29
by @oumfatima33
✨✨✨✨✨✨✨✨
_*ALLON ƘADDARA*_
_*By*_
*_OUM FATIMA_*
_*(Hakimar D. A. W. A)*_
✨✨✨✨✨✨✨✨
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S📚ASSOCIATION*_
_*TEAM*_
_*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*_
*PAGE 29*
_*بسم الله الر حمن الر حيم*_
**** Lokacin da ya isa sosai jikin ya rikice don sai suma take Mahaifiyarta sai rusa kuka take, cikin sauri ya nufi ɗakin da aka kaita ake ƙoƙarin ganin an ceto rayuwarta ko wurin su Hajiya Mama dake kuka bai tsaya ba ya shige cikin sauri. Sosai hankalinsa ya tashi ganin yanda take fizgo numfashi da ƙyar, cikin sauri ya shiga ƙoƙarin haɗa allurar da zai yi mata, sai dai yana kama hannunta zai tsira allurar jikinta ya ƙarasa sakewa gaba ɗaya Allah ya ƙarɓi abinsa.
Ba yau ya fara ganin mutuwa ba sabo da shi likita ne da yake aiki a ɓangarori da dama, ya saba ganin mutuwa kala-kala amma a wannan karon da Matarsa ta mutu a hannunsa sai yake ganin kamar ba gaske ba. Suɓucewa allurar hannunsa tayi ta faɗi ƙasa shima faɗuwar ya kusa yi sabo da juwar da ta kwashesa sai da Doctor Irfan da suke aikin tare ya tare sa ya sa masa kujera ya zauna yana faɗin "I'm sorry doctor Allah ya ƙarɓi shahadarta". Kasa magana yayi ya kuma kasa kuka sai idonsa da ya kaɗa yayi jawur.
Zane Nurse ɗin dake taimaka masu ta jawo ta rufe fuskar Kalisat da tayi wani irin haske fayau da ita kamar ka kira sunanta ta amsa. Ya daɗe a zaune yana sauke ajiyar zuciya kafin ya miƙe ya fice jikinsa a sanyaye, yana fitowa su Hajiya suka nufo shi suna tambayarsa "Yaya jikin nata?" Hajiya Mama ta faɗa tana riƙe hannunsa.
Ganin yayi shiru ya ya ƙi cewa komai ga idanunsa sun yi jawur yasa Hajiya Asabe fashewa da kuka tana banka ƙofar da ya fito ta faɗa ciki. Da gudu ta ƙara sa tana yaye rufar da akayi ma Kalisat da zane ta rumgumeta ta fashe da kuka tana surutai "Yanzu sai da kika tafi kika barmu Kalisat? Ashe dama da gaske kike da kika ce mutuwa zaki yi!". Da ƙyar aka kamata aka fito waje ana bata haƙuri.
*** Cikin ƙan-ƙanen lokaci labarin rasuwar Kalisat ta zagaye dangi, an ɗauke ta zuwa Gidan Mijinta inda za'a suturceta a kaita Gidanta na gaskiya ƙarshen ko wane mai rai (Allah yasa mu cika da imani). Faɗar irin halin da ahalinta suke ciki ma ba zai misaltu ba sabo da mutuwar ta gir-giza zukata da yawa musamman ma makusantanta, baka jin komai sai yabon kyawawan halayenta da kirkinta da son mutane.
Hamma Jabeer ya shiga matsananciyar damuwa da baza ta misaltu ba, domin kuwa yayi rashin Mata ta gari mai ƙaunarsa da duka zuciyarta, mai haƙuri da shi a ko wane yanayi. Gaba ɗaya ya zama wani shiru tun da aka ɗaukota har aka gama shiryata bai buɗe baki yayi magana ba sai da aka kirashi don yayi bankwana da ita sannan ya buɗe baki ya shiga zuba mata addu'oin neman gafara da rahamar Ubanguji, sai da ya kammala sannan hawaye masu zafi suka zubo masa yasa hannu ya ɗauke su, tun da aka yi rasuwar bai samu ya zubar da su ba sai yanzu.
Duk abinnan dake faruwa ina can ɗakin Ammy ina bacci don tunda na tashi nayi sallah zazzaɓi ya rufe ni don haka naje ɗakin Ammy na faɗa mata ta bani magani nasha na kwanta saman gadonta barcin wahala ya ɗauke ni. Lokacin da aka sanar da rasuwar ina kwance ne shi yasa Ammy bata tashe ni ba sabo da tasan nima ba cikakkiyar lafiya gare ni ba, shaƙuwar dake tsakanina da Aunty Kalisat ne yasa take shakkun sanar dani rasuwarta don Allah kaɗai ya san irin halin da zan shiga.
Ban farka ba har sai da aka gama mata sutura aka kai ta Gidanta na gaskiya kafin Ammy ta dawo don ganin ko na tashi. Lokacin da Ammy tazo tashi na kenan jikina a mace sabo da wani mummunan mafarkin da nayi. "Sannu Hanan, kin tashi, yaya jikin naki?" Ammy ta faɗa fuskarta ɗauke da damuwa tana zama kusa dani.
"Eh Ammy na tashi Alhamdulillah amma Ammy wani mummunan mafarki nayi!" Na faɗa a sanyaye. Ganin tayi shiru ta ƙi cewa komai yasa na tambayeta "Ammy wani abu ya faru ne? Naga damuwa a fuskarki!" Na faɗa cikin karyewar zuciya. "Allah ya yi wa Kalisat rasuwa Hanan har an yi mata sutura an kaita!" Ammy ta faɗa cikin sanyi tana riƙe hannuna.
Shiru nayi na ƙame kamar ko yaushe idan aka faɗa min maganar da ta gir-giza zuciyata abin da ke faruwa da ni kenan idan ba'a ci Sa'a ba daga haka sai numfashi ya fara ƙoƙarin gagara a gare ni wani lokacin har ya ɗauke gaba ɗaya in sume. A wannan lokacin Ammy tayi iya ƙoƙarin ganin ta maidoni cikin hayyacina ta hanyar shaƙa min inhaled ɗina aka samu numfashina ya dai-daita kafin ta shiga yi min nasiha mai ratsa jiki da zuciya, ta tunatar dani cewa Allah da ya halicce ta ya fimu sonta shi ya karɓe abinsa, soyayyar da zan nuna mata a yanzu shine yi mata addu'a da kyautatawa abin da ta bari.
Sosai magan-ganun Ammy suka sama min natsuwa amma duk da haka nayi kuka sosai wanda fuskata kaɗai zaka kalla ka shaida hakan domin Kuwa Aunty Kalisat a gareni tamkar ƴar'uwar da muka fito ciki ɗaya da ita na ɗauke ta sabo da ƙauna da soyayyar da ta nuna min. Wanka na shiga nayi na fito ɗaure da alwala nazo nayi Sallar azahar da lokancinta yayi kafin na shirya cikin doguwar rigar wani tattausan material marar nauyi ko kadan na saka dogon hijabi normal ɗinki mai hannu roba na fito na samu Ammy ta haɗa min abinci tana jiran fitowa ta, duk yanda taso inci ko kaɗan ne kasawa nayi sai peak yoghourt da ta sani dole nasha kaɗan muka wuce gidan gaisuwa. A ƙofar Gida muka samu duka Mazan Gidanmu da ƴan'uwan Aunty Kalisat suna karɓar gaisuwa, a kusa da Baba Malam na hango Hamma Jabeer a zaune yayi shiru da alama yayi nisa cikin tunani.
Kamar wanda aka bawa umarnin ɗagowa idanunsa basu sauka ko ina ba sai tsakiyar nawa idanun, gaba ɗaya naji raunina ya dawo tsananin tausayinsa da na Little na kamani, ji nayi kawai ina son fashewa da kuka don haka na kwaɓe fuska zan saka kuka na ma manta cewar a waje muke don mun tsaya muna gaishe da mutanen wurin. Yana ganin haka ya san mai take shirin yi don haka ya lumshe mata idanunsa ya buɗe su a tsakiyar nata yayi mata alamun 'kar kiyi kuka shiga ciki'. Hannuna Ammy ta ja bayan ta gama gaisawa da ƴan'uwan Aunty Kalisat muka shiga ciki.
Bedroom ɗin Aunty Kalisat muka samu Hajiya Asabe (Mamanta) don muyi mata gaisuwa, samu mukayi tana ta kuka Momy (Habiba)na rarrashinta. Gaishesu nayi gaba ɗaya tare da yi musu gaisuwa mai makon su amsa sai binmu da wani ƙasƙantaccen kallo suka yi kafin Momy ta fara fadin "To masu baƙar aniya da in kuka raɓi mutum sai kun ga bayanshi, wannan ma ta tafi sai kuma abi wani sarkin azzalumai dangin jaraba da masifa!". Ta karasa tana mana wani wulaƙantaccen kallo.
Wannan karin kasa jurewa nayi na buɗe baki zanyi magana jikina har rawa yake tsabar ɓacin rai, Ammy ce tasa hannu ta rufe min baki tace "kul! Kar ki fara abinda baki taɓa yi ba, ki barta taci gaba da cin darajar masu daraja!" Ammy ta faɗa cikin zafin zuciya ta ja hannuna muka fice.
Habibah tana ƙoƙarin kaita bango da hakan zai sa ta juyo kanta, tun farko ba tsoro yasa take ƙyaleta ba face kawaici da kara ko don amincin dake tsakanin Iyayensu da har suka rasu Mahaifinsu na ƙara jaddada musu cewar Malam Umaru Uba ne a gare su ko bayan rashi. Sai kuma darajar Nabeel da ya so ƴar'ta tsakani da Allah ya girmamata a matsayin uwa, amma Habibah taƙi ta ganewa duk kuwa randa ta fara maida mata martani abin ba zai yi kyau ba.
Ni kuwa muna fitowa na fashe da kuka nace wa Ammy zan koma Gida, bata hana ni ba don itama gaɓa ɗaya zaman wurin ya fice mata a kai sai dai dole ta haƙura sabo da ba zaiyu ba ta koma ɗin. Fita nayi na nufi in da nayi parking ɗin Motata na buɗe na shiga na jata nayi gida ina share hawaye, masifar Matarnan ta ishe ni haka na rasa yaushe zata gane gaskiya ta aje komai.
Tun da ta fito akan idonsa, yana kallon fuskarta ya san da matsala da abin da aka yi mata kuma.ya san ba zai wuce surukarsa da aminiyarta ba, ya rasa yaushe zasu daina abu irin na yara. Idonsa kawai ya lumshe yana fatan Allah yasa ta kula da hanya kar tayi wannan gudun....
Manage please ba yawa.