52
💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔
( shi ya san gidan mai rowa)
```By```
``` NAFISAT ALIYU SASAAL```
```Page 52```
________Sosai Mubeena taji sanyi a ranta,ta kuma gamsu da shawarar Yusrah É—ari bisa É—ari.
Kamar yanda Aminu ya sanar da Faisal haka ya sameta da duka kayanta a manyan luggage har guda huÉ—u,tasha kuka idanuwanta duk sun kumbura ga wani irin rama da tayi.
Daƙyar ya lallasheta tayi shiru Aminu ya mayar da kayanta ciki.
Bayan ta É—an ci abinci da Faisal ya tursasata,sai ya dawo living room É—in daya raba tsakaninta dasu Mallam Aminu.
Gwada kiran Maysarah yayi kai tsaye saboda yaji ta bakinshi duk da bai sa ran zai É—aga kiran ba,don rabonsu da waya tun bayan tafiyarshi.
Bugu na biyu yaÉ—aga.
Batare da jiran gaisuwarshi ba Faisal yafarayi yimishi bayani.
"Idan ta matsa ku barta ta tafi"
"Ta tafi fa kace Maysarah"
"Yes Faisal, tana da Æ´ancin ta yi rayuwa a duk inda take so,she is matured enough!!"
Ya faÉ—a da murya mai zafin gaske.
"Hmmm I'm sorry" Faisal ya faÉ—a yana katse kiran,baiga abunda faÉ—a ko É—aukar zafi ba,shima yace she is matured enough then what make him angry?.
Halima dake jin abinda Faisal ya maimaita ta kuma fuskanci abinda Maysarah yace, sai taji ta tsane su dukkan su har garin da take ciki.
"Halima kiyi haƙuri, In Sha Allah idan mungama bikin Maryam,zan mayar dake wajen Inna da kaina I promise you, don haka ki saki jikinki kinji"
Kai ta ɗagamishi idanuwanta na ƙara soyewa da tsananin ɓacin ran dayafi ƙarfin hawaye.
Har Faisal ya fita ta kasa motsi, sai takejin kamar har a gama bikin Maryam yayi mata nisa.
MAYSARAH,a ranar yayi shaye-shayen da bai taɓayi ba,zuciyarshi na ƙara ɗaukar zafi da bushewa akan komai. Sai dai bayajin hakan zai ɗore,kuma ya zama dole ya canza komai.
Bikin Maryam ya bayar da ma'ana sama da yanda suke so saboda tsadaddiyar wedding planner da ta shirya bikin ƙwararriya ce.
Babu wani abu ɗaya a bikin daya birge Yusrah da Mubeena saboda zuƙanta su dake hargitse da burin cikar muradin su bayan bikin.
Sama da Angon Sumayya haka Angon Maryam yayi kyau da ɓarnar dukiya ga maroƙa,babu wanda yayi tsamnin ganin Maysarah a ɗaurin auren.
Sai gashi a yanayin da ya sa ciwon Abdulnaseer tashi daƙyar yasa driver ya kaishi gida,a sirrince ya kira likitan dayake dubashi,batare da sanin kowa ba.
Ko makaho ya shafa wannan Maysarah da waccan yasan akwai tarin banbance-banbance.
Mussam bakinshi dayayi wani irin duhu fuskarshi tayi rama sosai,saboda bashi da wani mai gayamishi gaskiya ko maikula da damuwarshi.
Lokacin sanyi ne sosai don haka ba kowane ya lura da zuwanshi da tafiyar shi ba saboda yanayin shigar ƙananan kayan dayayi da ɓakin shade amma duk da haka dogon hancinshi da bakinshi kawai Abdulnaseer ya kalla ya ganeshi.
Aminu ne mutum na biyu da yasan da zuwanshi,domin shi yakaishi gida. Dagashi babu wanda yasan da zuwanshi kuma yaja kunnenshi da bayason kowa ya sani.
Tun a yammacin ranar akazo tafiya da amayar Ilorin saboda dama bayarabe ne, kusan dukka dangi sun tafi kai Amarya daga Abuja zuwa Ilorin saboda shagali na musamman da aka shirya acan.
★washe gari zuwa sha ɗaya na safe ragowar mutane duk sun tafi sai ƙannen Goggo maza da ƙannen Mahaifin su Uncle Ghali maza da mata.
Gaba É—aya a babban living room É—in gidan Uncle Suraj suke hira har da Goggo da sam hankalinta na kan Abdulnaseer da duk yazama shiru-shiru idanuwanshi duk sun faÉ—a kamar wanda yayi jinya mai tsaho.
Tsaf ta shirya cikin baƙin Abaya mara ado tana kiran Uncle Faisal idan bazai zoba zatayiwa Mallam Bala waya yazo ya tafi da ita.
Kamar Iska haka Yusrah dake sanye da fitted gown dai-dai jikinta sai scafe da ta yane kanta dashi da Mubeena da itama kusan shigar dake jikinta kenan sai ita bai kamata sosai ba.
Aminu suka fara gani yana É—aure igiyar takalmin shi.
A wulaƙance Yusrah dake ganin duk wannan dukiyar da Mijinta ya ɓarnatar duk don waɗannan dirty things ɗin yayi su tace" ina Halima" ta faɗa da gurɓatacciyar hausarta saboda turancin dayafi kama harshenta.
Ƙofar Halima ya nuna musu ƙirjin shi na bugawa.
Tanajin knocking ta taso dasauri a tunaninta Faisal ne.
Ganinta bai ƙarawa zuciyarsu komai ba sai baƙin ciki,don duk kyawun da Yusrah takeji dashi ajikinta takejin Halima ta fita,kuma ita tun tana yarinya ta tsani ko da abota ne da wanda yafita kyau.
Da zafin zuciya Mubeena ta sauke mata mari mai zafi,ganin rashin tsoron ganin su a idanuwan Halima. Wanda Yusrah ta sauke mata sai da hancinta ya ɓalle da jini.
Kamar kayan wanki haka Mubeena da tafi Yusrah girma ta fara jan wuyar rigar Halima.
Ganin zasu sata a mota kuma batasan Inda zasu kaita ba yasa ta fara kokawar bazata shiga ba. A nan suka taru sukayiwa Halima dukkan daya kusa haukata kanta rabin wuyar rigarta duk sun yagashi kwantaccen gashin kanta da yafi tsole idon Yusrah duk sunyi biji-biji da shi don da tanada almakashi a kusa saita yankeshi.
Baba mai gadi da ragowar ma'aikan gidan duk Yusrah korar su tayi da hayaniyarta,na ita Matar Maysarah ce.
Duk kiran layin wayar Maysarah da Aminu yakeyi yakasa samu dole ya koma kan na Faisal.
Bai tsayajin bayanin Aminu da kyau ba saboda ihun da Rahina takeyi,yabar gida.
Sai da suka tabbatar ko hannunta bata iya É—agawa sannan suka bawa wani ma'aikaci umarnin ya É—auketa ya sa musu a mota.
Da mugun speed suka bar gidan.
Wani ma'aikacin suka ƙarasa ya ɗauko musu ita har cikin living room ɗin da su Goggo suke.
"Meye wannan" dukka mutanen wajen suka haÉ—a baki wajen faÉ—a banda Abdulnaseer da yayi tsit a zaune.
Cikin kuka har da shesheƙa Mubeena ta maimaitawa Mahaifinta wacece Halima a taƙaice kafin takai aya itama Yusrah ta ɗora da zaman Halima a gidan Maysarah da su kan su basusan da shi ba.
"Ina Faisal É—in" Uncle Ghali yafaÉ—a kamar mahaukaci,babu wanda bai saki baki yana kallon ikon Allah ba.
A dai-dai lokacin Faisal ya shigo don Aminu ya sanar dashi sun tafi da ita. Tun kafin ya iso gare su Uncle Ghali ya nufeshi mari mai raÉ—aÉ—i da zafi ya sauke mai.
"Faisal! Waye kai har da zaka wulaƙantamun yarinya akan ƴar mabarata" ya faɗa da ƙarfin murya sai dai kafin ya dire aya yaji Muryar ƙaninshi kuma Mahaifin Faisal don tuni Mommyn su tasa kuka mai ƙarfi don har zuciyar taji marin daya saukewa ɗanta." Idan har ni na haifeka yanzu basai anjima ba ka sakar mishi ƴar shi, yanzu!!!"
Yana rufe baki Faisal ya saukewa Mubeena saki uku.
Salati da sallalmi ƙannen Mahaifan su suka ɗauka.
Allah Sarki babu wanda yabi takan Halima dake numfashi daƙyar sai Abdulnaseer dake kallonta kamar zai yi magana amma bai motsa ba,kamar baya wajen.
"Goggo A'isha haka kike kallon wannan shaiɗancin,zuri'arki na neman lalacewa saboda kwaɗayi da son zuciya" ƙanin Mahaifin su ya faɗa kamar zai yi kuka.
"Wallahi Salahu Ɗan juma da Matarshi sun fitine ni narasa halinwa yaɗauko na tsananin son duniya" ta faɗa da tsanin kukan baƙin cikin abinda ke faruwa.lallashinta suka komayi.
Zama Uncle Ghali da Uncle Suraj dasu Mubeena da take kuka kamar zata mutu sukayi Mahaifiyar su da tayi fiƙi-fiƙi da ido na lallashin ta. Raɗaɗin jin kamar hukuncin sakin da yayimata yayi kaɗan yasa Faisal kasa zama yana tsaye har lokacin idanuwanshi na kan Halima.
Fitar su baifi da Minti É—aya ba Maysarah ya farka sai da yayi wanka yana shirin fita yaga tarin kiran Aminu dana Faisal.kai tsaye Aminu ya fara kira don yasan matsalar Halima ne kaÉ—ai zaisa yayi mishi Miss called haka.
Da kuka kamar mace Aminu yake yimishi bayani.
Sai da ya gama sauraron shi tsaf sannan yabashi umarnin ya fito da mota ya kuma gayawa Dr Aryaan gashinan zuwa da ita.
A mota yabar Aminu na jiranshi, Sallama kawai yayi musu ya É—auki Halima dake yashe a tsakiyar parlourn, sai lokacin suma sukaga rashin dacewar barinta a haka,har lokacin Goggo kuka takeyi.
Sai da ya kwantar da ita sannan ya kulle motar batare da kallon Fuskarta da duk ya kumbura da duka ba,saboda kallon idanuwanshi a wannan lokacin zai iya sumar da ita,tunda dama akan gaɓa take.
Duk wannan haniyar Mom Fahima na can da Sumayya tana ƙara gyarata saboda ranar zata koma.
Kai tsaye yana dawowa living room É—in gefen Mahaifinshi ya tafi ya zauna.
Duk yanda yaso ɗaurewa ya buɗe baki yayi magana ko da gaishe su ne yayi yakasa saiyakejin kamar idan ya buɗe baki kuka ne zai ƙwacemai.
Kowa kallonshi yamayar kan Maysarah har da Goggo dake kuka.
"Saukar yaushe? Kaima ciwon kayi ne Maysarah" Kakanninshi suka haÉ—a baki wajen faÉ—a girgiza kanshi yayi.
Yusrah daga nesa kamar zata cinyeshi saboda kallo.
Ganin Maysarah da Yusrah a waje É—aya ga dukka kawunnan su yasa ran Uncle Ghali yayi haske don a yanzu zaisa a É—aura auren su don Abdulnaseer bai isa yayi musa ba.
"Naga daga kai har Abdulnaseer duk kun zama bebaye" Baba Salahu yaƙara faɗa cikin jimami.
"Daddy good morning"Maysarah ya faɗa da ƙaramin sauti.
Sai dai Abdulnaseer bai amsa mai ba.
"Daddy kayi haƙuri na daina"ya ƙara da sautin da Abdulnaseer ɗin ne kawai zai iyaji. Still bai amsa ba
A hankali ya juyo da kanshi wajen Mahaifinshi nashi sai yaga wani waje can daban yake kallo. Hannayen shi yaje kamowa da sunan yabashi haƙuri sai ya ga ya zube a jikinshi gaba ɗaya.
Ihun daya girgiza parlourn Maysarah ya saki bayan ya tabbatar da Mahaifinshi ya rasu.
Tun zubar da Halima da sukayi aƙasa kamar mara rai ajiki,Allah ya karɓi ran Abdulnaseer.
Duk yawansu awajen kasa riƙe Maysarah sukayi,yayi rantsuwar sai ya kulle Uncle Ghali da Yusrah yafi a ƙirga. Da iya gudun su suka faɗa mota shi da iyalanshi.jikin kowannen su rawa. Samun damar tsere mai da sukayi ne yasa yasaki ihun dayafi na farko kafin ya zube kamar gini babu numfashi a jikinshi.
Wannan shine abinda Faisal yajiyewa Mubeena. Don bata isa ta canza ikon Allah da nata muradin ba.
🥹 Barkanmu da dare