Page 7
by @gureenjoh
⚡️*GAMON JINI*⚡️
*NA FATIMA MOH'D GURIN*
*GUREENJO*
*E.W.F*
*PAID BOOK*
*FREE PAGE SEVEN*
*TAURARI BIYU⭐️⭐️ DAGA TASKAR MARUBUTA BIYU✍️✍️*
*****
Fasa fad'ar abinda yake son fad'a yayi tare da kallon inda ta rike a hannunshi tsab ya gane wani abin ta shafa mishi, tsiririn tsakin takaici ya ja tare da kallonta.
Wata arniyar armless half straight gown ce jikinta brown ya kamata sossai se pencil wando coffee shima ya mugun kamata ko d'an kwali babu attachment na lilo be san ya saki murmushin takaici ba se gani yayi ta murmusa cike da yanga tace
"Yaya ni kake ta sharewa ba?"
Wara lumsassun idanunshi yayi yace
"Mene? Ba de kin d'auka asirin da kika Shafa min yanzu ya ci ni ba?"
Zaro ido ta fara ya kuma yin wani murmushin takaicin yace
"Idan kina tunanin ni Muhammad Abrar zan so ki a haka to kiyi maza ki mutsini kanki ki farka tabbas mafarki ne... dubeki"
Ya nunata yana kyabe baki kaman yaga kashi yace
"Ina me gargad'inki ki kiyaye irin shigar nan cikin gidan nan, ki ringa tuna muna kallon gabas ba gidan kafirai bane"
A tarihi yau ne rana na farko da Abrar yayi mata dogon magana dukda bakaken maganganu ne amma... tunaninta ne ya katse ganin ze wuce tayi saurin cewa
"Dan Allah Abrar ka aureni ka riga ka yiwa zuciyata illa kar ka bari na mutu da sanka"
Juyowa yayi ya d'age gira yace
"Au haba? Allah ko?"
Cikin sigar rainin hankali daga haka yayi gaba abinshi ihu ta tsala tare da zubewa wurin.
Driving yake yana tuna irin rud'ewar da tayi jiya ganin be da lafiya har ga Allah tausayinta yayi mugun samun wuri a ranshi, wace irin rayuwa ta fuskanta? Me ya faru da ita har ya gigitata rayuwarta haka?
"Yayanmu sannu ka zauna bari in kira maka likita ya dubaka, Dan Allah karka mutu ka barni kaman yadda sameer ya mutu da ciwon ciki ya barni...."
Kalamanta suka fad'o mai, waye Sameer? Ya tambayi kanshi, tsiririn tsaki yaja tare da mika hannu ya kara sautin qira'ar dake tashi a motar, yana isa asibitin yayi office d'in Dr Alpha suka tattauna dukda Drn ya bari da dogon jawabi ya de tabbatar mishi karshen satin za'a sallameta ciwo ne ke shiga lokaci d'aya lafiya se a hankali, daga nan ya wuce wurin therapist d'inta shima ya mishi bayanin d'an improvement da aka samu.
Ta kofar d'akin ya bi ya wuce ba tare da ya shiga ba seda ya tsaya yayi clearing komai na kud'i har zuwa ranar sallamanta kan ya bar asibitin.
Washegari kuwa yayi komawarshi bakin aikinshi.
Zaune take a kasa ta had'a kai da gwiwa duk ta damu sede bazata iya yiwa kowa magananshi ba, yau kwana biyar kenan bata ganshi ba, Allah kad'ai ya san me ya hanashi zuwa gareta.
Turo kofar da akayi ne yasa ta d'ago a hankali Amah ce da khalid, a sanyaye ta gaida su suka amsa cikin kulawa Amah tace
"Alhamdulillah yau kam an sallamemu zamu huta jegelan asibiti, Tashi Amatullah mu tafi"
Hindatu da ta gama had'a musu komai nasu ne ta d'auka Khalid ya di'bi wasu yayinda Amah ta rike hannunta suka fito zuwa mota drivern Amah shi ya kar'bi khalid bayan ya bud'e musu baya sun zauna ya sa kayan a booth, hindatu ta zauna gaba.
Dukawa khalid yayi yace
"Toh Amah se na tashi dawowa zan dawo da sauran drugs d'in da babu anan pharmacy d'in"
Tace
"Ba damuwa se ka dawo d'in"
Daga haka drivern ya ja suka bar asibitin hanya ta zubawa idanu tana kallo bata ma san wani gari bane nan d'in sede chan a kalle kallen da take yi ta ga signboard na wasu makatantu a nan ta fahimci kano take, tabbas ta yadda kano Tumbin giwa ne ko da me kazo an fika.
Motoci da mutane da suke kai kawo da hada hada ma kad'ai sun isheka kallo, kaman daga sama taji Amah tace
"Lafiya lau lamido ya wurin aikin?"
Da sauri ta juyo ta kalli Amah d'in jin sunan wadda ta kira, Ashe komawa yayi wurin aikinshi ba tare da ya sallameta ba, wata zuciyar tace ke a su wa daddawa a kayan miya? In ba sbd taimako na musulunci ba ai ko hanya baki isa ki had'a da Yayanmu ba.
Tana ji Amah na mishi bayanin an sallamesu yanzu ma suna hanyar gida, kanta ta saukar kasa jin sun yi sallama ba tare da ya nemi yaji yadda take daga bakinta ba, hawayenta ta mayar tare da had'iye wani abu da ya tsaya mata a wuya...
Isowarsu kofar tangamemen gidan ne yasa ta d'ago kanta tana karewa gidan da girmanshi kallo, sashe sashe masu cike da tsari da kyau, dukda girman gidan baka jin hayaniya ko motsi kaman ba kowa gidan, tsoro ne ya kamata kaman Amah ta fahimci haka ta rike hannunta tace
"Karki tsorata 'yata nan da kika gani zuri'a guda ce ke rayuwa, bazamu cutar dake ba kinji?"
Kanta ta dukar cikin yanayin sanyin muryanta tace
"Kiyi hakuri Amah, na sani da kuna da niyyar cutar dani da tun a asibiti kun yi hakan, girman gidan ne kawai ya tsorata ni ban ta'ba ganin gida haka ba. Amma wadda ya ginashi yana da tarin shanukai ko?"
Ta sake kallon gidan daidai driver na parking tace
"Tab masu gini sun sha aiki"
Daga hindu har Amah basu san sadda sukayi dariya ba, tsantsar yaranta ya nuna a maganarta, Amah kuwa taji daad'i sbd bata ta'ba ji Amatullah d'in tayi magana me tsawo haka ba se yau.
Hindu da driver ne suka kwaso kaya yayinda Amah tayi gaba Amatullah na binta a baya tana kalle kalle a hankali, da sallama Amah ta tura kofan parlornta Maher da shi kad'ai zata iya ganewa sbd sun ta'ba zuwar mata da Amah se wasu yara kyawawa da ta tabbatar duka Maher d'in ya girme musu mata hud'u da namiji d'aya dukkansu sukayo kan Amah suka rungumeta kowa na kokarin se taji abinda yake son fad'a...
Abu d'aya da ita tana da mugu mugun son yara gasu kyawawa en gayu hakan yasa ta shagala da kallonsu tana murmushi, Amah tace
"Maher Dan Allah ja su kuje ku cigaba da Wasa anjima duk zan amsawa kowa magananshi kunga yanzu mun dawo asibiti da Aunty Amatullah duk mun gaji"
Dakatawa sukayi suna kallon wacce aka ce Aunty Amatullah, Amrah tace
"Amah ita ce bata da lafiya?"
Kai Amah ta gyad'a, khausar tace
"Hii Aunty Amatullah, tunda na riga cewa hi ai da ni zakiyi kawa ko? In je school ina kuri nayi Aunty kyakyawa"
Dariya Amah da Amatullah sukayi nan fa musu ya kaure kowa na cewa sede ta zama kawarshi, yarinyar da ta fi jan hankalinta kuma bata magana se Shan sweet d'inta take ta duka a gabanta tace
"Uhm uhm ni kam ga kawata nan, ba zan kara ba kuma se wadda yafi kokari both school da Islamiyya"
Amah tace
"Chab ki rasa wacce zakiyi kawa da ita se iyayen kiyuya? Afra ko lallai da gudu zaku rab..."
Bata karasa ba Afrah tayi sauri ta fad'a jikin Amatullah Amah tace
"Eyyeh kaji ja'irar yarinya"
Sossai hindu da Amatullah ke dariya, Amah ma murmushi take taji matukar daad'i da alamu samun saukin Amatullah baze yi wuya ba tunda har tana son yara haka tana iya wasa da dariya dasu, tunda Lamidonta ya kawo Amatullah bata ta'ba tunanin tayi dariya irin wannan ba.
Duba time Amah tayi tace
"Oya to aje a shirya lokacin islamiyya yayi"
Amrah wacce itace Babba bayan Maher d'iya ga Abdulkadir ta d'auki Afrar wacce take d'iyar khalid suka fice suna cewa se sun dawo...
Da kallon sha'awa Amatullah ta bi su gabad'aya lokaci kalilan da tayi da yaran se taji kaman bata da wani damuwa a duniya, ji tayi kaman an wanke mata zuciya da Ruwan kankara, maganan Amah ne ya katseta
"Jikokina ne duka karki damu nan ne wurin hiransu da sun dawo islamiyya ko boko"
Murmushi kawai tayi Amah tace
"Hindu rakata d'akin Lamido na da nan ya zama nata na d'an lokaci"
Da hindu suka yi varender d'in da d'akunan sashen suke a jere me had'addiyar console daga karshenshi da aka baje turarukan wuta da wasu designers kwalabe da bata san na menene ba, yalwataccen d'aki ne wadda a kauyensu se yayi gidan mutum guda, be da hayaniyar furnitures sede a tsare yake komai dake ciki farare ne.
Hindu ta juya zata fita kenan bayan ta nuna mata komai tayi saurin rike riganta tace
"Bazan iya zama ni kad'ai ba, Dan Allah mu zauna"
Hindu tace
"Nima ina da nawa d'akin kinga a gidan nan ba d'akin da zaki samu mutum biyu ko sashen samarin, bari in Kara bud'e miki windows dukda hasken kwayayen fitilun"
Zama tayi a kasa shiru, hindu cike da tausayinta tace
"Ki saki jikinki nan d'in yanzu ya zama kaman naki ne, babu wadda ze shigo se da izininki kiyi Wanka bari in je in d'aura abincin dare"
Fita tayi, ita kuwa anan ta cigaba da zama tana tunane tunane daga karshe ta fara kuka da ni kaina ban san na menene ba seda tayi ma'ishi tukuna ta Mike ta shiga toilet yadda Hindu ta nuna mata tayi ta yi wanka ta fito ta shirya cikin kayayyakin da ta samu a asibiti wadda na waye taji ana cewa? Bata sani ba, sake samun wuri tayi a kasa ta zauna.
A ta 'bangaren Amah kuma wannan d'an corridor da ze kaika kofar parlorn mai gidanta ta bi ta fita parlorn da seda tayi Dana sanin zuwanta, Hajiya Babba, Hajiya Yaya da Abbu ne ciki ta sashi gaba da mitar Amatullah akan wai ko me Amah take so jikinshi na rawa ze mata amma su sun kawo kokensu yayi kunnen uwar shegu da su..
Ganin Amah yasa Hajiya Babba jan tsaki, a kasa ta zauna kan ta gaidata cikin ladabi kaman yadda bata gajiyawa a ko da yaushe, amsar da ta Saba samu shi ta samu na "Lafiya in da gaske kike, in be kai zuci ba kuma a kasheni a huta"
Idanunta ta d'an runtse kan ta Mike ta zauna kan kujera Abbu ya dubeta yace
"Kun dawo?"
Tace
"Eh, Amatullah d'in ta shiga ta watsa ruwa ta d'an huta se ta zo ta gaidaka"
Tsaki Hajiya Yaya ta ja tace
"Tsintacciyar mage fa... hmmm"
Hajiya Babba tace
"Ni ban kai ta zo ta gaida ni ba kenan se shi, to daad'in abun da ban haifeshi ba da be yi arzikin da aka zo ci ba, Idan ta gama ko ma menene ki turomin ita sashe na in kuma ban isa ba in ji"
Kan Amah a kasa tace
"In shaa Allahu yanzu zan sa hindu ta rakota kiyi hakuri"
Mikewa tayi ta kalli Abbu tace
"Na rasa me yasa kai Muhammad a duk sadda zan ce ga abinda nake so se kayi min jayayya sa'banin Almustapha, kaje ka kara nazari baza'a zo ana kuka da zuri'ana akan abinda muka fi karfinshi ba idan mutuwa ze yi in an d'aura ya mutu Alhamdulillah"
Da sauri Amah ta d'an kalleta kab matan Abbu ita kad'aice me yara maza kuma ta sani sarai babu wadda Hajiya Babba ta tsana irin Lamido me take shirin aikata mai?
"Get out of my sight halimatu"
Baki hajiya yaya ta kwa'be tace
"Oho dae ko yanzu kasuwa ta tashi Dan koli yaci riba, ba zan zauna wata chan ta take ni ba bayan ni ta zo ta samu da mijina da gidana, tunda ka aurota na gayama Muhammad bazaka ta'ba samun kwanciyar hankali ba in har ba rabuwa kukayi ba dukda shekaru sun ja amma har yanzu ban gaji ba kuma bazan gaji ba, yanzu ma na d'aura d'amara, Mu zuba mu gani.."
Daga haka ta fice fuuu tana mitar an kaiwa bokan gado sunanta ya hanata yara maza duka ya tattara ya bawa god'iyarsu to dukda haka kwalele zama daram kuma tashin bankali ka fasa...
Ajiyar zuciya Abbu ya sauke yana tuna yadda kaddarar shi na auren halimatu har ta kaishi tashin hankalin da be ta'ba hutawa ba tun auren Saudatu(Amah) har zuwa kawo yanzu, duk yadda ya so d'aukan mataki Hajiya Babba ke kawo mishi cikas, ba don mutuwa me tonon asiri ba da mahifinsu na nan ya san shi kad'ai ne me iya taka ma Hajiya babba birki... a take ya lula tunanin baya ba tare da ya farga da Amah dake zaune ba.
****
*Ko kin shirya mallakar Wad'annan TAURARI Guda biyu😉 Da Naira Dari biyar kachal zaki mallaki gawurtattun littatafan nan guda biyu...
*GAMON JINI Na Fatima Muhammad Gureen (Gureenjo)*
*Da Kuma*
*SABABI Na Amina Ibrahim (Oum Ameer)*
*Akan Naira D'ari uku kuma zaki mallaki Guda d'aya cikin biyun, karku manta mun shirya tsab domin Nishad'antar daku, fad'akar daku da kuma Nishad'antar da ku masoya, Mallaki naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali er uwa👌*
Zaku iya biya ta account number kamar haka
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Se a turo shedar biya ta wannan layin
***
Note: Banda Recharge card.
🖤Gureenjoh🖤