BAZLA❤️

Page 12

by @farnanahhh

Tana shiga daki ta kira Ammi tana kuka, Ammi tace “kirana kikayi kimin kuka” Bazla batace komai ba, Ammi tace “toh zan kashe wayata in kin tashi magana sai ki kira” tayi sauri tace “Ammi don Allah kiyi haquri ku yafemin, nasan ban kyauta ba, banida mafita ne saboda banason shi wallahi Ammi” Ammi tayi shiru tana saurarenta tana Jin kukanta har cikin zuciyarta, Bazla ta cigaba da cewa “Ammi na haqura zan aureshi idan har hakan zai sakaku farinciki” ta qarashe maganar tana kuka, Ammi tayi ajiyar zuciya tace “ya isa kukan, tabbas baki kyauta ba, bai kamata ki saka qafa ki fita daga gidan nan ba ko da kuwa me Abien naki zai miki, Haquri da kike gani yana gaba akan komai Khadija, ki zama yarinya mai haquri da juriya akan duk abunda ya tunkaroki, ki zama mai biyayya da bin umarnin iyayenki, idan kikayi hakan tabbas zakiyi nasara a rayuwa, mahaifinki yayi fushi sosai kuma yace ko ina zakije shi bazai janye maganarshi ba, wannan tafiyar da kikayi kina ganin hakan ne mafita, angode Allah ma da yasa kikayi dabarar zuwa daura, ina mai qara gayamiki ki zama mai haquri a rayuwarki” Bazla da tunda Ammi ta fara magana jikinta yayi sanyi tayi nadamar abunda tayi, tace “Ammi InshaAllah daga yau zan zama mai haquri akan komai kamar ke, kuma gobe zan dawo InshaAllah Ammi” Ammi tace “A’a ni banason ma ki dawo yanzu, kaiwa Inna wayar” Bazla ta tashi ta kaiwa Inna wayar

Inna ta amsa tace “To Lubabatu gobe yarinyar zata dawo in Allah ya kaimu” Ammi tace “A’a Inna banason ta dawo nafison ayiwa tufkar hanci, a bar maganar auren nan tunda dai bataso, don Allah Inna kiyi mun Alqawarin bazaki gayawa mahaifin nata ba” Inna tayi shiru tace “toh tunda Kince haka shikenan amma dai ni naso ta koma goben” Ammi tace “Inna tunda tace bataso me zaisa ya dage yace dole sai anyi, kawai saboda taimakon da yayi mishi a rayuwa, haba Inna ai ba dole sai ta wannan hanyar zai saka mishi ba” Inna tace “to shikenan Luba Allah ya sawwaqa yasa mu dace” Ammi ta amsa da Ameen sukayi sallama



___________________________


Sufyan yana wurin aiki Isma’eel yazo yace “ga chewing gum dinka nan tazo” Sufyan ya kalleshi yace “Wacece haka kuma” Isma’eel yace “wata ka sani bayan Maryam” Sufyan yace “ohh Maryam me tazoyi nan kuma” Isma’eel yace “sai kaje ka tambayeta”


Sufyan ya tashi ya isko ta inda ta samu wuri ta zauna, da ‘yar fara’a a fuskarshi yace “Maryam kece haka” tace “Eyh ko bakaji dadin ganina ba” yace “ni na isa”


Tayi dariya tace “dama danwake ne nayi nace bari na kawo maka nasanka da son danwake” ta fada tana dariya, yace “Meyasa zaki wahalar da kanki” tace “wane irin wahala kuma, nidai ka karba zan wuce” ya karba yace “nagode Maryama” tana dariya tace mishi “bakomai yayana” sukayi sallama ta juya ta wuce


Yana komawa wurin Isma’eel, Isma’eel yace “soyayya ruwan zuma, waton abinci ma aka kawo maka” Sufyan yace “ka ji dashi dai” Isma’eel yayi dariya yace “abokina mu dai kawai ku sasanta mu sha biki” Sufyan bai kulashi ya bude danwaken ya wanke hannu ya fara ci


____________________________



Yasmeen ta qara kiran Ammi tana tambayar lafiya Bazla take kuwa, Ammi tace “Yasmeen ki kwantar da hankalinki tana lafiya” Yasmeen tace “to Ammi ki hadani da ita don Allah” Ammi tayi shiru ta rasa me xata cewa Yasmeen tun safe take kira, Sai can tace mata “Yasmeen na gayamiki tana lafiya, yanzu bata kusa dani” Yasmeen tace “to Ammi Ina gaidata sai da safe, zan shigo InshaAllah” Ammi tace “to sai kinzo” ta kashe wayar


Tana gama wayar ta tashi tayi sallar Isha, ta gama tayi zaune akan daddumar tana tunanin ya zata bullowa lamarin, sai taji shigowar motar Abie, bata tashi daga inda take ba har ya shigo


Ya shigo da sallama ta amsa mishi, ta tashi tana mishi sannu da zuwa, ya amsa mata, yace “da Yunwa na dawo Hajiya” tace “amma ai ka fara yin wanka ko” yace “eh to bari nayi wankan” ya shiga toilet ita kuma taje ta hada kayan abincin ta kawo masa


Ya fito ya gama shiryawa, ta kawo mishi abincin ta zuba mishi, yace “ke bazaki ci bane” tace “na qoshi” bai ce mata komai ba ya cigaba da cin abincin 


Da taga baida niyyar yin maganar Bazla, tace “wai bakace komai akan tafiyar yarinyar nan ba, nifa hankalina ya kasa natsuwa” ya dago ya kalleta yace “dama shi ya hanaki cin abincin” bata ce komai ba, ya qara kallonta yace “tunda haka ta zaba ki kyaleta mana, yanda ta fita da kanta haka zata dawo, kuma na manta ban gaya miki ba, gobe Idan Allah ya kaimu mukeso mu tsayarda ranar bikin Saboda banason a saka lokaci sosai” Ammi da tunda yake maganar take kallonshi taga hankali kwance ma yake maganar, ta zaci ya dan sakko ko maganar ya daina har Bazla ta dawo, tace “Amma kana ganin hakan shine ya dace kayiwa yarinyar nan, yarinyar da bayan ita bakada wani, yarinya daya tilo a gareka, kana ganin ka aurar da ita ga wanda bataso shine daidai, tunda ta nuna bataso baza’a kyaleta ba, ita Bazlar ma guda nawa take da har za’ace ma a dage sai tayi aure yanzu, bawai ina goyon bayanta bane, kawai inason idan ma auren ne ta auri wanda zata samu natsuwa a gidanta bawai inda zata dinga damuwa ba, na tabbatar tunda har ta iya saka qafa ta bar gidan nan to tabbasa bata son shi, yarinyar da ta fison farincikin ka akan komai wadda ko menene kakeso tana yin shi, tunda yanzu kaga taqi ai sai ayi mata uzuri” ta qarashe maganar muryarta na dan rawa


Maganganunta sun shige shi amma sai yace “yanzu dai kina nufin na watsawa Alhaji Abdullahi kasa a ido kenan, yaron shi ya nuna yanason yarinyata ni kuma naqi, to dame za’a kirani, butulu ko kuma me, amma yarinyar nan batada hujjar da zatace batason yaron nan” Ammi tace “ai ba dole sai ta wannan hanyar zaka saka mishi ba, kuma ma ita tace bawani dalili kawai dai batason shi ne” Abie yace “nidai na gama magana, bazan zama mai magana biyu ba, idan akayi auren zata fara sonshi, maganar saka rana tana nan gobe” ya fada yana wanke hannun shi, Ammi tace “ba dai zaka bar maganar auren nan ba” yace “eh, ni yanzu hutawa zanyi don na gaji sosai” bata tanka shi ta juya tana tunanin ya zatayi



______________________________



Bazla tana kwance tana tunani, Inna ta shigo tace “Khadija kinyi bacci” Bazla ta tashi tace “A’a banyi ba” Inna tace mata “Khadija mamanki tace karki dawo a bari sai ta nemi mafita” Bazla tace “to Inna badamuwa, Allah ya kawo mafita ta Alkhairi” Inna tace “Ameen, amma meyasa shi yaron baki son shi” Bazla tace “nifa Inna babu wani abu da yasa wai banason shi, kawai ni banason shi” Inna tace “to Ana qin son mutum haka kawai, in dai mutumin kirki ne kawai ki yadda Khadija tunda mahaifinki yanaso, kuma bazai zaba miki abunda zai cutar dake ba” Bazla tace “ni yanzu ai kuma sai abunda Ammi tace, amma idan na koma Abie bai haqura da maganar auren ba to ba yadda zanyi sai in aureshi” Inna tace “to Khadija Allah ya miki zabi mafi Alkhairi, idan auren yaron Alkhairi Allah ya tabbatar, Idan ba Alkhairi bane Allah ya musanya miki da mafi Alkhairi” Bazla ta amsa da Ameen. Inna ta fita ita kuma ta koma ta kwanta



___________________________



Da safe Sufyan ya tashi ya je ya gaida Abba da Umma, bayan sun gaisa Abba yace “wai kai haka zaka zauna babu aure ne” umma tace “to gane min dai, yaro gashi nan zaune babu aure” ya Sosa kansa yace “Abba lokaci ne baiyi ba, in lokaci yayi za’ayi” Abba yace “rabani da lokacin nan, kaine dai kake shashanci ba wani lokaci” Umma tace “ni yarinyar nan ma Maryam nake tunanin ko dai soyayya suke, idan ma soyayyar kuke kawai azo ayi abun nan a wuce wurin” ya dago ya kalli Umma yace “nifa babu komai tsakaninmu mutunchi ne kawai” Umma tace “indai tayi wari ma jii” yace “zan tafi wurin aiki, sai na dawo” suka mishi Addu’a ya amsa, yace “ba abunda ake buqata” Umma tace “ba abunda ake buqata” yace “to” ya tashi ya fita


Ya dauki flask din da ta saka mishi danwake ya fita da shi don ya biya ya bata, yana zuwa qofar gidansu ba kowa yana tunanin ya zai bata sai ga wani yaro, ya kirashi yace yaje ciki yace Ana kiran Maryam, yaron yaje ciki ya dawo yace ance tana zuwa, yacewa yaron ya gode 


Yana tsaye sai gata ta fito, tace “wai dama kaine, meyasa baka kirani a waya ba” yace “ba gaisuwa sai tambaya” tace “laaa yi haquri ina kwana” yace “riqe gaisuwarki” ya miqa mata flask din, ta karba, yace “nagode sosai” tace “meye na godiyar” suna magana sai ga babanta ya dawo, Sufyan ya duqa har qasa ya gaisheshi, ya amsa fuska a sake, yace “ya Mallam da mamanka” yace “duk suna lafiya” yace “to agaidasu” ya wuce ciki


Yana shiga ciki Sufyan yace “to koma ciki, ni zan tafi aiki” tace “Allah ya tsare ka ya kareka ya kuma baka sa’a” yaji dadin Addu’ar ya amsa da Ameen ya wuce


______________________________



Yasmeen ta tashi tunda safe ta shirya ta fito parlor, parlor ne wanda ya amsa sunan sa, qawataccen parlor mai girma, ga kujeru na Alfarma, set uku ne na kujeru a parlorn, ga wata faskaceciyar tv, ga kuma dining area wanda yasha kwalliya, kyan parlorn kyau ne mai daukar hankali, wanda da ganinshi kasan dukiya tayi kuka a wurin


Mamie ta samu zaune tana kallon Africa tv, ta qaraso kusada ita tace “Mamie ina kwana” Mamie ta dago kanta, wata matace da Aqalla zatayi shekaru 40 zuwa 43, wadda hutu ya boye shekarunta, baza’a kirata da baqa ba kuma baza’a kirata da fara ba, fatar jikinta ta nuna tsantsar hutu da Jindadi, ta kalleta tace “lafiya lau Yasmeen, ya na ganki cikin shiri haka, ina ce baku koma school ba” tace “eyh mamie dama zanje gidansu Bazla ne” Mamie tace “Bazla kuma kwatakwata yaushe kuka rabu kamar baifi kwana biyu ba” tace “eyh Mamie ina kiranta ne wayarta bata dauka kuma na kira Ammi yadda naji muryarta nasan ba lafiya” Mamie tace “ai ko zuwan zakiyi ki bari Rana ta fito ko, ki bari kuma sai kinci abinci” tace “don Allah ki bari inje yanzu, hankalina ba’a kwance yake ba” Mamie tace “yanzu fa Qarfe bakwai da rabi Yasmeen ko su basu tashi bacci ba, banason gardama ki bari sai anjima” Yasmeen tace “to Mamie na bari” Mamie tace “kuma kin san yau babanku zai dawo ko, idan ma kinje karki dade” Yasmeen tace “kinsan mamie tsabar bana cikin natsuwa na manta yau zai dawo” ta fada tana murmushin dake nuna Jin dadin ganin babanta, Mamie tace “lallai ko zan gaya mishi kin manta da dawowarshi” Yasmeen tace “ai yasan bazan taba manta dawowarshi ba, kusan 3months ban saka shi a ido na ba” Mamie tace “shi junior ma yace ko makarantar bazaije ba, nayi nayi yace ba inda zaije” Yasmeen tayi dariya tace “junior hukuma” suna hira inda masu aiki sun gama komai na breakfast, suka tashi sukaje dining area domin suyi breakfast, Mamie tace “Nasiba kije ki tada Junior yazo yayi breakfast” wadda aka kira da Nasiba wadda ta kasance daya dga cikin ‘yan aikin tace “toh Hajiya” taje ta tada shi yayi brush ya fito, yarone da bazai wuce shekaru 13 ba, ya samesu suna cin abinci, ya gaida Mamie Sannan ya gaida Yasmeen, suka amsa mishi, shima ya zuba nashi ya fara ci



_____________________________



Sufyan yana zuwa aiki ya tadda Isma’eel sai wasar baki yake, inda yake tsakiyar ’yan wurin aikin nasu, suna kiran Ango Ango shi kuma sai dariya yake, Sufyan ya qaraso yana dariya yace “wa ake kira da Ango kuma”, wani da ake kira liti yace “kar kace baka san an saka ranar auren Isma’eel ba” da mamaki Sufyan yake kallon Isma’eel don ko da wasa bai gaya mishi ba, Isma’eel yace “kai liti ina ruwanka ai suprise nake so nayi mishi” Sufyan yace “a’a duniya ba suprise ba” Isma’eel yace “haba abokina zo kaji” yaja hannun Sufyan sukaje inda suka saba zama, yace “abokina wallahi suprise nakeso na maka, jiya da na koma gida ne ake sanar mun an saka ranar, amma kayi haquri” Sufyan yace “bakomai, Allah ya sanya Alkhairi, yaushe ne bikin” yace “nan da wata biyu” Sufyan yace “lallai munada biki, muzo mu fara shiri” Isma’eel yace “kaima abokina ka motsa ku sasanta da Maryam ayi abun nan” Sufyan yace “ni nace maka soyayya muke da yarinyar nan, haka dazu Umma tamun maganar” Isma’eel yace “to in kai baka sonta ita dai alamu sun nuna tana sonka” Sufyan yace “ni ka rabani da shirme, girmamawace kawai da mutunchi amma bakomai” Isma’eel yace “to shikenan” suka cigaba da abunda sukeyi 



_____________________________



Maryam tana shiga gida babanta yace “wai Maryam menene alaqarki da yaron nan” Mamanta tace “Nima dai nace ko dai akwai wani abu a qasa” Maryam tayi shiru kanta a qasa batace komai ba, Babanta yayi murmushi yace “tashi kije” ta tashi ta koma daki 


Mallam yace “koma minene idan akwai abu ai zamuji” Mama tace “Ai kuwa Mallam, Allah yasa muji Alkhairi” ya amsa da Ameen


Maryam tunda ta koma daki take tunanin ina ma abunda ake zaton ya zama gaskiya, ita kawai tasan irin son da take mishi


________________________



Sufyan yana fita babanshi yace “nifa gani nake shida Maryam akwai wani abu amma Kinsan shi da shegen zurfin ciki idan aka biyeshi b bayyanawa zaiyi ba” Umma tace “Nima haka na gani Mallam” yace “ki barni dashi bari ya dawo”


_____________________________


Yasmeen 11 nayi tayiwa Mamie sallama ta dauki mukullin motar ta ta kama hanyar gidansu Bazla, tana isa mai gadi ya bude mata ta shiga, ta samu Ammi zaune tana breakfast a parlor, kulu kuma tana ‘yan goge gogenta suka gaisa Ammi tace “Yasmeen zo kici abinci” Yasmeen tace “na qoshi Ammi” nan sukayi shiru har Ammi ta gama, Yasmeen tace “Ammi ina Bazla din banji ko motsinta ba, ko tana dakinta” Ammi tace “Yasmeen Bazla bata nan” Yasmeen tace “Ammi bata nan tana ina” Ammi tace “muje dakina” ta tashi ta bita dakin


Nan Ammi ta gaya mata komai bata boye mata ba saboda hankalinta ya kwanta, ta kuma gaya mata babanta bai sani ba, sai a lokacin Yasmeen ta samu natsuwa 


Tace Ammi ta bata number Inna tayi magana da Bazla din, Ammi ta number, tayi godiya ta tashi ta koma gida


__________________________


Sufyan ya dawo gida, umma ta kawo mishi abinci, yana gama ci tace “Kaje Mallam yana kiranka” Yace to ya tashi ya tafi, yana zuwa da sallama dauke a bakinshi ya shiga dakin, Abba ya amsa, yace “zo ka zauna” Sufyan ya zauna, Abba yace “dalilin kiran shine, na fuskanci wani abu akan ka da Maryam” Sufyan da sai da gabashi ya fadi ya dago ya kalli Abba, Abba ya cigaba da cewa “ni zan muku wani gata kai da ita, zanje na nemo maka aurenta” rasssss gabanshi ya qara faduwa 


______________________