59
💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔
( shi ya san gidan mai rowa)
```By```
``` NAFISAT ALIYU SASAAL```
```Page 59```
________Zafi-zafi kaɗan-kaɗan da ta faraji ne yasa ta buɗe idanuwanta acikin nashi jajayen idanuwan, hawaye masu sanyi na cigaba da biyowa kuncinta. A hankali yasaketa yana ƙara mayar da ita cikin jikinshi,saboda sauyin dayakeji a zuciya da ma gangar jikinshi gaba ɗaya.
"Halimahhhta kinyi ƙewana? Ki yafemin kinji,bazan ƙara ba,zaki rayu da Maysarahnki har gaban abadan,babu wanda zai ƙara taɓaminke" ya faɗa a cikin kunnenta,da hausarshi mai daɗin gaske.
Shiru tayi don kalamai irin waɗannan abakin Maza irin su Maysarah abin so ne ga kowacce ƴa mace don baya magana biyu,ba shi da ra'ayin yin ƙarya ko yaudara,komai nashi daga zuciyarshi yake.
Dumi da sanyin zuciyar da Halima ta samu ne,yasa barci ya kwasheta.
Sauyin nauyinta dayaji a jikinshi ne yabashi tabbacin haka.
Gaba ɗayanta ya ɗauketa zuwa Bedroom ɗin shi,yafi minti goma yana kallon fuskar data ragemai amatsayin farin cikin shi.
Daƙin ya bari gaba ɗaya zuwa wani daban,shima barcin daya kwana biyu baiyiba ne ya ɗaukeshi.
Har ya farka yaƙarayin wanka Halima na barci,kulleta yayi ya nufi wajen Naseer don bayason yazo inda yake.
Gidane dayafi wanda Maysarah yake ciki girma da kayan more rayuwa,motar daya ɗauko Halima dashi na gefen ɗaya da wasu ragowan motocin.
Bai ƙarasa ciki ba yakirashi. Shima ya sauya kayan jikinshi zuwa guntaye na shan iska. Magana sukayi na mintuna kaɗan bayan yayi signing ɗin wasu peppers,har Maysarah ya juya Naseer yake tambayarshi lafiyarta.
"Wa kenan"
"Halimah"
Still fuskarshi bai sauya ba kamar yanda shima na Naseer ɗin yake a kame,yace tana lafiya,sannan ya shige mota sukabar gidan.
Har ya dawo bata tashi ba,don haka ya dawo zaman jiranta yana rage aiki a system ɗinshi.
Da wani irin yunwa ta farka,Abayar jikinta ta fara cirewa ta shiga wanka. Cikin doguwar riga wanda bai ƙarasa ƙasa ba ta shirya orage color Free size,kanta ba ɗan kwali, haka ta fito Parlon komai na dawowa cikin kanta,kunyar kanta na kamata da kuma kasa yarda da abinda taji kamar Maysarah yana faɗa.
Batayi tunanin gininshi ba don haka kai tsaye cikin tafiyarta da sangatar ya huda takebin ko ina na Parlon da kallo har idonta ya sauka a kanshi.
Kallonta yake yi da iya ganinshi,da kai yayi mata alamar ta zo.
A hankali ta zauna a gefenshi tanayin ƙasa da kanta,wanda hakan ya bashi daman ganin kwantaccen yalwataccen sumar kanta mai laushi da tsaho ga shi baƙiƙirin,bai taɓa ganinta a haka ba sai ranar don haka ya kasa jurewa ya janyota jikinshi gaba ɗaya,yana shafa sumar haɗe da subbatar ta a goshi.
Marairace fuska tayi tana kallon bakinshi.
"Kinaso ki subbaceni,bakina na burgeki ko" ya faɗa yana ɓoye dariyarshi.
Komawa jikinshi tayi tana sakin ƙaramin dariyar daya haɗe da kukan da babu hawaye.
"Nifa ba shi nakeso ba,yunwa nakeji" ta faɗa da iya gaskiyar abinda yake ranta.
Naseer yaƙara kira yagayamai abinda yakeso.
Bai bata daman barin jikinshi ba yacigaba da aikinshi.
Ƙaramin kukan wunya da taƙi dainawane yasa ya ajjiye aikin gaba ɗaya ya miƙe da kanshi. Yana fita suka haɗu da Naseer.
Kwanciya tayi saboda sosai takejin yunwa.
Abinci ma ajikinshi yazaunar da ita tana ci yana kallonta.
"Ka bari na zauna karna ɓatama jikinka" ta faɗa a hankali itama tana kallon shi lokacin da ketchup ya ɗisar mishi a wando
"Jikina kayana duk naki ne,kinji Halimahhhta" ɓata fuska tayi tana kallon bakin dayake maganar da shi.
"Baki tambayeni naci abinci ba".
" I'm sorry" ta faɗa tana kai ragowar abinda take ci bakinshi,ga mamakinta sai taga ya karɓa yana lumshe idanuwanshi.
A haka suka cinye dukka abincin da Naseer ya siyo.
Tashi tayi ta koma ɗaki tana sakin ɓoyayyen ajiyar zuciya,wani irin farin ciki na mamaye zuciyar ta,wai dama haka masoya suke jin daɗi dayawa,ta tambayi kanta dariya na kamata.
Da daddare bayan tayi wanka ta shirya cikin Pyjamas tayi kwanciyarta ba tare da taƙara neman shi ba.
Har barci ya fara ɗaukarta taji shigowar shi,bata motsaba don batayi tunanin kwanciya yazo yi ba,sai da ta taga ya zauna a bakin gadon yana kashe wayoyinshi.
A zabure ta miƙe tana turo baki da magana ƙasa-ƙasa wanda ita kaɗai tasan me take faɗa.
A bazata ya komata gaba ɗayanta zuwa jikinshi,ya fara subbatar cikin sanyi da soyayyar dayake mata.
Bayan wasu mintuna yasaketa ya gyara mata kwanciya a jikinshi,duk da ƙananan koke-koken da takeyi tana tureshi.
"Bazan miki komai ba Halimata,kiyi barci kinji" ya faɗa yana shafa kwantaccen sumar kanta.
Kai ta ɗagamai. Barci mai daɗi da nutsuwa ne ya ɗauke kowannen su.
★washe gari ma a jikinshi tayi Breakfast tana sane duk ta ɓatamai kaya duk don ya ƙyaleta,tana zama ita ɗaya,amma da lokacin lunch yayi haka ya ƙara yayimata, na dare sai yafi na ko yaushe takura agareta don sai bayan ta gama ci yasata tabashi wanda ta rage.
Miƙa tafariyi alamun tanajin barci,amma bai bata damar miƙewa ba harta fara a inda take,sai da yagama komai sannan ya kaita ɗaki, wannan karon kasayiwa kanshi iyaka yayi da jikinta,a shekaru ne Halima take yarinya amma ajiki bata da banbanci da budurwa ƴar shekara ashirin. Sama-sama takejin abinda yake mata kafin ta dawo hayyacinta baki ɗaya, bakinta har zafi yake mata. Kuka tasamishi tana tureshi,dole ya haƙura ya mayar da ita jikinshi,saboda girman abinda yakeji.
Ko da ta farka bata ganshi a ɗakin ba.
Iyalin Naseer wanda take baƙar fata ƴar asalin ƙabilar kalaba ce ta kawowa Halimah abin kari,bayan sun ɗan taɓa hira tayimata sallama.
Har ta gama bata ganshi ba,bata kuma nemishi ba.
Da dare yayi maid ɗin gidan Naseer ce ta kowa mata Dinner.
Har ta gama bataga Maysarah ba, hankalinta ne ya fara tashi,to ko ta kunna wayanta batasan Number shi ba.
Bedroom ɗin gidan tafara bi tana dubawa ana ƙarshen taji alamun mutum yana wanka.
Zama tayi abakin gadon tana ƙarewa ɗakin kallo.
Tanaji ya buɗe ƙofa tamiƙe a hanzarce,kafin ya samu damar cewa ta fita tayimishi allurar daya hanashi magana ta hanyar shigewa lafiyayyen jikinshi da babu kaya sai towel dake ɗaure a ƙugunshi.
Kuka tasaimai tana ƙara ƙanƙanmeshi,da mitar shine ya gudu yabarta.
A haka ya zauna a bakin gadon still tana manne da shi. "Halimah"
Ya faɗa yana ɗago kanta.
"Kinsan me ma'aurata sukeyi" kai ta ɗagamai alamar ta sani.
"To maiyasa kike guduna,kina kuka?"
Ya faɗa yana kallonta da jajayen idanuwanshi,da sha'awar son kasancewa da ita ya mai da su haka.
"Saboda kayi babba dayawa,kabari idan ka dawo ɗan ƙarami" ta faɗa da iya gaskiyarta.
Murmushi mai sauti yasaki yana shafa gashin kanta.
"Bazan taɓa dawowa ƙarami ba Halimah,sai dai idan ciwo nayi,kinaso nayi ciwo?"
"Uhm uhm"
"Ko na samo wata Matar"
"Uhm uhm"
"To yakikeso muyi Halimah?"
Shiru tayi tana ƙara narkemishi.
"Kije kiyi barci,nizan kwanta anan"
"Uhm uhm nima anan zan kwanta"
Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke,saboda abinda yake ƙoƙarin dannewa na neman rinjayar Tausayinta a ranshi.
"Naji zaki kwana anan tashi kije kiyi wanka sai ki dawo"
Bata musamai ba ta miƙe yana binta da kallo harta ɓacewa ganinshi.
A gurguje tayi wanka ta shirya cikin kayan barci masu santsi da taushi.
Sai dai tana zuwa ta samu daƙin a kulle bugun duniya yaƙi buɗe mata. Kuka mai ƙarfi ta fasa wanda dole yasashi tasowa ya buɗe ƙofan.
Ba kaya a jikinshi sai ɗan ƙaramin wando,dasauri ta juyamai baya tana rufe fuskarta.
" menene matsalan Halimah"
"Barci nakeji" ta faɗa tana ɓata Fuskarta.
Matsa mata yayi ta wuce tanayin gaba ya rungumeta ta baya.
" Kinaso ki kashe ni ko Halimah"
"Uhm uhm"
"Kidaina yin kuka kullum kinji" kai ta ɗagamai alamar to.
Tasaki jikinta dashi yanda yakeso,sukayi barcin su mai daɗi.
★Da safe ya shirya cikin Suit Dark blue daya ƙara fito da kwarjinin shi da asalin kyawunshi da kuɗi yaƙara tasirantar da shi sama da na baya. Yana da important meeting da client wanda dole sai yaje.
Kamar zata shiɗe haka take kukan ya tafi da ita, Breakfast ma daƙyar tayi. Duk abinda zai damu Halima abune mai girma a zuciyar Maysarah,daƙyar ta yarda zata zauna bayan faman dayasha.
Har ya zauna a mota Fuskarta na maƙale a idanuwanshi,fitar gaba ɗaya sai ya fice mai akai.
Maysarah yayi ɓatan kiran sunan Halimata a taron yafi sau uku.sai ya faɗa sai ya sosa goshin shi, Naseer dariyarshi ya maƙale yana ƙara jinjinawa soyayya mai mayar babba yaro ƙarami, banda haka yasan babu wani abu da zai canza Maysarah ko susuta shi,to wannan idan ta daɗe dashi kowa sai sunanshi ya dawo Halimata.😄
Bayan sun gama kai tsaye layinta ya kira,yanajin kamar yayi shekara bai ji muryarta ba.
Bugu biyu ta ɗaga.
"Halimahhhta"
"Uhm" ta faɗa a hankali.
"Ya lafiyanki,kin daina kuka,kinyi lunch?"
"Uhm uhm"
"To maiyasa banace kiyi haƙuri ba?"
"Uhm uhm bana son haƙuri,fuskarka nakeso ka dawo nagani kaji"
"Ya Salam" ya faɗa a hankali yana lumshe idanuwanshi saboda wani irin soyayyarta dake bijiromai ta ko ina......✍🏻
😄😄😄😄😄 Barkan mu da dare