GAMON JINI

Page 6

by @gureenjoh

⚡️*GAMON JINI*⚡️


   *NA FATIMA MOH'D GURIN*

        *GUREENJO*


*E.W.F*


*PAID BOOK*


*FREE PAGE SIX*


*TAURARI BIYU⭐️⭐️ DAGA TASKAR MARUBUTA BIYU✍️✍️*


*****


A sadda ya taka wawan birki a kofar gidan be jira gate man ya bud'e gate d'in ba ya sauka ya tura karamar kofar ya shiga cikin hanzari kaman an koroshi, cikin zafin nama ya tura kofar parlorn wani wawan ajiyar zuciya ya sauke ganinta zaune kan kujera khalid duke a gabanta hannunshi da ruwa me rangwamen sanyi yana bata, gefenta ya karasa ya zauna yana kallonta har lokacin kirjinshi be dena bugawa da sauri sauri ba.


Mikawa khalid tayi cup d'in ruwan a sanyaye take kallon Abrar d'in ta san baze iya magana ba sbd da gaske ya tsorata bata ta'ba ganin abinda ke tsorata Lamidon ta ba irin ace bata da lafiya, hannunshi ta rike tace 

"Karka d'aga hankalinka ba wani Abu bane... ya Amatullah?"

Ganin yana so yayi magana kaman ya kasa yasa ta sake kar'ban cup da ruwa dake hannun khalid yana kallonsu ta tsiyaya ta bashi ya sha.


Shiru na mintuna kan yace

"Amah me ya sameki?"

Tace

"Ba komai lamido kawai jiri naji ina fitowa daga sashen Hajiya Babba, ya Amatullah d'in hope da sauki?"

Ya san ta fad'a ne kawai sede akwai abinda ya faru d'in ze yi magana Abbu ya shigo sashen wadda ya sa khalid mikewa, idanunshi a kansu ya karaso fuskanshi har lokacin ba walwala...


Khalid mikewa yayi ya fice ranshi a 'bace tsohuwar nan tana bukatar a taka mata birki babu me iya aikata hakan se Yayansu amma ya rasa me yasa ya ke kau da kai akansu daga ita har Hajiya Yaya dukda ya san tsawatawa babba baya daga cikin tarbiyarsu, motar shi ya shige ko side d'inshi be koma ba ya kira matarshi a waya ta fito suka tafi asibiti wurin Amatullah...


A parlor kuwa Da ido Amah tabi Abbu har ya zauna kanshi a kasa zatayi magana yace

"Kiyi hakuri... ki kara a kan wadda kike."


Abrar da ya runtse idanunshi ne ya mike yana shirin fita Abbu ya kirashi ya dawo ya zauna, yana jin yadda Abbun ke kara bata hakuri, itama hakuri ta bashi ta nuna mishi ai Hajiya Babba itama a matsayin mahaifiya take wurinta duk abinda tayi daidai ne, yaji daad'i sossai nan ya sanar mata ya samu ya shawo kanta ta amince, tattaunawa sukayi sossai kan Amatullah wadda su biyun ke maganganun shi be saka baki ba yana de jinsu. 


Bayan sun gama yace da dare da kanshi za shi ya dubata, a nan ma seda suka yiwa yaron nasu fad'a akan aure, kanshi dae kasa yana sauraronsu, shi fa be ce ze yi aure ba gani yake kaman masu uzzurawa iyayen nashi har su ta'azzareshi zasu yi su gaji...


Har bayan kwana biyu baya cikin walwala a gidan sbd maganan auren da suke matsa mishi yau yana Neman cika sati biyu hutun da ya d'auka, kuma a jibi yake son tafiya, yana tunanin ta yadda ze tafi ya bar Amatullah a situation d'in da take ciki, bata ta'ba yarda hindu, ruqayya ko Aisha su taimaka mata tayi wanka in ba yana zaune d'akin ba abinci kuwa se in shine ze bata da kanshi, dukda yanzu baya wani yi mata magana don akwai randa ta so tada mishi fitina ya tsawatar mata har ta samu attack hakan ya sa ya ma rage d'an saukin hali da yake nuna mata, ita kuwa kaman me tsoronshi kaman kuwa shi kad'ai ta yarda dashi a duniya har gwara Amah ta kan yarda da ita, a sati biyun kyaunta ya kara fitowa da hasken fatarta sbd gyara da kulan da take samu...


Sau d'aya Hajiya Yaya da yaranta tare da Nadra suka zo abin be yi daad'i ba sossai suka sake tsoratata wadda dalilin da ya sa ma kenan har lokacin ba'a sallameta ba, Aunty da ba ruwanta bata shiga harkar Amah idan aka cire gaisuwa sannan bata zagi ko ya'ba mata habaice habaice irin na hajiya yaya dukda itama 'ya'yanta duka mata ne sau biyu tana zuwa duba Amatullah haka matan daddy ma su biyu sun zo sun dubata matar Uncle maraq da bata nan ne kawai bata je ba se hajiya Babba..


Zaune yake a d'akin yana sarrafa wayan hannunshi sanye yake da three quarter brown da t-shirt baka da tayi mugun fito da farar fatarshi, Amatullah na zaune tsakiyar gado ta buga tagumi tare da kurawa wuri guda ido, lokaci lokaci ta kan kalleshi sede ko sau d'aya be yi kuskuren kallonta ba harkar gabanshi kawai yake, ba don hindu bata dawo ba har yanzu da ya tafi, duba time yayi a tsadaddiyar agogon fatar dake hannunshi, Goma saura...


Iska me karfi da ya fara d'age labulayen d'akin ne ya sakashi mikewa ya taka ya isa ga labulen ya d'age, iskar ruwa ne sossai ya tashi ajiyar zuciya ya sauke tare da d'an kallonta yadda ta zazzaro ido ya so bashi mamaki sede tuno tana tsoron ruwa yasa ya ta'be baki ya koma kujeran ya zauna, sede me kaman jira, mararshi yayi wani mummnar murd'ewa da ya sa shi ba shiri ya runtse ido yana chabke lip d'inshi na kasa.


What? Ba de ciwon mararshi ba ya ayyana hakan ba tare da ya bud'e idanu ba, sunayen Allah ya fara ambata a hankali d'aya bayan d'aya a daidai lokacin da aka barke da ruwa me tsananin karfi had'a da tsawa wutar asibitin ya d'auke, wani irin kara da ta sake seda ya tsorata duk dakiyar zuciyarshi cikin wani irin karfin hali ya mike sbd kaman ya fara ganin bibbiyu bibbiyu ita kuwa a gigice sbd duhu da walkiya da tsawar da ake yasa ta gigice ta fara kokarin nufan inda yake...


Tana rike hannunshi ba wata wata ta fad'a jikinshi tare da rukunkumeshi, kaman yadda jikinta ke rawa haka shima jikinshi ya d'auki wani irin rawa, gabad'aya ta gigitashi ta gigita kanta. 


Cikin wani irin murya yace

"Amatullah..! Please calm down, ki natsu nothing will happen to you as long as I'm with you in shaa Allah... sakeni bari in kunna torch"


Yadda yake magana a rarrabe yasa ta sakeshi tana kuma rike hannunshi a rud'e tace

"Yayanmu baka da lafiya ne? Me ke damunka all of a sudden?"

So yake ya daka mata tsawa ko zata sake shi ya samu natsuwa sede zuciyarshi ta kasa aikata hakan.


Yana shirin magana aka dawo da wuta haske ya gauraye d'akin dukda irin Ruwan dake zuba da iska da ake be hana gumi tsatsafo mishi ba idanunshi sun rine sun chanza gabad'aya.... ai se ta gigice tana tuna Sameer.


"Yayanmu sannu ka zauna bari in kira maka likita ya dubaka, Dan Allah karka mutu ka barni kaman yadda sameer ya mutu da ciwon ciki ya barni...."

Gabad'aya ta rikice se kuka take yi, tana rike dashi har ya zauna ya kuma runtse ido yana shirin fita hayyacinshi, se ta nemi sakeshi ta fita...


Riko hannunta yayi a tare suka kallo hannun se suka kalli juna, kau da idanunshi yayi tare da saketa yace da kyar..

"Just stay still, I will be fine"


Sannu take ta jera mishi hawaye na zuba mata ganin kaman da gaske yake Shan wahala sun fi mintuna ashirin a haka ko sau d'aya hawayenta be dena zuba ba kaman yadda bakinta be yi shiru da mishi sannu ba haka idanunta basu iya kaucewa daga gareshi ba.


Chan yace 

"Bani ruwa"

Da sauri ta d'auko ta bashi bottle water ne da ya d'aga be sauke ba seda ya shanye tas, wani wawan ajiyar zuciya yake saukewa a jere a jere, he have to take his pills gashi....


Be gama tunanin ba aka turo kofa, Khalid ne da hindu tare da Uncle murtala. 


"Sorry yayanmu hold up ne yayi mugun 'bata mana lokaci bamu zo da wuri ba"


Ba tare da ya ce komai ko ya kalli kowa a cikin su ba ya nufi kofa yana cewa

"Maraq take me home I can't drive"


Da sauri maraq ya bishi ganin yadda yake tafiya sauri sauri, Khalid yace

"He looks sick ko me ya sameshi oho"


Yayi maganan yana kallon Amatu sanin ba amsa shi zatayi ba yasa ya juya ya fita, gado ta koma ta zauna tana takurewa a hankali kuka ya kwace mata tunanin halin da yake ciki zuwa yanzu ya addabi kwakwalwanta a lokaci d'aya da tunanin Sameer, masoyi na hakika a gareta sede Allah da ya fita sonshi ya d'auke shi bata tunani akwai wadda zata so a duniya irin Sameer, kukanta ne ya karu had'e da rawar jiki sbd Ruwan da ake tsugawa...


A haka ta kwana cikin rashin natsuwa da damuwa, da safe aka kaita office d'in likitan kwakwalwa da yake mata physiotherapy, doctorn ya mugun sanin kan aikinshi hakan ya sa har ta fara sakewa dashi dukda ba maganan take mishi kaman yadda yake so ba, suna shigowa da hindu yace


"A'a Amatullah baiwar Allah I hope dae kina cikin koshin lafiya?"

Gyad'a kai kawai tayi sbd zuciyarta sam ba daad'i tunanin halin da ya kwana ciki ya hanata sukuni as her saviour he owns her more than life it self, da kyar ta iya cewa

"Ina kwana"


Ya amsa tare da mata bayanin yau fita zasu yi su tattaka, umarni ya bawa hindu ta koma in sun dawo ze rakota har d'aki, fita sukayi ward ward suna tafiya yana janta da hira me kama da nasiha, yana nuna mata duk abinda ze chunkushe kwakwalwarta da zuciyarta ya hanata sukuni da zaman lafiya be kai ga lafiyan jikinta ba, ta kasance me Godiya ga Allah se ya nuna mata hanya mafi 'bullewa, tana ganin wasu numfashin da zasu shaka se sun saya, kafar yawo se an saka na roba ko na karfe, wani na struggling tsakanin mutuwa da rayuwa...


Ga su nan dae birjik me yasa bazata hakura ta taimaki kanta ko zata samu lafiya na jiki da jini? Me ze sa ba zatayi open up damuwarta su magantu ba yadda zata ji saukin abin... a fakaice cike da tsantsar ilimi ya nuna mata baze iya taimakonta ba in har bata taimaki kanta ba..


Sun dawo office d'inshi ya bud'e wani abu dake reading kaman system yana shigar da record da bata fahimta kaman daga sama yaji tace

"Na rasa dalilin da yake sa nake ganin hakan"

Da sauri ya kalleta yana jin daad'in yau ta bud'e baki kai ya gyad'a yace 

"Uhm me kike gani? Menene shi abinda kike ji?"

"Seeing many things even when it's not present"


Kallonta yake da kyau dukda turancinta akwai kusakurai sede yayi mamakin yadda ya jishi a bakinta ita karan kanta a duk sadda tayi turanci se ta tuna Sameer d'inta daga zuwa bautar kasa kauyensu ya zama wani sashe na rayuwarta da jikinta daga karshe ya tafi ya barta me yasa ne bata da sa'a duk wadda yake a rayuwarta ya tafi sun barta ita kad'ai cikin wata sabuwar duniyar da bata gane karatunshi bare tayi bita, Najma, Yaya Munir, Ummah, Baba malam duk babu kowa bata san kuma halin da suke ciki ba...


Hawayenta ne suka zubo, se lokacin dr yace

"Ko zaki iya bani misali?"

"Bazaka ta'ba ganewa ba likita... Just leave me.."

Katseta yayi

"Tabbas zan gane idan har kika min bayani, I told you before therapy is not me giving you a solution, it is a process of finding the cause through conversations... you really have to help your self Amatullah"


Kuka ta fashe dashi ganin tana Neman birkicewa se kawai ya lalla'bata suka koma d'akinta se kuma wani sati ze sake ganinta, ko da suka koma ta sa ganinshi a ranta sede ko alamunshi babu, hindu ce da Amah da yanzu zuwanta ita da Maher a d'akin, a sanyaye ta gaida Amah ta amsa tana tambayarta jikinta da kyar ta iya amsawa ta karasa gado ta zauna, Abinci ta d'ibo mata da kanta ta lalla'bata bata ci na kirki ba ta ki kar'ba, duk yadda Amah ta so ta kara taki dama ta ci ne ma sbd tana mugun jin nauyin Amah d'in...


Motsin kofa taji zatayi sauri ta kalli kofan ko shine sede har bayan azahar babu shi ba alamunshi, takurewa tayi tare da tura kanta tsakankanin kafafunta, hindu da ta koma gida tayi abincin rana ta dawo kan Amah ta tafi ne take ta mata labari da tatsuniyoyi sede bata ma jinta bare ta fahimta se hawaye ke zarya akan kyakyawar fuskanta...


Tafiya yake cikin sauri yana duba time a Rolex dake d'aure tsintsiyar hannunshi bakinshi be dena ambaton Allah ba kaman yadda d'abi'arshi yake a ko da wani lokaci, kananun kaya ne a jikinshi jeans da shirt da ya kamashi ya fito da duk wani kirar karfi da Allah yayi mishi, Sam be kula da tahowarta ba se ji yayi ta bugeshi da karfi.


"Subhanallah..." a zafafe ya d'ago cike da 'bacin rai ya....



****


*Ko kin shirya mallakar Wad'annan TAURARI Guda biyu😉 Da Naira Dari biyar kachal zaki mallaki gawurtattun littatafan nan guda biyu...


*GAMON JINI Na Fatima Muhammad Gureen (Gureenjo)*


*Da Kuma*


*SABABI Na Amina Ibrahim (Oum Ameer)*


*Akan Naira D'ari uku kuma zaki mallaki Guda d'aya cikin biyun, karku manta mun shirya tsab domin Nishad'antar daku, fad'akar daku da kuma Nishad'antar da ku masoya, Mallaki naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali er uwa👌*


Zaku iya biya ta account number kamar haka

3118518476

First bank

Fatima Muhammad Gurin

  Se a turo shedar biya ta wannan layin

***

Note: Banda Recharge card. 




          🖤Gureenjoh🖤