57
💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔
( shi ya san gidan mai rowa)
```By```
``` NAFISAT ALIYU SASAAL```
```Page 57```
________"🥹 labarinki akwai tausayi Halimah,Nima haushin wannan mijin naki duk yakamani. Nikam ina tsananin son Matata,don na matsu na koma gareta".
"Dama kanada aure😳?"
"Eh mana😊"
"Allah Ya baku zaman lafiya"
"Ameen"
"Amma ko zan iya ganin hotonki idan ba damuwa😉"
"Eh amma kafara turomin naka"
Sai da ta tabbatar ya turo har hoton ya buÉ—e sannan tayi maza ta kashe Data ta tana dariyar nishaÉ—i.
Hoton take kallo da iya ganinta,tana ganin kyawawa a dangin su Maysarah amma wannan ƙirarshi da tsananin kyawunshi yafi na su. Yafi Maysarah buɗewar jiki da hasken fata,sannan ƙasumbar dake fuskarshi wanda Maysarah ba shi dashi,a dogon hanci da samfurin sirara laɓansu zata iya cewa zasu goga. A tsaye yayi hoton da ƙananun kaya da gibgegen saint Laurent jacket daya ɗora a sama.
Ƙasumbar dayayiwa fuskarshi ado da gilashin daya taimaka wajen rage gano asalin kamannin shi duk da gilashin mai haske ne daya ƙara ƙawata fuskarshi.
Takai minti 20 tana kallon shi,da son tantace kamannin shi,amma bata gano komai ba,sai tsananin baiwar kyawun da Allah yayimishi.
Da tunanin hoton Naseer Halima tayi barci.
★washe gari bayan ta tafi makarantar sai taji gaba ɗaya ta matsu ta dawo suyi chating da Naseer,duk da tasan tayi mishi laifi naƙin tura hoton ta.
Bayan ta dawo, Parlon Goggo ta fara biyawa,sai dai kafin ta shiga taji alamun da tayi baƙi, silalewa tayi ta koma nata sashen.
Sai bayan tayi sallar Ishsha'i ta kunna Data ta,tana sakin murmushi,da saƙon shi ta fara cin karo na tayi mishi wayo bata turo na ta ba.
"Ni ina da aure,amma ka bari idan Goggo tace na tafi Maysarah ya sakeni zan turama, am nace ba dan Allah na tambayeka?"
"🤨 Ina jinki"
"😄 Sai kayi murmushi sannan zan tambayeka"
"Ina jinki Halimah"
"Nace yaya kakeji idan ka kalli kyawunka a mudubi🤔"
"😄 Banajin komai Halimah"
"Dagaske? To maiyasa nake ta kallonka"
" Saboda nafi Maysarah kyau"
"😳 Shima kyakyawane,sai dai bashi da gemu,kuma bashi da fari sosai,kuma baya dariya,kuma shi ba ƙato bane irinka"
Ta turamai da iya gaskiyarta.
"🤣🤣🤣🤣🤣🤣 Halimah, kinada abun dariya"
Da ire-iren wannan hirarrakin da kullum Naseer da Halimah sukeyi shaƙuwa mai ƙarfin gaske ya shiga tsakanin su. Sai ya zamana idan dare yayi bata ganshi Online ba har kuka take yi a wasu lokutan.
Babu abinda ya sauya ta ɓangaren jin tsananin tsanar Halima a zuƙatan kaso mafi rinjaye na dangin Maysarah na kusa da na nesa,musamman masu alaƙanta rashin dawowarshi da zaman jiranshi da Halima take yi.
Babu biki ko Suna dazai zo,wanda basu ƙafa gulmar Halima ba.
Ana cikin wannan yanayin batun auren Faisal da ƙanwar Mijin Maryam ya fito har an tsayar da ranar aure.
Wannan abun baƙin cikin a zuciyar Mubeena kaɗai yake gudana banda na iyayenta don basuga abin yiwa kishi a mutum irin Faisal da bashi da wani dukiya ko cikakken ƴanci na ƙashin kanshi ba.
Kuma dama tun farko basu so aurenta da Faisal ba Allah ne yaƙaddara.
Wani irin tsanar Halima mai zafin gaske ne yayiwa zuciyar Mubeena dabaibayi tanajin ko kashe Halima ne zata iya yi.
A ɓangaren Halimah ko tari tayi to Naseer sai ya sani,haka duk wanda ya ɓata mata rai sai ta gayamai,shine abokin shawararta kuma abokin gayawa sirrinta,tunda babu wanda yajata ajiki don jin matsalolinta na rayuwar yau da gobe. Dama-dama Inna bata gajiya da tambayarta idan da akwai wata matsalar karta ɓoye mata ta sanar da ita.
A haka har wani shekarar ya ƙara shuɗewa babu alamun Maysarah zai dawo gareta.
Fushin Uncle Suraj da asalin baƙin halinshi ne ya bayyana na lallai sai Halima tabar gidan,cin mutuncin da baisan Goggo zata iya yimai ba tayi mai,ta kuma fito mishi da kwaɗayin abinda sukeyiwa don kawai Maysarah ya dawo su sa shi ya wakilta su akan dukiyar da Abdulnaseer ya bar mai da sunan zasu juya suma su kwashin haramun ɗin da suka saba ci.
Bai taɓa sanin Goggo na da masaniya akan duk abubuwan da suke yi ba,tunda bata tanka musu. Sai zuwan Halimah,rantsuwa yayi na dole sai ya ɓatar da Halima har abada.
Hidimar bikin Faisal ne yaƙara sasanta Goggo da ƴaƴanta,sukayi ta raha da nunawa juna so kamar rashin fahimta bai taɓa gilmawa tsakanin su ba.
Sumayya da Maryam duk sun halarci bikin kowacce na kallon Æ´ar uwarta sama-sama saboda sanin sirrin juna da sukayi wanda ba kowane yasani ba.
Kamar dai yanda suka saba wannan karon ma Biki sukayi na bajinta da birgiya,daga dukka bangarorin, bakin Uncle Suraj kamar zai yage saboda fara'ar da bai saba yiba, saɓanin Uncle Ghali da ko fara'ar yaƙen yakasayi saboda wutar hassadar dake ruruwa acikin zuciyarshi.
Gajiyar hidimar Biki da damuwar rashin samun Maysarah ta kowani hanya,yasa jikin Goggo fara rikicewa,ga jikin tsufa.
Da farko likita ne yake zuwa duba ta,jikinta yayi sauƙi sosai,bayan wasu kwanaki jikinta yaƙara rikicewa.
Maruka Halima dake gefenta tana kuka tasha a hannun Uncle Suraj,ya kumayi rantsuwar duk abinda ya samu Mahaifiyar su ita ce sila don haka ta kwana da shiri.
Da tsananin kukanta akaron farko ta kira Naseer video call, wajen Naseer babu wuta don haka bata wani ganin fuskarshi,sai nata kyakkyawar fuskar dayayi jajir da kuka da kuma zafafan marukan da tasha.
"ðŸ˜ðŸ˜ Kayi shiru kaÆ™iyin magana,jifa ya kumburamin fuskana bakace nayi haÆ™uri ba"ta faÉ—a da tsananin sanyinta daya haÉ—e da damuwa
Still bai bata amsa ba kuma tasan yana kallonta. Kuka tasa mai ƙarfi ta kashe wayan gaba ɗaya.
Yanke shawarar fitar da Goggo Uncle Suraj yayi saboda samun damar cikar kuÉ—urinshi.
Da sassafe Shamsiyya ta shirya breakfast É—in Goggo ta tafi kai mata.
"Nan da kwana biyu nakeson idan ka ɗaukota daga Makaranta ka wuce da ita,don Banason kowa ya zargi ɓacewarta ta hannun mu"
"Okay Sir"
"Sai ka turamin Account number ka,fitar zance na nufin komai"
Uncle Suraj yafaɗa yana cigaba da danna wayar dake hannunshi,drivern dake kai Halima Makaranta na durƙushe a ƙasa.
A zancen da Shamsiyya ta É—anji sam bata fuskanci komai ba,amma dole zata bibiyi drivern Halima,komawa tayi da abincin gudun kar su ganta.
Da zazzaɓi mai zafi Halima ta kwana,saboda
Kukan da tasha. Tsoron fita ma takeyi gudun haÉ—uwa da Æ´aÆ´an Goggon da suka zame mata dodanni.
Har su Goggo suka bar gidan Halima takasa fitowa, Goggo dake jin jiki duk batasan wainar da ake toyawa ba.
Da ƙarfin Hali Shamsiyya ta nufi rumfar da Drivern Halima yake zaune yana waya.
Da taku a hankali Shamsiyya ta biyo ta bayanshi ko Allah zaisa taji wani abun a wayar dayakeyi.
"Ka fuskanceni wallahi tsoro nakeji,kasan babbar Hajiyar su ta yarda dani,kuma idan na kai musu Halima wallahi kasheta zasuyi ina zan kai dukka wannan haƙƙin,amma kuma ina son aikina kabeeru don Allah kaban shawara,don jibi ne zan kai musu ita".
A hankali Shamsiyya da gabanta ke faɗuwa ta juya,da gudu ta ƙarasa sashen Halima amma harta gama bugunta Halima bata buɗe ba ga wayoyinta a kashe,har zuwa dare.
Ranar Shamsiyya bata rutsaba.
★da sassafe ta ƙara komawa zaman jiranta ko zatayi shirin Makaranta ta fito amma shiru har zuwa yamma. A haukace Shamsiyya ta fara buga ƙofar tana kiran sunanta,wanda yasa dole Halima ta buɗe ƙofan,duk ta zabge idanuwanta duk sunyi jajir.
Dukka Hannayenta biyu Shamsiyya ta kama jinkinta na rawa suka dawo Parlon.
"Halima wa kika sani da zai iya ɓoyeki kafin gobe da safe"
"Inna" ta faÉ—a muryarta na rawa itama.
"A'a Halima zasu iya binki can kiyi tunani wa kika sani bakida ƙawa,baki kowa ko a wani ƙasa ne"
"A'a Sister Shamsiyya bansan kowa ba"
Ta faÉ—a tana fashewa da kuka.
"Ohhh na tuna akwai Naseer amma hotonshi kawai na sani kar shima ya kashe ni".
"A'a Halima bani shi awaya muyi magana"
Batayi niyyar ƙara neman Naseer ba amma batada yanda zatayi. Suna kunna wayan kiranshi na shigowa Shamsiyya ce ta ɗaga ta nufi Bedroom ɗin Halima tana tattaro nutsuwar.
A hanzarce ta fito tana cewa Halima ta shiga tayi wanka,kayan Halima ta haɗa a ƙaramin jaka sai passport ɗinta dayaso bawa Shamsiyya ciwon kai don yana ɓangaren Goggo.
Bayan ta ɗauko a hanyar dawowarta ta haɗu da Mom Fahima,daƙyar tayi jarumtar ɓoye fargaban da take ciki har ta samu tabar sashen gaba ɗaya bayan kallon banza da tambayoyin da tasha.
Da daddare Shamsiyya takai Halima dake kuka kamar ranta zai fita inda Naseer yace a kaita,saboda tsoro kasa tafiya Shamsiyya tayi ta barta tare suka kwana.
Immigration ne mutumin da Iyalanshi ma su kirki,da kanshi ya ƙarɓi Number Inna yayi mata bayanin da basusan na menene ba,sai lallashin Halima da ta komayi,wanda hakan ya sanya nutsuwa a zuƙatan dukkan su tunda Inna ta yarda.
Dai-dai lokacin da Halima suka isa Airport, Driver yake knocking É—in sashen Halima....
Allah Sarki Halima🥹🥹🥹🥹🥹