54
💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔
( shi ya san gidan mai rowa)
```By```
``` NAFISAT ALIYU SASAAL```
```Page 54```
________Lakwas Halima tayi saboda girman damuwar da take ciki. Batasan Abdulnaseer a fuska ba amma mutuwar shi ya taɓata matuƙa.
Tana kwance a jikin Inna har su ka isa garin Kano. Maimakon gidan su Inna wani gidan daban driver ya wuce da su, bisa Umarnin Goggo.
Matsakaicin gidan ne amma maikyau da tsari a unguwar masu hannu da shuni babu hayaniya sai giftawar mutane jefi-jefi. Shi ya buɗe mu su gidan ya yi musu iso har babban living room ɗin gidan,sannan yayi mu su sallama.
Baba Isiyaku bai jima ba shi da Bala suka yimusu sallama tare da tafiya da tarin alkhairin kuɗin da Goggo tasa driver yaba su. Shima Babangida gida ya wuce. Don ko basu tambaya ba sun san don Halima yanzu da take surukan su aka kawo su gidan.
A ɓangaren dangin Halima ta ɓangaren Uwa da Uba dayawan su auren bai yimusu daɗi ba,acewar su zallar kwaɗayi ne zai sa su bawa masu kuɗi auren jikar su daga zuwa dubiya,dama kuma tun farko ai kwaɗayin ne yasa sukabar Halima a wajen waɗanda basu sani ba saboda su ɗin masu kuɗi ne.
Dayawan ma su faɗar hakan hassada ne yake ci musu tuwo a ƙwarya,domin duk cikin su babu wanda ya taɓa siyawa Halima ko da ƴar rigar sawa ne, sanda Mahaifiyarta ta rasu ta barta. Kuma da na su ƴaƴan ne da gudu zasu bayarda auren su.
Ɗai-ɗaikun cikin su,suka yi mata fatan alkhairi,da zaman lafiya a gidan Mijinta.
Da yamma liƙis Inna ta tafi gida saboda barcin daya ɗauke Halima,idan dare yayi sai ta dawo.
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Bayan tafiyar su Halima muhawara mai zafi ya ɓarke a tsakanin dangin,sai jimamin rashin Abdulnaseer ya farabin ruwa.
Ba komai yaƙara baƙanta ran su ba sai yanda Goggo ta hanawa idanuwansu samun abincin kaiwa gaba.
Mitar su bai wuce an ɓatawa dangin su suna ba, mussamman ragowar ƙannen Mahaifin su Abdulnaseer da suke tunanin yanzu dukiyar Maysarah zaifi na da,don haka ƴaƴan su ya dace ya aura,bawai a ɗauko bare daga waje ba,baren ma ƴar gidan talakawar da zata zuƙewa ɗan su jini.
Shi dai Uncle Suraj bai tofa ba haka ma dukka Iyalanshi,dama Maryam suke yiwa zalamar samun matsayin da Halima ta samu,kuma Allah baiyi ba don haka ba su da damuwa a kan haka sai tsatson talaucin da Halima ta fito, don su anasu fahimtar ita da mara asali duk ɗaya suke.
Ranar da matsalar Maysarah ya bayyana,suka bar ƙasar da shi,kuma alhamdulillah yana samun sauƙi da fahimtar da suke buƙata.
Dangi ɗaya bayan ɗaya suka dinga zuwa dubashi,duk da yawanci basa samun ganin shi sai dai Faisal dake tare dashi.
Jikin Uncle Ghali ba sauƙi sai na Allah, a cikin kwanaki bakwan da Abdulnaseer yayi a makwanshi Uncle Ghali yayi wani irin rama,haka dukka ƴaƴanshi.
Musamman Yusrah da Mubeena da suka rasa damarmakin su acikin kwana da wuni. Kuma ko ta kira Faisal baya ɗauka tunda babu abinda ya rage tsakanin su sai dai zumunci.
Da lallashi da ban baki Baba Salahu da Goggo tafi jin maganar yasa ta yafewa Uncle Ghali, ko zai samu sauƙin halin dayake ciki,har Asibiti taje ta dubashi.
Kunya da nauyin girman laifin da ya aikata ne yasa ya kasa kallonta har ta bar Asibitin.
A cikin waɗannan kwanakin jikin Halima yayi sauƙi sosai. Kullum sai Goggo ta kira taji lafiyarta. Ita kaɗai take wuni a gidan da saƙe-saƙe kala-kala a ranta sai dare Inna tazo su kwana tare.
Zuga da bin ba'asin rashin kwana Inna a gida duk ta sanar Baba Shehu uzurinta kuma shima yaje ya ganewa idanun shi ne ya ɓarke a gidan. A gaban Yayyanshi ta shaida mu su auren Halima da dalilin rashin kwananta a gida,maimakon su fahimceta sai hassada yayiwa jin su da ganin su yana, sai yaushe Haliman zata warke tunda kwaɗayi yasa sun siyar da kurwarta da sunan aure,sukam sai dai ta zaɓa ko zaman gidan aurenta ko zaman gidan Halima. Shine furucin kowannen su.
Baba Shehu bai ce komai ba,kuma ya kwana da sani Inna bazata taɓa zaɓar zaman gidan shi tabar Halima ba.
Babangida ne yabawa Mahaifiyarshi karfin gwiwar tafiyarta,don shima abinda suke yimata bayajin daɗin a shekarun Mahaifan shi yaci ace sun bar irin waɗannan ƙananun maganganun na gilmawa tsakanin su,amma yayyan Mahaifinshi bazasu bari ba,don haka tafiyarta shi yafi alkhairi.
Saboda son ganin ƙwaƙwaf da gulma,su dayawa sukabi diddigin gidan da Halima take ta hanyar babbar ƴar Malam Bala. Daga su har ƴar Malam Balan sabon sojan dake gadin gidan hanasu shiga yayi. Duk da tsinkewar da yawun su yayi,haka suka tattara suka kamo haryar gida su na tsinemai albarka.
Har kawo wannan lokacin Halima batasan da auren kowa a kanta ba,kamar yanda Inna da ka tare da ita da Goggo da suke waya basu sanar da ita ba.
Tunanin Maysarah wajibin zuciyar tane kullum sai ta yi shi,amma saboda gudun faɗar Inna yasa ta haƙure wa ranta,tare da yimishi fatan alkhairin da zuri'arshi na sabon muhallin da su ka ba su.
Kamar kuɗin guzuri haka Halima take ta ƙarewa,magana kaɗan kuka,duk da kai tsaye Inna tasan damuwarta amma sai tayi biris da ita,kamar bata gane ba.
Shima Baba Isiyaku kullum sai ya kira yaji lafiyarta,amma Allah bai taɓa bashi ikon sako mata zancen aurenta ba, acewarshi yanzu samun lafiyarta shi ne buƙatar su.
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Watan Maysarah biyu ya samu sauƙi sosai,don haka suka tattara suka dawo gida.
Keɓance kanshi yayi ya hana kowa shigowa inda yake.
Washe gari Baba Salahu yazo dubashi,daƙyar Maysarah ya fito parlon don su gaisa.
Ramar fuskarshi a bun tsoro ne, sai dogon hanci da gargasar daya cika fuskarshi, bai sauya ba,sai zafi da bauɗaɗɗun halayyarshi da suka ƙara muni da tsanani,tausayi da Soyayya duk sun gushe daga zuciyarshi,don kowa yanzu a nashi fahimtar kuɗi yakeso.
Bayan Baba Salahu yayi mishi yaya jikin da bai samu amsa ba, sai ya soma jawabi " to Maysarah sai ka ƙara haƙuri da ɗaukar dangana,ina ƙara yimaka ta'aziyya, Allah Ya jiƙanshi Ya kai haske kabarin shi. Sai magana ta biyu,Goggo A'isha ta bamu umarnin ɗaura maka aure,saboda tace shine cikar muradin Mahaifinka,amma saboda farin cikin ƴan uwanshi yasa yakasa cika wannan muradin,har Allah Yayi ikon Shi, to Dafatan zaka fahimcemu ka kuma rungumi iyalinka hannun bibbiyu"
Ya daɗe da daina fahimtar maganar Baba Salahu tun daga inda yace anɗaura mai aure da cikar muradin Mahaifinshi,Yusrah kenan? Don ita ya sani a cikar muradin Maihaifinshi na shi.
Har Baba Salahu ya ƙarasa duk bayanan da zai yi Maysarah baya tare da shi,kuma dama bai tofa ko kalma ɗaya ba,har Baba Salahu ya bar parlon.
★Ƙarfe ɗayan rana Goggo ta nufo sashen ƴar aiki na bin ta a baya da jug maikyau da kunun gyaɗa a ciki.
Knocking ta farayi sai dai bai buɗe ba,tana murɗa ƙofar tajishi a buɗe, a hankali tashiga komai na zaune a muhallinshi,sallama tayi ta kwaɗawa amma bai amsa ba kuma bai fito ba, kamar yanda ya saba.
Kai tsaye Bedroom ɗin tayi knocking sai taji shima a buɗe yake,kamar dai parlon shima tsaf yake,sai dai babu alamun mutum a ɗakin gaba ɗaya,zuciyar Goggo na bugu sosai ta murɗa Bathroom ɗin nan ma ba kowa.
Jikinta na rawa da tafiyarta da babu sauri sosai ta nufi sashen ta,don kiran Faisal,kafin ta ƙarasa sukayi kiciɓus shima yazo duba Maysarah.
"Faisal ina Maysarah"
Goggo ta faɗa bakinta na rawa.
"Shi na zo dubawa Goggo"
"Na shiga uku ni A'isha maiyake shirin faruwa,kiramin layinshi"
Babu layinshi ɗaya da suka samu.
Ɓangaren Maysarah Faisal ya ƙara nufa ko Goggo ce bata duba da kyau ba. Itama rufa mishi baya tayi.
Takardar da Maysarah ya bari a tsakiyar gadon Faisal ya ɗauka,zuciyarshi na tsinkewa.
A hankali kuma a sarari yake karantawa Goggo najinshi.
"Ni Maysarah Abdulnaseer Bari,na saki matar da kuka auramin saki ɗaya,idan ta samu Miji tayi aure"......✍🏻