INA GA KAM LITTAFIN NAN BAI SAMU KARƁUWA BA NE
by @umaimah2024
KUKAN KURCIYA
By
🧕 UMAIMAH ADO GAYA 🧕
To
Aunty Khadija candy
Page 06
Haseeya :
Tunda Haseeb ya fita take kuka Bata taba tunanin abn zai zo da haka ba da bazata taba ydd da abnd su salimat suka fada mata ba, Ina laifin ma tunda ta riga ta samu cikin idan ta haife shi sai tai planning kafin ta samu wani cikin har zuwa sanda take tunanin ya dace ta sake,
Koda umman ta ta dawo ta tarar da ita tana KUKA sosai hnkln ta ya tashi don tunanin ta ko wani abun ne ke damuna ta sai dai juyin duniyar Nan ta fada Bata abnd ke damun ta taki fada har tai zuciya ta rabu da ita, Koda ta hada mata shayi ma kin sha tai har sai da umman ta wanke ta tasss snn ta sha,
Lateefa : bayan tayi wanka tayi sallah yayanta ya saka ta gaba bayan taci abinci suka tafi asibiti bayan la'asar, don acewar sa gara a duba ta kar abinda ta sha yai mata illa, sai da likita ya duba ta ya Bata maganin da zai wanke kwarayar da ta sha snn suka fito, Kiran wayar sa da akai ne ya sanya yai gaba don amsawa ita km ta biyo shi a baya har sukai karo da Haseeb,
Tana tafiya tana zabga murmushi don sosai Haseeb ya burgeta sai dai taga idanun sa cike da bacin Rai Wanda a tunanin ta ko wani abun ne ya samu Wanda ya kawo hsptl din, rufe idanu tai da tafikan hannunta SANDA ta tuna da kyakkyawar fuskar sa sai km dariya ta biyo baya tunawa da ydd ya fara mata masifa km yai shiru Yana kallonta SANDA ya juyowa da ydd ya gyada mata Kai ya juya ya cigaba da tafiya,
Kallon ta yayanta yai yana fadin are you okay latifa? Anya kwayar Nan Bata fara taba ki ba? Turo baki tai tana fadin Yaya! Abin dariya fa akai wajen GOPD bayan tawowar ka shine ba nake dariya , tabe baki yai yana Bude motar snn yace muje ni dai sauri nake ynx mahfuz ya kira yace min muna da test gobe ya kamata muje library karatu.
......
Nuraddern :
Driving yake Amma sai zabga murmushi yake, haka nan ya koma kwana biyun Nan Daya kadaice tunanin nafeesat yake more especially mgnr da ta fada masa akan feenah tana matukar sanya shi NISHADI, mgnr tana nuna masa kishi da soyayyar sa a cikin su sai dai ya rasa tsoron me yake gani a ckn idanuwanta, haka nan zuciyarsa ke sanar dashi there is something behind it,
Shi dai ya riga ya sani tuni ya fada tarkun soyayyar ta sai dai ya rasa abnd yake hana shi tunkarar ta, duk da yana ganin son shi a kwayar idanunta sai dai bayan wnn son Yana ganin firgici da tsoro wnd ya kasa na mene? Shafa kansa yai yana kudurtawa aransa cewar dole ckn satin nan zai bayyana mata sirrin zuciyar sa, km Yana fatan samun goyon bayan ta, furzar da iskar bakin sa yai a fili ya furta so help me God!
*******
Haseeb:
Bin bayan lateefa yai da idanu bai san lkcn da murmushi ya subuce masa ba a fili ya furta silly girl, Kai tsaye mosque din hsptl din ya nifa ckn zuciyarsa Yana ayyana irin hukuncin da zai yankewa hasiya, duk da a wani bangaren na zuciyarsa Yana sanar dashi cewar ya barta da ciwon da ya same ta sai dai Wani bangaren na zuciyarsa Yana sanar dashi wnn bai isa hukunci agare ta ba,
*****
Nafeesat :
Kwance take akan gadon dakin ta Banda juyi ba abnd take sosai zuciyarta ke mata zafi da radadi, Bata taba Jin haushin kanta ba irin wnn lkcn tbbs ta aikata babban kuskure a rayuwar ta wnd gogewar shi a tarihin rayuwar ta ba zai taba yiwuwa ba,
Wayace a hannunta tana dannawa gefe km kanwar tace Khadija tana cike form din midwifery ta jiyo ta kalle ta tana fadin ynx dai Allah deejah sai kin riga ni sanya uniform a hsptl ko?
Dariya Mai murmushi Khadija tai tana fadin aikam dai sis tunda ynx computer science kika tafi ba? Ni gani dama midwife din kk fara inyaso sai ki koma buk din kiyi Wani course din dg baya,
Hmm deejah kenan kin san fa halin Yaya ynx sai yace zan sa Abbee asarar kudi , so tunda na riga na fara c s din I will manage zuwa sanda zan gama ai ba wani jumawa bane,
To ynx km ki gama computer science snn km ki koma bangaren lpy? Cewar deejah kana ta Dora da fadin
To wai ma Wani course zaki Yi ? Snn ki Yaya da karatun computer science din?
Murmushi nafeesat tai snn tace Allah ne kadai yasan abnd zai faru Amma ni burika na harkar lafiya suna da yawa,
Dage kafada Khadija tai tana fadin to Allah ya taimaka ya zaba mafi alkhairi idan km kamin lkcn an samu wnd yai wuff Dake km to shiknn,
Ta bude baki zata amsa mata wayar Dake hannunta ta fara ringing, kurawa screen din Ido tai tana kallon number kafin ta daga ta Kara a kunnenta gaf da wayar zata tsinke,
Sai da ta lumshe idanunta sbd ydd muryar da akai mata sallama ta shige ta, a hnkl km ckn zakin muryarta ta amsa sallamar, kana tai shiru tana sauraron Mai mgnr,
Daga Daya bangaren Akram ya furta da fatan Ina mgn da gimbiya nafeesat ? Sai da ta nade kafafunta akan cushion din da take zaune snn ckn juya idanu ta furta kana mgn da nafeesat dai Amma ba gimbiya ba,
Fadin Hakan da tai ya sanya Khadija ajiye form din hannunta da biro tai ta gumi tana kallon yayar tata,
Hmmm lallai kam to sarauniya zance kenan don idan har ba gimbiya ce ba to tbbs ke din sarauniya ce, aka fada dg Daya bangaren ,
Okay as you wish plz! Ko zan San da Wanda nake mgn and dame zan iya taimaka masa?
Well kina mgn da Muhammad ishaq wato dai Akram wnd kuka hadu dazu a kofar poly? Ya Bata amsa ckn kwantar da murya,
Da idanu Khadija ke bin nafeesat ganin ydd take wani kudundunewa sosai mamakin ta ya bayyana a fuskar ta Domin ita da nafeesat sako da sakuwa ne km tsiran shekara biyu ne tsakanin su Hakan ya sanya suke tamkar kawayen juna, tafi kowa km sanin nafeesat Sam Maza ba gabanta suke ba Amma yau har Wani narkewa take tamkar sunyi shekaru da haduwa da wnn guy din lallai da zafin sa ya shigo,
Nafeesat tace oh to ya kake? Toh! Ina Nan dai Nan da nake ta gangar jiki na lpy Amma ta zuciya da kwakwalwa Sam ba sauki don soyayyar ki da tunanin ki gaf suke da kassara min rayuwa idan har ban samu karbuwa ba,
Sauke nannauyar ajiyar zuciya tai snn tace aikam dai ya kamata ka cire nafeesat a zuciyar da kwakwalwarka ka maye gurbin ta da wata Domin wnn nafeesat Bata da lkcn soyayya sam,
Ko rufe bakinta ba tai ba tajiyo shi Yana fadin Ahhh! Wayyo zuciya ta , haba feesat nasan tbbbs kamar yadda Allah ya kawata Miki kyakkyar fuska haka ya kawata Miki kyakkyawar zuciya ki daure ki taimaki wnn bawan Allan ki bashi damar da zai bawa soyayya damar shiga rayuwar ki Hakan zai iya zama abin alfahari a gare ni,
Okay zan duba naga idan da damar Hakan ta fada da alamun kosawa a muryarta yayin da kasan ranta take Jin ydd duk wata kalmar sa take sauka da tarin soyayyar sa a ckn zuciyarta,
Yauwa ko ke fa jarumar mata! Ki dauki dukkan iya lkcn da kk ganin ya Miki dmn bani dama Amma kafin Hakan Ina neman alfarmar turo miki da sakon barka da safiya da na dare , ya fada Yana Kara narkar mata da murya irin ta mazan da suka San takan mata,
Sai da ta janye wayar daga kunnenta ta zuki numfashi ta fesar kana ta mayar da wayar tace okay fine Amma ynx zan aje waya don Ina Wani Abu Mai muhimmanci ne,
Sa hanzarin sa ya furta Angama ranki ya dade farar mace alkyabbar mata, zinariyar mata km sarauniya a fadar zuciya ta, sauke wayar tai daga kunnenta tana murmushi kana ta datse wayar, tana wurgawa Khadija harara ganin ydd ta kafe ta da idanu ko kiftawa Bata son yi?
Pillow ta jefa mata tare da mikewa tana fadin munafuka ni wallahi na manta kina kusa Dani da daki zan tafi, tabe ki Khadija tai tana fadin kyaji da gulmar ki dai km dai wallahi ko a bini sannu ko km mutum ya San sauran, ba tare da nafeesat ta kulata ba tai shigewar ta daki,
Tun daga ranar Akram ya dage da turo mata sakonni, da safe da shi take fara cin karo haka Nan da dare shine yake zamowa Abu na karshe da take gani a wayar ta don kmr yasan lkcn kwanciyar ta,
Nafeesat Kam sai da sukai almost one month a haka kafin ta bashi damar, ai Kam kafin a rufe sati Akram ya gama baibaye dukkan Wani lungu da sako na zuciyar ta dmn soyayya yake nuna mata kamar rayuwa da mutuwa , gaba Daya Yan gidan sai da suka San Akram a waya dmn indai ya kira km da Wani kusa da ita sai yace ta bashi su gaisa,
Suna wata na uku da haduwa ya sanar mata da cewar Yana son yazo gidan su km Yana son ya samu mahaifin ta Domin ya nemi izini a gurin shi km ya mika gaisuwar sa, ba musu ta sanar da Ammi ita km ta sanar da Abbansu ya zaba masa ranar da yake Nan yace km yazo da yamma,
Ilai kuwa a ranar asabar da misalin karfe biyar na yamma Akram ya faka motarsa a kofar gidan su snn ya kirata awaya, Khadija ce da kanta ta fita ta shigo dashi Yana sanye ckn dakakkiyar shadda sky blue yar yayi Tasha dinkin zamani, ya kafa hula da takalmin sa cover shoe blue sai zafga uban kamshi yake , sosai suka gaisa da Khadija kana ya biyo bayanta zuwa falon saukar baki na gidan Yana tsokanar ta, suna shiga kannen su suka ringa shigo Mai da kayan motsa baki kana suna kwasar gaisuwa kafin nafeesat ta fito suka bar su ita da shi,
Kafe ta yai da idanu Yana ta zabga murmushi kamar wnd akaiwa albishir da shiga Aljanna yayin da ita kuma ta sunkuyar da kanta tana wasa da hannunta bayan sun gaisa,
Sun dade a haka kafin ta karya shirun da fadin baka taba komai ba, ko basu Yi maka ba ne a canzo maka da Wani abun ? Girgiza kansa yai still idanuwansa na kanta yake fadin tabbas na Tara kishirwa da yunwa sbd zumudin zanzo nai gamo da abar kaunar Raina , Amma ganin ki kadai ya Kore mun dukkannin Wani damuwa ta, agaskiya nafeesat sanki yayi min wata irin damka wadda nake Jin idan har ban same ki ba zan iya rasa rayuwa ta dan Allah nafeesat karki rabu da ni,
Murmushi tai snn ckn sunkuyar da Kai ta furta insha Allah mutuwa ce zata raba mu ka sanya a ranka nafeesat da duk wani Abu da ta mallaka a rayuwar ta naka ne har karshen numfashi,
Kayataccen murmushi yai kana ya dauki sassanyar kunun ayar da Khadija ta zuba masa kafin fitar ta ya Kai baki ya kurba, sai da ya lumshe idanu ya Bude kana ya Kara kurba ckn salo ya furta tested and trusted ,
Uhm? Ta fada da sigar tambaya, kashe mata idanu yai Yana fadin Ina magana ne akan lemon yayi fiye da yadda ake so ma, murmushi kawai tai dg haka kuma suka Bude shafin soyayyar su,
Duk kin nafeesat da son aure haka duk soyayyar nafeesat da karatu haka ta hakura ta amincewa Akram akai musu baiko da sanya rana Wanda yace baya so a wuce wata uku abinka da masu abun Suma iyayen nafeesat basu ja ba saboda itama Bata musa ba aka sanya rana,
Kusan duk weekend sai nafeesat da Akram sun fita outing tare da rakiyar Khadija kanwarta km aminiyarta, duk da Ammi ta nuna da farko Bata so Amma ganin tare da Khadija ne ya sanya Bata Kara magana ba,
KADDARAH! wata ranar asabar da safe lokacin saura sati uku bikin su , tana zaune a bakin gado daure da towel tana Kiran Khadija da tun safe ta tafi asibiti dubiyan mamar kawar ta Amma shiru Bata dawo ba gashi lkcn zuwan Akram ya kusa Amma wayar Bata shiga, Kara danna mata kira tai sai dai Kiran ya katse sakamakon shigowar Kiran Akram dafe goshin ta tai tana fadin oh my goodness,
Da sallama ta amsa wayar kana cikin ladabi ta gaida shi, amsawa yai da murmushi kana yace I hope dai Kun shirya more especially ma sister don nasan halin ta kullum sai ta shanya ni,
Dariya tai tana fadin ai Kam shanyar taka ta yau tafi ta kullum don Bata Nan ma YANZU ma kiranta nake Amma wayar Bata shiga I hope dai komai lafiya,
Lafiya insha Allah may be sharrin network ne kinsan haka yake, kuma yau dai ko ba komai na huta da shanya fitowa zaki ynx gani Nan kan kwanar layin ku ynx zan karaso ki fito mu tafi don yau uncle Dina ma zamu je mu duba dama an kwantar da shi hospital kuma kin san 6pm suke rufe lokacin ziyara gashi YANZU har 5pm tayi,
Sai da ta sauke numfashi snn tace okay bari na sanar ma Ammi kasan Bata son fitar mu mu kadai, hmm ai Ammi dama ni gani nake kamar Bata yarda da ni ba,
Kai kuma Wani irin yadda da Kai ne ba ta Yi ba? Kawai dai tace abinda adding yai Hani dashi to ka guje shi, kuma kaga idan mace da namiji suka kebe na ukun shedan ne,
Haka ne malama ta Amma YANZU kije ki sanar ma Ammi nazo zamu je duniyar uncle Dina a hospital,please kar kice Bata yarda ba saboda bazan ji dadi ba,
Hmm kuma idan ta hana ai ba YANDA zamu Yi Kai dai kawai Kai addu'a Allah ya Dora mu akanta kawai, okay Ameen am waiting please ya fada Yana kashe wayar ba tare da ya Jira amsar ta ba,
Koda ta sanar ma Ammi da farko kin yarda tai tace su Jira Khadija Amma magiyar da nafeesat ta DINGA mata kuma ta nuna mata lokacin visiting ya kusa fita yasa ba don ta so ba ta amince mata,
Sai dai taja kunnenta sosai akan kare mutuncin ta
Da murna ta shirya cikin doguwar rigar material tai rolling din karamin mayafi snn ta dauki jaka da takalmin ta sanya kana ta fito,
Tunda ta fito daga kofar main falon gidan su yake binta da idanu har ta karaso inda yake, kamshin turaren ta da humra ya shaka ya lumshe idanu Sannan cikin rissinar da Kai ya furta welcome ma'am,
Murmushi tai tana hararar sa sannan cikin yauki ta mu yi sauri Ammi tace 40 minuet kawai ta bamu muje mu dawo, okay NAGODE ma da Hakan muje ko? Ya fada Yana Bude mata front sit,
A farkon layin su suka hadu da Khadija sai da ta sanya shi ya tsaya tai mata magana akan ta shigo ta raka su Amma tace aa suje kawai yau ita ta gaji kuma ba'a shirye suke ba,
Sai da suka dau hanya sannan yace kinsan fa ba wata duniya da zamu fa! Kallon shi tai da mamaki kafin ta furta to Ina kuma zamu?
Murmushi yai da fadin pre-wedding pictures zamu je saboda abokai na suna ta damu na wai har YANZU bamu Yi ba nasan kema may be friends din ki sun Miki maganar ko?
Kasan da yake ni ba wasu kawayen ne Dani ba Khadija ta ishe shiyasa, Amma ai da ka fada min ba sai mu shirya yadda zamu Yi ba and ko gobe ma ai zamu iya zuwa da ba sai muje da Khadija ba?
Eh haka ne Amma gani nai kamar idan Ammi ta sani bazata bari ba shiyasa, kuma shiri kar ki damu na tanadar mana duk wasu kaya da zamu Yi amfani da su YANZU kawai wucewa zamu Yi gurin hoton,
Kamar yadda yace Kam haka ne ya faru Domin Kam sai da sukai pix kusan kala goma kuma duk kaya daban sai dai sam nafeesat kasa sakewa tai saboda Bata Saba ba, styles din ma idan akace ga yadda za'ai sai tace ita sam baza tai ba, sai da yai mata Jan Ido har Yana sanar da ita dama ba sanshi take ba tunda Bata yarda da shi ba da har take kyamar ya taba jikin ta,
Badan taso ba haka ta hakura har aka gama kuma a take aka wanke musu shi fesss kuma hotunan sun fita sosai, a hanya ya tsaya ya Siya musu ice cream da lemon sai ruwa duk yadda yai da ita akan ta sha Wani abun ki tai sai daga karshe ne Tasha ruwa Wanda ba'a fi minti goma da shan ta ba ta fara jin Wani iri a jikinta kafin Wani lokaci ta fita hayyacin ta,
Meet in the next page......
***
Slm barka mu dare fatan kuna lpy masha Allah kamar yanda kuka sani litafin DAGA MAFARKI ZUWA ZAHIRI na kudi ne so mun gama free book yanzu zamu fara book two wich is paid book ne
👇👇👇👇👇
Ama a nan channel bazan barku hk ba zan ringa yimuku Update ama fa ba DAGA MAFARKI ZUWA ZAHIRI ba fa 😂😂😂yauwa karku yi tunani shine aa zandai baku kyautar daya daga ciki litafin na ne so ama kafin ku sami hkn sai kuna faranta min rai da Imoji wato like shine kadai zai saka kusamu yanda kuke so ina fatan in dinga ganin like 😍😂