60
💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔
( shi ya san gidan mai rowa)
```By```
``` NAFISAT ALIYU SASAAL```
```Page 60```
________Goggo kullum sai ta tambayi ya Halima take ko a bata ita a waya suyi magana,amma sai su sako mata uzurin wayar Haliman ya lalace.
Rashin ƙaunar Halima da Goggo tasan sunayi ne yasa bata kawo komai aranta ba,sai don kawai basaso taji muryarta badon wayarta ya lalace ba.
Har lokacin Uncle Suraj bai haƙura da neman Halima ba,duk da kowa na kallon hakan a matsayin farin cikin Goggo yasa yake nemanta,basu taɓa kawo wani mugun abu aransu ba,musamman Uncle Ghali dayake ganin don yaƙara samun wajen zama a zuciyar Goggon yasa yake haka. Shamsiyya ce kawai tasan gaskiya kuma babu damar faɗa.
Faisal da Matarshi zaman su baya wani yimishi daɗi don sai yake ganin Mubeena tafita tarbiyya da iya kula da Miji,don ita burinta kullum bai wuce dare yayi ba suyi ta abu ɗaya,ga shi bata tanƙwarar mai kamar Mubeena,bata iya girki ba,sai yawon siyan abinci kullum.
A karon farko ya fara dayasanin sakin dayayiwa Mubeena har uku bai dace ba,ga shi kuma babu halin gyarawa.
Lissafin ɓatar Halima bai dameshi ba,tunda tuni komai ya hau mishi kai,ko ba komai daina ganinta a halin dayake ciki yafi mishi sauƙi da salama.
Ranar wani yammaci Uncle Suraj ya buƙaci ganin Faisal. Tambayar ko Halima tasan wani a wata ƙasar yayimishi,misali da Nijar ko Ghana da dai ira-iren su. Kai Faisal ya girgiza don baya manta ko lokacin da Goggo tasa akayimata Passport dariya yayita yi mu su na Ina Halima zataje har da zata sa ayi mata Passport.
"Gaskiya Daddy bata da kowa,don ko lokacin da Goggo tasa aka yi mata Passport,tasa anyimata ne kawai" kai Uncle Suraj ya jinjina zuciyarshi na ƙara ɗaukar zafin jin har Passport ne da Halima.
A daren ranar yasa Maids kusan guda goma su bincikemishi sashen Goggo,amma sai ya zame Shamsiyya a ciki,don kar tsautsayi yasa ta bawa Goggo labari,dan har lokacin Shamsiyya bata kwanta mai a rai ba,a matsayin munafuka yake kallonta
Sai da su ka bincike ko ina amma babu wani littafi da yayi kama da Passport ɗin Halima.
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Maysarah yafi minti biyar bai motsaba duk da tajima da katse kiran saboda kukan dayaci ƙarfinta, yana tsananin son Halima so mai zafin da har abada baya gushewa a zuciyar Bawa sai dai wani babban dalilin da samunshi abune mai matuƙar wahala.
Farkon komai ne yake dawowa cikin kanshi,da wani zai ce hakan zai faru da shi daya ƙaryata,itace nutsuwarshi,farin cikin shi,ganinta a cikin kwana biyu da wuni na neman samishi raunin da baisan yana da shi ba, ba shi da uwa ba shi da Uba,kuma Goggo ƴaƴanta bazasu taɓa bari ya samu nutsuwar zuciya dana gangar jiki ba,da ƙasarshi zai koma da ita kullum suyita rayuwar su tare.
Bayan ta gama shan kukanta ta miƙe ta shiga wanka,cikin guntayen kaya marasa nauyi ta shirya ko bra bata saba saboda takura matan dayake yi. Kimtsa ko ina tayi, ta zura dogon hijabi tayi kwanciyarta a daƙi karatun Abdul Rahman Bin Mus'ad na tashi ƙasa-ƙasa cikin ƙirarshi mai daɗin gaske a lafiyayyen wayarta.
A haka ɓarawon barci ya ɗauketa,batafi awa ɗaya ba ta farka. Alola tayi, tayi sallah sannan ta zame hijjabin yalwataccen gashinta ya zubo kafaɗunta.
Parlon ta dawo tana kuka ƙasa-ƙasa,har lokacin kuma taƙi cin komai, zaman duk ya isheta ga shi babu motsin kowa.
Motsin buɗe ƙofar ne yasa ta daina kukan tana kallon hanyar shigowa gabanta na faɗuwa.
Lion face ɗin shi nanan yanda yake sai dai idanuwanshi da ƙewarta da yunwar dayake ji,yasa sukayi yaushi. Buɗe mata hannayenshi yayi yana kallonta,maƙe kafaɗarta tayi tana ɓata fuska.
Rausayar da kanshi yayi ya juyawa kamar wanda zai koma. Da gudu ta taso ta ƙanƙameshi ta baya.
Ƙaramin dariya ya saki,ya juyowa haɗe da maidata jikinshi.
"I Miss you soo much"
Ya faɗa a kunneta,da muryarshi da yunwa yasa yaƙarayin ƙasa.
Ƙara ƙanƙame shi tayi,tudu da laushin ƙirjinta na neman zubar da su ƙasa.
A haka yake tafiya da ita a jikinshi har suka zauna ya dawo da ita kan cinyarshi.
Da lumsassun idanuwanshi yake kallon abinda ke neman zautar da shi.
"Maiyasa baki sa bra ba" ya faɗa a hankali yana shafa girarta.
Idanuwanta ta mairairaice tana kallon cikin nashi idanuwan alamun so ne batayi.
" Idan na ƙara dawowa baki saba,zanyi miki bulala mai zafi" ba wani wayo ne da ita ba,don haka kai tsaye ta yarda da zanenta zai yi,don haka tasa kuka haɗe da ƙorafin itafa sone batayi takura mata yake yi.
"Yaushe zaki daina kuka,Halimahta" ya faɗa yana kallon hawayen da take yi.
Dasauri ta share tana faɗin ta daina.
Tana jikinshi har daƙinshi,sai da zai yi wanka ya ƙyaleta,da sunan taje ta shirya zasu fita.
Sai dare sosai suka dawo kowannen su a gajiye.don haka suna dawowa sukayi sallah suka shirin kwanciya barci.
A hankali Halimah tayiwa zuciyar Maysarah mamayar da baya cikakken awa baiji muryarta ko a ina yake ba,duk wanda yasan shi,sai yasan da zaman Halima indai zasu wuce hour ɗaya tare. Baya iya ɓoye soyayyar dayake mata.dalilin haka dukka Abokanan kasuwancin shi suka san Halima a baki amma a ido ko Naseer daga ranar daya ɗaukota baifi sau ɗaya yaƙara ganinta ba.
Itama anata ɓangaren shirmenta da koke-koken na rashin dalili basu sauya ba sai dai ta rage kuma tun ranar dayayi mata faɗan saka bra ta kiyaye,haka duk wani abu daya nuna mata bayaso tana ƙoƙarin kiyayewa saboda wasu lokutan ajjiye soyayyarta yakeyi yayi mata faɗa sosai idan taƙi daina shirmen da take yi.
Yau ma da rigimarta na rashin dalili suka rabu. Don nacewa tayi ita sai ta bishi.
Duk kiran dayayi mata ƙin ɗagawa tayi,da ƙunci ta wuni,ita kanta batasan iya adadin soyayyar da take mishi ba.
Batayi tsammanin dawowarshi ba,don haka ta yi zaman babu kayan arziƙi balle bra dayace tana sawa. Kamar daga Sama taji alamun buɗe ƙofa,da hanzari da jefar da wayan da take game da shi a gefe tana ƙoƙarin gudawa.
"Come back here Halimah" ya faɗa da Muryar dayasan yake tsoratar da ita.
Kamar mara gaskiya haka ta juyo tanayin ƙasa da kanta.
Daga kwantaccen sumar kanta data kama a tsakiya zuwa ɗan ƙaramin rigar da dukka kusan jikinta yake a waje yake kallon ta,idanuwanshi na juyewa saboda girman abinda yakeji.
Baya neman Mata,ko da,da sunan rage zafi ne,amma akan Halima yasan girman tasirin Mace a rayuwar ɗa Namiji.
Idanuwanshi har ruwan tausayin kanshi suke tarawa.
"Zo" ya faɗa a hankali kamar ba shi ba.
Maƙe kafaɗarta tayi,tana ja da baya-da baya a hankali.
"Idan kika gudu zan hukunta ki"
Kuka tasa ta juyawa da gudu.
Kulle idanuwanshi yayi yana zubewa akan kujera.
Sai bayan magrib Halima ta fito. Yana zauna yana aiki.
Ƙamshin mai sanyi da shigarta mai burgewa ne suka hanashi yi mata shamaki da kwanciya a jikinshi.
"I'm sorry" ta faɗa a kunnenshi,saura kaɗan System ɗin dake gabanshi ya kife,amma bai kula ta ba,kuma fuskarshi na nan kamar bai santa ba.
"I said I'm sorry" ta faɗa tana shafa ƙasumbarshi.
Kasa jurewa yayi ya haɗe fuskar su.
Bata hanashi ba,don so take yi ya haƙura.
Bayan sunyi Dinner sunyi sallah yaƙara jan su nafila sannan suka kwanta,ranta fari ƙal ɗin ya yafe mata.
"Maiyasa ɗazun kika gudu"gabanta ne yafaɗi don batayi tunanin har lokacin bai manta da abinda ya faru ba.
"Ban Sa ba"
"Menene baki saba" ya faɗa yana kallon fuskarta da take ƙoƙarin yimishi wayo ta hanyar marairaiceshi.
Shiru tayi tanayin ƙasa da kanta kamar batasan komai ba.
"Ba nace zanyi miki bulala ba duk ranar da baki saka ba?" tanajin yace haka ta fara ba shi haƙuri. Da koke-kokenta na rashin gaskiya.
Maysarah yayiwa Halimarshi bulala mai zafin gasken da bazai taɓa gogewa ba a kanta har abada. Don baya rabawa sadaka a Wajen matan banza,sai akan Halimarshi,wannan dalilin yasa yake da ƙoshashshen lafiya ta ko ina.
Babu inda Soyayyarta baiyiwa Maysarah illa mai girman gaske ba a cikin zuciyarshi da ma gangar jikinshi,darajarta soyayyarta mai girma,da son rayuwa da ita har gaban abadan ne suka zama bitar shi a wannan dare. Sai ya rena duk wani girman jiki dana kuɗi dayakeji yana taƙama da shi,duk wannan nauyin da yake yawo da shi tsahon shekaru duk sun sauka saiyakejin shi kamar sabon mutum.
Halimah....✍🏻
😔😔Barkan mu da dare