MAI KWAƊAYI

64

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

``` NAFISAT ALIYU SASAAL```



 ```Page 64```


________murmushi ta yi ta na ƙara ɓoye fuskarta a jikinshi."idan baki faɗa ba zan koma" ya faɗa don yaji abinda zata ce.

"Wallahi bazaka iya komawa ba, ni zakayiwa wayo, kai da kakeyin kuka a waya,saying Halimata zaki kashe ni ko?" Ta faɗa da kwaikwayon muryarshi.

Dariyar da bata taɓa ganin yayiba ya saki yana ƙoƙarin ɓanɓarota daga jikinshi, amma taƙi yarda saboda kunyar kalamanta da ya lulluɓeta,don sai bayan furtawarta ta gane shirmen da ta tafka.


"Ki bari naga bakin dayakeson yimin sharri,dama haka kika iya sharri,tukunna ma wa ya ma gayamiki haka Halimahta"ya faɗa still yana dariya haɗe da mamakin wayonta. Wato duk tana sane.


ƙin yarda tayi ya ga Fuskarta har ya haƙura.

Ajiyar zuciya ya sauke yana ƙara godewa Allah dayabashi Halimarshi a matsayin Matar aurenshi.


Juriya jajircewa shi Halimah ta aro a wannan dare,ta kuma yarda Mijinta na tsananin sonta da ƙaunarta,ta kuma sake zana mishi sunanta a ƙwalkwalwarshi,zuciyarshi,da ma harshen shi.


★washe garin bayan sunyi Breakfast Halima ta koma barcin gajiyar da ya tara mata. Kasa fita ko da Parlon ya yi,a gefenta ya zauna ya na aiki a system duk bayan minti sai ya kalli kyakkyawar fuskarta,a wasu lokutan sai ya saki murmushin kamar sakarai.


🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂


Duk juriyar Maryam da son cikawa Mahaifinta burinshi,sai ta gaza, saboda kullum lamarin Mijin nata ƙara muni ya ke yi.

Wannan dalilin yasa tafara haɗa kayanta don komawa gida gaba ɗaya.


Tun bayan Magrib take sa rai da shigowarshi amma har bayan ƙarfe tara bai shigo ba.


Har lokacin tana Parlon a zaune tana kallon da bata tsintar komai a ciki.


Da ƙarfi ta ji a na knocking ɗin ƙofar kamar za'a ɓalla,mamaki ne ya kamata don idan har shine ba sai yayi knocking ba yanada key.


Su kusan biyar ne manya da su,ririƙe da shi yana layi alamun a buge yake.


A'uziya ne yazo kan harshenta, duk da ba wannan ne karon farko da ya saba shigo mata a irin wannan yanayin ba,amma a waccan lokutan shi kaɗai yake shigo mata.


A lafiyayyen living room ɗin da duk wani makwaɗaici zai so mallaka batare da tunanin waɗan da suka mallakeshi ta wani hanya sukabi suka samu kuɗin da suka ƙawata shi ba, suka zubar da shi kamar kayan wanki. Sannan duk suka dawo da hankalin su kanta,tare da ƙarewa halittar ta kallo.


A wannan dare dukka sai da suka sadu da ita ta gaba da baya,sannan suka bar gidan.


★da asubar fari Mijinta yaci karo da abinda a take nadamar ɗabi'arshi ta dirar mai. Jiki na rawa ya nemi layin Mahaifanshi. Abin tausayi har kayan cikin Maryam a na hangowa.


Kwananta ɗaya a Asibitin Allah Ya karɓi ranta batare da sun sanar da iyayenta ba,kuma a take suka binne maganar,a ka suturtata kafin zuwan Iyayenta da kawai labarin mutuwar ne ya riske su.


Kuka mai ban tausayi Mommyn su Faisal take yi a hankali, musamman da taga yanda fuskar Maryam ɗinta ya koma ɗan ƙarami,a take ta nemi a kwance mata gawar Maryam ta gani,don sam ita batayarda mutuwarta babu wani dalili ba.

Mari mai zafi da ƙasƙanci Uncle Suraj ya sauke mata,yana sauke  hannun shi Goggo da jikinta ke rawa itama ta sauke mai haka Uncle Ghali,dole hayaniyar su tasa aka ɗauke gawar Maryam zuwa wani ɗakin, Kuma Goggo tayi rantsuwar sai a kwance mu su gawar Maryam sun gani,kamar yanda Mahaifiyarta ta buƙata.


Takaddama mai zafi ne ya ɓarke kamar ba a gidan Mutuwa ba. Suna wannan rikicin Iyayen Mijin Maryam da haɗin bakin Uncle Suraj aka ɗauke gawar Maryam zuwa Maƙwancinta.


Zafi da takaicin da Goggo taji a ranar ne yasa dukka suka tattara sukabar Uncle Suraj a can, wanda sai bayan tafiyar su,ya ankara ai garin su ka bari gaba ɗaya.



Shima a washegari ya baro gidan Iyayen Mijin Maryam don yaƙara ladabtar da Iyalinshi kan nuna mishi iyakarshi da tayi.


Wallahi gara mutuwar Maryam sau dubu da dai ace yau duniya suyi mishi dariyar ƴarshi Mai auren jinin su Abdulfatah aurenta ya mutu,mai yafi wannan zafi da ciwo,shashar Matarshi zata zubar mai da Mutunci har su Goggo na biye mata uban me zata gani a jikin gawar Maryam ɗin tunda dai ta riga ta Mutu,ai baza'a dawo da hannun agogo baya ba.


Kafin isowarshi duk Magiyar Goggo da su Uncle Ghali sai da Mahaifiyar su Faisal ta tafi garinsu ta kumayi alƙawarin ta tafi kenan har abada. Don idan tana ganinsu bazata taɓa daina tuna rashin adalcin ta tayiwa ɗiyarta ta cikinta ba. Shima Faisal Mahaifiyarshi na tafiya ya turawa Matar shi dake can saƙon saki,saboda shima ya lura son kashe shi takeyi.


Duk a labaran da Uncle Suraj ya samu sakin da Faisal yayiwa Matarshi duk yafi yimishi ciwo,don haka ya karɓe har gidan zaman Faisal dayake mallakin shi.ya tattara yabar garin gaba ɗaya. Acewarshi duk wanda zai zage shi sai dai ya yi zagin a bayan idonshi.


Dangi gaba ɗaya babu wanda bai hallara a gidan Goggo da ake zaman makoki ba sai Maysarah da Halimarshi. Sai kuma Mom Fahima da tajima da barin gidan tun bayan rikicin su da Goggo.

🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂


Babu abinda Goggo bata sanar da Maysarah ba. Ya kuma nuna damuwarshi sosai sai dai ba shi da wani matakin ɗauka,tunda Mahaifinta ne da kanshi ya hana a buɗeta su ga ko da akwai wani sheda da yayi silar mutuwarta ta.


Jikinshi a mace ya dawo gida,sai dai a kwance ya samu Halimarshi jikinta ba daɗi,gaba ɗaya sai kanshi yaƙara ɗaukar zafi,saboda baya wasa da lafiyarta,ko abun dazai dameta duk ƙanƙantar shi.


Da idanuwanta ma su kashe mishi jiki take kallonshi.

Haɗa baki sukayi wajen tambayar damuwar junan su. Kasa riƙe kanshi ya yi, ya yi mata rungumar dayasata sakin ƙara kaɗan tana turo ƙaramin bakinta. Ya sumbaceta yafi sau goma bayan yaji ƙorafin gajiya da zazzaɓin da ta yini da shi.

Batare da ya samu cikakken hutu ba yace ta tashi suje Asibiti a duba mi shi ita.


Hannunshi na sarƙe da na ta,haka rabin jikinta na kwance a nashi jikinshi suke magana ƙasa-ƙasa.


"Kina son ganin Inna da Goggo" ya faɗa ya na yin ƙasa da kanshi dai-dai saitin kunnenta.

Kai ta ɗagamai saboda zazzaɓin dake ƙara shigarta.


"Okay zamu tafi jibi Sister na Maryam ta rasu"ya faɗa yana gyara mata zaman Vail ɗin kanta da ya ɗan zame.


"Subhanallah yaushe,shi ne baka gayamin ba,duk da bansanta ba ai zanyi mata addu'a ko?" Ta faɗa sluggishly.


"Ki yi haƙuri kinji".


Kalmar bata haƙuri akan ɗan ƙaramin laifi abune mai sauƙi a wajenshi amma duk da haka sai da ta ɗago kanta tana kallon kyakkyawar fuskar shi.


"Tayi ciwo ne?"


"A'a kawai Mijintane ya kira ya ce ta rasu" dasauri Halima ta gyara zamanta saboda Shukura ce ta faɗo mata.


"kar ku yarda may be kasheta yayi,haka mijin ƙawata ya kasheta da duka and her parents have nothing to do talakawa ne" ta faɗa da kukanta mai sanyi.


"Halimahta" 

"Na'am", "kidaina kuka kinji zan bincika In Sha Allah".

"To kaima zaka dakeni wata rana?" ta tambaya tana kallonshi.

"Ko bayan raina wani ya taɓamin ko da yatsarki ne ban yafe ba Halima,Namiji mara daraja shine yake ɗora hannunshi a jikin Mace,ko da wasa karki ƙara irin wannan tunanin kinji" dasauri ta ɗaga mishi kai tana sauke ajiyar Zuciya haɗe da shigewa jikinshi. Kafin sukai har barci ya ɗauketa.



Abubuwan da suke faruwa acikin shuɗewar wata da kwanaki ne yasa dukka ahalin ƙara shiga taitayinsu musamman Yusrah da take Kwaɗayin mai kuɗin dayafi na ta Uban kuɗi. Yau ga shi duk zafin kan Uncle Suraj an mayar da shi susu saboda son Duniya.


Wajen cin abinci ta tafi ranta sam ba daɗi. Tun shigowar kyakkyawan Matashin da ko tattama batayi ta taɓa ganin fuskarshi a tsakanin kwana biyun da suka shuɗe takeyi,a ɓangare ɗaya kuma kama yake mata da Matar Maysarah. Har ya gama Uzirinshi ya bar wajen bai lura da ita ba.


Washe garin ranar ma sai suka ƙara haɗuwa duk da haka bai lura da ita ba balle irin kallon nacin da takemai. Da tunaninshi ta dawo gida,ranar ko barcin kirki bata samu ba,saboda tunani.


Baƙon Mota ne kuma sabo dal daga nesa take ƙarewa motar kallo ko ita da ta taso a gidan arziƙi tasan sai wanda yaci ya ƙoshi ne zai iya mallakar irinshi,maimakon ta tafi sai ta tsaya bawa idanuwanta abinci duk da Mazan dangin su da basu gama tafiya ba na zazzaune suna hira ƙasa-ƙasa.



Matashin dai da take yawan gani kwana biyun da suka wuce ne,cikin shigarshi mai birgewa. Wanda ya fito a na biyu ne yasa Yusrah jin kamar ana kwara mata ruwa mai tsananin sanyi, shima dai cikin ƙananun kayan RL yayi adonshi mai birgewa. Sai macen da tayi fitowar ƙarshe cikin golding Yellow Abaya daya fito da haskenta kamar Pakistani.....✍🏻