MAI KWAƊAYI

62

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

``` NAFISAT ALIYU SASAAL```



 ```Page 62```


_______Da ire-iren waɗannan tunanin Maysarah ya zaɓi barin Halima a gidan Iyayen Naseer don tasamu hutu da kyau.


A ranar yabar garin da suke batare da yaƙara komawa wajen Halima ba,don matsawar yaganta bazai iya tafiya ya barta ba.


 Ƙarin Ruwa da magani,Dr.Ateekaa tayiwa Halimah,tare da Bayanin da zai taimaka mata wajen kula da jurewa buƙatun Mijinta.



A waya Maysarah yayiwa Dr.Ateekaa bayanin zai turo a ɗauki Halima.



 Halima tayi mamakin ganin Matar Naseer tazo ɗaukarta,ba don ranta ya so ba ta bita. Gidan Iyayen Naseer ta wuce da ita.


Kamar zasu goya Halima haka suke ta nan nan da ita. Mahaifin Naseer Ghanian ne kuma yana ɗaya daga cikin waɗan da suka hidimtawa ma'aikatar Maysarah kafin yasamu Matsalar kafar daya roƙi Maysarah ya taimaka ya maye gurbin shi da Naseer ɗanshi. Mahaifiyar su Russian ce amma ta jima da rasuwa sai Matar Mahaifin shi ƴar asalin ƙabilar Kanurin Nigeria,itama ta na da ƴar ta ɗaya wanda sam bata kama Naseer.


Surutun Lili ƙanwar Naseer har hawa kan Halima yakeyi. A bakinta takejin duk gidajen da suke ciki na Maysarah ne,da surutan abubuwan da sam Halima ba gane su takeyi ba, saboda ta kira Number Maysarah bata samun shi.


Kuka sosai Halima ta sa mu su, ta mirje idanuwanta sai an kaita wajen Mijinta,ƙuruciya da tsananin son Mijinta da take yi ya hanata yin kara da alkunya.


Dole Aunty(matar mahaifin Naseer) ta yanke shawarar neman Dr.Ateekaa har Asibitin su,tun da Number Maysarah dana Naseer dukka baya zuwa.


Bayani sosai Dr.Ateekaa tayiwa Aunty da irin taimakon daya kamata su yiwa Halima idan da hali.


Daƙyar Aunty da Lili suka lallashi Halima taci abinci. 


Kai tsaye zarginta kan Likita ya tafi,dole ita ta gayawa Maysarah abinda ta gayama mata.


Tayi kuka, ta kirashi sau babu adadi amma takasa samunshi kuma last seen ɗin shi kwana ɗaya daya wuce ne,Voice note ɗin kuka da magiya da roƙon ya dawo takasa barci ta turamai, amma har Ɓarawon Barcin gajiyar da ya jima yana tara ma ta ya ɗauketa bai kunna Data shi ba.


Sai ukun dare ya kunna Data shi yana gyara kwanciyar da sam baya mishi daɗi.Voice note ɗinta ya shiga ya fara sauraren roƙo da Magiyar da takemai. Jajayen Idanuwanshi ya lumshe,mayen sonta da tsananin son kasancewa da ita na neman kwance mishi kai. Ya sani zatayi kuka maiyawa da ƙewarshi,amma dole tana buƙatar hutu domin lafiyarta. Sai bayan sallar Asubahi barci wahala ya ɗaukeshi cike da mafarkanta.


★Cikin dabara Aunty tafara hidimar gyara Halima washe garin zuwanta. Duk da taƙi sakin jiki da su tana ɗaki.


Tsoro da fargaban ganin ya shiga saƙonta kuma bai mata reply ba yasa zazzaɓi ya rufeta,shikenan dagaske rabuwa zai yi da ita tunda dama Dr.Ateekaa tace matsalarta zai iya raba aure.


Daƙyar Aunty ta lallasheta suka fita cin abinci ita da Lili.


Ko Aunty Maysarah bai kira ba ya toshe duk wani hanya dayasan zai iyajin halin da Halima take ci,don bazai juri jin halin da take ciki batare da yaje inda take ba.


Kwanan shi biyu a Texas ya nufi Nigeria wajen Goggo,saboda jikinta daya ƙara birkicewa bayan ta dawowarta bataga Halima ba.


Duk ya faɗa saboda ƙewar Iyalinshi dake ɗawaniya da shi.


🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂


Goggo birkice mu su tayi sama da yanda suke tunani, sai da ta tashi hankalin kowa kamar batasan su ba,don bata raba ɗayan biyu sune suka korar mata Halima,har Mom Fahima sai da Goggo ta tada ɓallacin sai ta bar gidan tunda baya cikin gadonta. Gaba ɗaya jikin ahalin sai yayi sanyi,banda Shamsiyya da likitan dayake dubata bata bari kowa ya shigo inda take.


A wannan halin Maysarah yayi mu su dirar mikiya.


Goggo takasa motsi saboda jininta dake neman ƙara hawa,me zata cewa Maysarah?Matarshi ta ɓata idan har dagaske ya mayar da ita,gaba ɗaya sai ta kasa nuna farin cikin ganinshi sai kukan da ta ɓarke da shi.


Zuwa dare babu wanda bai halarta a ɓangaren Goggo ba,idanuwan kowannen su a kanshi musamman na Yusrah da takejin kamar ta haɗiyeshi. Canji komai na shi ta ɓangaren Halittar jiki a bayyane yake,kamammiyar fuskarshi na nan bai canza ba sai ƙaruwa dayayi.

Muryar Uncle Ghali cike da rauni yake neman yafiyar Maysarah akan abubuwan da suka faru,Mommyn su Mubeena kamar ta shaƙe shi,saboda takaici ƙiyayyar da ya nunawa ƴar su.

Kamar daga sama kowa dake wajen yaji furucinta na"Maysarah ka fitar damu daga cikin duhun da Goggo ta samu na ka mayar da Matar da ka saka kafin ta gaji da zama ta gudu,menene gaskiya?" Ta faɗa kanta tsaye saboda kishin dake cin zuciyarta.

Kallon dayake mata da dukka girman Idanuwanshi ne yasa duk girman Living room ɗin yayi tsit zuciyar kowannen su na bugawa, ita kanta sai a lokacin ta gane shirmen da ta tafka.

"Dama Goggo na ƙarya ne?" Ya tambayeta da Husky voice ɗin shi Lion face ɗin shi na ƙara komawa abin tsoro.

Jikinta Mommyn Mubeena da masu irin burinta na cewar dagaske ya saki Halima duk yayi sanyi sai zuciyoyin su dake bugawa kamar za su fito.


Kuka Goggo tasa jikin tsufarta na rawa,tare da fara roƙon Maysarah gafarar ɓatan Halima daya hanata sukuni.


Shamsiyya dake bakin ƙofa tuntuni tausayin Goggo ne yakamata,kuma kullum da tunanin a wani hali Halima take, take kwana tana tashi. Jikinta na rawa ta shiga Parlon a kusa da Goggo taje ta tsugunna,hakan da tayi ne yajawo hankalin kowa kanta. Da murya kuka da kuma ƙarfin Muryar da kowa zai jita take bayani tun daga cin Mutuncin da Faisal yayiwa Halima a wajen shan Ice cream har marukan da Uncle Suraj ya zuba mata sanda Goggo take rashin lafiya,da dalilin tafiyar Halima.


Uncle Suraj bai taɓajin kunya ba a rayuwarshi ba kamar ranar haka Faisal,da Mahaifiyarshi.


Salati da sallallami Goggo tasa,ta na miƙewa tsaye,korar su ta hau, da ƙananun duka da dukka hannayenta,jikinta na rawa,riƙota Maysarah yayi ya rungumeta amma duk da haka ƙoƙarin barin jikinshi takeyi. A haka duk suka suɗaɗe suka gudu.


A daren ranar Shamsiyya ta haɗa kayanta batare da sanin kowaba ta bar gidan.


Sai da ya tabbatar barci ya ɗauketa sannan yabar sashen da takunshi kamar zai huda ƙasa. Bazai dai na nanata girman soyayyar Halima da tausayinta a ranshi. Labarin Shamsiyya kamar famin miki ne na ciwon dake cikin zuciyarshi,kamar yanda suka kashe mai Mahaifi da ɓakin cikin su,suna so su ƙara kashe mai Matar da zame mai sanyi idaniyarshi,kenan da bazai ƙara ganin Halima ba. Tuna hakan yasa zafin zuciyarshi ya ƙaru ƙewarta na bijiromishi ta ko ina.


A daddafe yayi wanka ya kwanta a ɗakin da har lokacin bai daina ƙamshin ta ba.


Kai tsaye layinta ya kira yana rage girman idanuwanshi da suke jajir.


Har yayi kira bakwai bata ɗauka ba,gaba ɗaya sai hankalinshi ya tashi.

Duk da dare ne sosai acan layin Aunty ya kira, kiran farko ta ɗaga. Ko cikakken gaisawa ba suyi ba ta fara bashi haƙurin rashin sanar dashi ciwon Halima saboda kar Hankalinshi ya tashi ne,don duk a tunaninta a wajen Naseer da ɗazun yazo yaga halin da take ciki yaji labari.


Alfarma takaiwa Halima wayan ya roƙa.

Har lokacin Halima batayi barci ba, ta kira dukka layukanshi da ta sani amma baya zuwa,don haka tasa wayan tasa wayan a silent ta cigaba da kukan data saba.


Taji shigowar Mutum amma bata motsaba,sai da Aunty tayi magana.

"Halima jikinne"Aunty ta faɗa da tausayinta, tana ƙoƙarin kiran layin Maysarah.

Miƙewa tayi ta zauna daƙyar duk ta rame gwanin tausayi.


"Ga Mijinki Halima zakuyi magana" da sauri ta miƙe garin saukowa har faɗuwa tayi,"Halima kibi a hankali karkiji ciwo"

Hannunta na rawa ta karɓi wayan itama Aunty sai ta juya tabar ɗakin.

Kafin yayi magana ta riga shi.

"Shine ka gudu ko🥹?ka daina sona ko🥹? Bana iyacin abinci,bana iyayin barci, ka dawo kaji🥹 kadaina guduwa kana barina banaso"ta faɗa cikin kuka.


Muryarshi har rawa yake yi wajen kiran "Halimahhhta 🥹".....✍🏻