KUKAN KURCIYA masu iya magana suka ce jawabi ne, kuma gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah, labari ne da ke ƙunshe da gwagwarmaya, soyayya, cin amana, rudin sheɗan da dai sauran su , ku dai ku biyo ni umaimah ado gaya don jin me ya ƙunsa?

Follow, share, like and comment please

by @umaimah2024

UKAN KURCIYA 






  Written and edited by 




  UMAIMAH ADO GAYA 

   

   

   

   

   

  To Aunty Khadija candy 

   

   

   

  Page 05 



   

   

  HASEEB: Zaune yake akan kujerar kusa da gadon da haseeya ke kwance ya zuba mata jajayen idanunsa ko kyafta su baya yi, Jira kawai yake yaga farkawar ta, ta farka da sanar dashi abnd likita ya fada ba gsky bane, to ma wai Taya Hakan zai zama gsky? Shi yasan haseeya tana matukar kaunar cikin nan ba ydd za'ai ace wai da kanta take akai mata injection din Abortion,

   

   

   

   

  Ya shafe fuskar sa da tafin hannunsa kafin ya harde su guri Daya ya Dora habarsa akai, 

   

   

   

   

  Turo kofar akai ba tare Daya jiyo ba ya amsa sallamar sai da yaji muryar mamansu haseeya na fadin sannu da kokari Haseeb ya Mai jikin? 

   

   

   

  Da sauri ya mike Yana fadin mama Ina wuni? Ya hanya? Murmushi tai tana fadin lpy lou Haseeb ya Mai jikin? Yana shafa kansa yace Mai jiki ga tanan dai da sauki, 

   

   

   

  To Allah ya sauwake Mai yake damun tane? Mama ta fada tana karasawa bakin gdon ganin Haseeb yai hanyar fita? 

   

   

   

  Shafa keyar sa yai yana fadin ammm..emmm dama...dama kawai Ina....dawowa ne sai ...sai na ganta a sume a daki tana zubar da jini....shine...shine shine likitan yace wai...wai...ta...tayi....

   

   

   

  Katse shi tai da fadin ya isa wnn kame kamen Haseeb na rasa sai yaushe ne zaka dauke ni uwa kabari sirikantakar Nan da ni, tunda Allah yasa Alhaji ya furta ya bar maka haseeya shiknn ka koma sirikin dole ko? Ka tuna nifa uwarka ce bana son wnn kunyar taka, Allah ya mayar da na aike Allah yasa moran can ne , 

   

   

   

   

  A zuciyar sa ya amsa da Ameen Yana ficewa dg dakin, yayin da mama ta raka shi da idanu tana fadin oh ni salamatu wnn yaro sai kace bafulatanin daji? 

   

   

   

   

   

   

  Sai da haseeya tai awanni uku kafin ta farko, nurse ce tazo ta duba ta ta shire mata drip kafin tace abata Abu Mai ruwa ta sha, mama da kanta ta tafi gd dmn hado mata abnd zata sha, a snn Haseeb ya samu ganawa da ita, 

   

   

   

   

  Kafe ta yai SANDA yake zaune a kujerar bakin gadon bayan ya gama tambayar ta jikin ta, tana kallon sa take fadin hubby lpy naga ka tsare ni da idanu? 

   

   

  Ckn kakkausar murya ya furta wane shegen likitan kika je ya Miki Allurar zubar da ciki? 

 

   

  Zaro idanu tai waje ckn firgici take fadin waye ya fada maka? Dan Allah Haseeb kayi hkr, 

   

   

   

   

  Sosai yaji zuciyar sa ta buga don da kawai barazana yake mata don ya gwada mgnr likitan Amma ba don ya yarda cewar haseeya zata iya zubar da cikin jikinta ba,

   

   

   

   

   

  Sosai ransa ya baci har bai san SANDA ya mike a fusace Yana fadin ynx kina nufin kina sane akai miki Allurar da zata zubar Miki da ciki haseeya? Ashe dama haseeya ba Sona kk ba tunda har zaki iya zubar min da gudan jini na, 

   

   

   

   

  KUKA haseeya ta fashe da shi tana fadin Dan Allah hubby kayi hkr wlh sharrin shedan ne Amma ai kasan Ina sanka km Ina son duk abnd ya shafe ka, 

   

   

   

  Kimin shiru ! Ya fada fusace kana ya a Dora da fadin , kin bani mamaki haseeya wlh bantaba tunanin shedanun kawayen ki zasu iya zigaki akan abnd Allah ya haramta km ki biye musu ba , Koda likita ya fada min kawai na jishi ne sai dai zuciya ta ta kasa daina tunanin mgnr Hakan yasa na tambaye ki da yakinin zaki karyata abnd ya fada Ashe kallon kitse nakewa rogo , ngd haseeya snn Ina son ki saurari hukuncin da zai biyo baya






   Yana gama fadan haka ya juya ya fice a fusace ckn kunar rai, bakin kofar GOPD suka bangaji juna da Wani, yanayin da yake na fusata yasanya shi juyowa a fusace Yana fadin who the hell..... Cak kalamansa suka tsaya sbd tozali da yayi da kyakkyawar fuskar ta ckn marairaita take fadin am sorry plz! Wlh Ina sauri ne banga tahowar ka ba, kada kai kawai yai ba tare da yace komai ba kowannensu ya juya ya cigaba da tafiya,






........


 

Nafeesat :





Dafe kanta tai Dake Sara mata tayi tana ambaton Allah, tbbs tasan tana kokarin tayar da hawan jinin ta da tunani, more especially tunanin wnn Dan rainin hnkln yayan name sake dinta, tsaki taja tana daukan wayar ta da tun dazu take vibrating ganin name sake ya sanya da sauri tai picking call din, 




Eh Ina office lafiya dai? Ta fada bayan ta saurari abnd feenat ta fada, tai Jim kafin tace okay am waiting for you, 



Sauke wayar tai tana fadin Allah yasa tare zasu zo, wait wait wait! Nafeesat Ina class din ki ne wai? Zuciyarta ta tuna mata, girgiza kai tai tana fadin bani da Wani class tun lkcn da..... Knock don da Kai ya tsayar Mata da tunanin ta ckn sanyin muryar ta ta furta yes come in, 






......



Lateefa : 



Rintse idanunta tai tana jiran saukar mari a fuskar ta, tsaye take abakin kofar falo bayan ta danna door bell zuciyarta na tsinkewa addu'a fal ranta kan cewar Allah yasa yayanta Yana school ko km bai farka ba, sai dai addu'ar ta Bata karbu ba sbd kwana yai a falo Yana jiran yaga ta inda zata bullo sai wajen 3: 50 am bacci yai awan gaba dashi, 




Shi da kansa Yana Bude kofar ckn hanzari dmn tunda ya farka around 6 pm bai Kara komawa ba, zuciyarsa ce ta matse lkcn da ya ganta dmn duk wnd yasan Dan maye Yana ganin ta yasan tbbs a buge take don har zuwa lkcn abnd ta sha bai gama sakin ta ba, daga hannu yai da niyar da bata KYAWAWAN Mari wnd shi kansa baisan adadin su ba sai dai me? 





Hannunsa ya tsayar dadin kumatun nata Yana ganin ydd ta rintse idanu tana jiran saukar hannunsa akan fuskar tata, sauke hannunsa yai yaja nata da karfi ya wurga ta kan kujerar ckn masifa yake furta uban me kk sha latifa? 





Firgita tai da ydd taga yayan nata ckn KUKA take fadin wlh Yaya bansan ansaka Wani Abu ba na dauka juice ne kawai, idanu ya sakar mata yana Jin Wani irin haushin iyayen su dmn yasan duk abnd latifa tai to tbbs da laifin su musamman ma mahaifiyar su, zama yai gefenta ya riko hannunta Yana share mata hawayen dake bin fuskar ta ckn sassanyar muryarsa ya ke fadin ya isa latifa, nasan baki taba yi ba shiyasa naki tsoron kar ace kawayen ki sun zigaki kin biye musu kema kin fara Shan kayan maye, 





Ki sani latifa duk wnd zai baka abnd zai gusar maka da hnkl to tbbs ba mai son ka bane, km duk abnd zaki sha dmn ya mantar Dake wata damuwar ki na Dan lkc ne amma ba na har abada ba snn zaki Bata rayuwar ki ne, don Allah latifa ki bar wayannn kawayen naki dmn kyautata rayuwar ki ta gaba, kinji kanwata? Kada Kai tai tana fadin in Allah ya yrd yayana ban sake ba ngd da fahimta ta,





Sorry for the absence Kun san banji dd bane ga page din ba yawa ku Kara hkr na Dan lkc 





UMAIMAH ADO GAYA 🧕