Chapter 18
by @oumfatima33
✨ *ALLON* *ƘADDARA* ✨
*OUM FATIMA*
*DASHEN ALLAH* *WRITERS* *ASSOCIATION*
*PAGE 18*
**** Jiki a sanyaye ta miƙe tabi bayanta zuwa sittin Room ɗin da aka sauke shi, Habiba ta fara shiga bakinta ɗauke da sallama cikin yauƙi da yanga. Daddaɗan ƙamshin turarensa ya fara shiga hancinta ta shaƙa ta lumshe ido kafin daga bisani daddaɗar muryarsa ta ratsa kunnuwansu, hakan yayi dai-dai da faɗuwar gaban da ta riski Harira.
Cikin dauriya ta yakice faduwar gaban da take ji tayi sallama cikin siririyar muryarta wadda ta ɗauki hankalin Sulaiman ya ɗago a hankali ya sauke idanunsa saman kyakykyawar fuskarta yana mata kallon da ya kasa ɗauke wa. Gyaran murya Habiba tayi tana jin ba daɗi a cikin ranta ganin kwata-kwata bai kalli inda take ba sai ido da ya zubawa aminiyarta yana mata kallon da ya shige ƙa'ida.
Jin gyaran muryar Habiba yasa shi ɗauke ido akan Harira da taji duk ta takura kuma zuciyarta ta kasa zama wuri ɗaya. Bai damu da yanayin da yaga Habiba ta shiga ba sai kawai yace musu "Bismillah ku zauna mana". Zaman suka yi saman kujera kafin Habiba ta fara gaishe sa cikin ƙoƙarin danne yanayin da take ciki, amsawa yayi kafin itama Harira ta gaishe sa cikin sanyin muryarta ya amsa mata da tsananin kulawa yana kafe fuskarta da kallo.
Jin da tayi gaba ɗaya ta takura da kallon da yake binta da shine yasata miƙewa tana faɗin "Aminiya bari in baku wuri kuyi magana". Hakan yayiwa Habiba daɗi don tuni ta fara nadamar gayyato ta da tayi, sai dai kafin tace komai suka tsinci Muryar Sulaiman na faɗin "A'a ya kuma zaki tafi?, Ki jira zan yi magana dake idan mun gama da ƙawarki" ba tare ta damuwa ko shakkar komai ba yayi maganarsa. Yayin da wani maƙoƙon baƙin ciki ya tokare zuciyar Habiba ta kasa magana.
Harira kuwa ba tare da ta zauna ba tace "A'a ya kamata na baku wuri tukuna, Aminiya bari in shiga ciki" kai kawai ta ɗaga mata don ta kasa buɗe baki.
Shiru ta kasa cewa komai bayan fitar Harira har sai da yace mata "kin kira ni kuma kin yi shiru, ina da abin yi so ki faɗi abin da yasa kika kirani". Duk da bata ji daɗin maganar da ya faɗa ba amma ta danne ta fuskance sa cikin ƙwarin gwiwar da take bawa kanta tace "alfarma nake nema a wurinka Ya Sulaiman don Allah kada kace A'a bayan na faɗa ma abinda ke raina!" Ta faɗa cikin rauni da fargabar abin da zai iya kasancewa.
"Ok ina sauraren ki, Allah yasa abinda zan iya baki zaki nema a gare ni". Ya faɗa hankalinsa na kan yarinyar da ta fita yanzu sakamakon tunda ta shigo ya ɗora ido a kanta ta ɗauke natsuwarsa gaba ɗaya.
"Ina sonka ina matuaƙar ƙaunarka Ya Sulaiman, tun ranar farko da na fara ganinka naji da kai kaɗai zan iya rayuwa, shi yasa tun daga lokacin na maida gidanku wurin zuwana duk don sabo da kai, nayi iya yina wurin nuna maka soyayyar da nake maka amma kaƙi fahimta, sanin da nayi ba zan iya haƙura in rasaka ba yasa na yanke hukuncin sanar da kai, don Allah ka taimaka min ka aure ni!" Ta ƙara sa faɗa kuka na kwace mata.
Sosai yaji tausayinta ya kamasa sai dai bazai iya bata abinda ta roƙa ba, tun farko ya gane inda ta dosa sai dai shi kwata-kwata bata cikin jerin matar da yake so, shi yasa ya ɗauke ta a matsayin ƙanwa. Sai kuma babban al'amari da ya risaka yanzu na faɗawa soyayya a kallon farko, a yanda yake ji a cikin zuciyarsa game da yarinyar da ta fita yanzu ya lullunka yanda ita take ji akansa shi yasa yake tausaya mata matuƙar haka take ji a kansa.
Ajiyar zuciya ya sauke ya ɗago ya fuskanceta yace "Ya isa ki bar kukan haka muyi magana" shiru tayi tana share hawanta, sai da ya tabbatar ta natsu sannan yace "kiyi haƙuri Habibah, ki janye maganar soyayya a tsakaninmu ba wai don baki isa bane a'a ni kawai na ɗaukeki ne a matsayin ƙanwata, keda Badura matsayi ɗaya na baku, don haka duk abinda kike buƙata a gareni a matsayina na Yayanki ki tambaye ni kai tsaye na maki alkawarin zan yi miki shi matuaƙar bai fi ƙarfina ba".
Kuka ta fashe dashi mai tsanani jin kalamansa da suke nuna kai tsaye bai amince da buƙatarta ba, ba kuma zai amince ba sabo da ya riga ya bata matsayin ƙanwarsa. Cikin kuka tace mai yasa baka sona!".
"Kada kice haka mana, ina son ki a matsayin ƙanwa amma ba wacce zan aura ba".
"Wa kake so a matsayin mata" ta tambaye shi zuciyarta na bugawa da fargabar amsar da zata samu daga gare sa. Ba tare da shakkar komai ba yace mata "yarinyar da ta fita yanzu" kamar saukar aradu taji maganar amma ta danne tace masa "baka santa ba, baka taɓa ganinta ba sai yau".
Ƙwarai kuwa yau na fara ganinta, a kuma yau ɗin na kamu da zazzafar soyayyar ta da zata iya halakani idan na rasa ta, don Allah ki taimaka min ƙanwata"
'Kaji wani lukutin rainin hankali, wai ki taimaka min ƙanwata" Habiba ta raya a cikin zuciyarta dake ci da wutar baƙin ciki da wata irin tsanar Harira da ta shige ta lokaci ɗaya "kamar yanda kake jin zaka iya mutuwa idan ka rasata to nima haka nake ji a kanka, kaga kenan sai mu mutu duka don bazan taɓa bari ka same taba!" Habiba ta faɗa cikin fushi tana miƙe wa a zafafe tabar ɗakin yayinda ya miƙe yabi bayanta yana ƙwala mata kira.
A dai-dai ƙofar da zata shiga cikin ainahin Gidansu sukaci karo da Harira da ta fito da niyar tafiya gida magriba ta kusa kuma Habiba bata fito ba shi yasa tace bari ta tafi kawai sayi waya. Ƙoƙarin yiwa Habiba magana take amma ta bankaɗeta har tana ƙoƙarin faɗuwa amma bata tsaya ba ta shige tana share hawanta.
Mamaki ya kama Harira tana faɗin "Ita kuma mai ya same ta" ƙoƙarin binta take cikin gidan taji abinda ke faruwa taji muryarsa yana faɗin "kada ki bita, ki bari ba yanzuba, ki bani No ɗinki zan kiraki muyi magana".
Bata kawo komai a ranta ba ta bashi No da tunanin ko basu dai-daita ba, haka dai ta tafi Gida cike da wasi-wasin abinda ya faru.
**** Habiba kuwa tana shiga bata tsaya ko ina ba sai da ta kai ɗakinta ta zube kan gado ta saki wani uban ihun da ya jawo hankalin Mahaifiyarta da ƙanwarta Sakina suka shigo da gudu suna tambayarta mai ke faruwa.
"Na tsane ki! Na tsane ki!! Na tsane ki!!! Harira, nayi nadamar saninki da nayi a rayuwata, da ace nasan kece zaki shiga tsakanina da farin cikina a rayuwa to da ba zan taɓa bari ki raɓe ni ba har abada. Kuma ki sani yadda yaƙi karɓar soyayya ta sabo dake, bazan taɓa bari ki same shi ba in dai zan rasa abu to sai dai uban kowa ma ya rasa!". Habiba ta ƙarashe cikin hargagi da gursheƙar kuka.
Baki da hanci Mamansu da Sakina suka saki suna kallon yanda ta zama kamar wata mahaukaciya, duk wannan kwalliyar ta caɓe ta haɗe da hawaye da majina an tsige ɗaurin da aka ɓata lokaci wurin yinsa.
"Ke dan Ubanki ki natsu ki faɗa min abinda yake faruwa" Hajara (Mamansu) ta faɗa. Cikin kuka mai tsanani ta zayyane mata duk abin da ya faru ta ɗora da cewa "dama ƙawayena sunsha faɗa min matuƙar ina tare da Harira bazan taɓa samun ci gaba ba, sabo da ta fini komai amma naƙi ji, gashinan zata raba ni da Mutumin da nake matuƙar ƙauna a duniya, ina! Ba zan bar hakan ya faru ba, zan nuna mata ba irina ake shiga ma hanci ba!" Ta ƙare maganar ba tare da duba cewar duka fa a cikin wannan lamarin babu laifin Harira ba, sabo da ita ma bata san abin da ya faru ba amma kishi ya rufe mata ido take ɗaukar munanan alwashi akan Aminiyarta da suka taso tare tun yarinta akan ɗa na Miji.
"Allah ya kyauta" kawai Mahaifiyarta ta faɗa tana ficewa a ɗakin, Mamansu mace ce mara damuwa da al'amurra irin haka, bata cika maida hankali akan abinda ke tsakanin ƴaƴanta da ƙawauensu ba bare har ta ɗaure musu ƙugun yin rashin kyautatawa ba. Sakina ce ta zauna taci gaba da famfata tana ƙara zugata, don dama can ita ke jiwa Yayarta haushin yanda ƙawarta ta fita komai na rayuwa.
***** Kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba a ɓangaren Sulaiman, don tun da ya koma Gida ya kasa manta fuskarta, duk abin da zai yi tanaaƙale a zuciyarsa, ya kasa samun nutsuwa har sai da ya kirata. A ɓangarenta ita ta manta ma da ya karɓi No yace zai kirata suyi magana, abu ɗaya ne ya tsaye mata a rai shine yanda Habiba ta hankaɗeta ta shige lokcin da take ƙoƙarin yi mata magana, kuma har yanzu da take kiranta don jin mai ya faru bata ɗauki wayarba, ƙarshe ma sai ta daina shiga alamar an yi blocking ɗin ta.
Sosai mamaki ya rufe ta da tunanin mai haka yake nufi? Haka dai ta haƙura ta kwanta da niyar gobe zata je Gidansu taji abin da ke faruwa. Sai dai kiran da Sulaiman yayi mata yasa ta samu duka amsoshin tambayoyin da zata je nema wurin Habiba wanda ba ƙaramin firgici ta shiga ba da jin maganganunsa da ƙudurinsa a gare taba.
Idan tace bataji wani abu a kansa ba to tayi ƙarya, amma sai dai tun a lokacin tayi yaƙi da koma miye ta ture shi sabo da sanin shine wanda Aminiyarta ke tsananin so da ƙauna, kuma cikin ikon Allah abin baiyi wani tasirin da zai dame taba, amma jin wannan maganar daga bakinsa yasa hankalinta ya tashi, bata ɓoye masa ba ta shaida masa cewa har abada ta haramtawa kanta shi tun da Aminiyarta ke son shi, ta kuma roƙe shi akan ya taimaka ya bar maganar ya kuma amshi Aminiyarta, shima ya shaida mata cewar bazai iya barin maganar ba sabo da ba zai iya haƙura da ita ba, ƙawarta kuma shi bai taɓa cewa yana son taba hasali ma a matsayin ƙanwa ya ɗauke ta.
Cikin rashin mafita da tsoron da ya shige ta ta kashe wayar ba tare da ta tsaya sauraren roƙon da yake mata ba, tasa a zuciyarta gobe zata je ta samu Habiba ta shai da mata har abada ba ita ba saurayin da take so, sabo da tasan Habiba ciki da bai akan kafiya da nacin abinda ta ƙwallafa rai, tasan akan wannan maganar Habiba zata iya rabuwa da ita.
Haka daren yau ya kasance mara daɗi a wurin mutane ukun nan, kowa da abinda ke zuciyarsa. A ɓangaren Habiba baƙin ciki da ɗacin zuciya da wata irin tsanar Harira da bata taɓa jin makamanciyarta ba, don ita a rayuwarta duk wanda yayi ƙoƙarin ƙwace wani abu daga hannunta to suna saka ƙafar wando ɗaya da shi.
Sai Harira da tsoro da fargaba suka haɗu suka hana ta bacci cikin salama har sai da ƙanwarta Ade ta ta tsareta da tambaya ta sanar da ita abin da ya faru.
"Kai! Daɗina dake wallahi Yaya wani lokacin in kika yi wani abin kamar wata sokuwa, to sai me don yace ke yake so ba ita ba? Ana tursasa zuciya ne taso abin da bata ra'ayi daman?, To kin ga ki kwantar da hankalinki in dai kina son sa kawai ki bashi dama musha biki, ai ba'a wasa da irin wannan damar Yaya".
"Kina da hankali kuwa Ade? Wanda Habiba Amiiyata ta ƙwallafa rai a kansa fa nake magana?".
"Eh shi ɗin fa, to sai me? Ke yake so ba ita ba, ko ke bakya son sa?" Shiru tayi ta kasa bata amsa.
"Kinga Yaya kwanta kawai kiyi barcinki gobe da safe ki kira shi kice kin amince" Ade ta faɗa tana gyara kwanciyar ta a kan gadon da suke kwance ita da Yayar ta ta a ɗakin da yake mallakin su.
Kwanciya Harira tayi ba don ta gamsu da shawar da ƙanwar ta ta ta bata ba. Saƙe-saƙe tayi tayi har ɓarawon da yafi kowa iya sata ya sace ta.
Na ukun shine Sulaiman da soyayya tayiwa mugun kamu a kallon farko take ƙoƙarin hana shi natsuwa, ji yake in ba mallakarta yayi ba to ba zai taɓa samun natsuwa ba, don haka ya yanke hukuncin ba zai tsaya wasa ba a gobe zai sanar da Abbansu cewar ya samu Matar, don Hausawa sunce da zafi a kan daki ƙarfe...
Kansa'u Bello (Oum Fatima)