Page 5
by @farnanahhh
Page 5
Ammi ta duba agogo taga har 6 ta kusa basu dawo ba ta dauki waya ta kira Bazla, ta fara ringing ta dauka, cikin fada Ammi tace “shi gyaran gashin ne har yanzu ba’a gama bane da baku dawo ba” cikin wayar Bazla tace “Ammi wallahi motar ce ta tsaya mana” Ammi tace “shine kuma bazaku kira ba asan abunda za’ayi” Bazla tace “Ammi mun kira mai gyaransu yasmeen ne wayarshi bata shiga, amma ai mun samu mai gyara InshaAllah bada jimawa ba zamu dawo” Ammi tace “a ina kuka samu mai gyaran” Bazla tace muna tsaye ne yazo wucewa sai ya tsaya” Ammi tace to “Allah ya tsare ya kuma kareku” ta amsa da Ameen Ammi ta katse wayar
Ammi ta kira kulu tana tambayarta ta qare abinci, kulu tace “ey hajiya an kusa dai saura kadan” Ammi tace “to don Allah ayi sauri yaran nan sun kusa dawowa kuma nasan da Yunwa zasu dawo” kulu tace “to hajiya InshaAllah” Ammi tace “yawwa je ki cigaba da aikinki, sannan inason kimin list abunda babu ko ya kusa qarewa, jibi xaayi girki Alhaji zai dawo” kulu ta amsa da to hajiya
Ammi ta tashi ta koma dakinta
____________________________
Bazla da ta kalleshi suka hada ido sai d taji zuciyarta ta buga, wanda shima a nashi bangaren haka ta kasance, ta kawar da kanta a daidai lokacin da kiran Ammi ya shigo wayarta, shi kuma ya duba motar
Y duba abunda zai duba yacewa yasmeen “bari naje nan garejinmu ba nisa na dauko wasu kayan na dawo, yasmeen tace “to badamuwa”
Sufyanu ya buga mashin yaje ya bawa Oga saqonsa ya kuma ce mishi zai fita ya duba wata mota, Oga yace badamuwa, Sufyanu ya dau abunda zai buqata na gyaran ya fito
Ya qaraso suna cikin mota, yasmeen ya fito tace “har ka dawo kenan” ya amsa mata da eyh ya fara duba motar
Cikin ikon Allah bai dauki lokaci ba ya gyara mota, yace ya kunna motar, ta koma cikin mota ta tayar, tashin farko bata tashi ba, har yasmeen ta bata fuska, yace ta sake tadawa, aikuwa tana tadawa motar ta tashi,
Bazla aranta da aka kunna da farko cewa tayi dama da ganin wannan me ya iya, sai gashi ta tashi, bata daice komai ba duk abunda ake
Yasmeen ta fito tana murmushi tace “kaga kuwa ta tashi nagode sosaii” nawa ne kudin gyaran, Sufyanu yace ai da kin barshi, yasmeen tace “aa baza’ayi haka ba dan uwa, ka fada dai kawai” yace “to ko nawa kika bayar” Bazla ta fito tace “wai don Allah yasmeen kina gani marece yanayi muyi mu tafi kafin Ammi ta sake kira” yasmeen tayi mata wani kallon raini ta juya ta kalli Sufyanu tace “ina zuwa” taje cikin mota ta dauko jakarta ta ciro 20k zata bashi, yace “haba wannan kudin yayi yawa” yasmeen tace “don Allah karka ce komai ka karba kawai, kuma kar kace a’a” Bazla da abun ya bata haushi ta juya ta shige mota
Sufyanu ya karba yace “to nagode Allah ya biya” ta amsa da Ameen tace “ai mune da godiya, in ba damuwa ka bani number ka ko da nan gaba nima na samu nawa mai gyaran motar” yace to, ya karanto mata number ta rubuta, ta kira tace “ga tawa number nan ka saka yasmeen, ni kuma mai zan saka” Yace mata “Sufyanu” tace “sufyan dai wane sufyanu kuma” yayi dariya sukayi sallama ya hau mashin ya tafi su kuma suka shiga mota suka wuce
__________________________
A bangaren mommy kuwa suna gama waya da Ammi ta kira Kamal tace yazo tana nemanshi
Yazo tace mishi “ka shirya anjima kaje wurin Bazla ka gaya mata, kaga idan ta amince shikenan sai a sanarwa abbanka da nata, nasan ma InshaAllah zata amince” ta fada cike da farinciki
Kamal yace “to mommy InshaAllah zanje, zan kira Abdulhakim sai ya rakani” mommy tace “hakan ma yayi, Allah yasa a dace” ya amsa da Ameen
Ya fita yana Jin dadi a ransa, ya dauki wayarsa ya kira Abdul ya sanar da shi fitar da zasuyi yace da an gama sallar Isha zasuje, Abdul yace “Allah ya kaimu Ango” kamal yayi dariya sukayi sallama
_____________________
Suna hanya Bazla tace “ke dai wallahi yasmeen kin fiye shishshigi, meye kuma na wani karbar number sa” yasmeen da ta gaji ga Yunwa batason dogon musu kawai tace da ita “saboda nan gaba” Bazla ta tabe baki bata ce komai ba
Suna isa gida har an kusa magrib a galabaice suka shiga gida barin Bazla da bata da juriyar Yunwa
Suka shiga da sallama Ammi na zaune tana batun qara kiran bazla kenan suka shigo ta amsa musu sallamar tana musu sannu
Suka zauna sukace yau Ammi mun wahala, tace “sannunku kam” yasmeen tace “ni Ammi zan wuce gida naga dare yanayi” Ammi tace “ai ko gida zaki sai ki tsaya kici abinci ko” yasmeen tace “Ammi idan naje zan ci” Ammi batace komai ba ta dauki wayarta tana dannawa ta kara a kunnenta alamun waya ta kira, suka gaisa da wacce ta kira, sai ji sukayi Ammi tace “yasmeen a nan zata kwana saboda sun dawo sun gaji ga magrib tayi, nan Ammi tayi wa matar bayanin cewa motar Yasmeen ce ta lalace a hanya amma an gyara”, matar da ta kasance mahaifiyar yasmeen ce tace “ai bakomai nan ma ai gidane, Allah ya kaimu goben, nima yanzu nake batun kiranta naji naga har yanzu bata dawo ba, nasan in dai sun hadu ai sai kai dare ba’a rababu ba” Ammi tace “haka fa, to nagode hajiya a gaida su zainab” maman yasmeen tace “zasuji nima nagode” sukayi sallama
Ammi ta kalli yasmeen tace “yanzu zakici abincin ko kuwa” yasmeen tayi dariya tace “Ammi ai kuma shikenan, bari muyi wanka muyi sallah naji ma an fara kiran sallar”
Ammi ta miqe tace “to nima bari na shiga nayi sallah, abincin yana kan dining don ni sai nayi Isha zan fito” suka amsa da to duk suka tashi suka wuce
__________________________
Sufyanu yana komawa gareji ya bawa Oga mukullin mashin dinshi sannan ya nuna wa Oga kudin da su yasmeen suka bada, Oga yace “kaga fita tayi amfani, Allah yasa Albarka” sufyanu yace Ameen ya miqawa Oga kudin, Oga yace “me zanyi dasu ai nakane ka qara a siyowa mallam magani” sufyanu ya ce “Oga ko Rabine ka karba mana” Oga yace shi bazai karba ba, sufyanu yace Oga nagode, zan wuce gida” Oga yace “a gaida mallam zan shigo anjima InshaAllah” sufyanu yace InshaAllah sukayi sallama ya wuce kasancewar dama Karfe 6 yake tashi daga aikin
Ya nufi gida cike da murnar samun kudin da yayi
____________________
Ammi na sallame sallah sai ga kiran mommy, ya dauka da sallama dauke a bakinta suka gaisa take sanar mata zuwan Kamal din tareda abokin shi, Ammi tace “to sai sunzo” sukayi sallama
Su yasmeen kuwa sunyi wanka sunyi sallah, suka sauko qasa don cin abinci, suna zaune ne suna cin abincin suna hira Ammi ta sauko tace “Bazla zakiyi baqo da anyi sallar Isha” Bazla ta kalli Ammi da mamaki tace “baqo kuma Ammi” Ammi tace ey baqo Bazla tace “waye” Ammi tace “idan yazo zaki ganshi” ta qara da cewa “yasmeen ku tashi ku dan hada wani abun tabawa mai sauqi kafin suzo, bansan d zuwan nasu bane da nasa kulu tayi kafin ta wuce” yasmeen da take qunshe dariya saboda yanda Bazla ta wani bata fuska tace “to Ammi yanzu da mun gama InshaAllah” Ammi tace “yawwa kuyi da sauri kuma” yasmeen ta amsa da to Ammi ta juya zata koma dakinta sai taji alamun bude gate tayi zaton ko su kamal din ne, ta dan tsaya ba’a jima ba aka bude kofar parlor
Bazla da idonta na qofar don ganin waye yazo tayi wani tsalle ta tashi da gudu ta rungumeshi tana Abie na oyoyoooo
Ammi da take mamaki bayan dazun yace mata jibi zai dawo sai kuma gashi ta gani, Abie ya katse mata tunani yace surprise nayi muku, ya kalli Bazla yace ni fushi nake dake shalele jiya da yau baki kirani ba, tace “Abie tuba nake, nayi kewarka Abie” yayi dariya yace “bansan yaushe shalele zata girma ba” duk sukayi dariya, Yasmeen ya taso tace “Abie sannu da zuwa” Ya amsa mata cikin fara’a
Ammi tace “zakuje kuyi abunda na sakaku ko sai lokaci ya qure” Bazla ta turo baki tace “ni sai na gaisa da Abie” Yace aa shalele kuje kuyi aikin kafin na huta nima sai muyi hira ko shalelen Abie” tayi dariya tana Jin dadi suka juya itada yasmeen
Ammi ta mishi sannu da zuwa, ya amsa da murmushi akan fuskarshi
Suka wuce dakin Abie ta hada mishi ruwan wanka ta fito domin hada mishi abunda zaici
Yasmeen tace bari su dafa Jollof din taliya akwai zobo a fridge sai hada musu haka kuwa sukayi nan suka hada komai suka koma daki yasmeen nayiwa Bazla tsiya tana “iyyeee Amarya” Bazla taqi kulata har akayi Isha sukayi sallah Ammi ta kirata a waya tace ta shirya fa da kyau, Bazla ta dauko atampa doguwar riga blue mai ratsin red aciki ta sha stone work ta saka veil fari, tayi kyau sosaii ai kuwa yasmeen ta dinga damunta ita dai sai hararta take, a ranta tana waye wannan wanda zaizo…..
A bangaren Ammi kuwa bayan Abie yayi wanka yaci abinci, take gayamishi zuwan na kamal, ai kuwa Abie yayi farinciki sosaii yaji dadin hakan
________________
Ana gama magrib Abdulhakim yazo wurin Kamal, suka zauna suna hira har akayi Isha suka shiga sukayi sallama da mommy suka fito suka je masallaci Ana gama sallah suka wuce zuwa gidansu Bazla, Abdulhakim yaso su tsaya su siyi ko da turare ne amma Kamal yace baza’a siya ba, Abdul ya kyaleshi suka qarasa gidansu Bazla inda mai gadi ya bude musu suka shigo
Ammi da Abie suna parlor Kamal da Abdul suka shigo, Kamal yayi mama kin ganin Abie, suka gaisa yana sauke kansa qasa, kunya da ladabin Kamal ya sanya Ammi da Abie duk sukaji zasuso ya zama surukinsu
Sun gaisa Abie yace “to kuje parlon baqi yanzu zatazo” suka amsa da to suka tashi suka nufi parlon kasancewar Kamal yasan parlon
Ammi ta tashi taje dakin Bazla tace suje parlon baqi ga baqin nan sunzo, yasmeen ce ta amsa mata, yasmeen ta saka doguwar riga Itama tayi kyanta suka jero suka fito
Suna zuwa parlon sai d gabanta ya fadi ganin Kamal ne, haka dai suka qarasa ciki Yasmeen ce taketa murmushi suka zauna, tunda suka shigo Abdul yake kallon yasmeen
Suka gaisa Kamal yace “nasan zaki yi mamaki kou Bazla” Bazla dai kanta na qasa don ita dai tasan ko me za’ayi bazata iya son shi ba, ita a matsayin yaya ta daukeshi, ya katse mata tunanin da takeyi, yace kinyi shiru “ta qaqalo murmushi tace nayi mamaki gaskiya” yace “ai ba abun mamaki bane nidai idan kin amince inaso ki zama matata kuma uwar ‘ya’ya na” batace komai ba
Yasmeen ta tashi tace bari akawo muku ruwa ta koma cikin gida ta dauko kayan da suka hada, kular taliya da jug da aka zuba zobo mai sanyi, sai cups da plates da spoon ta kawo ta aje, Abdul yace “kai ni dai na qoshi amma a bani zobon nan ya burgeni” ta zuba mishi ta zuba wa Kamal abincin da zobon ta tashi tace to bari a baku wuri Abdul shima ya tashi yace “qaramin zobon nan nima na fita” Bazla ji tayi kamar ta riqe yasmeen amma tana zuba wa Abdul zobon suka juya a tare suka fita aka barta ita da shi
Yace mata “Bazla bakice komai ba” tace “zanyi tunani” a ranshi yace kila kunya takeji yace “to Allah yasa naji Alkhairi” tace Ameen
Ya fara cin abincin, yaci kadan yace zasu wuce
Tace “to” ya tashi tabi bayanshi, anan farfajiyar gidan inda aka ajiye wasu kujeru guda uku sukaga Yasmeen da Abdul suna hira
Bazla a ranta tace “ta samu dan uwanta mai surutu ta saki baki tana dariya”
Suka qarasa Abdul ya yiwa yasmeen sallama sannan ya yiwa Bazla suka shiga mota suka wuce
Su kuma suka shiga cikin gida Ammi da Abie dai suna zaune suna kallo suka shigo
Abie ya kalli Bazla yaga da damuwa a fuskarta, yace shalelena menene ya faru kike ta hade rai
Kamar jira take tace “ni wallahi bana son shi kuma ni bazan aureshi ba” ta fada kamar zatayi kuka
Abie tace “meyasa shalele kamal din ne bakyaso me yayi kiki meye kuma dalilinki” ya jero mata wannan tambayoyin
Tace “ni Abie kawai banason shi” yasmeen da tana Jin haka ta tashi t hau sama dakin Bazla ta shige
Abie yace Bazla ta dago da mamaki Jin yadda y kira sunanta kai tsaye
Yace “aurenki da kamal kamar anyi an gama kinji na gaya miki” Ammi tace “haba Alhaji mubi abun a hankali” Abie yace “na gama maganata sai ta auri Kamal” Ammi tace auren dole kenan fa” yace “tabbasa sai ta auri kamal” Ammi tace “a’a fa Alhaji ni dai ba za’ayiwa ‘yata kwal auren dole ba”
Abie yace “idan ma auren dolen ne ai tarihi ne ya maimaita kansa”!!!! Bazla ta kalli Abie ta kalli Ammi cikin rashin fahimtar abunda Abie ya fada…