KUKAN KURCIYA masu iya magana suka ce jawabi ne, kuma gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah, labari ne da ke ƙunshe da gwagwarmaya, soyayya, cin amana, rudin sheɗan da dai sauran su , ku dai ku biyo ni umaimah ado gaya don jin me ya ƙunsa?

Ga mai bukatar turaruka humrah, kwalaccam da kayan gyaran jiki sai ya tuntuɓe ni ta wannan number 09070127320 kira ko chat

by @umaimah2024

KUKAN KURCIYA 




   By UMAIMAH ADO GAYA  

   

   

   To Aunty Khadija candy 



  Page 07 



    A hankali take Bude idanunta da take Jin su tamkar zasu cire saboda radadi yaji gami da azabar da take ji suna mata, tayi KUKA Wanda Bata taba tunanin a rayuwar ta zata Yi Saba har karshen numfashin ta, Kara yunkurawa tai akaro da barkatai Domin ta mike Amma kar dai yadda take ji haka ma yanzu ta Kara ji saboda yadda Akram ya jigata ta, 


 Da sauri Akram ya karasa inda take Yana fadin am very sorry my feesat let me help you, wata irin zabura tai kamar taga kumurcin miciji har tana yin karar wahala cikin karfin hali da fusata take fadin don't there touch me with your dirty hands, 


  Murmushi yai yana fadin haba mana nafeesat? Mene kuma abin Jin haushi anan nifa zan aure ki kuma na zama mijin ki, ba wani Abu bane Dan na karbi abinda yake nawa ,



  A fusace ta furta karka Kara Dangantani da Kai Allah ya tsare ni da zama matar fasiki irin ka kasani wallahi ko Maza sun kare ba abinda zanyi da Kai, Kai! Bari ma na fada maka ko da zan kare rayuwa ta ba aure wallahi ba zan taba auren ka ba, 


 Wani killer smile ya saki cikin dariyar shakiyanci yake fadin kina tunanin idan baki aure ni ba zaki samu miji nagari da zai iya auren ragowar Wani ne? Garama kiyi hakuri mu rufawa juna asiri ki aure ni, Domin tunda nake ban taba samun mace dai dai Dani ta wannan fannin ba kamar ke,dama Ina gwajin takalmin ne Domin naga ya dace na kafa ta ko kuwa? To YANZU na samu dai dai da ni Amma idan kina ganin zaki iya tonawa kanki asiri ta hanyar sanar da Wani sirrin ki sannan daga baya ya juya Miki baya yaki auren naki? Fine sai na Kara lalibo dai dai da ni, 


  Rintse idanu nafeesat tai sosai take Jin saukar kalaman Akram a kunnen ta tamkar digar dalma, ba tare da ta ko kalli inda yake ba ta dauki kayan ta ta sanya tana cike baki kana ta dauki duk abinda idanunta ya hau Kai nata ta fice ba ko waiwaye, 


  Kai tsaye asibiti ta nufa sai da akai mata dukkan Wani Abu da ya kamata nurse din da doctor ya hada ta ita dai mitar yadda mijinta yai mata kuma ya kasa kawo ta asibiti da kanta take, da kyar suka salllame ta bayan an mata allurai kuma an Bata magungunan bayan ta sha uban gashi, 


  Cikin dauriya ta isa gida ba karamin kokari tai ba gurin ganin ba Wanda ya gano abinda yake damun ta sai dai kasancewar Ammi uwa ce Mai tsanani kulawa ya sanya ta fuskantar akwai abinda ke damun ta, takanas ta iske ta a bedroom din su ita da Khadija ta tambaye ta Amma sai ta sanar da Ammi halin da taga uncle din Akram ne ya sanya ta damuwa, 


  Sosai Ammi taji tausayin sa har tana fadin Suma zasu je dubo shi, sai dai bayan fitar ta Khadija da tun shigowar nafeesat take binta da idanu ta dafa kafadar nafeesat tana fadin sis idan kina tunanin karyar da kika sanar ma Ammi kika ninke ta baibai nima zaki min haka to wallahi kin ci amanae yarda da amincin Dake tsakanin mu, 

   

  Ina son ki sanar da ni abinda ya faru bayan fitar ku da Akram shin kunje duniyar ko kuwa? Idan kunje bayan Nan Ina KUKA je? Ina so ki sani wannan maganar most be secrect between us idan ma Wani ne bakya son ya sani, 

   

   

  Fashewa nafeesat tai da KUKA tare da rungume ta, sai da tai Mai isar ta sannan cikin dashassgiya muryar ta fara fadin Khadija nayi dana sanin amincewa da Akram, Khadija Akram ba mutumin kirki bane mayaudari ne Maci amana ne fasiki ne mara tsoron Allah Khadija Akram ya ..... Sai ta Kara fashewa da KUKA har tana shidewa, 


  Wani irin dago ta Khadija tai cikin kidima da karfi take girgiza nafeesat tana fadin Akram ya mike me? Kar ki so ma sanar min da cewar Akram ya lalata Miki rayuwa sai itama ta fashe da Wani irin KUKA tamkar ita ce abin ya faru da ita Domin tafi nafeesat shiga tashin hankali, 


  Cikin shakewar murya nafeesat ta furta Wani Abu ya sanya min a cikin ruwa Wanda ya kashe min jiki Ina ji ina 

gani Amma ko hannu na bazan iya dagawa ba, daga karshe ya kaini gidan sa yai min duk abinda yaga dama ba tare da na iya aiwatar da komai ba, 


  Sannan ta kwashe duk yadda sukai da shi ta sanar mata, kada Kai Khadija tai tana share hawayen ta sannan tace ki rabu da Dan iska wallahi ba mijin aure bane kuma insha Allah zaKi samu miji Daya tamkar da dubu Wanda zai share hawayen bakin cikin da Akram ya sanya ki, YANZU ki tashi ki wanka ki gasa jikin ki ki samu lafiya tukunna sai mu San yadda zamu bullowa al'amarin shi kuma Dan iskan idan yazo Allah ya hada ni da shi, 

 Kada Kai tai sannan ta shiga bandaki kamr yadda Khadija ta fada, yayin da Khadija ta bita da Ido tana tausayawa yayar tata don ko ba komai mace ce Mai KAMUN Kai Amma lokaci Daya Wani banza ya ruguza tattalin da taiwa kanta, 



Kamar wasa tun daga wannan rana nafeesat ta fara ciwo a tsaitsaye Wanda har ya kai ta ga kwanciyar asibiti na tsawon sati kafin ta dawo daidai, sai dai har lokacin ba Wanda yasan abinda ya faru bayan Khadija, 



Har tsawon wata biyu ba akram babu dalilin sa, tun nafeesat na jiran zuwan sa har ta fitar da Rai don daga baya itama Khadija ta Bata shawarar ta amince ta auri Akram ko da na rana Daya ne Hakan zai Fi mata sauki a kira ta da bazawarar da ta taba aure akan zawarcin dole da Akram ya SATA , ko da su Ammi suka ga shiru ba Akram ba iyayen sa sai Yan uwan mahaifin su nafeesat suka he gurin iyayen sa akan maganar auren inda Kai tsaye suka sanar da sun janye, 


Ammi ta sanya ta a gaba kan ta sanar da ita abinda taiwa Akram ya janye ita Kam ta rasa abin fada ta dai sanar da Ammi ita Bata San abinda ya hada su ba kawai dai ya daina Kiran tane kuma taga ya daina zuwa, Amma shine baki damu ba? Cewar Ammi a wannan lokacin murmushi kawai nafeesat tai kuma tun daga ranar Ammi Bata Kara tada mata maganar ba, 



Kwance take akan doguwar kujera idanunta a rintse Ammi Dake kan one sitter ta jiyo ta kalle ta tana fadin nafi ba dai wannan dan iskan baccin da kika koyo kika fara ba, mikewa tai tana Dan murmushi take fadin wallahi Kam Ammi Kinga har ya fara fizgata nima kaina YANZU abin damh na yake tunda Kinga fa YANZU ko a school haka nake yi idan aka fara lecture Dani saboda bacci kamr wadda tse-tse fly ta ciza, dariya Ammi tai tana fadin ai ke dince tse-tse fly din, may be shawarar ce ko kuma ki je asibiti kiyi wa likita bayani, 



Mikewa tai tana fadin okay Ammi bari na taso deejah sai ta raka ni muje gun doctor Tahir, oh ni kam wannan kawance na ku ke da yar uwar ki Yana bani mamaki duk sakanni suna rigima Amma Banda ku, Allah ya dawwamar muku har Aljanna , Ameen Ammi nafeesat ta fada tana yin hanyar dakin su da Ido Ammi ta bita tana mamakin ganin yadda fatar ta ta Kara kyau ga sheki da haske ta take sai kiba da ta Kara kamr sabuwar amarya, 


  Ammi na Nan zaune suka fito da shirin su sukai mata sallama tana sanar dasu su saka driver ya Kai su kar su ce za suyi driving tunda yamma ce, 


 Har Khadija ta fita nafeesat ma na shirin fita Ammi da kira su da karfi, da sauri suka dawo suna fadin Ammi lafiya? Sosai ta kurawa nafeesat idanu kafin cikin wata murya da Kai tsaye ba zaka ce tame ce ba ta furta yaushe rabon ki da period ? 


  A tare gaban su ya Fadi har suna dafe kirjin kafin su shiga kallon kallo tsakanin su, tambayar ki nake kinyi shiru nace yaushe rabon ki da period ? Wasu zafafan hawaye ne suka fara sintiri a kumatun ta don lokaci Daya zuciyarta ta sanar mata cewar abinda suke biyewa ba mai yiwuwa bane Domin dan duma ya bayyana, 


Next page .......***


*Shin kun fara karanta ƙayataccen labarin nan na _Kuka kurciya?_ wallafar Umaima Ado Gaya?, if not! Ku hanzatrta following channel ɗin ta don samun update.*