61
💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔
( shi ya san gidan mai rowa)
```By```
``` NAFISAT ALIYU SASAAL```
```Page 61```
________Halima ta yi kukan da har sai da ta dawo gani dishi-dishi.
Kafin gari yayi haske sosai yakaita Asibiti.
A wannan yinin barcin azaba Halima tayi. Yana zaune a gefenta bayan anyimata stitches,da ƙarin ruwa zazzafan zazzaɓin daya rufeta,sai dare suka dawo gida,har lokacin kuma barci take yi.
Fargaba da tsoron farkawarta yakeyi don Lokacin da ta farka a Asibiti baya kusa,gaba ɗaya rauninshi na ranar a bayyane yake.
Tashi yayi yabar ɗakin domin yin wanka.
Baifi 45 minutes ba yaƙara dawowa ya zauna yana kallon kyakkyawar fuskarta,a hankali ta buɗe idanuwanta suka sauka cikin nashi. Batayi kukan dayake tunanin zatayi ba,sai kallonshi da takeyi da idanuwanta da kusan rabi yake a rufe rabi a buɗe.
"Halimata kice wani abu kinji,kiyi kuka naji Please" ya faɗa yana matsa hannunta dake cikin nashi,da sanyin da bata sanshi da shi ba. Kanta ta girgiza a hankali alamun a'a.
A hankali yamiƙar da ita gaba ɗayanta yasanta a jikinshi,yana cemata tayi kuka ko zataji sanyi a ranta don ko ba ta faɗa ba yasan nauyin yayimata yawa.
Shiru tayi kamar ruwa ya cinyeta kuma batayi yunƙurin tureshiba,abinda tayi yasaɓawa tunaninshi da hasashen shi,sai yaƙarajin Tausayinta da tsananin soyayyarta da na ƙara mamayarshi.
A cikin wasu kwanaki Halimah taji sauki sosai.
Bashida juriya ko kange kanshi daga gareta don haka yaƙara kai mata ziyara a karo na biyu.nan ma wani sabon karatun ne mai wahala da azabar fahimta a wajen Halima.
Babu wani abu da Matar so take sawa ko take ado dashi indai Mijinta ya amsa sunanshi mai arziƙi da wadatar zuci wanda Maysarah baya siyowa Halima. Kulawarshi wani abu ne na daban mai wuyar mantawa. A wajen abokanan kasuwanci shi da na mu'amalar yau da gobe duk sun san shiɗin na Halimarsa ne,don akasin yawan faɗar sunanta a maganganun shi har ya zama sabo a kunnen duk wani wanda abu zai haɗa su ta fuskar rayuwar yau da kullum.
Halima bata rasa komai ba a watanni biyar ɗin da suka shuɗe tayi wani irin kyau da ƙiba,kafin ta fara ramewa. Dalili, Halima bata daga cikin jerin Mata masu zurfin buƙata saɓanin Maysarah,baya iya ko da cikakken kallonta ne batare da ya kusanceta ba, lamarin na damunta sosai har yafara taɓa lafiyarta, gashi batada wanda zata gayawa,duk da a lokacin sosai take waya da Inna har da su Baba Isiyaku. Raɗaɗi da damunta da lamarin yakeyi ba kowa bane zai fuskanceta ya kuma gane mai takeji ba sai Macen da take da irin Halittar ta,gaba ɗaya sai komai yafara fice mata a rai musamman idan ya fita haka zata wuni tana kuka don ko cikakken zama bata iya yi.
Kyautatawarshi da yanda yake nuna ita ɗin mai daraja ce da ƙima,ya hana tsanar Maysarah tasiri a ranta sai soyayyarshi,maganarshi mai sanyi da taushi ne a gareta,kuma ita shaida ce soyayyarta ne ya mayar da shi mai sanyi hali da sauƙin kai idan yana tare da ita,to ita ƴar wacece? ƴar Halime da duniya keyiwa gorin nakasa da Salmanu da akeyiwa gorin samowa aiki. Duk da haka Maysarah bai duba wannan ƙasƙancin da danginshi suke kallonta da shi ba,yayi ƙoƙarin mantar da ita waɗannan gorinka da suke kamar maɗaci a cikin zuciyar ta,bata da wani hanya na ba shi farin ciki sai ta wannan hanyar kaɗai.
Ko da zata rasa ranta wajen raɗaɗi da azabar kasancewa da shi da takeji zata jure tayi haƙuri ko Allah zai kawo mata sauƙi.
A lokuta da dama sha'awa da giyar soyayya na makantar da wasu Mazan wajen fuskarta yaya matan su,sukeji lokacin da suke kasancewa da su,indai suna samun cikakken gamsuwar da su suke so to hankalin su gaba ɗaya baya kan irin wannan matsalar. Babban ƙalubalen da Halima ta fuskanta kenan a gidan aurenta.
Kuka kullum sai ta yi shi,sai dai idan Maysarah bai fita ba.
Ramarta dayafara yawa ne ya ankarar da shi da akwai abinda yake damunta,sai ya lura gaba ɗaya ko zama batason yi,kuma ko ya tambayeta sai ta ce bakomai.
Kullum sai ya tambayeta haɗe da lallashinta amma sai taƙi faɗa ta kwanta a jikinshi tana sauke a ajiyar zuciya.
Sosai Maysarah ya matsawa kanshi wajen gano asalin damuwarta amma ya kasa,don lokuta da dama ba'a cikakken hayyacinshi yake samun damar zuwar mata ba,don tun kafin komai yayi nisa yake rasa tunaninshi,kuma itama duk juriyarta da ƙarfin take tattarowa wajen nuna itama tanajin daɗi.
Ran shi fes ya fita wajen taron da zaije saboda cikakken gamsuwa da nutsuwar dayake samu,ya ƙara ƙiba da haske mai birgewa,kallo ɗaya zaka mishi kasan bashi da damuwar komai. Ranar tsabar wahalan da tasha bataso ya gane,sai tayi kamar mai barci,shima kuma bai tasheta ba saboda yasan irin ƙoƙari da jarumtar da take nunawa.
Bayan fitar shi tayi kuka iyakar iyawarta,irin wanda bata taɓayi ba tun bayan zuwanta,ƙarshe zazzaɓi mai zafi ya rufeta. Bata tashi ba ta kwance har zuwa sha biyu na rana. Ƙarar buɗe ƙofar ɗakinne yasa ta fara ƙoƙarin miƙewa da iyakar jarumtar ta.
Da zafin naman shi yaƙaraso inda take, fuskarshi babu walwala don yakirata yafi sau goma bata ɗaga ba.
"Sannu da dawowa" ta faɗa a hankali bayan ta jingina da fuskar Bed ɗin da take kai.
"Halimah menene yake damunki" ya faɗa kamar wanda abu yatoshewa maƙoshi yana kallonta.
Murmushi tayi haɗe da gyara sumar kanta zuwa baya,ta na taune leɓenta,"babu komai"
"Halimah Ni zakiyiwa ƙarya,kin daina so na ko🥹?" Dasauri ta girgiza kanta. Kafin ta ɗago idanuwanta da ƙwalla ya cika su taf tana kallon shi.
"To menene matsalan"
Hannayenshi ta kamo, duk da haka ta ƙiyin magana. Bata ankaraba taga yaɗauketa gaba ɗayanta,kai tsaye cikin Mota ya ajjiyeta,sannan ya koma ciki ya ɗauko mata Abaya da Vail.
Duk Nacin da likitar data dubata waccen karon tayi Halima taƙi magana sai kuka ƙasa-ƙasa.
Tashi yayi suka fita waje da likitan kafin ta dawo da wayan da kiranshi yake kai don yafison yaji matsalar daga bakinta.
"Ya fita Halima kiyimin bayani zan fuskanceki"Dr Ateekaa ƴar asalin ƙasar Pakistan ta faɗa tana kama hannayen Halima dake rawa.
"Babu komai" ta ƙara faɗa kukanta na ƙaruwa.
"Halima ki ɗaukeni kamar Mahaifiyarki kinji bazan gayamishi ba kinji" ta faɗa da sigar dabarar shekarun da ta ɗara ta da shi. Duk Maysarah na jin su.
"Uhm,uhm🥹"sai kuma tayi shiru.
"Ina jinki Halima"
"Dama idan yazo ne sai naji nagaji,komai sai yadaina yimin daɗi saboda wahalan danake sha,amma don Allah karki gayamai zai yi fushi,kuma banaso" ta faɗa da kuka ƙasa-ƙasa.
Dr.Ateekaa murmushin tayi bata taɓa tunanin iya wannan matsalar ne Halima ta kasa faɗa ba." maiyasa bakyason ya sani Halima, Kinsan irin matsalarki na raba aure"
Ta faɗa tana kallon yanda Halima zata ɗauki maganar.
Kai ta girgiza alamun bata sani ba kafin ta ɗora da
"Yanayimun duk abin nakeso,kuma bani da komai da zan ba shi,sai kasancewa dani kaɗai kowa baya sona amma shi yana sona.
Ta faɗa tana kuka sosai.
"Saboda yana sonki yana siyo miki abunda kikeso yasa kikaƙi faɗar matsalarki Halima, kuma kikeson zama da shi"
Girgiza kai alamun a'a
"To menene dalilinki"
"Ko da fita yayi kaɗai yadaɗe banganshi ba,sai naji kamar narasa komai ina sonshi sosai bazan iya rayuwa bana ganinshi ba" wannan karon Dr.Ateekaa ƙaramin dariya ta saki tana jinjinawa soyayyar su.
"Amma Halima Mijinki zai iya rasa dukiyarshi wata rana,kina ganin idan ya daina siyomiki abinda kikeso zaki zama da shi" tayi mata wannan tambayarne saboda Maysarah dayake jin su,don tun wuri su samu mafita,duk da akwai wa su mafitan idan har zata jure.
"Ai shi baicemin yanada kuɗi ba kawai ya na siyomin ne don naji daɗi,inason komai nashi, Ni dai kawai girmanshi ne banaso,kuma yace ciwo ne zai sa yadawo ƙarami,Ni kuma banaso yayi ciwo yasha wahala" ta faɗa da iya gaskiyarta,tana share hawayenta.
Wannan karon dariyar mai bayyana haƙora Dr. Ateekaa tayi,saboda faɗin Halima na ita Bama tasan Mijinta na kuɗi ba balle ma ta so shi dan shi.
A tsaye yake amma dole ya nemi waje ya zauna, maizaiyiwa Halima tajita kamar sauran ƴaƴa masu gata da cikakken ƴanci, tun yaushe take fama da azabar da har sai da yaci ƙarfin ya gane. Idanuwanshi ya lumshe saboda ƙwallar daya fara taruwa a cikin su,ta zaɓi ya rayu yayi walwala ita kuma ta rasa lafiyarta ta dinga kwana tana yini cikin ƙunci. Dame zai sakawa Halima.
Bashi kowa sai ita itama bata kowa sai shi. Sai Kakannin su dasuka rage musu.
Da ire-iren waɗannan tunanin Maysarah ya zaɓi barin Halima....✍🏻