56
💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔
( shi ya san gidan mai rowa)
```By```
``` NAFISAT ALIYU SASAAL```
```Page 56```
________Kuka Halima takeyi ko ina na jikinta na rawa kafin ta silale ƙasa,zuciyar kamar ana hura mata wuta.
Kallon takaici dana tsana mai zafi Uncle Suraj ya bita da shi,yanajan siririn tsaki.
"Ka gama Sirajo? Nace ka gama? Idan ka gama sai ka tashi ku tafi,na kuma gode da iyakata da ku ke nunamin".
Daga haka ta ƙwalawa Shamsiyya kira.
Fitar da Halima tasa tayi zuwa ɗakinta don har lokacin kuka takeyi.
Babu irin lallashin da Goggo batayiwa Halima ba,amma haka ta raba dare ta na kuka.
Tun daga ranar sai Halima ta ƙauracewa zaman Parlon Goggo gaba ɗaya kullum tana ɗaki, ko da ranar weekend ne.
Sauyin Halima na damun Goggo matuƙa,ga shi har lokacin babu wanda yake goyon bayan zaman Halima sai Baba Salahu dake ƙarawa Goggo ƙarfin gwiwar ƙwaɗayi yasa sukeyin duk waɗannan maganganun.
Waya mai tsadan gaske Goggo tasa aka kawowa Halima,ɓangaren Maysarah Goggo tasa aka canza komai zuwa sababbi masu tsananin kyau da tsada,gaba ɗaya tasa Halima ta koma can da zama. Hakan ba ƙaramin daɗi yayiwa Halima ba,ko ba komai zata huta da ƙananun maganganun ɓakin da basa rabuwa da sashen Goggo.
Haka kawai tayi sha'awar buɗe duk wani shafukan sada zumunta domin ta samun abinda zai na ɗebe mata kaɗaicin da take ciki idan babu school.
A haka shekara har ɗaya da rabi ya shuɗe babu wani labari akan Maysarah ko dawowar shi. A cikin wannan shuɗewar shekara ɗaya har da rabi,Halima ta ƙara zama ƴan mata,taƙara hankali da nutsuwa.
Bata da wasu ƙawaye ko a social media ko a Makaranta,ita kaɗai take rayuwarta, saboda gudun tozarci,don dayawan mutane suna son kane idan su na tunanin wani ne kai,amma da zarar sun fuskanci kai ba kowa bane sai su fara gudunka.
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
New York
Fort Hamilton Barrack
1:34pm
Cikin ƙananun kayan Saint Laurent da suka kama jikinta kuma suka amshi kalar skin ɗinta ta shirya.
Duk wani turare daya dace tayi amfani da shi,duk tayi bayan Mommynta taƙara tabbatar mata bata samu mistake ba.
Labarin barin aikinshi tun shekara ɗaya daya wuce ne ya kusa haukata ƙaramin ƙwaƙwalwar Yusrah.
Babu wanda bata nema ta tambaya ba a Abokanan aikinshi amma dukka amsa ɗaya take samu,na babu wanda yasan ƙasar da Maysarah yakoma.
Da kuka mai tsanani ta dawo masaukinta, jinkinta na rawa ta kira Layin Mommyn su,tsinuwa mai girma ta fara aikawa Maysarah kafin takaici yasa kuka kwace mata. "Duk kuɗin dana kashe Yusrah? Wallahi dole ya bayashi,sai na nemoshi duk inda ya shiga wallahi.
Ƙwarin gwiwar sai an nemo Maysarah ko ta halin yaya,yasa zuciyar Yusrah samu nutsuwa,don haka tasamu barci mai daɗi ya kwashe ta.
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Komai na tafiyarwa Halima daidai gwargwado,don bazata ce hundred percent tanajin daɗi ba don har lokacin bata daina samun gori da ga bakunan dangin Maysarah ba.
Amma tasawa ranta duk ranar data kammala secondry school ɗinta zata tafi,kuma ita da shi har abada.
Ranar wani Weekend layin Halima yasamu Matsala, garin zuwa wajen Goggo shima wayan ya suɓuce ya faɗi ƙasa screen ɗin ya fashe gabaɗaya.
A take Goggo da batason duk abinda zai damu Halima tace suje Driver yakaisu ita da Shamsiyya ta zaɓi duk wayan da take so,daganan su siyo sabon layi.
Sabon wayan ba irin na da bane don haka takasa gane kanshi gaba ɗaya.
Wajen Shamsiyya dake directing ragowar masu aiki wajen fitar da abinci ta tafi. Saboda ta fita Ilimi.
Da girmawawar da takewa bawa Goggo ta tarbe ta,ganin tana aiki yasa Halima komawa Sashenta,idan tagama sai ta dawo.
Bata jima da komawa ba Shamsiyya tayi knocking.
Bayan ta gamajin ƙorafin Halima murmushi tayi,ta karɓi wayan da girmawawa.
Gaba ɗaya ta sauke mata app ɗin da take amfani da su.kuma kowanne da Sunan Mrs Maysarah Abdulnaseer ta buɗe mata.
Godiya tayi mata sannan ta koma bakin aikinta.
Sababbun Friends Halima tayi,sai dai bata chating da Maza sai waɗanda baza'arasa ba.
A haka Abotar su ya fara da Naseer wanda ya shaida mata shi baƙin ba'amurke ne,amma yanada Abokanai Hausawa sosai don flat mate ɗin shi ma Bahaushe ne,shiyasa yakejin Hausa sosai.
Da farko gaisuwa sama-sama ne yake haɗasu,kafin a hankali ta fara sakin jiki da shi.
Wata rana ta na zaune a school aka turo yayanta na nemanta. Mamaki ne ya kamata don tasan bata da kowa.
Ga mamakinta Faisal ta gani,fuskarshi babu fara'a kamar lokutan baya,kuma dama batasan ran ganin fara'a a fuskar shi ba,tunda a gabanshi Mahaifinshi yaci mutuncinta, amma ko a waya bai kirata ya lallasheta ba.
"Mrs Maysarah Abdulnaseer" ya faɗa yana wasa da keys ɗin hannunshi.
"Ina wuni"
"Ai baki amsa sunan naki ba,balle na amsa gaisuwarki".
Ya faɗa yana kallonta da kyau.
"Yanzu Halima bazaki yiwa kanki faɗa ba,ki koma gida,tayaya zaki yarda Goggo ta ajjiyeki,har kina biye mata har kina amfani da wani sunan Maysarah a shafukan ki anya lafiyarki ƙalau" gaba ɗaya Halima bata fuskanci ina ya dosa ba.
Ganin ta saki baki tana kallonshi yasa zuciya ta kwashe shi ya faɗa mata maganganu son ranshi,sannan ya baɗe ta da ƙurar motar shi,batare da la'akari da halin da zata shiga ba.
Ta kasa kuka kamar yanda takasa motsawa.
Kenan dagaske shima Uncle Faisal yazama abinda take zargi kenan,na bin ra'ayin danginshi da suke ƙyamarta,to da maiyasa bai yi mata haka ba,"saboda taimako ne kawai tsakanin ki da su ba auren ɗan uwansu ba" zuciyarta ta bata amsa.
Kamar akan ƙaya haka Halima take jinta har lokacin tashi yayi.
Parlon Goggo da batason zuwa ta nufa don taje kitchen bataga Shamsiyya ba.
Ranta a ɗan bace duk da ƙoƙarin ɓoyewa da takeyi sai da ya bayyana a sautin muryarta.
Bayan ta gaishe su ta mayar da hankalinta kan Shamsiyya.
"Uhm Dan Allah Sister Shamsiyya User name ɗina na facebook zaki canza min nakasa" ta faɗa tana miƙa mata wayar.
"A kwai matsala ne Halima" Goggo ta faɗa da damuwa a Fuskarta.
Kamar mai jiran a tambayeta sai ta fashe da kuka tana rufe Fuskarta.
"Zo nan Halima menene matsalar gayaminin kinji"
Muryarta na rawa sosai take ba su labari.
Tsaki mai ƙarfi Goggo taja " babu sunan da zaki canza Halima,duk baƙin kishi ne ke damun su,narasa zuciya irin ta su,karki ƙara kuka akan su kinji"
Goggo ta faɗa cikin lallashi.
Maza kije ki huta anjima zan kira Aminu ya kai ki sha iska kinji.
"Da Sister Shamsiyya?"
Ta faɗa da ragowar kukan da bai ƙarasa tafiya ba.
"Eh mana tare zaku je maza kije ki huta kafin anjima".
Baƙin Abaya da stone mai ƙyalli yayiwa ƙawa tayi ado dashi,kamar matashiyar Balarabiya.
Hotuna masu kyau Shamsiyya ta ɗauke ta,tana shan Ice cream.
"Wannan shine abinda kike kwaɗayi yasa zuciyarki ta mutu,kika kasa rungumar baƙauyiyar kakarki ku zauna ko,ko da yake kwaratan dangin ku bazasu barki ba. Halima duk girman Halaccin da nayimiki da nasihar dana yi miki shine kika ƙi canza sunan ki ko. Har abada abinda kike kwaɗayi yayi miki nisa,don bazai taɓa son ƴar nakashashiya mai ido ɗaya ba".
Kuka mai ƙarfin daya janyo hankalin dukka mutanen wajen ta fasa tana dafe kanta dake juya mata. A hankali Faisal ya silale,duk da Shamsiyya dake kallon shi amma ta kasa magana saboda tasan waye Faisal da girman tasirin makircin Mahaifinshi.
Ko gama parking dakyau driver baiyi ba Halima dake dafe da kanta ta fito kai tsaye sashenta ta nufa ta datse kanta a ciki.
Tausayin bugun ƙofar da Goggo take yi ne yasa ta tashi ta buɗe mata.
Lallashi da ban baki tayi ta yiwa Halima har da ƙwallarta,tana son Halima ta kuma san dukka wannan ƙalubalen zasu wuce wata rana,amma dole sai Halima ta jure.
Sai da barci ya ɗauke Halima sannan Goggo tabar wajenta.
1:00am ta farka wayarta ta ɗauko tana duba saƙonni har ta zo kan na Naseer,kuma har lokacin yana online.
"Me kakeyi har yanzu bakayi barci ba🥹?"
"Ke nake jira naji lafiyarki😔"
"Yau banajin daɗi😔🥹?"
"Subhanallah maiya sameki😟?"
"😭😭 Labarina mai tsaho ne"
"Karki damu ina jinki"
"Inajin tsoron baka Labarina kar ka daina kulani😟"
"Karki damu ina tare dake"
"Bazan iya typing ba,zaka iya sauraren murya na"
"Of course Halimah"
Labarin abinda Faisal yayi mata ta bashi cikin kuka mai sanyi da taɓa zuciya,ta turamai
"Ohh to maiyasa yayi Miki haka😟🤔?"
"Shima labarin mai tsaho ne🥹🥹"
"Karki damu ina jinki"
Kamar mai raira waƙa haka ta zauna ta juyemai labarinta,ƙarshe ta shaida mishi zata koma wajen Innarta,ita ta haƙura da karatun,kuma ta haƙura da Maysarah har abadah...