ALLON ƘADDARA

Chapter 23

by @oumfatima33

✨✨✨✨✨✨✨✨  

 _*ALLON ƘADDARA*_

        _*By*_

   *_OUM FATIMA_* 

_*(Hakimar D. A. W. A)*_

✨✨✨✨✨✨✨✨ 


     _*DASHEN🌲ALLAH*_ 

_*WRITER'S📚ASSOCIATION*_


            _*TEAM*_

_*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*_





 *PAGE 23* 


_*بسم الله الر حمن الر حيم*_




Saura kwana ɗaya tafiyar ya ɗauke mu duka zuwa Gida, muna isa sashen Hajiya Mama muka nufa bayan mun gaisa ni ban zauna ba na fito na nufi sashen Ammyna don nayi kewarta sosai. 


A parlour na samu Ammy zaune saman kujera da laptop saman cinyarta tana duba wasu kaya da aka turo mata. Da gudu na ƙara sa na rungume ta ina sauke ajiyar zuciya "Nayi kewarki Ammyna" na faɗa a hankali ina ƙara lafewa a jikinta.


Ammy da tun da na shigo da gudu ta rufe laptop ɗin tana jiran ƙarasowata sai murmushi take yi domin kuwa itama tayi kewar gudan jininta ƙwallin ƙwal a duniya. "Nima nayi kewarki Habibty, yaya kike? Ya jikinki? Yaya Kalisat ɗin? Ina fata dai babu wata matsalar?".


"Duk muna lafiya Ammy babu wata matsala"


"Masha Allah haka ake so, Hammannaku kuma gobe zai yi tafiya".


"Eh Ammy sallama yazo yi ma"


"To Allah ya bada Sa'ar abinda aka je nema"


"Ameen" na faɗa muka ci gaba da hira da Ammy take tambaya ta game da Alhaji Bilal "ya kuke ciki ne da Alhaji Bilal ne Hanan, kun dai-daita ko kuwa har yanzu kin kasa sakin jiki ki fuskanci gaba, ya kamata ace zuwa yanzu kin yiwa kanki faɗa Hanan shekarunki gaba suke ba baya ba, nan da wata biyu zaki cika Ashirin da huɗu, Nabeel ya riga ya tafi ba zai dawo ba addu'a kawai zaki ci gaba da yi masa itace soyayyar da zaki nuna masa amma maganar bazaki kula kowa ba bata taso, ba don Kinga Babanku ya maki shiru ba yana nufin abin baya damunsa bane kawai yana tausaya maki ne shi yasa ya baki lokaci ki samu natsuwa tukuna, ya kamata kije kiyi tunani". 


Kuka sosai nake yi zuwa yanzu don duk lokacin da aka taso min da maganar aure irin wannan halin nake shiga, in na tuna cewar wai rayuwa ake so in yi da wani ba Ya Nabeel ba rayuwar da na gama tsarata dashi shi kaɗai, sai nake jin abin is very difficult to me na iya sakewa. Sai dai ba yanda na iya nasan ko ba daɗe ko ba jima dole zanyi aure tunda ba zan dauwama a haka ba, amma dai ban shirya ma hakan a yanzu ba, amma da alama su Ammy bazasu ƙyaleni ba.


"Haƙuri zakiyi Hanan na san da ciwo da wahalar mantawa amma in kika yi haƙuri kika barwa Allah lamarin sai kiga ribar hakan".


"In sha Allah Ammy ke dai kiyi min addu'a Allah ya sanyaya lamari na".


In sha Allah addu'a kullum cikin yi miki nake yi kuma insha Allah zakici nasara, Allah zai miki zaɓin da yafi Alkairi".


"Allah yasa Ammy!" Na faɗa ina share hawaye na. Da haka muka tashi muka shiga sallar azahar.


Bayan mun yi salla mun ci abinci sashen Hajjo na tafi don nayi kewarta sosai don ma muna waya da ita. Ina zaune Nataccen ƙamshinsa ya fara mamaye parlourn kafin daga bisani sallamarsa ta biyo baya.


Hajjo ce ta amsa masa da fara'a tana masa maraba, kujerar dake fuskantata ya zauna yana bina da kallonnan dai da bana so. "Me yasakata kuka kuma?" Ya faɗa a saman laɓbansa ba tare da kowa yaji ba, yana kallon fuskarta yasan tayi kuka sabo da yanda tayi ja idanunta suka tasa, ya san ba haka suka fito ba dukda dama tun da abubuwannan suka faru ta daina walwala, amma zamanta da Kalisat kwana biyu yasa ta fara sakewa, ko yaya ta samu sauyi yana ganewa sabo da ya santa tun tana zanin goyo. Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya gama wannan tunanin ya maida kallonsa saman fuskar Hajjo da ta tsare shi da kallo, fuskarsa ya ɗinke tsaf don kar ta sako masa zancen da ba shi ba. Cikin natsuwarsa ya buɗe baki ya gaisheta. Kai kawai ta gyaɗa tana amsa masa da tambayarsa Kalisat "Tana tare da Hajiya, zata shigo zuwa jimawa" ya faɗa yana zaro kyakykyawar wayarsa daga aljihu ya amsa kiran da ya shigo masa.


Jin zaman shirun ya gundure ni yasa ni miƙewa nayiwa Hajjo sallama na nufi sashenmu ina amsa wayar Anisa da ta kira ni. Ina shiga Ammy ta tambaye ni "kin shiga kin gaida mutanen Gidan kuwa?".


"Daga ɓangaren Hajjo nake Ammy"


"To kije ki gaishe da Mamanku ƴan uwanki ma sunzo kwa gaisa"


"To" kawai nace na juya na nufi ɓangaren Mammah, a parlour na same su dukan su sun baje suna ta hira su Aunty Zainaba sun zo daga gidajensu. Da sallama na shiga suka amsa min ba yabo ba fallasa, sai idanu da suka zuba min suna bina da kallo.


Zama nayi a saman Capet kusa da Aunty Halimatu da tace min na zauna, naji daɗin ganinsu har zuciyata don Allah ya sani ina son ƴan uwana sune dai basu jani a jikinsu ba suka wareni suke kyarata da tsangwamata tun ina ƙarama shi yasa babu wata shaƙuwa a tsakaninmu. Mammah na fara gaisarwa kafin na gaida su Aunty Zainaba da ta amsa min kamar yanda ta saba, Aunty Halimatu ce ma ta amsa min da sakewa har tana min tayin wainar fulawa da take ci.


"Alhamdulillah ngd" na faɗa kafin na kalli Bilkisu da zamu iya yin Sa'a don ba wani sosai ta girme ni ba "sannu" tace min na amsamata da "yauwa sannu" jina a takure yasa nayi musu sallama na fita. Ɓangaren Hajiya Mama na nufa ina kallon ɓangaren Momy zuciyata ce ta shiga nuna min hoton Ya Nabeel yana fitowa daga sashen fuskarsa ɗauke da murmushi. Ban san lokacin da na nufi hanyar ba nima ina yin murmushi, dafanin da aka yi ne ya maido ni a hayyacina na ɗago don ganin wanene, Aminatu ce ta dafa ni tace "sannu Hanan, yaushe kika dawo?" Da sauri na share hawayen da suka zubo saman fuskata nace mata "ɗazu muka zo da Hamma Jabeer da Aunty Kalisat"


"Ok muje ciki to" ta faɗa tana kama hannuna domin yanzu sosai take tausayin Hanan duk sanda ta ganta sai ta tuna da ɗan uwanta "A'a kije an jima na shigo" na faɗa mata haka kawai amma ba shiga zan yi ba. A yanda Momy ta tsaneni bata son ganina na shiga ban san ya zamu ƙare ba. Itama bata matsa ba don tasan komai don haka na juya na nufi sashen Hajiya Mama jiki a sanyaya, gaishe da Hajiya Mama naƙara yi ta amsa da kulawa na tambayeta Asiya tace min ta aike ta, ban jima ba muka fito tare da Aunty Kalisat da zata je ɓangaren Hajjo. Haka na shiga na gaishe da duk sauran Matan gidan kamar yanda Ammy ta umarce ni, ina komawa na samu Baba Malam ya dawo don haka na tafi wurinsa na gaishe sa yayi ta jana da hira yana yi min nasiha cikin hikima. 


Ranar haka na yini da Iyayena suna jana a jiki da kyautata min. Sai dare Hamma Jabeer yazo ɗaukarmu bayan yayi sallama da Iyayensa gaba ɗaya, sun jima da Baba Malam yana masa nasiha da addu'a kafin ya shigo sashen Ammy kira na. Dambun naman kaza mai yawa Ammy ta bani tace in bashi, haka nayiwa Ammy sallama na fito ba don na gaji da ganinta ba.



 *Washegari*


Da sassafe muka tashi domin jirgin ƙarfe 10:30am Hamma Jabeer zai bi don haka muka shiga kiching nida Aunty Kalisat da duk yanda nayi da ita akan ta bari nayi ta ƙiya sai da ta bini. Break fast mai kyau muka haɗa sannan muka ƙara sa haɗa snacks ɗin da muka yiwa Hamma Jabeer.


A dining muka haɗu gaba ɗaya muna ƙaryawa, inda Hamma Jabeer yayi amfani da wannan damar yayi mana nasiha sannan ya bamu amanar juna yace mu kula da kanmu "Nasan baki matsala Madam" ya faɗa yana kallon matarsa cike da kulawa fuskarsa ɗauke da kyakykyawan murmushi, itama murmushin tayi tace "in sha Allah zan kuka da ita " ta faɗa tana kallona. Nima kallon su nake cike da sha'awar yanda suke son junansu suke kyautatawa junansu.


"Ban da rigima Sofiyyah, ki kula sosai bana son jin ance kina yin kuka ok" ya faɗa yana kallo na. Baki na tura gaba jin cewar wai wani banda rigima sai kace wata yarinya.


Wani ɓoyayyen murmushi ya saki yana girgiza kai don yaga abin da take "Fitinanniyar yarinya kawai dole sai tayi halin" ya faɗa a kasan maƙoshi. Kalisat kuwa kallonsu take yi tana sakin murmushi, da haka muka gama break fast muka tashi. Knowking aka yi naje na buɗe, Ya Shaheed ne ya shigo da sallama a bakinsa "Autar Ammy kin samu lafiya har wani ƙiba kike kina ƙara yin fresh!" Ya faɗa cike da zaulaya.


"Haba Yaya wace irin ƙiba a nan?" Na faɗa ina murmushi.


"Tafiya zamu yi ko kuma surutu kazo yi?" Hamma Jabeer ya faɗa yana ɗaure fuska "Sorry Babban Yaya, Bismillah muje" Shaheed ya faɗa yana sosa kansa. Ina ɗagowa muka haɗa ido ya watsa min waɗannan azababbun idanun nasa masu sa mutum shiga tai-tayinsa, baki na tura gaba na nufi ɗakina don ɗauko mayafi. Sai da ta ɓace wa ganinsa ya ɗauke ido daga hanyar da ta bi yana ɗagowa yaga Shaheed ya tsaresa da ido yana kallonsa, fuskarsa ya kara haɗe wa yayi gaba. A ɓangaren Shaheed kuwa mamakin kallon da yaga Yayansa yabi Hanan da shi ne ya kamasa sabo da yasan shi ba ma'abocin kallon Mutane bane shi, hasali ma ɗabi'ar da ya tsana kenan ta ƙure Mutum da kallo. Kafaɗarsa ya ɗaga ya ɗauki loggage ɗin sa ya fita shima.


Sanda na fito duk sun fita don haka nice ƙarshen fita, yana tsaye jikin Mota yana amsa waya cikin natsuwarsa. Yayi kyau sosai cikin white Tuxedo with Green Floral Trim _ 3 pieces Suit ƙafafunsa sanye cikin Black leather boots hannunsa ɗaure da kyakykyawan agogon Rolex, permanent ƙamshinsa na turaren AZZARO da aka san shi ne ya sirka da wani ƙamshin da na kasa tan-tancew ne ke tashi a jikinsa, sassalƙan baƙin gashinsa ya sha gyara sai shining yake, haka kwantaccen baƙin sajensa da ya zagaye kyakykyawar fuskarsa ya ƙara masa kyau sai ɗaukar ido yake.

Duka a cikin abin da bai fi minti biyu ba na gama kare masa kallon nan "Masha Allah in dai kyau da ƙwalisa ne Hamma Jabeer maƙura ne sai dai baƙin hali fuska kullum ba rahama" nake mitar a hankali lokacin da nake ƙarasowa jikin motar.


Abin da bata sani ba shine tun da ta fito idonsa yake a kanta, sai dai ba wanda zai gane hakan sabo a zahiri hankalinsa yana kan wayarsa da yake daƙila, sai dai a baɗini duk wani takunta ɗaya akan idonsa take yi, yana kuma ankare da kallon da ta ƙare masa har mitar da take yana kallon bakinta na motsa wa yasan halin ne take. Sosai itama shigar da tayi na doguwar rigar Atamfa straight gawon yayi mata kyau ɗinkin ya zauna ɗas a jikinta kamar ko yaushe ta kashe ɗaurin Zarah Buhari sai yalwataccen mayafin da ya shiga da Atamfar da ta yafa tun daga saman kanta, ƙafafunta sanye cikin dogon takami ƙirar Italiya baƙi mai tsini sosai, sai ƴar ƙaramar hand bag ɗin su, sansanyar ƙamshinta yana ratsa hancinan mutanen gurin.


Gaɓa ɗayan su ido suka zuba min lokacin da na iso, don sosai wankan nawa ya yaƙe su. Kamar yanda Hamma Jabeer yake gwani wurin iya tsara kwalliyar da ta dace da shi to nima fa gwanace a wannan fannin don shi yasa friend ɗina suke kira na da Babbar Yarinya "Na fito" na faɗa ina kallon Aunty Kalisat dake kallo na "Masha Allah kin yi kyau sosai Hanan".


"Na gode Aunty" na faɗa ina sakar mata murmushi. Duk Mota ɗaya muka shiga nida aunty Kalisat muna baya su kuma suna gaba, a haka muka ƙara sa airport muna taɓa hira nake fadawa Aunty Kalisat daga can Office zan wuce.


Lokaci zuwa lokaci muke haɗa ido ta mirror duk in na ɗago. Da na gaji da hararar da yake min duk in mun haɗa ido ne na kwaɓe fuska ina masa kallon "me kuma nayi" kai kawai ya ɗauke ba tare da yace komai ba.


Mun isa dai-dai an fara Cigiyar fasinjoji don haka ba ɓata lokaci ya nufi inda ake nemansu bayan ya rungume matarsa ya sumbaci goshinta, itama rungumesa tayi hawayen da take maƙalewa na zubo mata. "Kar kiyi kuka mana, in sha Allah ba zan daɗe ba zan dawo" kai ta ɗaga masa kafin ya saketa suka rungume junan shi da ƙanensa kafin ya sake shi ya ɗan daki kafadarsa.


Ni kuwa idanu kawai ya zuba min yana min kallon da na kasa fassara shi kafin a hankali ya furta "take very good care of yourself" nima don ina kallonsa yasa na fahci abin da ya faɗa.


Sai da ya shige kafin muka shiga Mota jikin kowa a sanyayae na kewar sa da muka fara tun yanzu musamman Aunty Kalisat, wurin aikin da ban samu zuwa ba muka koma gida sabo da Aunty Kalisat da naga tana cikin damuwa kawai tana dannewa ne, kafin mu isa zazzaɓi ya rufeta.....




Fatan alkairi daga 


 *OUMbFATIMA*