MAI KWAƊAYI

53

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

``` NAFISAT ALIYU SASAAL```



 ```Page 53```


________Duk ƙarfin AC dake lafiyayyan living room ɗin daya lamushe manyan kuɗaɗen Maysarah da suke sata,Uncle Ghali da dukka Iyalanshi gumi suke yi.


Ba wanda ba ya kuka a cikin su sai Uncle Ghali da nashi idanuwan sukayi matuƙar kaɗawa sukayi jajir. 


Har gaban abadan yayi zubewar da bazai taɓa kwasuwa ba, Mutuwar Abdulnaseer na nufin rushewar tashi rayuwa ne gaba ɗaya.


A haka Salim ya same su shima nashi idanuwan babu kyan gani saboda gidan Uncle Suraj yafara biyawa,bai samu kowa ba, duk suna Asibiti,a bakin ma'akantan gidan da ke ta kuka ya samu labarin abinda ya faru.



Sun samu tabbacin Mutuwar Abdulnaseer daga baƙin ƙwararren Cardiologist ɗin dake kula da lafiyarshi.


Ba da sanin Maysarah da barcin azaba ya kwashe ba aka koma da gawar Abdulnaseer gida.


Tun kafin dawowar su Faisal da tsabar kuka har dishi-dishi yake gani ya kira Bala ya taho da Inna Abuja.



Maimakon bidiri a Ilorin sai juyowa sukayi da Amarya da dukka dangi baki ɗaya har da Angon.


Mom Fahima, Goggo, da Uncle Suraj sune mafi kusanci da Abdulnaseer da suke cikin hayyacin su, amma kallo ɗaya zaka yimusu tausayin su yasaka kuka.



Rashin Abdulnaseer a cikin ahalinshi babban rashine da har abada bazasu mayar da madadin shi ba.



Lokacin da Bala yaje taho da Inna,da Baba Isiyaku ya sameta a ƙofar gida,ɗaurin aure su ka zo birni,ya biyo gaishe da Inna tunda ya jima da sanin Halima na Abuja.


Kafewa yayi dole sai ya bisu ya ga halin da Halima take ciki, tunda Bala ya shaida musu lafiya ne bata da shi, don Faisal bai sanar da shi rasuwar Abdulnaseer ba, ba don Inna taso ba suka ɗauki hanyar Abuja har da Babangida daya kafe sai ya bi su.



Babu wani dangi na kusa da na nesa da babu a makeken gidan Abdulnaseer sai Uncle Ghali da iyalanshi.



★har wayewar gari babu wanda ya runtsa a gidan Uncle Ghali saboda fargabar da suke ciki,ga zafi da raɗaɗin tabbacin da suka samu na rasuwar Abdulnaseer har ankaishi makwancinshi.


Kuka mai raɗaɗi da ciwo ne ya ƙwace mai,danasanin komai na kamashi a daidai lokacin da komai yariga ya kwaɓe mai,duk kwaɗayin shi da son duniyar shi,yana son Abdulnaseer sama da yanda yakejin son Surajo a ranshi.


Keɓe kanshi yayi,saboda lallashin shi da iyalinsa suke yi ƙara tunamishi komai suke yi.

Baiyiwa Abdulnaseer adalci ba,bai kuma yiwa ɗansa Maysarah halacci ba. Tayaya zai gyara wannan gagarumin kuskuren?



Sai zuwa yamma su Inna suka iso, sai dai basu samu kowa ba har Rahina. Sai kuma alokacin ne Bala ya samu labarin abinda yake faruwa.


Tun kafin su isa gidan,jikin kowannen su yayi sanyi musamman Baba Isiyaku da gidan Maysarah ya gusar da nutsuwarshi.


Da taimakon Aminu su Bala suka kai gidan da yasa Baba Isiyaku ƙara zaro manyan idanuwanshi, saɓanin Inna da Babangida da su dai burin su suga Halima.


Faisal har gaban Goggo da su Baba Salahu da suma sun koma ciki don ƙara lallashin Goggo duk da suma nasu ran sam ba daɗi yakai su Inna.


Da farko tsabar kiɗimar da Goggo take ciki bata gane su Inna ba musamman ganinta da baƙin fuska,sai da Faisal yayi mata bayani.


Hannun Inna ta damƙo da hannunta na dama sannan ta damƙo na Baba Salahu da hannun hagu.


"Salahu ku taimake ni kafin Abdulnaseer ya kwana a makwancin shi ku ɗaurawa Maysarah aure da abinda suke so shi da ɗanshi,kara da son karya ɓata ran ƴan uwanshi,yasa ya zaɓi na su ɓacin ran,akan farin cikin ƴan uwanshi. Idan har sun amince tunda har da kakanta suka zo su taimaka su bawa Maysarah auren ƴar su,wataƙila idan ya farka zai samu salama da sauƙi acikin zuciyarshi. Bazan juri rasa Abdulnaseer da Maysarah a lokaci ɗaya ba,don Allah ku bashi auren Halima na roƙeku Dan Allah"ta faɗa da tsananin kuka tana kallon Baba Isiyaku.


Babu wanda zancen Goggo bai shiga ba a cikin su,musamman Faisal da ya kasa yarda mutum kamar Maysarah zai so mace irin Halima da ta fito daga ƙaramin gida.


Jingina kai Baba Isiyaku yayiwa Goggo dake kallonshi har lokacin alamun ya amince. Jikinshi ƙara sanyi yayi maganar garin son faranta ran ƴan uwanshi Abdulnaseer yarasa ranshi na taɓa zuciyarshi,sai yadawo mishi da Mutuwar Salmanu sabo.


Baya buƙatar sanin asali ko binciken waye Maysarah da ahalinshi iya karamcin su na tsayin shekaru da sukayiwa zuri'arshi ya isa ya sa ko kyautar Halima ne su ba su har abada.



Kamar yanda Goggo ta buƙata haka aka ɗaura auren daya gigita zuƙata da dama akan sadaki mai daraja.


Wacece HALIMA SALMAN ISHAQ shine tambayoyin da dubban jama'a suke yi a kaf gidan mutuwan.


Babu abinda Uncle Suraj yaji a ranshi sai nutsuwa mai sanyi da ɗaukar darasi mai girma,duk zafin kanka da dabararka baka isa kacanza hukuncin Allah ba.


Zafi ma su yawa ne suka haɗewa ahalin da suka tsame kan su,su ka kuma zama mujiyoyi saboda babu inda labarin su bai zaga ba, Uncle Ghali da iyalanshi.


Labarin Auren Maysarah da Halima shine labari mafi muni a kaf tarihin rayuwar su musamman Mahaifiyar su Mubeena da dukka ƴaƴanta idan ka cire Salim da dama yasan hakan zai faru.


Hawanjinin da basu san Uncle Ghali da shi ba ya tashi kamar ranshi zai bar jikinshi. A gigice suka nufi Asibiti da shi.



A ɓangaren Maysarah aka sauki su Baba Isiyaku da Babangida da basuyi niyar kwana ba don duk dare sun so ɗaukar hanya,Inna kuma na tare da su Goggo waɗanda auren yayi musu daɗi najanta a jiki waɗan da lamarin kuma baiyiwa daɗi ba na harararta da gefen ido.


Kamar yanda ba'a buƙaci su tafi ganin Halima ba suma sai suka danne muradin hakan har zuwa wayewar gari.



A ɓangaren Mom Fahima sam auren Maysarah a lokacin da batayi tunani ba, baiyi mata daɗi ba,sai zafi biyu ya haɗe mata.


Bala yayi kuka kuma yayi dariya a lokaci ɗaya,na cikar muradin Halime,har sama ma da yanda take buri.


A waya Rahina dake jinyar Halima ta samu labari kuka da guda tasaki lokaci ɗaya,tsabar Murna jikinta har rawa yake yi. Sai dai bata ƙara wani yunƙuri ba saboda motsin da Halima ta farayi.



★washe gari su Inna suka samu ganin Halima. Balaifi jinkinta yayi kyau sai ciwukan da baza'a rasa ba. Kamar yanda a baya basu sanar da ita dalilin ciwon Halima ba,yanzu ma basu sanar mu su ba,kuma su ma basu tambaya ba.


Baƙaramin farin cikin ganin su Halima tayi ba,sai kallonta Baba Isiyaku ya keyi, saboda kamanni biyun da ya haɗewa kyakkyawar Fuskarta. Yanajin tsananin soyayyarta a ranshi,sama da wanda yayiwa Salmanu da yana raye.


Gaisuwar ya haƙuri suka ƙara yimata a tunanin su tasan maiyake faruwa.


Sai da sukayi da sun sanin gaisuwar da sukayi ma ta,don gaba ɗaya birkicewa tayi,har sai da Likita ya buƙaci fitar su.


Har sai bayan tayi barci sannan su Inna suka ƙara dawowa wajen su Goggo suka barta da Rahina.


Sun so tafiya ranar amma shawarar da suka yanke na tafiya da Halima ne ya tsayar da su.

Goggo tayi amanna da shawarar su,duk da wa su sun so su nuna rashin dacewar hakan,saboda ciwon hassadar auren Maysarahn da ba su so ba da ƴar talakawa irin jinin su Inna,rashin samun karɓuwar ƙorafin izgilancin da suke son yiwa su Inna yasa kowannen su ya tsuke bakin shi.


Gaba ɗaya gidan mutuwar sai ya juye zancen auren Maysarah da Halima.


★washe gari duk da jikin Halima babu wani ƙarfi haka su Inna suka shirya tafiya da ita. Rahina ce ta haɗo kayan Halima. Kamar dai waccen zuwan na Inna wannan karon ma a lafiyayyen mota da driver aka haɗa su daga Asibiti suka wuce da Halima,duk da tarin mutanen da suke son ganinta don bawa idanuwan su abinci.


Babu wanda ya sanar da Halima ɗaurin aurenta saboda yanayin halin da take ciki.

🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂


Da ƙarfin daya bawa likitocin mamaki Maysarah yafarka da surutan sai ya kashe Uncle Ghali da Yusrah.daƙyar aka danne shi.


Yaga tashin hankali mabantata a rayuwarshi amma yanayin mutuwar Mahaifin shi abune dayake neman juyemishi kai,don Maysarah tunanin yafi karkata kan shaye-shayen da Mahaifinshi yayi zargin yanayi ne yayi silar ajalinshi,baiyi sallama da shi ba,kuma bai nemi yafiyarshi ba.


Babu wani halitta dake son Maysarah sama da Mahaifinshi,shi shaidane haka kowa ma.


A gwaje-gwajen da ƙwararrun Neurologist sukayi ne,suka gano matsalar ƙwaƙwalwar da Maysarah ya samu.....🥹


Barkan mu da dare