MAI KWAÆŠAYI

58

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

``` NAFISAT ALIYU SASAAL```



 ```Page 58```


________Yakai minti talatin yana bugawa amma ba'a buÉ—e ba,a hanzarce ya juya don zuwa Makarantar su ko ta wuce can. Kabeeru Abokinshi yabashi shawarar karya kuskura yayi wasa da damar daya samu,tunda ai baisan asalin mafarin rigimar na su ba,don haka karyasa kanshi a ciki yazo yarasa aikinshi da ya samu daÆ™yar kuma ga albashi mai tsoka 


Kai tsaye suka sana'arshi basu ga zuwan Halima ba,a haukace yafara neman Number Uncle Suraj.


Yaje ya duba indai Shamsiyya bata gida to tasan inda Halima take. Abin Uncle Suraj ya faÉ—a kenan fusace kamar wanda ya haÉ—iyi wuta.



Bayan tafiyarsu Halima airport dasauri Shamsiyya ta kimtsa ta nufi hanyar gida. Daga nesa ta hango fitar motar drivern Halima.

Da hanzari ta shige gidan ta nufi daƙinta ta kwanta biyan bashin barcin da basu samu yi ba ita da Halima.


Babu wanda yasan fitar Shamsiyya balle dawowarta,tunda ragowar masu aiki sunyi sallama da ita kafin su kwanta,kuma da safe babu wanda ya nemeta saboda dama girkin ɓangaren Goggo kawai takeyi kuma batanan.



Tsabar fargabar dayake ciki idanuwanshi har faÉ—awa sukayi lokaci É—aya.

"Ina Shamsiyya" ya tambayi wata maid dake ƙoƙarin fita daga sashen.


"Sister Shamsiyya bata tashi barci ba gaskiya"

Ta faɗa tana ƙoƙarin giftashi.

"Please taimaka kiyimin magana da ita"


Ran Shamsiyya a ɗan ɓace ta fito saboda barci da aka katse mata.


Bayan sun gaisa ya tambayeta Halima.

"Ai kai zan tambaya Halima" ta faÉ—a tana tsare shi da ido.

"Halima bata gidannan kuma naje Makarantar su,sunce bata zo ba"


Ihu mai ƙarfi Shamsiyya ta kurma wanda ya janyo hankalin dukka ma'aikatan gidan,da gudu tayi sashen tana surutai. Tasan mistake ɗaya zatayi komai ya faɗa da ita.


Yanke shawarar ɓalle ƙofar sashen akayi. Amma babu alamun Halima a ɗakin.


Cikin dabara Driver ya silale da duk wani abun arziƙi daya samu a gidan da uban kuɗin da Uncle Suraj ya turamai ya gudu asalin garin su da babu wanda yasan da shi.


Labari mai zafi da ciwon da Uncle Suraj yasamu ne yasa ya dawo yabar iyalanshi tare da Goggo.


Abun takaici har wajen Inna ya tura wasu Mata,tsoro da takaicin rayuwar da wasu suka É—orawa kansu ne yakama Inna,har gudanawa Halima take da har Mutum kamar wannan zai dinga bibiyarta.

Amsar da suka samo bai yiwa Uncle Suraj daÉ—i ba.



HALIMA wannan ne karonta na farko da tayi tafiya mai tsaho a jirgi a rayuwarta, ga damuwar da take ciki,ta kasa cin komai idanuwanta sun ƙanƙance sunyi ja.


Lokaci zuwa lokaci sai ta saki ƙaramin kuka tana rufe Fuskarta.

Naseer to tayayama zata iya rayuwa da stranger a waje ɗaya. Hirar su iya online ne ko muryarshi bata taɓa ji ba kamar yanda shima bai taɓajin na ta ba. Amma wani dalili zaisa har Inna ta amincewa tafiyarta har wani ƙasa gurin wanda basu taɓa gani ba. Ko dai itama ta gaji da ita ne ta daina sonta kamar yanda Uncle Faisal da Uncle Maysarah suka juyamata baya don kawai ita ƴar marasa arziƙi ce.


Da ire-iren waÉ—annan tunanin Halima tayi tafiyar wajen hour takwas ba kaÉ—an zuwa Birnin Birmingham dake Midlands É—in United kingdom. Lokacin da su ka isa yayyafi na sauka kaÉ—an-kaÉ—an 


Batada gogewar zuwa ire-iren waɗannan guraren tunda bata taɓa zuwa ba, amma yanayin kamewarta da sanyinta sai ya hana hakan bayyana,sai tayi kamar yanda taga kowa yanayi.


Dogo ne sosai mai ginannan jikin da hutu da gym ya huÉ—a.

Kalar fatarshi kwata-kwata baiyi kama dana ɓakin ba'amurke ba,kai tsaye haskenshi da kamaninshi yafi kama da na ƴan Russia.dai-dai da ƙasumbar fuskarshi ba baƙi ba ne,kuma baiyi mata kama da wanda ya tura shi ba,kamar dai halittar shi ce.


"Halimah" ya faɗa yana nunata,mamaki da al'ajabine yasa Halima binshi da kallo tana ƙamewa a tsaye.


Murmushin da kusan zatace baiyiwa fuskarshi kyauba yasakar mata.


"Nine Naseer ashe bazaki ganeni ba" ya faɗa da Hausar shi da baya fita dakyau amma sosai yayi ƙoƙari.


Girgiza kanta tayi,kuma taki motsawa daga inda take tsaye,tayaya ma zatayi rayuwa da wannan mutumin.


"Halima karki ja hankalin mutane kan mu,ki zo muje gida matata tana jiranki"

Ya faÉ—a yana gwamutsawa da turanci.


A hankali ta gyaÉ—a mishi kanta zuciyarta na tsinkewa. Kamar mara gaskiya haka ta bi bayanshi.


Motan daya haɗiye miliyoyin dollars driver ya buɗe mata,ta zauna a mazaunin baya tsoro na ƙara shigarta,ko dai safarar mata yake yi.ta tambayi kanta.

A haka batasan tsadar kayan jikinshi da agogo da sauran kayan kuɗin da yayi sauƙaƙƙiyar ado da su ba.


"Maiyasa kayi fari dayawa a waje?sannan kafi kyau a hoto. Gemunka ba haka yake ba nakasa yarda kai ne Naseer dan Allah karka cuceni Ni marainiyace".


Ta faɗa tana fashewa da ƙaramin kuka haɗe da toshe bakinta.


Murmushi ya saki haÉ—e da faÉ—in.

"Babu cuta tsakanin mu Halimah,tunda har Kakarki ta amince dani"


Wannan karon kukan dayasa Naseer dariya ta saki don yakasa riÆ™ewa duk da shima ba gwanin yin dariya ba ne,amma diramar Halima dole ya sashi darawa.


Daga haka bata ƙaracewa komai ba,sai zazzaɓi mai zafi daya rufeta gaba ɗaya ta gama sallamawa rayuwar da take ciki. Mahaifiyarta ma tafita kwanciyar hankali da jindaɗin rayuwa tunda ita rayuwar ƙauye tayi da babu wani tashin hankalin raba mutum da ranshi sai dai gulmammakin da baza'a rasaba.


Tafiyar minti hamsin ne ya kai su gidan Naseer mai É—an karen kyau da tsari gwanin sha'awa,saboda traffic É—in da suka É—an samu a hanya.


Kamar mara gaskiya haka Halima take bin bayanshi zuciyarta kamar zai faso ƙirjinta ya fito saboda tsananin tsoron dake shigar ta.


Living room ne mai kyau da tsari da akayiwa ƙawa da kayan more rayuwa,babu tarkace sosai wanda hakan ya taimaka wajen ƙawata shi a idon mai kallo.


"Zauna"Naseer ya faÉ—a yana nuna mata É—aya daga cikin cushion masu laushi da'akayiwa Parlon ado da shi.


Juyawa yayi da sunan yana zuwa,kasa zama tayi sai Æ™aramin kuka daya Æ™wace mata,siraran laɓɓanta har rawa sukeyi,mai yake shirin faruwa da ita,da gaske dai wannan farin mutumin shine Naseer É—in da take chating dashi.


Zaunannen ƙamshi ne na diman da'iman ga duk wanda ya sanshi ko a ina yaji makamancin ƙamshin to sai ya tuna dashi ko da bayan ranshi ne.


Lumshe idanuwanta tayi tana ƙara buɗe ƙofofin hancinta don basu damar shaƙar abinda suka rasa har abada. wataƙila nutsuwarta da ta rasa da ƙwarin gwiwar tunkarar rayuwar dake shirin zuwar mata zai dawo mata.


Kyakkyawar rungumar daya lulluɓeta da dukka wani sanyin dake shigarta ta samu daga bayanta,ko kanta ba'a hangowa ƙamshin shi naƙara yimata illar da batasan iyakarshi ba. Bata motsaba don kamar ta tafi wani duniyar ne daban.


Gajiyayyun idanuwanshi da azabar rashin samun barci tun ranar da kawunshi ya mareta ya lumshe kafin yaƙara buɗesu gaba ɗaya sunyi ja kuma sun ƙanƙance kamar wanda yayi ciwo.


"Halimahhh" ya faɗa kai tsaye da asalin sautin Muryashi, sannan yaƙara ƙanƙanmeta,don karta tsorata


Kuka mai sanyi daya haÉ—e da dariya ta saki,duk da bawai ta yarda da gaske shi É—in bane,amma muryarnan dole tashi ce, don shi kaÉ—ai ta taÉ“aji da irinshi a zahiri, sai kuma a talibijin ko tallolin kamfanonuwan da suka ci suka Æ™oshi kuma suka amsa sunan su.


Yaƙi bata damar barin jikinshi balle taga fuskarshi.


"Halimahhhta" yaƙara faɗa, amma wannan karon da sautin mai sanyi da shiga rai.


"Inaso naga fuskarka da gaske kaine" itama da faÉ—a da tsananin sanyin da takeji ya na bin kowani jijiya na jikinta.


Ƙaramin murmushi yasaki wanda sautinshi ya fita a hankali. "Za ki iya kallona bazan baki tsoro ba" ya faɗa saboda yanayin sauyin idanuwanshi dayasan abu kaɗan ke rikitamasa ita.


"Zan iya" ta faÉ—a da burin son ganinshi ko a wani yanayi yake.


Sakinta yayi yana kama hannayeta bayan ya zauna ya zaunar da ita kan Æ™oshashshen cinyarshi da gym yasa suka murÉ—e


Kai tsaye cikin idanuwanshi take kallo siraran hawaye na biyowa kumatunta,kasa jurewa tayi takai dogayen yatsunta kan fatar idanuwanshi da shi ma ya kafeta da su yana tantance sauye-sauye da ta samu.

Yaƙara fari da buɗewa mai birgewa amma fuskarshi na nan ana Maysarah data sani tun shekarun baya.


Har yatsunta suka sauka kan fatar idanuwanshi da sukayi yaushi bai motsa ba daga kallonta.


"Maiyasa idanuwanka sukayi ja"ta faÉ—a tana kallonshi da irin kallon da bata taÉ“ayimai ba. 

Kan siriran laɓɓanta da suka É—anyi ja yamayar da idanuwanshi,kafin a hankali ya haÉ—e fuskarshi da nata. Babu hayaniya ko gajare a yanda yake subbatar ta sai so da Æ™aunarta da suka yiwa zuciyarshi kamun da babu canji har gaban abadan.


Barka mu da dare