63
💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔
( shi ya san gidan mai rowa)
```By```
``` NAFISAT ALIYU SASAAL```
```Page 63```
________Ba ta amsa mai ba sai ajiyar zuciyar da ta sauke." Karki ƙarayin kuka kinji". Still batayi magana ba. "Yaushe kikeso na dawo" dasauri tace"yanzu" ta faɗa ta na ƙara sauke ajiyar zuciya.
Murmushin da bai shiryawa ba ne ya ƙwace mai" yanzu fa Halimata,to ai dare ne,ki zaɓa amma banda yanzu da gobe" tana jin haka taƙara fashewa da kukan ita dai yanzu takeso ya dawo,wayo yakeson yi mata. "Gobe zanje wajen Inna na taho da ƙanin Mom ɗinki kinaso" Shiru tayi bata ba shi amsa ba.
"To nafasa gobe da yamma zan taho,shikenan?"
"A'a yanzu nakeso ko gobe da safe,amma yamma yayi nisa".
"Okay naji"ya faɗa yana kulle Idanuwanshi.
"Promise me"
"Halimahh,kinason kashe ni ko"
Murmushi tayi mai sauti,duk lokacin da ta dameshi da ƙorafi da wannan kalmar yake amfani wajen yaudararta ta haƙura.
"Wayo kakeson yimin,nasan bazaka mutu ka barni ba ko?"
Shima murmushin yayi yana sumbatar wayan yanda zataji shi dakyau.
"Kiyi barci Halimahhhta,kuma ki ci abinci if not bazan dawo ba"ya faɗa kamar mai raɗa.
Kukan lalacinda da tasan girman illa dayake mashi bazatayi ba tasamai.
"Ohh Halimahta shikenan kin kasheni" ya faɗa da irin muryarta.
Dariyar nishaɗi ta kyalkyale da shi.
Sai da ya tabbatar barcin daya sata yayi nauyi sannan ya katse kiran ya ƙara yin wanka,barci nutsuwar zuciyan da ya samu ne ya ɗauke shi.
★washe gari sai da ya kirata Video call tayi Breakfast yana kallonta da idanuwanshi da suke a lumshe kamar za su cinyeta,ya tafi duba jikin Goggo.
Jikin Goggo da sauƙi sosai,a ɗan hirar da suka taɓa yayi kuskuren ambaton Halimata yafi sau biyar.
"Maysarah Halima tana wajenka" Goggo ta faɗa kai tsaye ta na kallon cikin Idanuwanshi.
Ƙeyarshi ya sosa yana ƙara ɗaure fuskarshi,sai yayi kamar bai ji abinda ta faɗa ba.
Dariyar nishaɗi Goggo ta sa tana rangaɗa guɗar dayasashi miƙewa yana yi mata sallama da ɓoyayyen murmushin da ya kasa riƙewa.
"Wallahi Halima zata dawo ta sameni,Alhaji Maysarah kenan,ko da nace irin wannan ƙiba da fari haka,zo kabani labari,ta kusa haihuwa?"
Goggo ta faɗa cikin nishaɗin daya gusar da duk wani nauyi da ƙunci dake cikin zuciyarta.
"Ki na ciwo amma bazaki canza ba". Ya faɗa yana barin sashen,saboda kunyar da Goggo take neman tara mai.
Kai tsaye Shamsiyya ya fara nema kafin ya bar gidan,amma ba bu ita alamu sun nuna tun daren jiya ta bar gidan.
Har ƙauyen su Inna Maysarah yaje ya yi mata bayanin yana buƙatar Babangida,saboda sai ya samu gogewa da kyau zai iya maye gurbin shi da Uncle Ghali.
Yara da Matan aure ƙauyen sai leƙe sukeyi da ga cikin gidajen su wasu kuma sun kasa tsayawa daga cikin gida sun fito waje. Don ganin Mijin daya siye Halima ƴar Halime,a cewar su
Babangida yayi kukan farin ciki saboda tun kammala karatunshi ba shi da wani ƙwaƙwaran aiki,aure sama da biyar yaje nema amma ƴan baƙin cikin gidan su na rusa shi. Alfarma tafiya tare da Inna Babangida ya nema kuma a take ya yarjemai da bazatan gidan zama,wanda ko bai gani ba yasan na masu kuɗi ne.
Lokacin da Maysarah yaje gaishe da Baba Isiyaku yayi kuka mara iyaka mutanen ƙauye na ta sabbarka ma su hassada kuwa kamar su kashe kan su. Da iyakacin Motocin da Maysarah yashiga ƙauyen da su ya isa ya kumbura zuciyar duk wani Maƙiyin Halimarshi balle kyawun halittar shi mai birgewa.
★washe garin ranar ya bar ƙasar saboda tuni Goggo ta warware kamar batayi ciwo ba saboda gaisawarta da Halima ta Video call ɗin da taƙi yarda daga Goggo har Inna su ga Fuskarta.
Uncle Ghali gaba ɗaya jikinshi sanyi ya ƙarayi nadama na bijiromai ta ko ina. Nasiha da ban bakin da iyalanshi ba su sanshi da shi ba yayi musu,har sai da jikin kowannen su yayi sanyi,har Mahaifiyar su Mubeena.
"Na fi shekaru talatin ina ƙasƙantar da kaina duk don nasamu damar morar arziƙin Abdulnaseer da Maysarah dakyau,amma Allah ya rusa duk wani shirina a cikin kwana ɗaya kacal. wannan babban karatune da kowannen ku ya kamata ya ɗauka".ya faɗa takaicin yanda Abdulnaseer ya mutu da baƙin cikin shi na dawo mai.
Yusrah da Mubeena da su ne suka rage a Mata basuyi aure ba ya basu umarnin fitar da mijin aure,da Salim da shima shine ya rage a Maza.
Uncle Suraj zuciyarshi kamar a na barbaɗa yaji mai zafin gaske haka yakeji,ita dai Mahaifiyar su Faisal takaicin abinda Faisal da Mahaifinshi su ka aikata yasa ta keɓance kanta daga kallon ko da fuskokin su ne.
A washe garin rana rantsatsun convoy ɗin da Maryam take fita da su suka kawowa gidan ziyara.
Kaya ma su manya kuɗi tayi ado da su kamar ɗawisu,amma idanuwanta kamar gauta ta cikin baƙin gilashin da tayi ado da shi.
A yanayin da tasamu Iyayenta ba kamar yanda ta san su ma'abota hira ba,sai jikinta yayi sanyi.
Fara'ar dole kowannen su ya ƙaƙalo suna yimata Barka da zuwa.
" Tun yaushe ku ka shigo Abuja?" Uncle Suraj ya tambaya yana kallon idanuwanta.
"Tun jiya" ta faɗa muryarta na rawa,kamar maison fashewa da kuka.
"Lafiyarki kuwa Maryam" Mommyn su da ta kasa jurewa ta tambaya.
"Mommy Daddy don Allah ku taimaki rayuwata ku raba auren nan na roƙe ku" ta faɗa da tsanin kukan baƙin cikin dake ranta.
"Raba aure? Baki da hankali ne Maryam,for what reason?
"Daddy tunda mukayi aure ta gaba da baya yake saduwa dani,nagaji Daddy dan Allah ka taimake ni"
"Maryam Ni zaki kunyata,kamar yanda wancan mahaukacin ya kunya ta mu,ya ɓata mana zuri'a da jinin talauci,to ki sani aurenki shine alfahari na, kuma shine taƙamar duk wani manyan kuɗaɗe da suke shigomin. Ba ta gaba da baya ba, ko ta inane kije kiyi haƙuri wata rana zai daina,don wallahi da aurenki ya mutu gara acemin ke ce kika mutu. Nonsense kawai!!"ya faɗa kamar zai yi Ball da ita yana miƙewa don barin parlon.
" Haba tayaya zakace haka bayan kasan tarin zunubi da illar dake cikin haka,sai yaushe kwaɗayin abun wani zai bar zuƙatan ku, gaskiya ban yarda Maryam ta zaunawa irin wannan auren ba" Mommyn su Faisal ta faɗa da tsananin kukan tausayin ƴarta.
" Ki ka ce kwaɗayi, akwai kwaɗayayyen irin ubanki,na zane ki,na kusanceki a ƙasƙance kuma a yanda naga dama,amma saboda kwaɗayin dukiyar da ba nawa ba na ɗan uwanane, ubanki ya koroki saboda ina ba shi na goro,duk wannan azabar na tsahon shekaru haka kika jure kinayimin addu'a yanzu ga ba shi nadaina ba, wallahi na rantse bazanyi kaffaraba indai kikasa Maryam ta kashe aurenta na rasa dukka contract ɗin da zasu bani,sai na wulaƙantaki,kema ai kwaɗayin ne ya zaunar dake har zuwa yau, sha-sha kawai" ya ƙarasa faɗa da jan tsakin da kamar zai tsinka harshen shi.
Durƙushe ƙasa tayi kusa da ƴarta kuka mai raɗaɗi da ciwo na zuwar mata,Maryam itama kukan takeyi kamar zata haɗiyi ranta.
Shima Faisal ɓangarenshi ba sauƙi don Matarshi manyan ƙwayoyi takesha,shima wa su lokutan ta samishi a lemo,haka zai yi ta saduwa da ita,tun yanada ƙarfi har sai ƙarfinshi yaƙare wannan dalilin yasa yayi wani rama kamar ba shi ba. Amma a haka jama'a dayawa idan suka kalli kyawun Halittar shi da gibgegen abin hawarshi sai suyi ta addu'ar ina ma sune.
A haka Maryam ta koma masauƙin su,ranta fal zullumin zuwan dare.
Inna da Babangida sun sauka a Abuja a cikin gidan da ya tafi da nutsuwar su saboda kyawunshi. Duk lokacin da wata ni'ima da sukunin rayuwa yazowa Inna sai ta tuna Halimenta mai burin yin rayuwa maikyau da ilimi mai zurfi🥹.
Gaba ɗaya ya matsu yajishi a jikin Halimarshi,yayi ƙewarta mara adadi.
Itama a nata ɓangaren ta matsu da dawowarshi.
Wani irin kyau mai birgewa Halima tayi saboda gyara da cikakken hutun da ta samu na kwana biyu.
Naseer da Lili ne suka kaita gida bayan tsiyar da ta a wajen Aunty,itama sai a lokacin takejin kunyar wa su maganganun na ta.
Bayan tafiyar su kimtsa ko ina tayi taƙarayin wanka tana jiran Mijinta.
Har ɓarawon barci ya ɗauke Halimah Maysarah bai shigo ba.
Iskar baƙinshi mai sanyi ƙamshine ya tasheta tanayin ido huɗu da ita ta miƙe da tsananin murnarta ta ƙanƙameshi.
Lumshe sexy eyes ɗin shi yayi Finally yau ga shi ga Halimarshi.
"Babu sannu da zuwa ko" ya faɗa a cikin kunnenta.....✍🏻