MAI KWAĆŠAYI

55

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

``` NAFISAT ALIYU SASAAL```



 ```Page 55```


________A gefen gadon Goggo ta zauna,jikinta a matuƙar sanyaye,ta sani Maysarah bazai taɓa sakin Halima ba,ita shaida ce. Shima Faisal waje yasamu ya zauna,kanshi na ɗaukar zafin da wani idon zasu kalli Halima da kakannin ta."Goggo kar ki damu In Sha Allah komai zai yi dai-dai.

"Dai-dai kuma Faisal? A yaushe,? Bansan ina zan kai wannan abun kunyar ba wallahi".

Goggo ta faÉ—a muryarta na rawa.

Dafata Faisal yayi,kowanne su ranshi ba daÉ—i.


Haka Goggo ta wuni cikin jimamin abinda Maysarah ya aikata.


Maimakon da Faisal yaje gida ya sirrince maganar a zuciyarshi,sai bai yi ba.

Kamar wanda abin yayiwa daÉ—i a rai.


A cikin kwana biyu,sai ga labari ta ko ina,har ya zagayo ya dawo kunnen Goggo.


Sai kuma a lokacin ne take ganin rashin laifin guduwar Maysarah da tsananin tausayin ɗanta mai jinƙanta,tare da ƙara yimishi addu'ar samun rahama. Wani irin dangi ne su,da basu da sirri,yanzu duk girman Faisal da hankalinshi ya rasa abun tonawa asiri sai yarinya ƙarama kamar Halima,don bazata ce ya tonawa Maysarah asiri ba,tun da bayanan ko da ma yananan ai Matar da ya saka ce abar tausayi.


Daga ranar Goggo ta haramtawa Faisal shigo mata sashe,kuma ta nemi ganin dukka Ć´aĆ´anta da jikoki saboda tana da abin faÉ—a.


Yini Goggo tayi da Shamsiyya mai yi mata girki suna kiran Maysarah, idanuwanta har zafi suke yimata,tsabar damuwar da take ciki.


Saƙo tasa Shamsiyya ta turamai na roƙo da ban bakin dan darajar Allah ya mayar da Matarshi,ta roƙeshi har da darajar soyayyar da yakewa Abdulnaseer da Zainab Mahaifansa,ya mayar da Matar shi.


Guntun amsar"na amince"daya turo ne yasa Goggo rungume Shamsiyya cikin tsananin farin ciki. Barcin Goggo na ranar har da munshari,saboda rabonta da barci irin wannan tun kafin rasuwar Abdulnaseer.



Iska mai zafi Uncle Ghali ya fitar, idanuwanshi na kara rinewa suna komawa jajaye abun tsoro,suffar shi na rashin Imani dayake ƙoƙarin ɓoyewa na ƙara bayyana a saman fuskarshi.


Maysarah ya cire hannun jarin shi daga kamfanin shi,wanda hakan ke nufin karyewar shi ƙasa gaba ɗaya saboda kaso rabi da kwata duk na Maysarah ne,a sahihin labarin ma daya samu Maysarah ya janye dukkanin harkokin kasuwancin shi daga ƙasar gaba ɗaya.


Labarin sakin Matarshi dayayi bai ƙarawa mishi komai ba duk da Mommyn su Mubeena tace damar su ce, na su shirya Yusrah zuwa Barrack ɗin su Maysarah da nasu shirin. Wanda dole ya shigo hannu,amma maganganunta ba su samu matsuguni a zuciyarshi ba,don har abada yasan Maysarah baya magana biyu musamman da yanzu Abdulnaseer baya raye.


Itama Mom Fahima ƙara gyara zama tayi,saboda dama na biyu dayake shirin zuwar mata. Sakin Halima babban nasara ne a gareta,saboda matsalar gidan auren Sumayya da ya fara girma, saboda ita da Mijin a mabanbanta ƙasa suke rayuwa,sai jefi-jefi idan yayi ra'ayi take zuwa inda yake,ya hanata fita kowacce ƙasa ga rowa,komai na shi baya ciyuwa a banza.

Kusan kullum da kuka suke rabuwa a waya da Sumayya,kuma ita take ƙara zugata.



Zaman Inna da Halima gwanin sha'awa basu da damuwar komai sai Halima da ke tuna Maysarah lokaci zuwa lokaci.



Waya mai tsaho Inna da Goggo sukayi,kuma Inna ta fahimceta. Bayan sun gama a ɓoye Inna tasha kukan abinda Maysarah yayi,don ita bata yarda da baisan Halima aka aura mai,kawai a matsayin izgilancin ta ɗauki sakin da yayiwa Halima.


Kayanta Inna ta umarceta ta haÉ—a zata koma gidan Goggo don cigaba da karatun ta.


Da farko Kukan ita bazata koma ba tasawa Inna,sai da ta zaunar da ita tayi mata bayanin auren dake kanta. kuka da dariya Halima tasa lokaci É—aya farin ciki na mamaye zuciyar ta.

"Inna dagaske Uncle Maysarah ya aureni"

Ta faÉ—a da dariyar farin ciki.

Kukan tausayinta ne yakama Inna, rungumeta tayi,haÉ—e da faÉ—in"Halima ki nutsu ki kuma dinga fahimtar abu da kyau,ke ba yarinya Ć™arama bace yanzu kinji."

Kanta ta É—aga mata jikinta nayin sanyi duk da bata fahimci maganar Inna ya dosa ba.


Har ƙauye Halima taje suka ƙarayin sallama da Baba Isiyaku,shima dai nasihar ya ƙara ɗora mata cikin tsananin son dayake mata.



🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂


A gaban dukka Ć´aĆ´a da jikokinta Inna ta sanar da Maysarah ya mayar da Matarshi,kuma zata zauna a wajenta har ta kammala karatun ta kafin dawowar Maysarah.


Babu wanda zancen Inna ya shiga a cikin su,matsawar ba Maysarah ne ya faÉ—a da bakin shi ba,to fa har abada bazasu yarda da wannan zancen na Goggo ba.


Mubeena sai satar kallon Faisal da ƴaƴanta da suka maƙalƙaleshi takeyi, tanajin ba daɗi da danasanin da bashi da iyaka.


Itama Mom Fahima sam zancen Goggo bai shige ta ba,kuma Indai tana gidan to Matar da Goggo zata kawo da sunan Matar Maysarah da ƙafafuwanta zatabar gidan.



Har lokacin su Aminu da Matarshi na zaune a gidan Maysarah bisa Umarnin Goggo,ko ba komai mutum rahama ne a gida, maimakon a barshi babu kowa.



Amintaccen drivern dayakai su Halima ne, yaje ya ɗaukota,da kuka suka rabu da Inna da itama tayi shirin tafiya ƙauye.


Babu inda gulmar tafiyar Halima bai zagaba a Ć™auye,duk da an sanar da su bawai tariya bane ta tafi ita É—aya ne don karatunta da zata Ć™arasa sai ta dawo ayi hidimar biki a kai Amarya,asali ma Mijin bayanan,amma duk da haka babu wanda ya gamsu a cikin su.



Babu wanda yaga zuwan Halima har Mom Fahima da tun safe take leƙen window. Gajiya tayi barci ya ɗauketa.



Da farko ganin Halima a matsayin Matar da Goggo ta tabbatar ta Maysarah ce,ya girgiza dukka zuƙanta su, musamman da Goggo ta kai ta gidajen kowannen su da kanta,duk yanda suka so dizgata da wulaƙantata hakan bai samu ba,sai a gidan Uncle Ghali lokacin da suke shirin tafiya.

"Goggo ki dai ƙara dakatawa, a tabbatar da adalci tunda Maysarah ya riga ya sake ta kuma,ya nuna ba ya sonta,kar fa a riƙe ƴar mutane yazo ya ce shi fa bai san maganar ba." Mommyn su Mubeena ta faɗa idanuwanta nakan Halima kamar zata cinyeta .


Fargaba da kunya ne suka dirarwa Goggo,juyawa tayi tana kallon Halima da kanta ke ƙasa.


Zancen Mommyn Mubeena yayiwa kowa na Parlourn daɗi musamman Yusrah da ganin Halima wannan karon yafi ɗaga hankalinta,don sai yanzu tasamu damar ƙare mata kallo da kyau.


Muzanta,tsanar Maysarah lokaci ɗaya,da danasanin sanin shi a cikin rayuwarta ne,ya dirarwa zuciyar Halima lokaci ɗaya,duk ƙarfin AC lafiyayyan living room ɗin gumi ne yake tsatsafowa goshinta da ƙwantaccen gashi yayimai ado.


"Nagode Ɗan juma,Allah ya saka maka,amma ka sani indai nina haifeka,to ka saki Matar nan ta ɗanɗana abinda tayiwa Halima,idan ba haka ba,ka nemi wata Uwar amma badai ni A'isha ba" Goggo ta faɗa kukan takaici na ƙwace mata taja hannun Halima dake rawa suka nufi Mota.


Babu wanda ya iya motsawa a Parlon sai Uncle Ghali daya rufawa Inna baya da magiya,jinin shi na neman ƙara hawa.


"Mommy yaushe zaku so mu zauna lafiya dan Allah,kalli yanda kike zuga Daddy komai na ta lalacewa, gaskiya I'm tired of all this".Salim ya faÉ—a da tsananin fushi yana barin parlon.



So take yi taji Goggo ta ƙaryata Mommy Mubeena,amma Maimakon haka sai ta fara lalallashinta ta da ita shaida ce Maysarah ya mayar da ita. Kanta kawai ta ɗagawa Goggo alamun ta gamsu tana ƙoƙarin mayar da ƙwallar daya cika idanuwanta don hanasu saukowa.


Ashe wannan ne mafari sai yazama kamar sharar fage Mummyn Mubeena tayiwa ragowar dangin su.


"Yanzu Goggo anyiwa yarinnan adalci,ku barta taje ta nemi masu sonta da gaskiya tayi aurenta"


Kullum shine furucin Mom Fahima sai dai idan bata shigo gaishe da Goggo ba,don kyawun Halima yafi maƙalemata a wuya.


Babu dangi Mahaifi shi ko na Goggo da suke ragawa Halima,kullum furucin su shine babu amfanin zamanta tunda Maysarah ya sake ta abarta ta tafi tayi rayuwarta da talakawa Ć´an uwanta ko zata samu Mijin aure.


Kullum sai ta laɓe tayi kuka mai raɗaɗi da ciwo,ashe shiyasa Farin cikinta yasa Inna kuka ranar da ta sanar da ita da auren Maysarah a kanta. Da tanajin haushin gorin talauci da rashin amfanin zamanta da sunan Maysarah da take kyautata zaton ya saketa,amma babu wanda zai yi rantsuwar ya mayar da ita,amma daga baya sai ta gane gaskiya suke gayamata a zahiri duk da su rashin son alaƙar su da ita yasa suke faɗar hakan.


Tayaya Mijin daya amince yana da Mata amma bazai kira yaji lafiyarta,ko jin damuwarta ba,don ita damuwarta kenan tunda Allah bai sa tana cikin jerin Mata masu kulafucin Namiji ba,amma idan da gaske ne ya yarda ita Matar shi ce dole ko da yaya ne zai so sauke nauyin dake kanshi.

Dole zancen su ne gaskiya, Maysarah ya bayasonta bai kuma maida ita a matsayin matar shi ba.



Zuwan Uncle Suraj da iyalanshi da kaifafen kalamanshi ne suka sauya zuciyar Halima gaba ɗaya ta kuma yarda da gaske bazasu taɓa son ta ba.


"Goggo bansan yaushe zaki daina wannan kwashe-kwashen naki ba,tayaya zaki yarda kamar Maysarah zai so yarinya irin wannan,da bata da wani cikakken asali da tushe mai kyau,idan da kinyi zargin ya so ta,to may be tausayi ne,yanzu kuma baya ra'ayi,bana raba ɗayan biyu rashin son ganinta ne yahanashi dawowa gare mu, don nasan yana sane da komai,Goggo dan Allah ki barta ta tafi,ta auri dai-dai da ita,shi kuma Allah ya bashi dai-dai da shi,idan ban da son zuciyar matsiyacin mutum dayake a mace,tayaya yarinya zatayita zama babu Miji babu dalilin shi amma duk da haka ta liƙe,ni ban ma yarda da ita ba wallahi" Uncle Suraj ya faɗa yana ƙarewa Halima dake durƙushe tazo gaishe su kallo kamar zai yi Ball da ita.


Kuka Halima take yi ko ina na jikinta na rawa kafin ta silila ƙas....✍🏻