HAJAR

{65..}

by @feenerhfeeche


Saura ƙiris motar ta kwasheta amma duk da haka saida ta gogeta, wata iriyar hantsilawa tayi ta faɗi ƙasan kwalta, ta dauje a duka guiwoyinta da tafin hannu, da sauri Nurain ya ƙaraso inda take, damtsenta ya riƙo ya ɗagata kamar ƴar kaza, ba karamin tashi hankalinsa yayi ba kuma har lokacin kansa bai dena sarawa ba, tin daga sama har ƙasa ya ringa kallonta fuskarsa a matuƙar murtuke, sakinta yayi kafin yasa bayan hannu ya falla mata mari, bata gama dawowa hayyacinta ba ya sake mangareta, saida Hajar taga stars tsabar gigicewa, ta fashe da matsanancin kuka a gigice tace "na shiga uku", wata tsawa da ya daka mata saida ta koma ta zube a ƙasa sbd yadda ƴan hanjinta suka juya, with stern voice yace "you must be mad, wawuya kawai..", a lokacin drivern motar da ya samu ya tsayar da motar far away from them ya ƙaraso inda suke da ɗan gudu gudu, kana ganinsa kasan ƙuruciya ke ɗebansa don bazai wuce 25yrs ba, duƙawa yayi gaban Hajar dake rusa kuka kamar ranta zai fita yace "am sorry", Nurain ya figi hannunta ya miƙar da ita, sosai ta firgita ta sake fashewa da kuka, young man din yace "should I take her to the hospital...?", a taƙaice Nurain yace "no need" da haka ya ja hannunta suka bar wajen tana rusa kuka, a haka yana figarta har suka koma cikin hotel din, direct elevator suka shiga bayan sun wuce reception, har lokacin Hajar bata dena kuka ba, suna isa room dinsu ya wani wancakalar da ita a kan carpet, da sauri da haɗe kanta da guiwarta da take jin tana mata zugi, ya zauna kan couch ya dafe kansa, ynxu idan da motar nan ta bigeta fa sai yadda Allah yayi, ya ɗago kansa ya kalleta zuciyarsa na ƙuna, slight hiss yayi ya tashi ya shiga bathroom yayo alwala, bayan yayi sallah after taking his bath ya saka pajamas, making coffee yayi ya zauna kan couch, ajiye mug din hannunsa yayi kafin ya kalli inda take, har lokacin kanta haɗe yake da guiwa tana shessheƙa a hankali, ya taɓe baki yace "ke!!", ko motsi ba tayi ba bare ta amsa, ya ɗan daga murya yace "ke!", ta ɗago jar fuskarta ba tare da ta dubesa ba, ya haɗe gira yace "tashi kije ki cire wnn black kayan sai kace a palace din sheɗanu", ba musu ta tashi tana jan ƙafa ta janyo box din kayanta, wata soft sleeping gown ta ɗauka ta shige bathroom zuciyarta tamkar za tay bindiga, yabi bayanta da kallo kafin ya ɗauki mug din coffee ya fara sipping wnda daman haɗasa yayi don ya rage masa takaici, ba ƙaramin ɓata masa rai Silly girl tayi ba, sai kace wacca kwai ya fashewa a ciki haka ta fito daga toilet din, a hankali ta zauna gefen gado after few minutes ta kwanta ta rufe da duvet, babu abinda take hangowa sai irin stars din da ta gani, Nurain na gama shanye coffee ya juya ya kalli gado, lokaci guda ya miƙe ya isa bakin gadon, kallonta ya ringa yi kafin ya zauna gefenta, Hajar ta rintse idonta don ba bacci take ba, duvet din da ta rufe ya yaye, bata motsa ba duk da hakan yazo mata unexpected, tin daga ƙafarta zuwa knees dinta da suke a bayyane ya ringa kallo, ya lura da bruises din dake guiwoyinta, a hankali ya kai dubansa kan hannayenta, bai ga ciwo a hannun ba, ya janyo hannun da ta danne yana dubasa shima, a palm yaga taji ciwo, in banda bugu bbu abinda zuciyarta take, me yasa yake taɓata wai, wani azabar tsoronsa take ji shiyasa taƙi motsi, ya ringa kallon fuskarta musamman ma soft cheeks dinta da ya hango zanen yatsunsa uku, wajen yayi jajur, shiyasa ya saka mata bayan hannu idan da front ya saka mata tsaf zai fitar mata da haƙori, ya kasa withstanding abinda ta aikata ne, the girl is so stubborn, ji tayi ya dafa forehead dinta sai kuma ya tuge mayafin da ta rufe gashinta, tini ta buɗe idonta ta miƙe zaune, tashin da tayi bai hanasa cigaba da duba jikinta da yake ba, hakan ne ma yasa ya fara ƙoƙarin ɗaga ƴar rigarta don ya duba inda rigar ta rufe, wata gigitacciyar ƙara ta fasa ta fara ture hannunsa, ganin ko gezau so yake fa ya ɗaga rigar nan sai ta fara kokawa, haɗe gira yayi ya rutsa hannayen nata da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma ya ɗage rigar yana ƙarewa fresh bodyn ta kallo, ƙoƙarin sauka ta fara daga kan gadon ya hanata don katamau ya riƙe ƴar farka, ai kam ta rushe da kuka jikinta har na rawa tace "wayyo Allahna na shiga uku, dan girman Allah ka dena taɓani, Ummata...", sakinta yayi bayan ya tabbatar bbu ciwo a jikin, da sauri taja rigar ta rufe jikinta tana zaro ido, tashi yayi ya shiga bathroom ya fito da kwalbar Dettol, kwalin tissue dake ajiye kan table ya dauka snn ya koma gefen gado ya zauna, Hajar ta muskuta baya tana turo baki, sam bata bari sun haɗa ido ba, haka nan ya goge mata bruises din da taji a hannu da knees da ruwan dettol, tinda ya zare mata ido ta tsaya bbu wani noƙe noƙe, ya mayar da kwalbar Dettol din bathroom ya fito ya rage hasken ɗakin ya hau couch ya kwanta, wajen ƙarfe ɗaya ya farka, zaune ya miƙe ya ringa massaging neck dinsa da ya riƙe, yafi minti biyar yana massaging neck din, ya juya yana kallon gado, can gefen gadon yaga Hajar tabar space sosai, ya murza sleepy eyes dinsa ya tashi ya koma kan gadon, ya kwanta a other side din gadon ya juya mata baya, da asuba Nurain ya farka yaga Hajar daf dashi sai kace yayi cuddling dinta, kanta bisa hannunsa, sauke sleepy eyes dinsa yayi kan innocent face ɗinta, baccinta take peacefully, ya gyara kwanciyarsa getting even more closer to her, kallon fuskarta yake without blinking musamman cheek dinta, a bazata ya kai other hand dinsa ya shafa cheek din nata, tin daga ƙololuwar kai yaji tamkar ana masa ruwan allurai, yayi ajiyar zuciya a hankali ya zame hannunsa da ta danne making sure bai tasheta ba, ya miƙe daga kan gadon ya nufi bathroom yana ciccilla hannunsa da ta kwanta a kai alamar dai ta daɗe akansa, sai takwas saura Hajar ta farka, tana sauka kan gado ta gansa zaune kan couch already well dressed up yana latsa wayarsa, bata masa second look ba tayi wucewarta ta shiga bathroom, yana ganin haka ya tashi ya bar mata ɗakin, har ta fito wanka ta shirya a tsanake snn ya dawo, ledar takeaway dake kan fridge ya nuna mata yace "ga breakfast", shiru tayi masa ba tace komai ba, ya daka mata tsawa yace "ba kiji me nace ba..?", ta sunkuyar da kanta tana wasa da fingers dinta tace "toh", murya ƙasan maƙoshi yace "Silly girl", kaɗan taci abincin ta ture, yana latsa wayarsa ba tare da ya dubeta ba yace "kin gama haɗa komai naki..?", gudun kar ya sake mata tsawa ta gyaɗa kai tace "Eh", fita yayi bayan minti biyar ya dawo tare da wnda zai fitar musu da kayansu don already bolt na waje tana jira, Hajar na ganin an fita da box dinta taji wani daɗi har cikin ranta, Nurain ya nufi door ya murɗa handle, juyowa yayi yana kallon Hajar da take saka takalminta, tana ɗago kanta sukay ido huɗu, tayi sauri ta saukar da kanta, dawowa yayi ya tsaya gabanta, jin scent dinsa ta ɗaga kanta, a hankali ya kai hannu ya shafa cheek dinta yace "ba kya jin magana..", da sauri taja baya tana juya lulu eyes dinta, ya sauke numfashi yace "wuce muje..", ƙofa ta nufa da sauri yabi bayanta, saida ya rufe ɗakin snn suka shiga Elevator tare zuwa ƙasa, Nurain ya dakata a reception domin checking out ya ajiye key kuma, receptionist ya duba Keycard din ganin numbern room dake jiki ya dakatar da Nurain, wata leda ya ɗakko ya miƙa masa yace "perhaps is this yours..?", Nurain ya ringa kallon ledar snn ya amsa yace "yess", ledar da matar Hammad ta bawa Hajar ce. before 9:50 suka isa Airport don jirgin 10 zasu shiga, Hajar dai na fahimtar wajen ta haɗe rai, tunowa da wahalar da tasha a jirgi tayi, saida suka shiga filin jirji ta ɗan kallesa tace "dan Allah dama mota muka hau", yace "ba nida lokacin tafiya daga Abuja zuwa kano a mota..", bata sake ce masa komai ba har suka hau jirgi, kamar lokacin da suka zo tafiyar ma ga seat dinsa ga nata, tinda suka shiga jirgin take addu'a a ranta, ai kam taci sa'a lokacin da jirgi yayi takeoff ba taji kamar yadda taji da zasu zo ba, da suka isa ma wajen landing yazo mata da sauƙi, suna fitowa Nurain ya amshi motarsa suka bar airport din, sha ɗaya da minti goma Nurain yayi horn a gate din gidansa, tini mai gadi ya buɗe gate, bayan Nurain yayi parking a parking space ya fito daga motar yana amsa sannu da zuwan da Inuwa ke masa, har bakin balcony Inuwa ya kai musu kayansu, Hajar dai na tsaye bakin ƙofa tana jiran ya buɗe mata ta shiga, deep inside her mind taji daɗi da ta ganta a gida, yana buɗe main door ta kai hannu zata ja box dinta kawai taga ya ɗauka ya shiga da ita, bayansa tabi zuwa palour taga ya haura upstairs, slowly ta fara tafiya ta haura saman itama, a bakin ƙofar ɗakinta taga ya ajiye box din, ta buɗe ɗakin taja box din ta shiga ta mayar da ƙofar ta rufe. sai wajen 4 ta sauka downstairs ta shiga kitchen ta nemawa kanta abinda za taci, plain Noodles ta dafa da boiled egg ta ci a kitchen din snn ta wanke komai da tayi amfani dashi, tinda ta koma room dinta bata sake sakkowa ba, ƙarfe tara na dare tayi wanka abinta ta saka kayan bacci, pillow da duvet ta ɗauka tayi kwanciyarta kan carpet, ko minti biyu ba tayi da kwanciya ba aka turo ƙofar ɗakin, waya ce kare a kunnensa yana sake dialing numbern Mami wacca suna cikin waya network ya yanke, bai samu Mami ba don hka ya sauke wayar daga kunnensa yana kallon Hajar, with a repartee yace "ke!! tashi daga ƙasan nan", ta miƙe zaune tana turo baki tace "ni nafi son nan..", ware ido yayi yace "what..?, magana kike min..?", ta shiga girgiza kai sai kuma ta miƙe ta koma kan gado ta kwanta, yace "daga yau kar na sake ganin wani soul ya kwanta kan carpet..", sai kace yana kallonta haka ta shiga bunka masa harara tamkar sabuwar kamu, ya juya ya bar ɗakin bayan ya kashe mata fitila. washe gari da Hajar ta farka abinda ta farayi shine wanka biyu snn ta haɗa da wankin hair dinta tinda ta jiƙasa, nannaɗe gashin tayi da towel ta fito, bayan ta gama rubbing lotion a fatarta ta fitar da kayan da zata saka riga da skirt na atampa, tana gama oiling gashinta ta ɗauki kayan zata saka, zip din riga dai da kyar ya zugu, da tazo saka skirt shi kam zip dinsa bai zugu ba, sakin baki tayi tana kallon kanta a mirror, though ita ɗin ba mai jiki bace don ko chubby ba ta kai ba, amma kuma duk wasu point da yake fitar da kyan mace a jiki toh nata aciki suke dam dam, haƙura tayi da saka riga da skirt din ta saka doguwar riga A-line ta feshe jikinta da 3 different perfumes, tin daga room dinta ta fara shara har ta kai downstairs palour shima ta share ta kaɗe ƙura, bayan tayi mopping ta goge kayan kallo ta jona turaren wuta a burner, haba tini gida ya ɗau harami yana baza ƙamshi, kitchen ta shiga don samawa kanta breakfast, ƙarfe goma da rabi Nurain dake sanye cikin sweat pant da shirt sky blue ya sakko downstairs, ya ringa bin ko ina da kallo yana mamakin yadda yaga guri yayi fes fes, uwa uba kuma ƙamshin da yaji wnda a wajen Maminsa ya sansa, kitchen ya shiga, Hajar dake chopping onion ta ɗaga kai ta ɗan kallesa kafin ta ɗauke kanta ta cigaba da abinda take, sosai yajin albarsa da take yankawa ya addabi Nurain dake jiran coffee dinsa ya kammala, Hajar na ɗago kanta a karo na biyu ta lura da yadda yake micincina ido yana jan pointed nose dinsa, bata san lokacin da wata dariya ta kufce mata ba, ta sunkuyar da kanta tana cigaba da dariya, haɗe gira Nurain yayi lokaci guda ya kashe Coffee makern ya fita daga kitchen din don bazai iya withstanding yajin ba, yana fita kitchen din yayi wani kasalallen murmushi ya haura sama, semosa da meat pie wnda suka ji isasshen nama tayi, daman Hafsah ta koya mata yadda ake yin minced meat a blender, semosa biyu meat pie biyu ta soya ragowar kuma ta ajiye cikin fridge, daga nan ta tafasa black tea mai kayan ƙamshi ta zuba sugar ta fita. bayan Hajar ta idar da sallar azahar ta tuna da wayar da ya bata, box din da ta mayar wardrobe ta dakko, already tin jiya ta kwashe kayanta wayar ce kawai bata dauka ba, ƙaramin zip ta bude ta ciro wayar da charger dinta, ba tayi wata wata ba ta cire sim dinta na cikin wayarta da ta lallace ta ɗora kan wayar, amma dai bata cire na kai ba tinda wayar ba dual bace, numbern Hafsah ta nemo tayi dialing, bata daɗe tana ringing ba tayi picking, bayan sun gaisa Hajar tace "yasu Antyna..?", Hafsah tace "wllh lfy alhmdllh", Hajar tace "amma yaushe zaki zo Hafsah..?", Hafsah ta zaro ido tace "ranar da fel waya tayi gashi..", Hajar tace "ke dan Allah", Hafsah ta fashe da dariya tace "nifa na fadi hakan ne naji me zakice, wllh na ɗauka zaki rufeni da bala'i", Hajar tace "sbd ga jarababbiya dage sarkin faɗa ko..?", Hafsah tace "A'a ni bance ba..", Hajar tace "Toh yaushe zaki zo tare da Humairah..?", Hafsah tace "ina nan tafe karki samu damuwa", fira suka taɓa snn sukay sallama Hajar ta katse kiran, tashi Hajar tayi ta sauka downstairs ta shiga kitchen, store ta wuce ta ɗebo rice flour ta damasa a small bucket ta zuba yeast snn ta rufe da leda da kuma murfin to proof it, daga haka ta koma room dinta, ba ita ta sakko ba sai hudu da rabi bayan tayi sallahr la'asar da azkar da ta saba, tsaye tayi jikin kitchen island tana tunanin da mai zata haɗa abin, deep freezer ta bude ta ɗakko nama, saida ta bari naman ya saki snn ta shiga sarrafa pepper soup, wata daddaɗar aroma ce take tashi a kitchen din, pepper soup din na kan wuta ta ɗakko ƙullun da ta kwaɓa, har ya tashi fumm ya cika bucket din, babu ɓata lokacin ta fara soya sinasir din da tayi amfani da easy way of making it, ƙofar kitchen din taji an buɗe, ta juya sukay ido huɗu dashi, ƙarasowa yayi gaban gas din ya miƙa mata abinda ke hannunsa, ta tattare gira tana kallon hijab dinta da yake bata, amsa tayi tace "what for..?", gaba ɗaya hancinsa ya gama cika da ƙamshin abincin, yace "ki fito palour ku gaisa", yana gama fadin haka ya juya ya fita a kichen din, saida ta sauke wnda ke kan wuta ta kashe gas din snn ta fita, tare da Farooq ta gansa zaune a palourn, walking gently ta ƙarasa palourn ta zauna ta gaida Farooq, da fara'a ya amsa mata yace "how are you doing Amarya...?", Hajar ta saukar da kanta ta amsa a taƙaice, Nurain dai sai satar kallonta yake ya wani haɗe gira, after a while yace "kije ki cigaba da abinda kike" don even with hijab baiso ta zauna a nan din da dai da niqab ne is okay, kitchen ta koma within few minutes ta fito hannunta riƙe da tray na bottle water da drink, kan Centre table ta ajiye, Farooq yayi murmushi yace "thank you..", ba tace komai ba sai murmushi da tayi, Nurain ya haɗe gira yabi bayanta da kallo, Nurain yace "Amm kunyi waya da iron lady kam tinda suka tafi..?", Farooq yace "yeah vid call ma mukay da ita ta wayar Noor", Nurain ya shafa kansa yace "ohh i see", Farooq yace "Dr what exactly my problem is nifa har ynxu lower abdominal pain din nan bai barni ba..?", Nurain ya gyara zama yace "i think i told you... kayi aure kawai", Farooq ya haɗe gira yace "is a different casa malam, tin fa ina yaro wnn ciwon yake har akamin surgery.." jin an buɗe ƙofa yayi shiru, Hajar ce ta fito ta ajiye wani tray din mai ɗauke da two warmer da plates da kuma bowls, ta ajiye saman Centre table, Farooq yace "Ahh harda baƙin yamma..", murmushi tayi ba tace komai ba ta koma kitchen, da plate din nata abincin ta fito ta haura sama, Nurain ya bita da kallo sai kuma ya dubi Farooq yace "Am coming", bai jira cewarsa ba ya haura sama yana tsallake steps da bibbiyu, ƙofar ɗakinta ya buɗe, tana zaune kan carpet tana cin abinci, daga bakin ƙofa ya tsaya girarsa a haɗe yace "karki sake fitowa", ya rufe mata ƙofar, taɓe baki tayi ta cigaba da cin abincinta, tini Farooq ya baje harka ya fara ɗebar dabge, tin kafin Nurain ya ƙaraso palourn yake kallonsa ganin yadda ya tattare hannun riga yana shan pepper soup, Nurain ya zauna position dinsa yace "ynxu pain din ne ya dawo..?", Farooq yace "bari na gama karna ƙware gsky, your wife is a good cook kaji daɗinka dude...", Nurain yayi resting jikin kujera yana latsa wayarsa, bayan Farooq ya gama da pepper soup din da ya zuba yace "dude kai bazaka ci ba..?", Nurain yace "am not eating..", Farooq yace "Alright naka ai special ne, amma dai the food is yummy..", Nurain yace "stop exaggerating..", Farooq yace "am not wollah", Nurain bai sake cewa komai ba, kafin Magrib Farooq ya tashi tafiya bayan sun gama mgana da brother din nasa, Farooq yace "toh kiramin madam muyi sallama", Nurain ya nufi door yace "no need", Farooq yace "toh hka zan tafi without giving her anything, please ka kirata..", firr Nurain yaƙi kiranta sam, haka nan Farooq ya wuce amma yaso ya bawa Hajar kyauta. Nurain ya shigo palour bayan tafiyar Farooq, kallon abincin da Farooq ya rage yayi, lokaci guda ya matsa gaban center table din, spoon ya ɗauka ya buɗe warmer din pepper soup, ya ɗan ɗebi soup din ya kai baki, bari dai yaji me Farooq yaji yake zuba wnn zancen, ji yayi kunnensa ya tsira tamkar an caka masa allura, ya ɗauki tsoka daya ya saka a baki, ɗayar warmer din ya buɗe yaga wainar sinasir, yayi pinching sinasir din ya kai baki, kamar ydda ear dinsa ya tsira lokacin da ya sha soup hakama yayi this time around, ɗaukar warmers din yayi ya haura sama. washe gari Monday Nurain na isa hospital after 40mins ya shiga surgery, wani emergency patient aka kawo wnda yake buƙatar aiki cikin gaggawa, ya tsaye a position dinsa na head of the surgery, Ruqayyah ma na surgery room din tana miƙa instruments, kana ganinta kasan bata jin daɗi, Nurain yace "Artery forcep", yanata jira a basa amma shiru, ga bleeding Artery din da zaiyi clamping sai zuba take, maimakon ta basa Artery forcep saita basa Dissecting forcep shi da ba sutures zaiyi ba, Khaleel dake first assistant yace "A Nurse concentrate or you wanna be a quack", sai a lokacin Ruqayyah ta lura da abinda take miƙawa, da sauri ta mayar ta ajiye ta miƙa masa wnda ya buƙata, ana cigaba da surgery da minti 10 Ruqayyah tayi collapsing, da Nurse Jiddah aka ƙarasa surgeryn, Nurain ya zare hands gloves din hannunsa yayi disposing ya fita daga surgery room din, saida ya cire surgeon gown da soft Clog shoe da yayi surgery dasu snn ya fita gaba ɗaya, bayan Nurain ya koma office dinsa ya kira Khaleel a waya, tambayarsa yayi ina aka kai Ruqayyah, Khaleel yace "Amenity 5", Nurain yace "Ohk" kafin ya katse kiran, ajiyar zuciya yayi ya tashi ya bar office din, yana zuwa ƙofar ward din da Ruqayyah take ya murɗa handle din ya shiga, ya ƙarasa gaban bed din da take kwance yana kallonta, bakinta ya bushe kamar ƙanxo, idonta a rufe tana bacci, a wahale take ajiye numfashi, ya dubi Nurse Amina dake tare da ita yace "anyi checking BP dinta..?", Nurse Amina tace "yess Dr", yace "bring the Bp gauge..", Nurse Amina tace "Okay" da haka ta juya ta fita daga ward din, Nurain dai na tsaye gefen gadon, ji yayi an riƙe hannunsa, ya juya yana kallonta, idanunta sunyi jajir tana kallonsa a sanyaye, da kyar ta motsa lips dinta da suka bushe tace "Dearest".......✍️