuciyarta. Da sassafe ta shirya tafiya school ko breakfast batayiba domin batajin akwai abinda zai samu shiga cikinta.



Sai wajen 12:39pm Maysarah yafarka tun bayan sallar Asubahi.sanin tana school yasa bai nemi wayanta ba. Bayan ya kimtsa gidan su ya wuce.


Baƙaramin murnar ganinshi Goggo ta nuna ba kamar yanda ta saba sai dai na wannan karon ya haɗe da ƙorafin maiyasa shi rama haka.

Duk bai amsa mata ba.


A wajenta yayi Breakfast kafin ya samu ganin Mahaifinshi.


Shima bayan sun gaisa kai tsaye tambayar dalilin dayasashi rama yayimai.


A daidai wannan lokacin Goggo ta taho domin su taru suji menene asalin matsalarshi tunda ita yaƙi gayamata may be idan yaga Mahaifinshi zai faɗa.


"Daddy.." sai kuma yayi shiru bawai kunyar faɗa yake ji ba amma yanaganin kamar akwai cutarwa a nashi tunanin.


"Uhm Maysarah ina jinka,baka taɓa ɓoyemin ba kuma banaso mufara daga yau"


"Daddy Halimah"

"Uhm maiyasameta anƙara samun wata matsalar ne"


"A'a" ya bashi amsa yana ɗago idanuwan da raunin su ya bayyana a sarari.


"Then what?" 

"Maysarah karka lalata zumuncin mu,da bayanin da kake ƙoƙarin yimin,bana ƙin jinin duk abinda idanuwanka suka gani kuma suka nuna suna so,amma a wannan karon ina roƙon da ka yafemin bana buƙatar jin bayanin komai daga bakin ka,idan har na fuskanci inda ka dosa"


Ya faɗa cikin sanyin murya da takaicin karon farko da Maysarah ya nemi abinda kuɗinshi bazasu iya siyamishi ba sai ta sanadiyarshi amma yakasa yimai.


Bai ce komai ba,kuma bai motsa ba.


Goggo dake bakin ƙofa komawa tayi,takaici da zafin zuciyar halayyar su Ghali na kamata,tarasa halin wa suka biyo nason duniya da tursasa ɗan uwan su yin abinda suke so. 


Tasowa Abdulnaseer yayi yadawo kusa da Maysarah jikin su na gogar na juna kamar Yaya da ƙani.


"Kayi haƙuri,ka cigaba da ɗaukar nauyinta,Allah zai baka lada,amma batun so ko aure babu shi a tsakanin ku har abada,Yusrah ce Matarka, a karon farko ka nemi abu nakasa yimaka in...."


"Daddy ba fa abinda nake nufi ba kenan" ya faɗa da tiriri mai zafin dake fita daga zuciyarshi,wani abu mai tsananin zafi na taso mai a ƙirjinshi.


Kafin Mahaifinshi yasamu damar ƙara mishi wani zafin sai ya miƙe.

"Daddy akwai aikin da zanje nayi,i will back" ya faɗa yana kama hannun Abdulnaseer dake rawa takaici da jin zafin abinda yake ƙoƙarin jefa su shida ɗanshi na kamashi.

"Okay take care" ya faɗa shima yana jinjina mai kai.


Ɓangarenshi ya koma ya ƙebance kanshi,kamar ƙaramin yaro haka yake kukan taran numfashin ɗanshi da yayi duk don farin cikin su Ghali.


 Dayawan mutanen kirki da suke zuwa a ƴan uwan wa sun mu,haka suke shan wahala wajen faranta ran ƴan uwan da tsinke bazasu iya sadaukarwa a kan su ba.


Kafin dare yayi Jinin Abdulnaseer yayi hawan da dole aka kai shi Asibiti.


Sai a lokacin kuma kowa yasan tun rana Maysarah yabar ƙasar,ta hanyar driven shi.



Ƙaramin rubutu bana waya ba yayi a pepper ya bawa Aminu ya bata da handwriting ɗin shi mai tsananin kyau da birgewa, " Bye bye Miss you my baby" shi ne abinda ke rubuce a ɗan ƙaramin takadda dake ƙamshin tsadadden turarenshi.


Duk da tana da ƙarancin shekaru, ta fassara rubutu Maysarah da fassarar dayasata yin kukan daya kwantar da ita zazzaɓi kafin safiya. Kafin tayiwa kanta alƙawarin mantashi har abada kamar yanda Inna take yawan gayamata.




Bayan Abdulnaseer ya samu sauƙi,cigaban shirye-shiryen bikin Maryam yaƙara ɗaukar harama.



Bayan wasu kwanaki da sallamo Abdulnaseer, nutsuwar Goggo ya dawo jikinta.


Video call ta kira Maysarah bai ɗaga ba,sai gashi washe gari ya kirata da kanshi.


Da kuka da magiya Goggo tafara ko gaisuwar shi bata amsa ba.


Kallonta kawai yakeyi da idanuwanshi da tuni sun jima da komawa jajayen ƙarfi da yaji,saboda sauyin halayya da yasamu na shaye-shaye sama-sama. Dama can shi ba mai rauni da tausayin mutane bane soyayya ce taso sauyashi,kuma tashin farko mutum mafi soyuwa a gareshi yaƙi bari ko da bayani ne yayi,ya samu damar rage raɗaɗin abinda yakeji amma yatari numfashin shi. Duk don kar ƴanuwanshi suji ba daɗi,alhali su farin cikin ta su ƴar suke yiwa fighting.


Magiyar ya dawo bikin Maryam da baifi saura wasu watanni ba a yanda suka tsayar take mishi.


Kai kawai ya ɗaga mata,daga haka wayan ya ɗauke,batare da Goggo tasan dalili ba.


Kiranta yaƙarayi voice call, Mahaifinshi ya tambayeta,kuka Goggo tasa,tayaya tana raye Ghali zai tarwatsa mata zuri'a wallahi sai ta ɗauki matakin da zai sosa ran shi,sai dai yahaɗiyi zuciya ya mutu.


Sashen Abdulnaseer ta tafi da wayan.batare da sanin Maysarah ba don cigaba tayi da janshi da hirar da ba samun amsa takeyi ba.


Muryar Mahaifinshi kawai yaji a kunnenshi.

"Maysarah shine ka gudu ka barni" Abdulnaseer ya faɗa da raunin Muryar marasa lafiya.


Tashi Goggo tayi ta basu waje ranta nayi mata sanyi.


 

Har gidan Maysarah Goggo tasa driver ya kaita wajen Halima,sai taga itama duk ta rame.


Bayan Goggo ta huta sai ta keɓe da Halima,tambayar tanason Maysarah tsakaninta da Allah bai mata tsufa tayimata.

Girgiza kai Halima tayi alamun bata son shi.

"Halima ki saki jikinki kinji ki gayamin tsakanin ki da Allah" nan ma ƙara girgiza kai tayi kuka na ƙwace mata.


Duk wani alamu da Goggo takeson gani ta gani duk da Halima ta ƙaryata hakan.



A ɓangaren Mubeena abubuwa sunyi kyau kamar gaske.


Sai dai ana saura wata biyu bikin Maryam aka kawo lefen daya tashi kan kowa don harda mukullin ɗanƙareren motar daya kusa sa iyalan gidan Uncle Ghali kwanciya ciwon ƙarfi da yaji. Musamman kalar dangin Mijin da irin motocin da suka zo kawo lefen Maryam da shi,ko a cikin masu kuɗin su ɗin mutane ne masu fariya da ɓarnar dukiya wajen aure.Ita kanta Maryam taji daɗi duk da ba wani son Mijin take ba.


Daga wannan ranar Mubeena ta daina gane kan Faisal,abu kamar wasa,zuwa shuɗewar wata sai Faisal yadaina ƙaunar zaman gidan da garin ma gaba ɗaya.

Tunaninta da komai sai yakoma kan Halima,kuma a wannan karon bazata yarda ba matsawar ta tabbatar Halima ce sila.


Abinda bata saniba acikin ƙannen Mijin Maryam da suka zo ganinta ranar da aka kawo lefen da dadddare Faisal yayi katari da mai tsananin kama da Halima acikin su,sai dai ita ɓaka ce kuma ta girmewa Halima a shekaru,amma kyakkyawar gaske ce.

Tun daga lokacin Faisal yafita nutsuwarshi don har Muryar su,na yanayi dana Halima.


🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂


Wata rana asabar dayayi dai-dai da ranar fara shagalin bikin Maryam.


Faisal ya samu kiran Aminu kan ga Halima ta kafe ita Kano zata tafi kuma kwana biyun nan batason cin abinci duk ta ƙara ramewa.

Cikin jimami da son Halima dayaƙi barinshi gaba ɗaya har lokacin yace Aminu yakai mata waya.

Duk kalaman lallaɓawa da ban baƙin da Faisal yake mata kamar zai cinyeta Mubeena dake bakin ƙofa tanaji,.

Da kuka ta wuce ɗakinta.

Batare da tunanin me hakan zai haifarba ta kira layin Yusrah dake wajen kwalliya itama duk ta rame,saboda rashin ɗaga wayarta balle kiranta da Maysarah bayayi,amma saboda cikar muradi duk tajure.


Bayanin komai ta juyewa Yusrah a taƙaice. Sai dai ita Yusrah zamanta a gidan Maysarah da ko su kansu basu san da shi bane yafi tsaya mata arai bawai ƙorafin Mubeena ba.


"Mubee kibari bayan an ɗaura aure baƙi sun ɗan ragu,da kaina zan rakaki muje muci Ubanta mu kaita har gaban su Daddy ayiwa kowa iyaka da ita." Ta faɗa cikin tsananin kishi da son sanin wacece ita.....✍🏻