65
💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔
( shi ya san gidan mai rowa)
```By```
``` NAFISAT ALIYU SASAAL```
```Page 65```
________Babangida ne a gaba sai Maysarah da Halima da hannayensu ke sarƙe.
Sai a lokacin take tantace a ina ta taɓa ganinshi da kuma ƙara tabbatar da kamannin su da Matar Maysarah. Duk sun fi Maysarah haske duk da shima yaƙara akan yanda ta sanshi,amma na su hasken yafi nashi fasowa.
Basuyi tafiyar dayakai taku goma ba Halima da tun suna hanya take ƙorafin batajin daɗi tayi baya da zafin nama Maysarah ya tarota zuwa jikinshi. Juyawa Mota sukayi,Yusrah da idanuwanta suka cika da ƙwalla dasauri ta ƙaraso tanayiwa Halima sannu.
"Idrees ka biyo mu,ni zanyi driving da kaina"Maysarah ya faɗa batare da ya lura da Yusrah dake rakuɓe a gefe tana kallon ikon Allah ba.
Ba shi da ikon musamai don haka ya fara laluben aljihunan wandon jikinshi ko ya taho da key ɗin motarshi daya bari a harabar gidan tun safe.
Yusrah na tsaye tana kallon shi. "Ka bari na kaika mana" ta faɗa da sanyin murya.
"Okay thanks"ya faɗa yana kallon kyakkyawar fuskarta. Ko kusa ko nesa da can Babangida ba shi kallan gidadawa ko kama da wanda ya fito a cikin talauci balle yanzu da komai ya sauya hutu da jindaɗi suka zauna mai dakyau.
Babu wanda yayi magana a cikinsu har suka kai Asibitin Dr.Aryaan da Babangida yake kyautata zaton su na can.
Murna da Dariyar da Yusrah ta ga Maysarah nayi lokacin ɗaya ya rungume Babangida ne yabata mamaki. Kafin a hankali ya sake shi yaƙara komawa ɗakin da Halima take.
Baki sake Babangida ya bishi da kallo ya na ƙara kallon jikinshi daya runguma da tsananin mamaki.
"Kasan meya sameshi?" Babangida ya girgiza kai.
"May be an sanar da shi Matarshi ta na da ciki" ta faɗa har lokacin muryarta a sanyaye kamar ba Yusrah ba.
"Allah ya amsa bakin ki" shima ya faɗa yana kallonta. Daga haka kowannen su yaja bakinshi ya tsuke.
Ya rungume Halima da sumbatarta kamar zai cinyeta itama tayi kuka,tayi farin ciki,idanuwanta har tasawa sukayi. Daga shi har ita ba su da Uwa ba su da Uba,ƙani,yaya,duk ba su da shi,sai yanzu da Allah ya ƙaddara ciki a jikin Halima.
Zuwa dare babu wanda bai zo duba Halima ba,sai Uncle Suraj da ya yi nisan kiwo. Sai raɗaɗin rashin Maryam da suke jimaminshi kullum ya zama kamar ba'ayiba.
A keɓance Yusrah ta sha kuka,tasan ko da ita Maysarah ya aura bazasuyi wannan farin cikin ba sai zullumin abinda zata haifa ya zama Namiji domin su samu Magaji,sai ta ƙara godewa Hikimar Ubangijinta da bai ƙaddara aure a tsakanin su ba.
A wannan ɗan jinyar da Halima tayi shaƙuwa mai ƙarfi ya shiga tsakanin Yusrah da Babangida,har ya kaishi ga furta mata kalmar so,da farko bata amince ba,don tasan su waye Mahaifanta,amma ga mamakinta sai ta samu goyon bayan su ɗari bisa ɗari. Bayan ta amince mai ya ke sanar da ita matsayinshi a dukiyar wanda suke kwaɗayi a lokutan baya. Daƙyar ta iya riƙe yanda taji kanta na ƙara girma har taje gida,da ta sanar da Iyayenta haɗuwa sukayi suka rungumeta.
Dole rabon bawa nashi ne,wani bayacin rabon wani, Allah ya karɓi wannan damar a hannunshi domin yazama sanadiyyar shiriyarshi,ya mayar da shi hannun Mijin ɗiyarshi da yardar Allah. Ya yarda haɗama batakai Bawa ga cikar muradinshi har sai Ubangiji Ya ƙaddara.
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Kwanan Halima biyar taji sauƙi sosai duk da bata daina ƙananun ciwuka ba.
Maysarah kamar zai goyata kowa yazo sai ya mishi tsiya duk da fuskarshi ta rashin fara'a dake ɗaure.
Babu wanda yakai Inna da Goggo farin cikin abu biyu lokaci ɗaya,cikin jikin Halima da kuma batun auren Idrees(Babangida) da Yusrah.
Babu wanda yayi mamakin sauyin lamura domin babu abinda yafi ƙarfin Allah.
Maysarah mutum ne mai tsantsami da kuma rashin yarda da masu aiki,don sun ci amanarshi sau babu adadi. Duk girman gidan dayasa yawun mutane dayawa tsiyaya babu mai aiki a sashen su,sai dai ma su hidimar gidan da mai dafa musu abinci.
Shi da Halimarshi sukeyin komai ranar da bata da lafiya yayi shi kaɗai. Soyayya da kulawa mai tsayawa a rai Halima take samu daga gwarzon Mijinta. Duk tattalin cikin da son shi da sukeyi tare suke tafiya duk inda zai je,Goggo tayi faɗa harta gaji.
Itama Halima ba irin faɗan da Inna batayi mata ba amma tayi biris,don batayi ƙaton ciki ba sai ƙibar da tayi.
Bikin Yusrah watanni shidda akasa bayan komai yayi yanda kowani ɓangare suke so, duk da a dukka dangin ansamu ma su zuga da munafurcin Mai Namiji kyakkyawa irin Babangida zai yi da macen da bawani shekaru ya bata ba kamar Yusrah wayo kawai suke son yimai don sun ga ya ɗaukaka. Itama a nata dangin suna sukar Allah yasa kar su wawashe dukiyar Maysarah su kashe shi, banda haka sun san Uncle Ghali bazai taɓa yarjewa Babangida auren Yusrah ba.
Bayan watanni uku aka ɗaura auren Mubeena da saurayi mai kuɗin da basuyi tunanin zai so bazawara irin Mubeena ba,a ranar da aka ɗaura auren tsabar kukan da Uncle Ghali yayi sai da aka dawo lallashin shi. Goggo taƙara yimishi nasihar yanzu ga shi dayayi haƙuri ya cire zalama da kwaɗayi ƴaƴanshi na ta samun Mazajen liƙawa a goshi.
Lefe irin wanda Yusrah bata taɓa hasasowa kanta ba Babangida da Halima suka haɗa mata da gudummawar Maysarah, hassada kamar zai cinye zuciyar ma su mugun ƙulli da mugun nufi.
Shima Faisal kasada yayi ya nemi auren wata Abokiyar aikin shi.
Bikin Yusrah ya bayar da duk wani abu da take buri har sama ma da haka.
Duk ƙorafin Maysarah da jan kunnen dayayiwa Halima na kar taje,sai tai biris ta biyewa zugar Goggo na cikinta yayi girman daya isa haihuwa dole tana da buƙatar motsa jiki. Inna dake jin su bata tofa mu su ba.
Rabonta da shiga shagali irin wannan ta daɗe wannan dalilin yasa taji nishaɗi sosai a ranta har sha ɗayan dare ya wuce.
A Parlon Goggo suka sameshi da fuskar da idan batayi ƙarya ba rabonta da gani tun ranar da ta fara ganin fuskarshi.
"Da izinin wa kika tafi irin wannan shirmen Halimata" ya faɗa furiously, ya saba da kiranta da Halimata sai hakan ya zame mishi kamar haka asalin sunanta yake.
Idanuwanta kamar za su fito,Goggo dariya tasa ta gudu tabar mu su Parlon da babu kowa a ciki duk su na gidan Uncle Ghali sai tsararu dake Bedroom su na barci.
Da zafin namanshi ya kamo hannunta har Mota. Duk kukanta da magiyarta bai kulata ba har sukaje gida.
Bai fasa taimaka mata tayi wanka ba,haka barcinta a jikinshi,don shine cikar nutsuwar barcinshi,kafin ta farka ya bar gidan batare da taimaka mata da aikin komai ba.
Baƙaramin wahala Halima tasha wajen kimtsa sashen ba. Da ta kira layinshi a kashe kuka ta sa da tura mishi text ɗin magiya kala-kala. Text ɗin baya gari ya turo mata don haka ta kulle ko ina bazai dawo ba.
Kuka har da magina Halima ta yi. Zuwan ƴan gidan su Inna da daddare domin yimata sallamane ya sa ta gyara fuskarta. Alheri na kuɗi da kayan sawa tayi mu su don washe gari da sassafe zasu tafi. Godiyar su har da duƙurso da masu ƙwallar borin kunya.
★Bata runtsa ba har wayewar gari.sai gabannin Asubahi barcin wahala ya ɗauketa,tana sakin ajiyar zuciya.
Ƙarfe takwas ta farka ta leƙa ko ina har harabar gidan ta fito amma bataga motar da take kyautata zaton da shi ya fita ba. Bayan ta shigo bata saka key ba tafara kimtsa ko ina jikinta a sanyaye,don batajin zata iya sakawa cikinta wani abun.
Tana cikin moping ta zame a ƙasa, ƙara mai ƙarfi ta saki,dai-dai lokacin da Aunty Rahina take daf da ƙaraso bakin ƙofan,tun Asubahi Maysarah ya kira Mijinta kan ya tura Iyalinshi ta dubo mishi lafiyar Halimarshi.
Knocking ɗin ƙofar ta farayi a kiɗime,amma ba a buɗe ba ga shi har lokacin Halima na salati da ihun neman ceto, jiki na rawa Rahina takira Mijinta ga Halin da ake ciki,shima a kiɗeme ya nemi layin Maysarah. Gwada murɗa handle ɗin tayi sai ta jishi a buɗe. A hanzarce taƙarasa kusa da Halima. Hannunta Halima ta ƙanƙame da faɗin ta taimaka mata zata mutu.
A zaune yake idanuwanshi a lumshe sun ɗanyi ja saboda rashin barci da ƙewarta da suka hanashi runtsawa, A Hotel ya kwana don ya lura son dayake yiwa Halima na neman sa ta, ta daina jin maganarshi,ba kuma komai ke ɗawaniya da shi ba sai kishin daya sawa ranshi na taje kowa yanata kallonta,kuma ko ta bashi haƙuri bayan sun dawo tayi barcinta hankali kwance.
Da guntayen kayan dake jikinshi ya ɗauki car key ɗin shi batare da ya gama sauraren bayanin Aminu ba.
Halima tasha wahala kafin haihuwar kyakkyawar ƴarta mace mai kama da dukka Mahaifanta. Faɗin murnar da farin cikin da wannan ahali sukayi ɓata bakine. Har lokacin Halima ba ta dai ƙorafin tafiyar da yayi ya barta ba,bayan ta samu nutsuwar lafewa a lafiyayyen jikinshi.
Maimakon ya bari ta tafi gidan Inna ko Goggo sai su suka dawo nashi gidan da zama don yayi rantsuwar Matarshi bazataje wani waje da sunan wanka ba.
Bikin Suna mai ma'ana da aji Halima da kafatanin dangi sukayi,na Halimatul Sa'adiya ƴar Halima jikar Halime.
Maysarah ya nunawa duniya matsayin Halimarshi,ya kuma ƙara ɗaga darajarta a idanunawan ma su shakkar hakan ta hanyar kyaututuƙa da suka girgiza mu su zuƙata da kafa tsanarta a zuciyar maƙiyi har abadah.
Kamar Mace haka Maysarah yake kula da Halima da Jaririyar su,baya ƙyashin kashe mu su kuɗi duk yawanshi da hidimta mu su da lafiyarshi,saboda a lokacin da har bayan rai su kaɗai ya mallaka da waɗan da yake fatan za su ƙara samu nan gaba.
Wata rana kwatsam su ka tsinci Uncle Suraj ya dawo gida ciwon Suger duk ya ramar da shi. A wannan ciwon dukiyar da ya tara yayi ta tafiya har ya dawo ba shi da ko sisi,sai dangi da suka dawo taimakamai har lokacin baiji nadamar komai ba a ranshi. Kullum idan Maysarah da kyawawan Iyalanshi su ka zo gaishe shi sai yaji kamar ya tashi ya shaƙe Halima har sai ta daina numfashi.
Tun waccan horon bata ƙara wasa da duk wani abu da zai ɓatamai rai ko ƙuntatamai ba. Wahalar shi da yanda yake hidimta mu su har tausayi yake bata.
A lokuta da dama idan ta ƙureshi da rigimarta ita da kyakkyawar ƴar su furucinshi na "kuna son ku kashe ko" na sanya Halima cikin nishaɗi da ƙara son shi a zuciyarta,bai iya zagi,duka,ko gori ba,sai dai wannan furucin da idan yayi yake sanyaya jikinta har take gane kuskurenta ta gyara.
ALHAMDULILLAH.
ku watsar da shirmen dake ciki,ku ɗauki saƙon da nakeson isar mu ku.
Nagode,Nagode,Nagode da bibiya da kuma addu'o'in ku ina tsananin son ku da ƙaunar ku,Allah Yabar zumunci my Facebook fam❤️ my WhatsApp fam❤️ and my Arewabooks Fam❤️.
Ina roƙon Allah ya yafe mini kuskuren da nayi aciki. Da fatan zakuyimin Uzurin inda ban taɓo ba,da guraren da nayi mantuna.
Sharhi ko shawara ***.
Sai kun ƙara jina a littafin *ABU ZAID* wanda zai fara zuwar muku nan kusa, Nagode🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻
Kuyi following ɗin Arewabooks Account ɗina domin karanta littafin Abu Zaid shima free ne In Sha Allah